MUHASEEN

Chapter 6

by @maryamstar248

"Alhaji Manga matsalar ita ce kasa bawa ƙungiya da Me girma dodo abin da suke muradi, yanzu lokaci ne da zaka manta da kowa da komi, ka fuskaci rayuwa dole ka aje komi a gefe kazo muyi yaƙin nemo muradin ƙungiya, da ace tun farko mun yi abin da ake so, da Me girma Shugaba ba zai yi fushi da mu, ka aje komi mu fuskanci matsalar da ke gabanmu, idan ba haka ba ka sa ni cikin biyu dole ayi ɗaya, rayuwa ko mutuwa."

Gaba ɗaya Alhaji Manga ya gama ruɗewa, tashin hankali ɓaro-ɓaro akan fuskarshi sai faman zare idanu ya ke yana shege lahira, yawu ya haɗiya da ƙarfi sannan ya ce.

"To yanzu ta ina zamu fara?."

"Suhail, shine yaron da na samo kuma shi yafi kwanta min a rai, yanayin da ƙirarsa sun dabbatar min da idan har muka mallaki zuciyarsa zamu samu cikar burinmu."

Alhaji Manga na sauke numfarfashi sannan ya ce.

"Kafin komi ya kamata a fara mallake zuciyarsa, a darenan ya kamata a sadaukar da zuciyarsa ina so ya dawwama wajen yin biyaya ga umarninmu."

LEGOS NIGERIA

Second na juyawa zuwa minyuna mintuna na juyawa zuwa awwani, sai da Muhaseen ya samu awwani biyar lafiyayu a halin mutuwa, yana gab da cika awa ta shidda Allah ya tashi Saleem daga barci me kama da mutuwa da yayi, sannu a hankali ya soma buɗe idanuwansa, ganin inda ya ke ya sakashi zabura ya tashi da ɗan sauri, sai de kuma bed ɗin wayam, a daidai saitin da tsadaddiyar ogogon bango ta ke ya kalla, bai san lokacin da ya hantsila da sauri zuwa ƙasa ba, ya miƙe akan diga-diganshi ya soma takawa da sassarfa, idonshi a rufe ya faɗa ɗayan toilet ɗin da ke a ɗakin wanda yasan Muhaseen bai fiye shiga ba, sai da ya fara yin wanka dan yaji ƙarfi a jikinshi sannan ya ɗauro alwala yana istigifari, a lokacin da ya fito ne ya samu gawar Muhaseen sandare a ƙasa, ga jini na fita ta hanci da baki.

Abin da ya samu Saleem a lokacin ba iya tsoro da firgici bane, za'a iya kiran yanayin da yanayin mutuwa cikin biyu dole ayi ɗaya, kodai shima ya rayu ko kuma ya mutu a wajen.

Bai tsaya daga ambaton Allah ba har ya isa jikon gawar, jikinshi na tsuma jininshi na tafarfasa akamar ruwa akan wuta, ɗigar ruwan alwalar jikinshi ne ya tsaida komi, ya tsaida mutuwar da ke kusa da wajen ya kuma tabbatar da rayuwar da ake son ɗauka ta ƙarfin tsiya.

Bayan saukar hannunshi akan Fuskar Muhaseen da tai fayau, alamun rashin rai ɓaro-ɓaro a yanayinsa, sai kawai ya shiga ambatar sunan Allah da ƙarfi tare da ja da baya tsoro na lulluɓe shi.

A lokaci ɗaya numfashinsa ya dawo, da iya ƙarfin da Allah ya hore masa ya damƙe tafukan hannayensa tare da ƙoƙarin sarrafa kanshi, da ƙarfin ikon Allah sai gashi ya buɗe idanuwansa da cikinsu ya koma jazur kamar garwashin wuta, kai tsaye ya watsasu akan Saleen har zuciyarsa yana so yayi magana, amma harshensa yayi nauyi hasalima ji ya ke kamar an ɗaɗɗaure shi da sarƙa.

Ɗagowar da Saleem zai yi sai idonshi ya sauka cikinna Muhaseen, ƙaunace wanzajiya daga Ubangiji ƙaryar mutum ko aljan ya shiga tsakanin zuciyoyinda Allah ya yarda da suyi tarayya me cike da tsafta, sam Saleem bai tsorata ba, duda ya kamata ya ji tsoron musamman da idanuwan Muhaseen suka juye zuwa launi me ban tsoro.

