MUHASEEN

Chapter 2

by @maryamstar248

Zuwa lokacin da ya gama wannan tulin wanke-wanke ya samu sauƙin nauyinda zucoyarshi ta yi kaso sittin cikin ɗari, sai da ya kammala sannan ya nufi wajenda ake zuba abinci, ya amsi na shi tare da ruwan leda, sai ya samawa kanshi mutsuguni ya soma cin abinci badan yana masa daɗi ba, sai dan yunwar da ta soma saƙalar ƴan hanjinsa, bayan ya gama yayi signing tare da yin sallama da su yabar wajen, sai kuma da dare idan wani aikin ya taru.

Bayan ya firo again sai ya ƙara nausar hanya yacigaba da tafiya, bai ko saurari ƙafaguwansa da ke shaida ma sa irin gajiyar da ke tattare da su ba, bai tsaya ako ina ba sai wani waje da ake wankin motoci da mashina, canma nannaɗe ƙafar wando yayi ya soma aiki ba ji ba gani, bayan ya gaggaisa da mutanen wajen, yana jin maganganun da wasu daga cikin yaran me wajen ke faɗi a kanshi amma sam bai damu ba yaci gaba da aikinshi.

"Dan Allah Abdul jibi jikinsa du datti, kalli ƙafafuwansa yanda suka tsatstsage gwanin ƙyanƙayamin, baya wanka bare wanki, sauya maka kuwa ba'a magana, gadai mutum har mutum malam amma ƙazanta ta gama lalatashi."

Caraf wanda aka kira da Abdul ya cafe zancen tare da faɗin.

"Yo kai Mustapha in banda abinka dama wannan ai ba'a sakashi a lissafi, nasha bawa oga shawarar a sauya shi karya korar mana costomers amma ya ƙi, wai yanada amfani barinshi a wajen, yo Allah na tuba taya barin ƙazamin kamar wannan a wuri zai yi amfani."

Haka sukaita maganganu marasa daɗi akan Suhail sai de bai ko ɗaga kai ya kallesu ba, hasalima aikinshi ya cigaba da yi babu ha'inci, ko a zuci maganganunsu basu wani ɗaɗashi da ƙasa ba, dan a irin waɗanda yake ji a rana suna ninka nasu muni, kuma baya bari suyi tasiri a zuciyarshi yana ƙoƙarin sanar da kanshi cewar shi ba kamar sauran mutane bane, sam bayada ƙawazuci yana nanatawa kanshi hakan aduk sanda wani abu yaso kutsowa cikin tunaninsa.

Wunin ranar haka ya ƙarar da shi da yawon aikace-aikace sai kace inji, ko inji yana tsayawa ya huta, bashi ya koma gida ba sai bayan da ya koma restaurant ya sake yin wani wanke-wanken, nan aka haɗa jimilar kuɗinsa tubu goma cis aka bashi, a hanya ya tsaya ya sayi lemo mw sanyi, yana tafiya yana shan roba ɗaya har ya shanye tas, yana jin sanyi na ratsa zuciyarsa, daga nan ya tsaya wajen mw tsire ya siyi ɗauri uku, ya koma shago ya siyi detergent da sabulun wanka, sannan ya durfafi gida agalabaici, hatta da kwayar idonsa bata ɓoye yanayin gajiyarda gangar jikinsa yayiba.

Kamar yanda ya tsammata, a lokacinda ya shiga gidan da sallama a bakinsa babu wanda ya amsha shi, ba kuma dan basa jinsa ba, hasalima duk sun ɗaga ido sun kalleshe, leda ya jefa a ɗakinsa sannan ya ƙarasa shiga a sanyaye yana kallon magidancin da ke sake haɗe fuska bayan ya ganshi, sannan ya kawar da jai gefe yana zungura baki.

"Abba da Umma barkanku da gida."

Idan sun tankashi ƙasar wajen ta tanak haka suka ɗauke kawunansu, sai Binta data kai hannu tana janyo ledojin gabansa tana bubbuɗawa tare da tame baki, tun kafin tace komi ya zaro kuɗi daga aljihunsa tare da miƙa ma ta yana fatan jin kalma ɗaya tak daga bakinta, yana so koda sau ɗayane a rana ta dinga binshi da albarka kamar yanda takewa sauran ɗiyanta, sai de shi kanshi yasan hakan ba abu ne me yiyuwaba, akan jima baiji kalmar daga bakinta ba da sunan shi ta sakawa albarka.

Ganin bata shi suke ba ya saka ya miƙe a sanyaye, sai ji yayi ɗaya daga cikin ƴan matan na faɗin.

