MUHASEEN

Chapter 9

by @maryamstar248

Bin yatsar Suhail ta yi da ido tana kallon wajen da yatsar ta nuna, ware ido ta yi sosai sai kuma ta kalle shi ta kalli wajen kamar zata yi magana sai kuma ta shanye bata ce komi ba, rigar ta sagala a kafaɗarshi sannan ta kalli Zainab da gaba ɗaya hankalinta na kan kuɗin da Jauhar ɗin ta fiddo amma bata kwashe ba.

"Am Sister please bani towel da takalmin wanka, ki haɗo min da sauran kayan wankan please."

Kallon juna Zainab da Fati suka yi sannan Zainab ta tashi ta shiga ɗaki, ba jimawa sai gata ta fito da ƙaramin kwandon wanka me ɗauke da sabulu da soso, baya Jauhar ta yi tana kallon kwandon cike da kyankyami sai kuma ta maida kallonta ga Suhail daya harɗe hannu a ƙirji fuskarshi aɗan sake yana kallon su.

"Suhail!!!!."

Ta ambaci sunan da wata irin siga, wanda hakan ya saka numfashin Suhail tsayuwar wata a ƙirjinshi, da ƙarfi ya fesar da numfashi sannan ya ɗaga mata gira ɗaya alamar ya dai?.

"Kace ta bani kayan wanka please."

Ta faɗi aɗan shagwaɓe kamar me shirin fashewa da kuka.

"Zainab bata kayan wanka." ya faɗa a taƙaice yana ɗauke gai zuwa gefe.

"Yo Suhail idan ba naka zan ɗauko ma ta ba kasan de iya wannan muke da."

Cikin rashin sanin abin yi ya ce.

"Ɗauko mata nawa ɗin."

Yana gama faɗin hakan yasoma ƙoƙarin janye hannu sa daga cikin nata, amma mi sai ta ƙara riƙeshi katamau tana girgiza kai, gaba ɗaya ya rasa abin yi zai iya cewa wannan shine first time da hannun wata mace ya taɓa jikinshi da sanin shi ba tare da ya shiryawa hakan ba, gaba ɗaya kanshi ya kulle katamau abubuwa biyu na ƙoƙarin haɗe mashi a lokaci ɗaya, cike da gajiya ya sauke idonsa akanta sannan ya ce.

"Please sakeni kije kiyi wankan."

Bata so hakan ba sam amma babu yanda zata yi hakanan ta sake shi tana ji kamar idan ya matsa daga wajenta wani abu marar daɗi zai iya faruwa da ita.

Ta ɗauki mintuna biyu tana kallon kewayen kamar ba zata shiga ba, ko mi ta tuna sai kuma ta shiga.

Lumshe ido Suhail ya yi yanajin kanshi naɗan sara mashi na surutun da ya yi me ɗan tsayi, dan surutu ba al'adarsa bace ko a wajen kasuwancinshi baya surutu sosai sai idan ta kama balle a gida da bawani samun sakin fuska ya ke ba, damƙar rigar data sagala mashi yayi tare da nufar wajen da ta zazzage jakarta, akan idonshi gaya Fati ta zare dala ɗaya baice da ita komi ba ya shiga tattara sauran yana mayar mata a jakar, sai lokacin yai danasanin ɗauko ma ta jakar kamar ya manta da su waye ƴan gidansu, musamman idan sukaga kuɗi ko waje me maiƙo.

Sautin hito ne ya daki dodon kunansa a daidai sanda ya ɗago yana zuge zif ɗin jakar, Hamza ya gani tsaye a bayanshi cikin shiga irinta gayu, kannan an tara suma an mummurɗeta kamar ƙuda wai ahakan du cikin gayu ne, yana wani boƙarewa ya kankwashe murya irin guy ɗinan sannan ya ce.

"Hi Suhail naga wata farar sol me kwarjini a waje, shine ake sanar min wai ai kai kazo da ita shine nace harka ta samu ba zaka neme ni ba haba Broth ka daina haka, kasan mu masu fita cilling dole sai da irin wanna, ammafa wallahi tayi iya yi wannan daidai wankan gobe wallahi Allah, to ya ne guy zaka yi mana ehhhh yane ni da freinds ɗina muɗan fantama."

