Chapter 7&8
Shi zai yi aikin duda kuwa baya jin daɗi, abin da Saleem bai saniba shine ko yayi aikin koya tsaya Muhaseen ba zai iya zama ba tare da yayi aikin ba, ba da jikinshi ya ke aikiba da duka zuciyarshi ya ke zama yin aikin shi yasa du abin da ya saka a gaba ba gudu ba ja da baya sai ya cimma nasara, ƙwazonshi ya ta'allaƙa ne da burukan da ke ƙunshe a zuciyarshi, ba zai gajiya ba har sai wannan burin ya cika.
Wanka ya sake yi ba tare da ya nemi komi ba ya zauna zaman aikin, Saleem shiru ya yi yana kallon ikon Allah yayinda shi gogan ko a jikinsa da yaji idanuwan Saleem ɗin na yawo a jikinshi sai cewa ya yi.
"Malam kallon fa?."
Ba tare da ya tsaya daga abin da ya ke yi ba, sai Saleem ɗin ya saki murmushi daya tuna da wani abu, fuskarshi ɗauke da murmushi ya kalli Muhaseen ɗin sannan ya ce.
"Sarki ka tuna, ka tuna wa ta rana bayan shuɗewar shekaru ranar da muka fara haɗuwa, ka tuna da wannan kalmar?."
Matse siraran lip ɗinshi ya yi sannan ya ce.
"Malam kallon fa?."
Sai Saleem ya saki siririyar dariyar nishaɗin abubuwan da suka faru a lokacin suka shiga dawo masa a kai, yayinda shima gogan yaɗan sake fuska sai de ba murmushi ya yi ba, fuskarshi kadaran kadahan ita ba'a ɗaure ba kuma ita ba'a sake ba, haka suka ci gaba da aikin Saleem na jefo hira jifa-jifa yayin da shi kuma amsarshi bata wuce "Uhmmm." gaba ɗaya hankalinsa nakan aikin da ya ke, su na a haka me wayar Saleem ta yi ƙarar shigowar saƙo yana dubawa sai yaga saƙon daga email ɗinshi na STAR GOLD ne, sai ya shiga dan ganin abin da saƙon ya ƙunsa, mamaki gami da al'ajabi ne ya kama shi lokaci ɗaya, da muryar mamaki ya cewa Muhaseen.
"Sarki wane irin brain ne da kai wallahi kaga jerin list ɗin abubuwan da suka ɓata nan Fawas ya turo kuma wallahi du an gano komi."
Muhaseen bai ɗago da kanshi ba sai cewa da ya yi a miskile.
"Good."
Daga hakan bai sake cewa komi ba yaci gaba da aikin gabanshi.
Saleem kuma kasa daina mamaki ya yi sai da ya kira daga company aka tabbatar masa da an saita komi yanzu angano kayan da suka ɓata sannan ya ci gaba da aikinsa shima.
Muhaseen jin da ya yi kanshi ya soma nauyi ya saka ya ajiye aikin ya kashe loptop ɗin tare da jingina kanshi akan sofa yana jin yanda jijiyoyin jikinshi suka soma amsawa da azabar da yake ji du daren duniya.
"Saleem, tea."
Ya faɗa yana shafa cikinsa, yayinda Saleem ɗin shima ya tashi ya tatare komi sannan ya fice da kanshi ya tsaya aka haɗa komi, inda ya aje maganin shi ya je ya ɗauko, sai de wannan karon bai yi gangancin saka ma shi ba sai ya ɗauko gaba ɗaya ya kawo ma shi, koda ya bashi umarnin ya haɗa maganin sai ya saka guda ɗaya, idan ya nemi ƙari sai ya ƙara mashi.
Sai da suka gama komi Saleem ya tabbatar da babu wani abu da Muhaseen ɗin zai buƙata sannan yai mashi sallama ya nufi nashi ɗakin da ke nesa dana Muhaseen ɗin.
Alwala ya ɗauro ya gabatar da sallar isha'i daga nan ya yi shafa'i da wuturi, ya jima yana tazbihi kafin ya fara jin maganin ya soma aiki a jikinshi sannan ya tashi ya saka kayan barci ya hau kan bed bayan ya kashe hasken zuwa dim light, wani shiru ne ya ziyarceshi a lokacin da ya kai kafaɗunsa ƙasa, yana jin kewar wannan abin me muhimmanci a gareshi na sake yin nesa da shi, irin nisan da bai san inda zai soma nemoshi ba, a hankali barci ya soma fizgarshi kafin duniyarshi tayi shiru komi ya tsaya da aiki a zahirinsa sai fitar numfashi da bugun zuciyarshi.
Suhail
Rintse idonshi ya yi da ƙarfi tare da ambatar sunan Allah a zuciyarsa, yayinda a zahiri ya shanye komi ya bai nuna komi ba, amma tabbas yana cikin azaba me raɗaɗin, gaba ɗaya ji ya yi kamar ana sukar naman jikinshi da ƙarfe me feshin wuta, ɗokaci ɗaya zufa ta soma tsiyaya daga kanshi tana gangarawa har izuwa tafin ƙafarshi, a can nesa sosai ya soma jiyo wani sauti me ban tsoro da firgitarwa ana faɗin.