"Am Suhail nace ba."

Juyawa tayi tare da jafeta da rikitattun idanuwansa yana kallonta, sai ta sunkui da kai saboda kwarjinin da idanuwansa masu kaifi suka yi ma ta, da wahalalliyar murya ya ce.

"Fatima ya aka yi ne?."

Tana sunne kai ta ce.

"Dama ina so ka bani kuɗi zan siyo kayan kwalliya nawa du sun tsufa wasuma sun ƙare?."

Sai da ya girgiza kai sannan ya ce da ita.

"Babu kuɗi a hannuna ki amsa a wajen Umma."

Zai juya kenan ya tsinkayi muryar Ummar na faɗin.

"Haba dan Allah, kayan kwalliyar duka nawa suke da zaka ce ta amsa a wajena, idai waɗannan kuɗaɗenne kake yiwa to wallahi sisi bazan cire ba, waye yake morar kuɗin bayan ku, du a wajen abinci da sutura sukw ƙarewa ai."

Baice komi ba ya zari dubu ɗaya ya bawa Fatimar yana fatan maganar ta tsaya iyakar nan.

"Bilkisu ɗaukowa Suhail nashi abincin."

Binta ta faɗa tana ƙidayar kuɗaɗen, tana jefa tsokar nama a baki, shiko Abba ba'a magana ya tasa nama a gaba ga lemo me sanyi yana korawa baice uffanba.

Wa ta sanƙararriyar shinkafa ce Bilki ta dire kwanonda da bakinsa yai baƙi ƙirin, saman shinkafar a bushe da alamun a buɗe ta wuni, kamar zai ce a'a sai kuma ya ɗauka gami da yin godiya ya juya ya wuce.

Bayan ya shiga ɗakinsa ya tura ƙofar, tare da kunna fitilar ƙaramar wayarsa data gama cin duniya, madannan jikinta du sun goge.

Kayan jikinshi ya shiga cirewa yanajin yanda suke tashin warin rana da ƙura, ƙaƙƙarfan numfashi ya saki yana jin wani sanyi na ratsa shi sanadiyar fitar da kayan da yayi, kai tsaye ya fita waje tare da ɗauka botiki ya saka kayan, ya zauna ya wanke su tas sannan ya shiga wanka, duda baya son wanka da ruwan sanyi amma bashida yanda zai yi hakanan yake yi dana sanyin, yanda ruwan ke sauka a jikinshi haka yake jin gakiya na baibayeshi, idonshi har lumshewa yake sanda ya fito daga wankan, best da boxer kawai ya iya sakawa addu'ar barcima rabi da rabi yayi, nannauyan barci ya ɗaukeshi, a can sama-sama ya dinga jiyo muryar Binta kamar tana faɗa, sai de baya iya gane abin da take faɗa, kuma yanajin kamar mutum a kanshi amma bai iya buɗe idoba saboda nauyin barci, a cikin barcinne kawai ya ke damun sauƙi, ananne yake samu isashen hutu, shiyasa baya kai dare sosai ba tare da dawo gida ba.

ASOKORO

MABATA MAIN HOUSE.

"Tasss, tasssss" kake jin ƙarar lafiyayun tagwayen maruka na sauka a lausasan kuncin wa ta budurwa.

Tsit duniyarta ta tsaya gaba ɗaya, azaba da raɗaɗin zuci dana mari suka haɗe ma ta a waje ɗaya, soma ja da baya-baya ta yi tana girgiza kanta da taji kamar baya jikinta, kafin cikin sarƙewar murya ta soma faɗin.

"Ni Papah, ni, niii! marina fa ka yi, akan wannan abar."

Ta faɗa tana yin nuni da wa ta lukutar yarinya da ke tsaye a wajen hannunta riƙe da taddy tana zunɓura ƙaramin bakinta.

A hasale wanda aka kira da Papah ya ce.

"Na mareki, nace na mareki ɗin Jauhar, bama iya mari ba, zan iya yi miki abin da yafi mari matuƙar kika sake ɗaga ƙazamin hannunki akan ƴata, ita ɗin ƴata ce, banida kamarta, zan wulaƙanta du wanda ya taɓa min ita ko waye shi, na faɗa na ƙara faɗa bakida wani amfani a rayuwata, bakida amfani a cikin zuriyata ni LAMINU GABATA.

Cak komi ya tsaya ma wacce aka kira da gabata, ɗif ta ji zafin marin ya ɗauke, yayinda zafin kalaman wanda ya ke amsa sunan Uba a gareta ya shiga ƙone zuciyarta, nan take zafafan hawaye suka shiga silala daga cikin rinannun idanuwanta, sai kawai ta ɗaga kanta ta kalli innuwar mutum da ke tsaye a jikin bene, a saman busasun laɓɓanta da ƙaramun sauti ta furta.