"Ka yaƙesu, ka yaƙesu Muhaseen ta hanyar ambaton Ubangiji har yanzu da sauran lokaci karka bari suyi galaba akanka, ni da kai muna da buƙatar ka rayu, ka rayu kamar ya da Allah ya baka iko, ba yanzu ne lokacin mutuwarka ba tabbas zaka mutu amma ba yanzu ba kuma ba'a hannunsu ba, Ubangiji ne kawai keda kamar ɗaukar ranka a sanda ya so, ya kamata ka tashi ka tashi tun kafin al'amurra su sauya."

Yunƙuri ne yayi da zuciyarsa, ya sarrafa gangar jikinsa da sukayi nasarar kassarata, ya tashi da taimakon Allah daya halicceshi da zuciya me juriya, ko bayan daya tashi zaunen yana jin azaba na ratsa du wa ta jijiya da jini ke gudana a cikinta, sannu a hankali ya soma buɗe tafin hannunsa ya damƙi hannun Saleem yanajin ya samu bangon da zai jingina.

Rintse ido da ƙarfi Saleem ya yi jin tafin hannun Muhaseen kamar wuta saboda zafi, yanajin yanda zufar azabar riƙo da kuma ƙunar da hannunsa ke yi kamar fulawa a cikin mai, amma sai ya daure tare da dafa kan Muhaseen ya shiga karanto ma shi addu'o'in tsari zuciyarashi fal tausayin halin da Muhaseen ɗin ya tsinci kanshi.

Sunfi awa ɗaya a wajen Saleem ya tufa ma shi addu'a cike da tausayawa, shi kuma Muhaseen yana jin kamar ana warwareshi daga ɗaurin sarƙa a hankali jikinshi ya soma motsawa tafarfasar da jininshi ke yi ta soma raguwa, kanshi yai nauyi gami da soma sarawa kamar ana doka ma shi guduma, hakan alamace da ke alamta ma shi cewar tabbas ya tsira, ya tsira da rayuwarshi ikon ransafa kanshi ya dawo gareshi zuciyarshi ta daidaita.

"Saleem."

Ya furta sautin acan ƙasa sosai, yana jin ƙauna ta musamman na sake shigarshi game da Saleem ɗin, wanda ya sadaukar da rayuwarshi wajen inganta tashi rayuwar, ya tsayu tsayin daka wajen magance du wasu matsaloli da zasu taso a rayuwar Muhaseen, ko a fuska bai taɓa nuna gazawaba sai ma kwarin gwuiwa da yake sake samu a kullum.

"Na,am ɗan uwa kuma abokina Muhaseen, mi kake so daga gare ni."

Ya yi maganar kwallar farin cikin tashinshi na cicciko idanuwansa.

"Ina son ka Saleem."

Muhasee ya faɗa da dukkan zuciyarshi, sai kawai Saleem ɗin ya fashe da kuka tare da rungumar Muhaseen ɗin, yana jin tsananin ƙauna da tausayinsa nasake baibaye rayuwarsa.

Sun ɗan jima ƙanƙame da juna kafin Saleem ya ce.

"Sarki yaufa mun makara a salla, muje in taimaka maka ka gyara jikinka sai muyi sallah.

Da taimakon Saleem Muhaseen ya soma taka ƙafafuwanshi da yake jinsu kamar ba nashi ba, bayan sun gida bathroom Saleem ya taimaka ma shi ya haɗa ma shi ruwan wanka, da kai yayi alamin godiya sannan ya sallami Saleem ɗin.

Kayan shara Saleem ya ɗauka ya shiga gyara wajen, yana mamakin yawan jinin da Muhaseen ya zubda ga kuma wasu abubuwa kamar tsutsotai da yake gani suna yawo a cikin jini, da hanzari ya gyara wajen kamar babu abin da ya faru, a gaggaice ya yo wanka ya sauya kaya sannan ya ɗauro alwala ya tayarda sallah cike da jin kunyar Ubangiji, ganin irin makarar da suka yi.