"Suhail ka shiga hannun, dole zaka sadaukar mana da kanka domin kai ɗin namu ne kai ɗin tsohon akƙawarine da aka yi mana tun a wancan ƙarnin, babu hanyar kuɓuta babu samun salama da nutsuwar ruhi har sai ka zo gabanmh mun sha jininka."
Sake dakewa ya yi a zahiri yayinda ya ƙara himma wajen ambaton Allah gami da furta addu'o'in kariya, ahankali ya soma dawowa daidai sai a sannan ne ya iya jin jijjigar da Jauhar ke yi ma shi, a hankali ya buɗe idanuwansa a kanta, ba tare da sanin abin da kallonta a wannan lokacin zai haifar ba ya nitsa idanuwansa a cikinnata, nan take alƙalamin ya rubuta sunanta a cikin jerin mutanen da zasu rayu tare da Suhail walau ta daɗi ko akasin hakan.
"Naga ka yi shiru inata magana, cewa na yi na tuna da wani abu na tuna da inda za'a iya samunsa nice banje wajen ba."
Bai bata damar ƙarasa faɗin hakan ba ya kama hannuwanta a cikin nasa ya miƙe tsaye tare da ita, muryarshi a sanyaye sosai ya ce da ita.
" Ba yanzu ba mu aje wannan maganar muje inkaiki gida da kaina daga can sai inga gidanku."
Da ace Suhail yasan abin da ze faru da ko kusa bazai yi maganar kai Jauhar gida ba, komi ya saitune daga lokacin da ta ce.
"A'ah ba yanzu ba bazan koma yanzu ba please ka kaini naku gidan."
Ta faɗa daga can ƙasan zuciyarta tana jin hakan shi ne mafita akan zuwanta gida a yanzu, shima kuma bai musa ba duda bai da tabbacin abin da zai iya faruwa da zuwanta gidan sai de kuma ya ji kasancewarta a tare da shi zai fi samun mutsuwa.
Shi ya tuƙa motar yana kallon hanya cike da mamakin yanda yai uwar tafiya ba tare da shi kanshi ya saniba, sai dw sanin da ya yi cewa bada gangar jikinshi kaɗai yayi tafiyar ba da ƙuntatacciyar zuciyarshi wacce ke son ya nisanta da gida yai tafiyar sai ya daina mamakin kansa.
A mamakance Jauhar ke kallon ƙofar gidan da Suhail ya yi parking, a zahiri ita bataga gida ba amma kuma sanar da ita cewa sun iso da ya yi ya tabbatar ma ta da lallai wannan waje me kama da kango shine gida, sai zuciyarta ta raya ma ta zata rayu cike da farin ciki a wannan gidan koba komi zata yi nesa sosai da matsalolinta ba kuma lallai ne Papanta yasan inda ta je ba.
Sai da tsigar jikinta ta mimmiƙe lokacin da fara sol ɗin ƙafarta ta taka ƙasar gidan, badan bata taɓa taka ƙasar ba sai yanda aka zubarda ruwa a wajen ƙasar ta cakwale, ɗan yamutse fuska ta yi kamar zata yi magana sai kuma ta fasa lokacin muryar wa ta ma ta ta dira a kunnenta.
"Suhail wacece wannan na shiga uku ni binta."
Binta ta faɗa tana dafe ƙirji lokacin da ta yi tozali da farar fuskar Jauhar.
*Suhail* Jauhar ta maimata sunan a zuciyarta.
"Umma mu shiga daga ciki zanyi maki bayani."
Suhail ya faɗa yana ƙoƙari wucewa ɗaki, da sauri binta ta jawo bayan rigarsa da ya ke ƙoƙarin wuceta ya shiga ɗaki.
"Bantan ubanka dawo nan, tayaya zaka shigo min gida da baturiyar rayinya irin wannan sanna ka ce inshiga ɗaki, Suhail faɗa min gaskiya wacece wannan ɗin, ko kidnapping ɗinta ka yi."
Ware idanuwansa da suka kaɗa ya yi akan Binta da sauri ya soma girgiza kai sannan ya ce.
"A,a dama wannan alhajinne ya haɗa ni aiki ni da ita shine na kawota nan zata zauna zuwa anjima kaɗan zata koma bayan ankawo saƙo."
"Madallah kace ƴar arziƙice ka kawo.
Yarinya sannu da zuwa shigo daga ciki kinji maraba lale."
Binta ta faɗa tana ƙoƙarin kamo hannun Jauhar, da sauri Jauhar ta matsa baya tana yamutse fuska.
"Ikon Allah kenan ƙyiuya ta ke yi, to shiga da ita ma sha Allah yarinya ƴar ɗagwas da ita."
