MUHASEEN

Chapter 12

by @maryamstar248

"Sannu zo mu je a duba miki."

Ya faɗi yana cirota daga jikinshi a hankula.

"A,ah Suhail lafiya dai mike faruwa??.".

Maganar Hamza ta tsaya lokacin da hasken fitilar ƙaramar wayarsa ya haske masa rabin fuskar Jauhar da ke gaban Suhail, da wani irin sauri ya ƙarasa yana sake hasketa da kyau.

"Kam bala'i mi zan gani kamar farar baturiya a gidanmu, ashe de Binta ta yi gaskiya."

Ya faɗa yana buɗe duka girman idanuwansa akan kyakkyawar farar fuskar Jauhar, matsawa ya kuma yi sosai tare da safa

kafaɗar Suhail mamaki bayyane akan fuskarshi.

Jauhar tuni hasken fitilar Hamza ya haske ma ta idanuwa ya zama bata gani sai faman saka hannu ta ke tana karewa, yayin da ƙyalƙyalin stons ɗin da aka yiwa rigarta ado da su suka shiga walwali, sai hakan ya bawa Suhail damar ƙare mata kallo, yana kallon yanda Allah ya zuba ruwan kyau a gareta, fara ce sol wanke hannu ka taɓa doguwa me siririn jiki, yayin da ta ke da cika a sama da ƙasa ma sha Allah, idanuwanta da ke ɗauke da ruwan hawaye a cikinsu yayin da dogayen gargasar saman idon suka jiƙe da hawayenta sai hakan ya saka idanuwanta yin kyau sosai a ganin Suhail, shagala ya yi wajen kallon yanda ta ke ƙifta idanuwan saboda hasken da ya dallare ta, har bai ji maganar da Hamza ya yi ma shi ba, sai da ya sake maimaitawa.

"Suhail wai ina ka samo wannan cikar ne, gaskiya an tafi da ni wallahi."

Maganar Suhail ce ta dawo da shi duniyar zahiri, da sauri ya janye idonshi daga kanta ya kuma janye hasken wayar Hamza ba tare da ya ce komi ba ya juya zuwa cikin gida, da sauri Jauhar ta bi bayanshi tare da jerawa da shi tana sauke ajiyar zuciya, saura kaɗan ta yi karo da bango kasancewar sam bata gani, da taimakon Suhail daya janyo ta baya ta lura da abin da ke shirin faruwa.

Hamza ma biyo bayansu ya yi yana ta faman washe baki ganin zuƙeƙiyar Baby a gidansu.

Zai iya ƙirga sau nawa ya taɓa shiga ɗakin Suhail tun tasowarsu, du da gida ɗaya suke amma sam baya shiga sabgogin Suhail ɗin, dan a kullum yana kallon kansa a matsayin gaba da Suhail.

BANANA ISLAND

Sautin shiru ne ya gifta ta cikin kansa, yayinda masarrafar tunaninsa ta soma dawowa aiki, sannu a hankali abubuwa masu tarin yawa suka soma giftawa ta cikin kansa, cikin ikon Allah ya soma motsawa tare da buɗe idanuwanshi, ya jima kwance a wajen bai gama dawowa hayyacinsa ba sai bayan shuɗewar mintuna, yunƙurawa ya yi da niyar tashi zaune amma mi, a maimakon ya ji an rirriƙe shi kamar baya sai ya ji ya yunƙura ya miƙe sawai da shi, ko da ya tashi tsaye sai ya ji shi ya tsayu akan diga-diganshi yana jin kamar an cire wani abu me kama da ƙaton dutse da ya danne shi, juyi ya soma yi yana dudduba jikinshi da kyau, abin mamaki sai ya ke jinshi a cikakken mutum kamar kowa, da sassarfa ya soma takawa zuwa gaban wawakeken miro, tae ya ke kallon idanuwansa da suka sauya launi daga jajaye zuwa farare tas kamar madara, lumshe su ya yi tare da sake buɗewa, amma still sai ya sake ganin sun washe sun yi fari tas kamar yanda suke a can baya, yawatawa da idanuwansa ya soma yi a duka sassan jikinsa ta jikin miro amma kuma sai ya sake ganin wasu sauye-sauyen a tattare da shi, akwai wani baƙin abu da yake firfitowa a jikinsa musamman a saitin jijiyoyi amma sanzu daya dudduba baiga komi ba, babu su duk sun ɓace.