Babu abin da ruwan wankan ke ƙarawa Muhaseen illa azaba, ga jikinshi dake sake ɗaukar zafi shiyasa bai jima ba bayan ya tabbatar da ya wanke najasar jikinshi da kyau ya fito yayi alwala a nitse, a daddafe ya fito daga bathroom ɗin sanye da rigae wanka, sai da ya ɗan zauna ya huta kaɗan sannan yaci gaba da shiryawa, sallarma gagararsa yi tayi daga tsaye sai de ya zauna ya gabatar da ita a nitse, bayan daya gama ya jima yana tazbihi da azkar, duda yanda jikinshi ya ɗauki zafi sosai. lokacin da ya gama har Saleem ya haɗa mashi tea me zafi, har da pain relive ya aje ma shi, da kyar ya iya yiwa tea ɗin kurɓa ɗaya ya haɗiye sai ya dire cup ɗin yana jin yanda zafin jikinshi ke daɗuwa.

"Fresh Milk tea, bazan iya cin abu me zafi ba please."

Da hanzari Saleem ya kwashe kayan wajen sannan ya bada umarnin a haɗo ice tea, cikin ƙanƙanin lokaci ƴan aiki suka sanar da shi sun gama, da kanshi ya je ya karɓo ya kawowa Muhaseen wanda ya lumshe ido yana saurara yanda zafin jikinshe ke ƙaruwa, tun da ya ɗaga cup ɗin bai dire ba sai da ya shanye tas, Saleem ya amsa cike da tausayawa ya ke jeranta ma shi sannu akai a kai, sai de baiyi minti biyu da sha ba wani rin ƙaƙƙarfan amai ya taso ma shi, miƙewa yayi a hanzarce dan nufar wajen sink amma tuni ya kubce ma shi, nan ya dinga aman jini guda-guda ya hanci da baki abin kwanin tausayi, Saleem ne ya taimaka ma shi tsigar jikinshi na tashi ganin yanda jini ke gudu a ƙasa kamar ruwa, sosai Muhaseen galabaita sai da takai ko miƙewa tsaye baya iya yi, Saleem ne ya taimaka ma shi ya kaishi wa ta ɓoyayyar kofa da garden da sweeming pool ke wajen, wajene me ban sha'awa da burgewa ga tsuntsaye kyawawa dake ta shawagi a wajan ga sanyin ruwa yanayin gwanin daɗi, akan kujera me kama da gado ya kwantar da shi, bayan ya taimaka ma shi ya rage kayan jikinshi da suka zafi rau kamar an gogesu da iron.

Babu jimawa Doctor ya ƙaraso, sai de a sirrance Saleem ya kirashi, har wajen yai ma shi iso, a kallo na farko da Doctor yai ma shi sai da ya razana, musamman da yai tozali da idanuwansa da sukai jazur babu launin fari ko ɗigo, da taimakon Saleem aka sagala ma shi ƙarin ruwa da kuma jini, kasancewar Saleem yayi ma shi bayanin komi ta waya kafin ya zo, magunguna ya rubuta tare da bawa Saleem, sosai Saleem yai ma shi godiya sannan ya sallame shi da kuɗi masu kauri.

BAYAN AWA HUƊU

A hankali Muhaseen ya soma buɗe idanuwansa da suka yi masa nauyi, hasken da ya shiga idon nashi ne ya tilasta ma shi sake rufesu, sannan ya sake buɗewa a hankali komi ya soma washewa, baya jin ciwon komi hatta zafin jikinshi duk babu, sai de yanajin jikinshi yayi ma shi nauyi sosai, idonshi bai sauka ako ina ba sai akan Saleem da ke zaune a ƙasa gabanshi barbaje da takardu ga kuma loptop har biyu yana aiki, gaba ɗayanshi a hargitse ya ke aiki kawai ya saka a gaba, wani irin kallo Muhaseen yake bin Saleem ɗin da shi, kallo me cike da ƙauna wacce haɗuwar jini ta asassa, a hankali ya yunƙura tare da tashi zaune, ya fizge ƙarin ruwan da kuma jinin, ya zura tausasan takalman da aka aje a ƙasan wajen, sai da yai dagaske sannan ya iya tashi tsaye, baice komi ba ya juya ya soma tafiya sannu a hankali ya buɗe ƙofar ya fice, direct toilet ya shiga yayi wanka sannan ya ɗauro alwala ya gabatar da sallah azahar ya zauna yana tazbihi, a rikice Saleem ya buɗe ƙofar ɗakin da yake ganinshi a zaune ya saka shi sakin nannauyar ajiyar zuciya gami da dafe goshinsa, idasa shigowa ya yi jikinshi a mace da tsantsar kulawa a muryarsa ya ce.