Hamza ya yi maganar yana lallankwashe jiki.

Murya a sanyaye Suhail ya ce

"Haba Hamza sau nawa zan yi maka magana akan rashin yin sallama, sai kace gidan arna zaka shigo mana kana fito."

"Kuturun..... waye kuma Hamza ba daɗin ji, gaskiya Suhail kana min yawa fa iya wuya ya zaka dinga kurana da wannan sunan kamar wani lezy gaskiya karka sake bana so, idan ba zaka kira ni da Handsome ba to ka daina kirana nayafe wallahi."

Ya faɗa yana sauya fuska daga fara'a zuwa ɗaure fuska.

Girgiza kai kawai Suhail ya yi tare da nufar ɗakin sa yana nemawa Hamza sauƙi a lamurransa.

Binta data laɓe daga tagar ɗaki tana leƙensu ta kwalla kiran Hamza da sauri haɗe da yafito shi tana ƴar murya, a maimakon ya hanzarta sai ya tsaya ƙanun surutai kafin ya shiga ɗakin.

LEGOS NIGERIA

AGEGE.

"Ƙwarfeshi ta baya,,,, yauwa naushi cikinshi, lanƙwasa hannayensa ka dira ta kansa,, yeeeeeeeeeeeee Zaki, Zaki, Zaki, Sarkina ka yi nasara kamar dai kullum."

A bin da ɗan mitsitsin bakinta ke faɗi kenan da ƙarfin sauti, yayinda siraran hannayenta suka shiga mommotsawa tare da kai duka a duk inda ta samu, gaba ɗaya zanin jikinta ya nannaɗe, fararen cinyoyinta a waje.

Kallon-kallo mutanen da ke tsaitsaye cirko-cirko kusa da ita suka soma yi, cikinsu an rasa wanda zai kusanceta, a zahiri barci ta ke amma doke-doken da take kaiwa da iya ƙardinta zaisa ka zaci iskokai gareta suka tashi.

Wani kyamusashe magidancine ya matsa kuda da ita, a daidai sanda ta ɗaga ƙafarta da iya ƙarfinta ta kai zazzafan harbi, ya yi ƙoƙarin kaucewa amma bai samu nasara ba, sai da ta kwaɗa mashi ƙafa a gefen fuska kamar ba bamiji ba yai gefe tare da kwalla ƙara yana soshe-soshe, yayinda hankulan mutanen yajen ya koma kanshi nan aka shiga jajanta ma shi.

"Wayyo Allah ta gama da ni ta kasara min muƙamuƙi munafukar, wayyo Allah, wayyo na bani na lalace ni Mamman."

Saukar ruwa masu sanyin gaske da taji a jikinta ya tilasta mata tashi a hargitse tana kwalla ihu kamar zautata sai ta ɗibi hanya ido a rufe zata arta bayan ta diro daga kan gadon amma sai ta ji an riƙeta gam.

"Wayyo Allah Sarki zoka ceceni ankawo min farmaki, wayyo karka tafi ka barni dan Allahhhhh...."

Ta faɗi tana watsal-watsal da hannuwanta tana son kwacewa, zazzafan marin da aka sauke mata ne ya tsaida ita cak, sannu a hankula ta soma buɗe idanuwanta, dishi-dishi take ganin mutanen ɗakin, sai da ta kwashi sakanni kafin ganinta ya saitu, sai faman haki ta ke ga jikinta sai ɗigar ruwa ya ke kamar wacce aka tsamo daga kogi.

Ɗaya bayan ɗaya ta dinga bin ƴan ɗakin da kallo ƙirjinta na hawa da sauka da sauri, yayinda idanuwanta suka fallasa asirin zuciyarta tsoro ɓaro-ɓaro ya bayyana a cikin su, sai kawai ta rintse su da ƙarfi wani abu me kama da zafi na dukan zuciyarta, muryarta da alamun kuka ta soma furta.

"Mafarki, yauma a mafarki na ganshi mi yasa?."

Ta yi tambayar tana tuhumar kanta yayinda ta fizge hannayenta da ƙarfi ta fice daga ɗaki tana fashewa da kuka me sauti.