"Jiya da yau kinci nasara a kaina, ki jira zuwan gobe."

Sannan ta fice a guje kuka me ƙarfi na kubce ma ta, kai tsaye wajen ajiyar motocin gidan ta nufa tana gujin kuka, jikin wa ta farar ƙal ɗin MBW ta nufa ta tsaya, ganin hakan ya saka me kula da motoci bata key yana tambayarta a kira driver, amma sam bata amsa shi ba ta wani fizgi key ɗin tare da buɗe motar ta shiga, ta jata da mugun gudu.

Tana tuƙi tana kuka sosai, tana kukan kasancewarta a wannan rayuwar me cike da ƙunci, sai da tai nisa sosai sanna taci burki a wani ƙaton fili ta fito daga motar tare da durƙusawa ta ɗibi ƙasar wajen da hannunta, da mugun ƙarfi ta furta kalmar.

"MUHASEEEEEEEEEEEEEEEEEEN." Sai da wajen ya amsa da ƙarfin amon sautinta, kafin ƙaƙƙarfarn kuka wanda yafi na baya ya sake kubce ma ta, kuka ta ke kashirɓan kamar me son zare zanta, nan take farar motarta tai jazur idanuwanta suka rini, yayinta jikinta ya shiga jijjigawa tsabar yanda ta ke kukan daga ƙasan ranta.

LEGOS NIGERIA

BANANA ISLAND.

Duniyar mafarki.

*Sai yaushe zaka zo gare ni, ka wadatani da abin da Ummana ke buri a rayuwa, ka sauya rayuwata ta koma kamar ta kowa, na gaji sosai da wannan wahalar da nike yi, ina so in huta koda na ƙanƙanin lokacine.*

Hasken da ke zagaye da shi ya ke faɗa ma shi cikin murya me cike da sanyi gami da gajiyawa, kafin ya samu zarafin yin wa ta magana ya jiyo muryarta ta kwalla masa kira da ƙarfi, a hankali hasken ya shiga disashewa, yayinda sautin muryarta da ke ambayar sunanshi cikin neman agaji ya karaɗe wajen.

Wani irin juyi ya yi a ƙoƙarinsa na gano inda sautin ya ke, sai de kuma ba tare da saninshi ba a zahiri yayi juyi, kuma yakai ƙarshen makeken royal bed ɗin da yake kwance akai, bai ankare ba sai jinsa yayi a ƙasa timmmm, ya faɗo, lamarin da ya sakashi wartsakewa daga baccin.

Yamutse kyakkyawar farar fuskarshi da saman hancinsa yai jazur yayi, yana jin raɗaɗi na ratsa ƙeyarshi datasha ƙasa, ga wani nauyi da kanshi yayi, wanda sam bai da alaƙa da faɗuwa, yakai tsayin mintuna biyar yana ƙoƙarin tashi, kafin daga bisani ya dafa gadon ya miƙe tsaye, jiri na kwasarsa, ga bacci sosai da yake ji, sai de kuma yasan barcinshi ya rigada ya ƙare, dama dakyar ya samu barcin ya ɗaukeshi bayan ya lodawa kansa magunguna masu ƙarfi, a gaban ƙofar bathroom ya tsaya dare da danna wasu madannai sannan ƙofar ta buɗe tana faɗin.

"Barka Muhaseen, na'ura ta tantanceka, zaka iya shiga kayi abin da kake so."

Tallabe kanshi ya yi jin sautin na'urar na ƙara saka mashi ciwo da nauyin kai.

HAƘƘIN MALLAKA DA RUBUTU

MARYAM STAR ⭐⭐✍🏻

Follow this link to join my WhatsApp group: ***

🌹𝙈𝙐𝙃𝘼𝙎𝙀𝙀𝙉🌹

(𝐿𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑧𝑢𝑐𝑖𝑦𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑘𝑢𝑛𝑐𝑖, 𝑟𝑎𝑦𝑢𝑤𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑘𝑎𝑙𝑢𝑏𝑎𝑙𝑒😔.)

𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀 𝘽𝙔

𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐.

💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍,𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪

🤝𝙏𝙃𝙀 𝙎𝙃𝙄𝘿𝙊𝙍𝙄𝘼 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝙏𝙀𝘼𝙈✊

𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙆

𝙎𝙀𝘼𝙎𝙊𝙉 𝙊𝙉𝙀