"Sarki ka bani tsoro wallahi, na duba banganka ba alhalin nasan kana kwance, taya har ka tashi ban saniba?."

Ya yi tambayar duda yasan cewar ba amsa shi zai yi ba, dan magana na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da keyiwa Muhaseen wahala sosai, bai gajiyaba ya kuma faɗin.

"Yanzu ya kake jin jikin naka, ko a sake kiran Doctor ya zo ya sake dubaka?."

Lumshe idanu kawai ya yi, yanajin yanda maganar Saleem ke ƙara mashi nauyi a kah.

Saleem dayasan ba amsa zai samu ba sai kawai ya haƙura yacigaba da zama yana yiwa Muhaseen kallo me cike da tausayi, sun kwashi tsayin mintuna a wajen, kafin Saleem ya tashi ya wuce.

Muhaseen duda baya jin ƙarfin jikinshi haka ya hau shiri cikin suit kalar kofi masu duhuwa, sosai kayan suka amshi jikinshi suka zauna ɗas gwanin burgewa, ramar da yayi ta sake fito da zallar kwayun shi, wayoyinsa ya ɗauka tare da danna kiran number Saleem yana fitowa, a main falo suka ci karo da juna shi da Saleem ɗin dake ƙoƙarin zuwa ganin kiran Muhaseen ɗin, wani kallo me cike da tuhuma da zallar Mamaki Saleem ɗin ke jifar Muhaseen daya sake tsuke fuska alamar ba warfi.

"Follow me🚶🏻‍♂."

Ya faɗa a gajarce tare da soma turawa drivera message akan su shirya za'a fita yanzu, kafin su fita haraba tuni an jere lafiyayyun motoci su kaɗai ake jira su isa, suna zuwa babu jimawa aka bubbuɗe musu cike da girmamawa, yayinda Muhaseen ya kame a gidan baya shi kuma Saleem yana a gaba kusa da driver kasancewar mota ɗaya suke hawa, kuma idan Muhaseen ɗin na buƙatar wani abu shi yake sabarmawa ta hanyar message.

Yauma a STAR GOLD Company suka fara isa, saɓanin Muhaseen yau Saleem ne ya binciki komi, sosai yasha mamaki ganin yanda al'amurra suka wakana kafin zuwansu, rasa ta inda zai fara yayi, domi daga safiya zuwa lokacin ansamu asarar kaya masu ɗinbun yawa, musamman ɗanyen gold, kuma sunyi missing ɗin babban business a ranar,sai a lokaci ya gane abin da yake saka Muhaseen zagewa wajen saka ido akan komi, wato harkarce dole sai tsayayye kuma jajirtacce me juriya, daga ƙarshe dai dole ya haƙura da wasu abubuwan ya turawa Muhaseen bayanai ta email yasan ida ya sami kanshi zai bibiya kuma yanada tabbacin sai ya gano daga inda matsalar ta ke........

MARYAM STAR⭐⭐⭐WRITER.......✍🏻

Follow the MARYAM UMAR HAUSA NOVELS BOOKS LIBRARY 📚📚 channel on WhatsApp: ***

🌹𝙈𝙐𝙃𝘼𝙎𝙀𝙀𝙉🌹

(𝐿𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑧𝑢𝑐𝑖𝑦𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑘𝑢𝑛𝑐𝑖, 𝑟𝑎𝑦𝑢𝑤𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑘𝑎𝑙𝑢𝑏𝑎𝑙𝑒😔.)

𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀 𝘽𝙔

𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐.

💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍,𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪

🤝𝙏𝙃𝙀 𝙎𝙃𝙄𝘿𝙊𝙍𝙄𝘼 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝙏𝙀𝘼𝙈✊

𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙆

𝙎𝙀𝘼𝙎𝙊𝙉 𝙊𝙉𝙀