Ƙur matar da ke zaune ta miƙe ƙafafuwa ta kafe ta da ido tana kallon yanda jikinta ke amsawa da kukan da ta ke yi, kamar ba zata tanka ba sai kuma ta kalleta tare da janyo hannayenta ta rungumota jikinta, tana jin tausayin yarinyar na ratsata bayanta ta soma bubbugawa a hankali, yayinda hayaniyar da mutanen gidan ke yi kamar kasuwa ya hanata yin magana, saboda batada murya me sauti.

Ta ɗauki lokaci me tsayi tana kukan badan wani abu sai dan yauma abin da ta gani ba zahiri bane, sau dubu zata kwanta sai tayi wannan mafarkin da jikinta ke sanar da ita gaskene, amma kuma tashin ta da mutanen gidan ke yi a kullum na sakata baƙin ciki, a ganinta da ace sun barta basu tasheta ba da wataƙila mafarkinta ya zama gaske, amma sau dubu zata kwanta sau dubu zasu tasheta.

"Innalillahi! Mamman kaga yanda ta kumbura maka haɓa, lallai kaji dukan manya."

Wata mata ta faɗi tana riƙe haɓa cike da jimami, yunƙurawa wanda aka kira da Mamman ya yi ya tashi tsaye, hannunsa akan haɓarshi da ke luguden azaba, kanshi tsaye ya yi hanyar ficewa daga ɗaki yabar sauran matan na shewa, wasu na masa dariya wasu na jajanta masa, waɗanda ke dariyar basu tsagaita ba sai da suka daina ganin wulginsa, sannan mutanen suka soma firfitowa kowa da abin da yake faɗi.

"Oh Najla shikenan tashin ki a barci ya zama annoba ko ince bala'i, yo annoba ka bala'i manah ayi mutum ƙarfi uwa doki, aiko wallahi kinji kunya ko aure kika yi ba lallai kibar wannan ɗabi'ar ba."

Sake fashewa da kuka wacce aka kira da Najla ta yi, bata kuma tsagaita ba sai da ta yi iya yinta, hawaye face-face a kan farar fuskarta manyan idanuwanta suka ture zuwa launin jah amma ba sosai ba, tsabar dagaske take kukan harda majina akan fuskarta, haka mutanen gidan suka dinga faɗar albarkacin bakunansu akanta, babu me faɗar alkairi sai faman kira mata bala'i suke.

Cikin sanyi matar ta sake janyota tare da soma goge mata hawayen idonta tana faɗi a tausashe.

"Haba Gimbiya taya za ki dinga asarar hawayenki masu tsada, hakan ai ba girmanki bane kiyi shiru ki daina kuka, suma basu fahimce ki bane shiyasa suke hantarar ki amma ni nasan ba hakanan kike doke-doke idan kina barci ba, kiyi haƙuri kinji ƴata wata rana sai labari Allah dai ya cika maki burinki."

Babu kunya Najla ta amsa da "Amin". kuma bata daina kukanba.

"Yauwa Sarauniya yanzu miƙe ki je kiyo alwala kiyi sallah kinga gari ya soma haske."

Matar ta faɗa tare da ƙoƙarin tada ita tsaye, har bagan babban baho na ruwa ta kaita sai da ta cika mata babbar buta sannan ta aje mata ta juya ta koma wajen zamanta murmushi shimfiɗe akan farar fuskarta, yayinda wani abu ke motsi a zuciyarta, wani abu wanda daidai da rana ɗaya bai taɓa barinta ta sararaba, ita ɗin me raunice amma bata bayyanar da rauninta ba saboda batason gundurar mutanen da ke baibaye da ita cikin aminci da girmamawa, a kullum rana tana saka rai da abin da batada yaƙinin faruwarsa sai de kallon fuskar Najla kawai na sanyaya ranta gami da bata ƙwarin gwuiwa, sannan jikinta na bata samun sauyin al'amurra daga ɓangarenta, iya mafarkanda tun wanzuwarta a gidan Najla ta soma yi na ɗisa ayar tambaya a zuciyarya, sannan tanada fata akan mafarki duda ba lallai fatanta ya tabbata ba amma tanaji a jikinta akwai wani abu me girma wanda take da alaƙa da shi da mafarkin da Najlar ke yawan yi.