Binta ta faɗi bakinta a washe, shiga ɗakin Suhail ya yi yana jin kallo yanda aka hargitsa ɗakin da kaya babu gyara kamar bola su Zainab basa nan sun fice yawo ita kuma Binta saboda baƙar ƙazanta bata iya sharewa koda zai shekara a haka.
Sai da ya kwashe kaya sannan ya samawa Jauhar wajen zaman a saman kujera wacce du ta ɓaɓɓarke soso da katakonta a waje, zama ta yi cike da kyankyami tama maraimaice fuska ta kalli Suhail zata yi magana, sai kawai burum Binta ta hwaɗo kamar wacce aka jefo tana dashare haƙora hannunta riƙe da wani tsohon jug na roba ta cikashi da ruwa har zuba ya ke ta aje a gaban Jauhar.
"Ƴarnan ga ruwa ai ki saki jikinki kamar kina gida, za ki ji daɗin zama da mu wallahi kingammu nan bamuda wa ta matsala hannu bibiyu muke tarɓar baƙi a gidanan."
Murmushin yaƙe Jauhar ta jefeta da shi dan ita sam matar bata kwanta ma ta ba.
"Kai Suhailu nace motar waje ya za'ayi da ita kar yara su kakkarce ma ta mota dan naga sabuwace dal har kashe ido ta ke."
Cike da gajiyawa Suhail ya ce.
"A,a Umma a barta a wajen wataƙila ba jimawa zata yi ba zata tafi."
Yana gama faɗin hakan ya miƙe tsaye tare da nufar hanyar fita, da sauri Jauhar ta miƙe itama har nata yin kwallo da kofin ruwan ya tarwatse a ƙasa da hanzari da damƙi rigar Suhail ta baya har idonta ya soma tara kwalla.
"Babu inda zan je alwala zanyi in dawo, baki ji ansoma kiran sallah ba, ki zauna a wajen Umma kafin indawo."
Kamar ba zata yarda ba sai kuma ta sake shi ba tare da ta koma ta zaunaba, ita ko Binta sai ta shiga ƙoƙarin janta da fira dudan ta sake da ita.
Da yaje masallacima ya jima bai dawo ba, daya dawo ne ya iske waya acijin motar na ƙara, sai da ya kasa kunne da kyau sannan ya ji cikin motarne, kasancewae mukullen na hannunshi ya saka ya buɗe motar ya ɗauko wayar ƙirar iphone 17 darta jakarta ya gani ajiye da kuɗaɗe a barbaje sai kawai ya tatta komi ya saka a jakar sannan ya shiga gida.
Tsugunne ya hangota tsakiyar ɗaki tana jin sallamarshi tai hanzarin tashi tare da nufoshi, fuskarta face-face da hawaye, hannunshi ta kama ta riƙe gam tana sakin sababbin hawaye, baice komi ba yaja hannunta zuwa kan shimfiɗar da Binta ta yi ma ta amma taƙi zama.
"Naje wucewa naji wayarki na ruri shine na tsaya ɗauko miki na haɗo da wanna."
Ya miƙa ma ta da jakar wacce ta kasance me ɗan girma, amsae jakar ta yi tare da zazzagewa nan samabibin daloli suka shiga faɗowa tare da wa ta leda me ɗan girma, da sauri ta soma buɗe ledar ta ciro abin da ke cike, kamar ba ita ta gama kuka yanzu ba ta kalli Suhail da ƴar fara'a akan fuskarta tare da faɗin.
"Ashe nan na aje ta, abaya ce na siya ina ta nemanta bangani ba." Bata jira amsarshi ba ta shiga warwareta tare da miƙewa tsaye ta soma gwadawa da tsayinta, lafiyayyar abayace wacce daga gani ba sai amnfaɗa ba me tsada ce sosai, sai ɗaukar ido ta ke duda ba wani hasken kirki bane a tsakar gidan, linkewa ta yi sannan ta ce.
"Ina so zan yi wanka ina Bathroom?."
Ta yi maganar tana yawata idanuwanta a tsakar gidan tana neman inda za'a kira da wajen wanka........✍️
ƳAN ALBARKA A TAYA NI DA SHARE.
MARYAM STAR ⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS💪🏻.
Follow the MARYAM UMAR HAUSA NOVELS BOOKS LIBRARY 📚📚 channel on WhatsApp: ***
🌹𝙈𝙐𝙃𝘼𝙎𝙀𝙀𝙉🌹
(𝐿𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑧𝑢𝑐𝑖𝑦𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑘𝑢𝑛𝑐𝑖, 𝑟𝑎𝑦𝑢𝑤𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑘𝑎𝑙𝑢𝑏𝑎𝑙𝑒😔.)
𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀 𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐.
💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍,𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪
✊ 𝙏𝙃𝙀 𝙎𝙃𝙄𝘿𝙊𝙍𝙄𝘼 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝙏𝙀𝘼𝙈🤝
***
𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙆
𝙎𝙀𝘼𝙎𝙊𝙉 𝙊𝙉𝙀