MUHASEEN

Chapter 11

by @maryamstar248

Gwauron numfashi Papa ya sauke sannan ya kalli matarshi da ta ci ado cikin jan leshi wanda ke nuna kuɗinshi a fili, ta yi kyau sosai a idonshi, sai de a zuciyar shi ba hakan ba ne wata fuskar daban ya ke hangowa kwance akan tata fuskar, fuskar da ta zama wani yanki na rayuwarshi, yanzu da babu ita sai ya ke jinsa kamar ba cikakken mutum ba, ko farinciki ya ke yi yana ji a jikinsa bai cika ba kamar can baya.

Tafin da ta yi a saitin fuskarshi ne ya dawo da shi hayyacinsa daga duniyar tunanin daya afka, far ta yi da ido cikin murya me jan hankali ta ce.

"Honey ya dai ko na yi maka kyau ne da yawa?."

Sai kawai ya janyota zuwa jikinshi sosai yana murmushi ya ce.

"A koda yaushe ke me kyau ce musamman idan kika yi kwalliya irin hakan."

Sosai farinciki ya bayyana akan fuskarta na jin daɗin yabon da ya yi mata.

"Ga tea ɗinka nan karya huce."

Ita ta bashi tea ɗin a baki tana yi tana masa iyayi, shi kuma yana biye mata duda zuciyarsa a ƙuntace ta ke, sai bayan da suka gama ne sannan ya sake kallonta tare da faɗin.

"Ko dai zan je da kaina Hotels mafi kusa in duba ko Jauhar tana can, kar wani abu marar kyau ya faru da ita kinga na kira wayarta sau da yawa amma ba'a ɗaga ba hankalina ya gaza kwanciya."

Ya yi maganar yana kallon yanda fuskarta ta soma sauyawa da wani abu me kama da ɓacin rai, da ƙyar ta janye yanayin ta wanu marairaice cije da kissa ta ce.

"Na ɗauka mun gama wannan zance ai Honey, sanin kanka ne ko sau dubu zaka kira ta ba za ta taɓa ɗagawa ba, so ka daina damuwa kawai koma ina zata je ni nasan dole za ta dawo nan tun da bata da wanda suka fi mu, amma tun da ka matsa bara in saka security su bibiyi motarta."

Bata barshi ba sai da ta tabbatar ta goge ma shi tunanin Jauhar a cikin kanshi, ko da ta fice sai ta kama sabgogin gabanta ta share shi.

Yanayin da ya saba shiga ne yanzunma ya riskeshi, a du sanda Jauhar zata bar gida abin na damunshi sosai sannan kuma yana so ya yi maganar amma sam matarsa Hajiya Fatima bata tari, daga ƙarshe idan ta bashi tea ya sha sai ta zauna ta yi mashi fira, daga nan kuma sai barci me nauyi ya ɗauke shi ba tare da ya shirya ba.

Wawan Tsaki Hajiya Fatima ta doka tare da ɗaukar danƙareriyar wayarta ta soma kiran wani layi da aka yi save da My Sister.

"Hello Matar Alhaji ya ake ciki ne, inace komi ya daidaita."

"Mtswwwwww wani daidaito fa yana can yanzu haka yana zancen mayyar yarinyar can, tun safe na kaɗa ƙeyarta ta fice daga gidan amma har yanzu bai daina damuwa ba, yana can na saka shi barcin dole ai."

Dariya aka sheƙe da ita daga can cikin wayar sannan sautin murya ya sake fitowa.

"Kai wallahi Fatima wannan mijin na ki anyi uban ƴan taurin kai, wai kina nufin har yanzu bai haƙura da waccan Mayyar ba, gaskiya sai kin zage dantse idan ba haka ba ba zamu samu abin da muke so ta sauƙi ba."

"Hummm ke dai ki bari kawai gabaɗaya kaina ya kulle wallahi na rasa abin yi yanzu haka ga damammaki sai wuce ni suke yi, gaba ɗaya kaina ya kulle a kan mutuminnan, ni tsoro nike kar zaman jiran shekarun da na yi ya tashi a banza wallahi."

Haka suka ci gaba da tattauna ko waccensu na faɗin albarkacin bakinta.