Tazbihi taci gaba da yi a fili fuskarta ɗauke da mirmushi tana fatan tayi wani abu da zai zama na alkairi tsakaninta da al'umar gidan.

Siririyar tattausar muryarta ce ta katseta daka tunanin data nitsa a ciki.

"Umma matsa min kusa da ke zanyi sallar."

Najla ta faɗa da sunanda ta laƙaba mata shi tun zuwanta gidan, sunanda ke sake haddasa danƙararriyar ƙaunar Najlar a zuciyarta, sassanyar murmushi ta sakar mata sannan ta janye ƙafafuwanta ta matsa sosai daidai wajen da ta tabbatar zai ishi Najlar yin sallar.

Itama Najlar Murmushi ta sakarwa Ummar sannan ta tayarda sallah cike da nutsuwa, harta gama idanuwan Ummar na kanta tana kallon yanda take nutsuwa sosai a wajen ibada duda tana da rawar kai sosai amma idan tana aikin ibada zaka sameta da nutsuwa.

Bayan ta gama azkar ta yi addu'o'i masu tsayi sannan ta shafa, sai ta cire hijabin jikinta tare da watsa kyawawan idanuwanta akan Ummar, da siririyar muryarta me taushi ta ce.

"Ummana ni kaɗai ina kwana fatan kin tashi garau, yau a gidannan ke kaɗai zan gaisar."

Ta yi maganar tawa watsa ma wata matashiya za zata girme mata a shekaru wani kallo me kamar harara.

"Lafiya ƙalau Sarauniyar Ummanta fatan Gimbiyar Sarki ta tashi cikin ƙoshin lafiya?."

Kyakyawan murmushi wanda ya bayyanar da kyawawan jerarun ƙananan haƙoranta ta saki, sannan ta tanƙwashe ƙafarta tare da faɗin.

"Gaskiya Umma kina kashe ni da ƙauna wallahi, in sha Allah idan na auri Sarki ke zaki zama Fulani a fada, wato muƙami na daban zan saka a baki hatta wanka ba zan bari kiyi da kanki ba sai de asamu me yi maki, su Uwale ko sune ƴan shara da wanke-wanke."

Ta ƙarashe faɗar maganar tana kafe Matar da ta fito daga wani ɗaki hannunta na riƙe da babbar roba.

"Kan uba, dan ubanki ni ce zan zama ƴar wanke-wanken wallahi ƙarya kike yarinya shairin mafarke-magarken da kika saba yi me kama da bugun iska ne ke gaya maki ƙarya, yo Allah na tuba kama da iska mana abu yaƙi ci ya ƙi cinyewa kullum jiya i yau, inaji kwanyarki ta soma taɓuwa gaskiya bari Mamman ya wartsakw daga jinyar haɓarshi da kika nakasta ya je ya taho da Malam na lungu naga ya kamata ayi maki ruƙiya."

Uwale ta faɗa tare da wucewa abinta tana kaɗa musu mazaunar.

Still Fuskar Umma da murmushi ta ke kallonsu, idan da sabo yaci ace ta saba da halayyar mutanen gidan da kullum cikin drama suke, baga manyan ba baga ƙananan ba......✍🏻

Dan Allah Masoya a tayani da share🙏🏻🙏🏻

A daidai nan zan ɗisa aya . ku kasance tare da ni taku har kullum me son ganin farin cikinku.

MARYAM STAR⭐⭐ YAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS💪✍🏻

***

🌹𝙈𝙐𝙃𝘼𝙎𝙀𝙀𝙉🌹

(𝐿𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑧𝑢𝑐𝑖𝑦𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑘𝑢𝑛𝑐𝑖, 𝑟𝑎𝑦𝑢𝑤𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑘𝑎𝑙𝑢𝑏𝑎𝑙𝑒😔.)

𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀 𝘽𝙔

𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐.

💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍,𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪

✊ 𝙏𝙃𝙀 𝙎𝙃𝙄𝘿𝙊𝙍𝙄𝘼 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝙏𝙀𝘼𝙈🤝

***

𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙆

𝙎𝙀𝘼𝙎𝙊𝙉 𝙊𝙉𝙀