KUBWA

Kwance Suhail ya ke a ɗakinsa saman katifarsa da ya gama kakkaɓewa ya shimfiɗa bargo, gaba ɗaya kanshi ya kulle tunanin yanayin da ya shiga a lokacin da ya furta sunan MUHASEEN kawai ya ke, ko yanzu da ya ke a kwance tunowa da sunan kawai da ya yi sai da ya ji kanshi ya doka da ƙarfin gaske, nan take ciwon kai ya safko ma shi, yunƙurawa ya yi tare da tashi zaune ya dafe kanshi yana aranto addu'o'i, ji ya yi kamar tsayuwar mutum a kusa da shi da sauri ya ɗaga kanshi da ke niyyar tarwatsewa abin da ya gani ne ya saka shi miƙewa ba shiri har jiri na kwasarshi.

Jauhar ce tsaye a gabanshi daga ita sai pant da bra ga kayan da ta cire a hannunta tana kallonshu cikin ɗan hasken da ke a kwai a ɗaki.

Da wani irin zafin nama ya tura ta baya ta faɗi ƙasa sannan ya juya baya a rikice gaba ɗaya ya rasa abin yi in banda rawa da sarawa babu abin da kan shi da jikin shi ke yi, sai faman zare idanu ya ke.

"Suhail."

Ta kira sunanshi a raunane tana jin azaba a hannunta data faɗa a kanshi.

Bai juyo ba kuma bai fita ba kawai de yana jinta ne.

"Wash hannuna, na yi wanka ba'a bani man da zan shafa ba ina jin sanyi sosai."

Yan da ya ji ta furta Wash hannunta ya tunasar da shi ya tura ta da ƙarfi kuma yasan zata iya faɗuwa harma ta ji ciwo.

Kamar ba zai juyo ba sai kuma ya juyo amma bai yadda ya kalli sashen da ta ke ba, sai kawai ya janyo abin da ya ke lulluɓi ya soma takawa da baya-baya zuwa inda ta ke, sunkuyawa ya yi tare da aje mayafin sannan ya ce a taƙaice yana tashi.

"Ki suturta jikinki."

A cikin ɗan hasken ta ke kallonshi tana kuma kallon abin da ya aje ma ta har ya fice daga ɗakin, sai kuma ta kalli jikinta tana son fahimtar mi ya ke nufi, dan ita bata gane komi ba ga hannunta da ke zugin azaba kamar zai ɓalle.

A ƙofar daƙin Binta ya zauna, sai de zamanshi ba jimawa ya tsinkayo muryar ta tana raɗa.

"Ka yi du yanda zaka yi ka samu kudanci da ita, yarinyar me arziƙi ce wataƙila ɗiyar shi Alhajin wanda zai ɗauke shi aiki ce ɓoye min ya yi bai faɗa min gaskiya ba, kai idan ma da hali kawai ku tafi wajen aikin a tare zan gobe idan zai ta fi kaima Alhajin ya baka aiki a wajensa ko mun huta da wannan baƙin talaucin."

Bai idasa jin abin za suke tattaunawa ba ya miƙe yabar wajen dafe da kanshi da ke masa ciwo bana wasa ba.

Jauhar ganin dai ba zata samu abin da ta ke so ba, ga hannunta sai zafi ya ke ma ta sai kawai ta zura rigar abayarta sannan ta fito daga ɗakin, hango shi da ta yi a ƙofar fita ya saka ta bi bayansa, sam tafiyarta babu sauti shiyasa bai ji tsayuwarta ba sai ji da ya yi ta kama hanunsa ta ɗaura ƙanƙame dare da ɗaura kanta a dantsen shi wasu ruwa wanda ya tabbatar da ruwan hawaye ne na sila su na taɓa fatar hannunsa, cak ya tsaya bai yi ko motsi ba shi gaba ɗaya kanshi ya gama kullewa da Jauhar daya ɗaukowa kansa ta zame masa jangwam.

Sake ƙanƙame hannunsa ta yi tare da fashewa da kuka me ɗan sauti a wannan karon, a hankali ya ɗago da kanshi da ya yi masa nauyi sosai ya kalleta sai ya saka hannunshi ɗaya ya kamota tare da tsayar da ita a gabanshi ya tsare ta da rikitattun idanuwan shi, kallon yanda ta ke yin kukan kawai ya ke yana ji da da hali shima da ya yi kukan wataƙila ya samu sauƙin abin da ya ke ji, kama hannunta ya yi da niyar yin magan sai kawai ya ga ta kwace tare da fasa ƙara marar sauti sosai, da sauri ya sake ta yana kallon yanda ta riƙe hannun tana sabunta kukanta.

Cikin tausasa harshe ya ce da ita.

"Kin ji ciwo ne?."

Ɗaga ma shi kai ta yi alamar amsawa tana kuma kallon hannunta data tattare hannun abayar zuwa sama, shima kallon farin siririn hannun ya yi yana iya hango yanda jini ya ɗan taru a ƙasan gwuiwarta ga shi wajen yaɗan tasa alamar kumburi, sai ya ji babu daɗi a ranshi a fili kuma sai ya kalleta cike da kulawa sannan ya ce.

"Mu je a duba miki hannun kin ga ya soma kumbura."

Kallon tsakiyar idanuwansa ta yi da limsasun idanuwanta, tana hango wani da ya yi nisa sosai da rayuwarta, nisan da ta jima tana gudu wajen kamo abin amma yana sake tsere mata, yanayin shiru ya gifta a cikin kanta, yayinda taushin magarsa ya samu wawakeken fili a zuciyarta ya zauna daram, a fili kuma sai ta sake narke fuska tana son sake ganin wannan abin, ba tare da saninta ba sai ta ɗan matae hannun mw ciwo, nan take ta sake furta sautin ƙara, tare da sakin hannun da sauri azaba na baibayeta daga tsakiyar kant har ƙarƙashin ƙafafuwanta, amma ko sau ɗaya bata janye idonta daga gare shi ba, ta yi hakanne dan son sake ganin gilmawar wannan abin a cikin idannuwansa.

Da sauri ya kama hannun na ta cikin rasa abin yi, cike da kulawa ya dinga furta ma ta kalmar sannu babu ƙaƙƙautawa.

Kawai se ta faɗa jikinshi ta ƙanƙameshi da iya ƙarfinta, tana jin wani abu na mata yawo a kansa.

Kulawa abacw da ta yi ƙaura a rayuwarta, tun tashinta bata san wani abu wai shi kulawa ba, kuma bata san ya ake ji idan aka samu wannan kulawar ba, ta rayune a cikin ƙunci da kuka ita kaɗai, ita kaɗai ta ke rayuwarta a du yanda ta zo ma ta, amma a yanzu da ta ke ganin wannan abar data rasa a wajen Suhail sai zuciyarta ta sake yin rauni sosai.

Rintse idnuwansa ya yi cike da gajiyawa, a ɓangare ɗaya yana tuhumar kanshi akan yanda ya turata ta faɗi har ta ji ciwo, ga kuma tausayi da ta bashi tun a ganinshi da ita a ɗazu.

Ƙawa zuci abune da sam Suhail baya da shi, musamman akan jin daɗi na rayuwar duniya, rayuwarshi gaba ɗaya ta ta'laƙƙa wajen nema tare da burin faranta ran wacce ita kaɗai ya ke kallo a matsayin wani na shi, a yanzu kuma da ya shigo da Jauhar a rayuwarsa sai ya ke jin kamar akwai abin da ya ke buƙata, sai de ba zai iya cewa ga abin ba amma tabbas akwai abin da babu shi a lissafinsa kuma rayuwarsa ba zata cika ba sai da wannan abun.....✍🏻

KUYI FOLLOWING WANNAN LIKN ƊIN DOMIN SAMUN DAMAR KARANTA WANNA LITTAFIN DA ZARAR MUN ƊORA

***

MARYAM STAR ⭐⭐

Follow this link to join my WhatsApp group: ***

🌹𝙈𝙐𝙃𝘼𝙎𝙀𝙀𝙉🌹

(𝐿𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑧𝑢𝑐𝑖𝑦𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑘𝑢𝑛𝑐𝑖, 𝑟𝑎𝑦𝑢𝑤𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑘𝑎𝑙𝑢𝑏𝑎𝑙𝑒😔.)

𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀 𝘽𝙔

𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐.

💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍,𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪

✊ 𝙏𝙃𝙀 𝙎𝙃𝙄𝘿𝙊𝙍𝙄𝘼 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝙏𝙀𝘼𝙈🤝

***

𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙆

𝙎𝙀𝘼𝙎𝙊𝙉 𝙊𝙉𝙀