Komawa da baya ya yi ya zauna daɓas a san bed cikin wani irin yanayi, da sauri ya tashi tare da kallon fari ƙar ɗin zanin gadon amma amma mi, sai yaga babu wannan jikin da ya zubar, shanye mamakinsa ya yi tare da kwashe zanin ya kai shi laundry ya aje, sannan ya shiga toilet ya sake yin wanka ya fito jallabiya kawai ya saka ya fita jin ƙarar alarm ɗin lokacin sallar asuba na dokawa.

Yawata idanuwansa ya ke akan tarin ma'aikatan gidan maza da ke ta firfitowa domin zuwa sallah, sai ya ji wani alfahari na kama shi gami da jin daɗin yanda du wani makusancinsa baya wasa da yin sallah akan lokaci.

Yau da ƙarfinsa ya ke gabatar da ibada cike da shauƙi, fuskarshi a sake babu komi a cikinta babu wannan ɗaurewar da ya ke kuma babu murmushi ammadai a sake ta ke, hatta ma'aikansa yau sunga sauyi domin kuwa musabiha ya dinga yi da su hand to hand lokacin da aka fito daga sallah.

Saleem kuwa bakinshi har kunne sosai ya karanci sauyi daga wajen oganshi, ko da suka koma cikin gida umarni Muhaseen ya bayar akan a dafa abinci me rai da motsi a yi sadaka.

"Sarki."

Saleem ya kira shi muryarsa da alamun nishaɗi a ciki.

"Uwummm."

Ya amsa shi tare da ɗaga fararen idanuwansa ya zuba su akan Saleem ɗin.

"Ko da sau ɗaya ne dan Allah."

Ya marairaice fuska kamar zai yi kuka.

Daga gira Muhaseen ya yi alamar tamba.

"Murmushi, ina so inga murmushi akan fuskarka aƙalla koda sau ɗaya ne."

Ya faɗa yana sake marairaicewa.

Ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya Muhaseen ya yi tare da aje hannayensa akan cinyoyinshi ya kafe Saleem da mayun idanuwanshi masu cike da kwarjini.

Turɓune fuska Saleem ya yi kamar zai fashe da kuka, ya kawar da kanshi gefe yana ƙun-ƙuni.

'Ɗass-ɗass-ɗass.'

Muhaseen ya ƙyasta ƴan yatsunsa suka fitar da sautin, juyowa Saleem ya yi amma kwarjini ya hana shi kallon cikin idon Muhaseen ɗin, a maimakon haka sai ya kafe siraran pink lips ɗinshi da suka motsa kaɗan, sai kuma suka dare kyakkyawan ƙasaitacen murmushi na bayyana a samansu, lokaci ɗaya kuma soka tsuke a yanda suke, dariya me cike da jin daɗi Saleem ya sheƙe da ita, ganin murmushi a fuskar Muhaseen ba abune me sauƙi ba bare kuma dariya, dariya ita ce abu na ƙarshe da zai iya ƙirgawa a cikin ƴan yatsunsa da yasan Muhaseen ɗin ya yaɓa yi, itama dariyar tashi daban ta ke ba kamar ta sauran mutane ba.

Surutu abune da Saleem ya saba zama ya yiwa Muhaseen duda yasan ba tanka shi ya ke yi ba, amma aƙalla yasan yana saurarenshi kuma yana fahimtarshi sosai da sosai, sannan shi Saleem Allah ya yi shi cikin sahun mutane masu ɗan banzan surutu, baya iya zama bakinshi shiru ga shi da mitar tsiya, haka zai yi mitarshi ya gama amma ko Uhumm Muhaseen baya tofawa.

Yauwa kamar kullum ƙarfe takwas jerin gwanon motocinsu suka shiga yin tsere a saman titi, basu tsaya ba sai a STAR GOLD COMPANY, isar su babu jimawa aka gabatar da gagarumin sauyi, sauyin da ya gigita duniyar wasu, yayinda duniyar wasu ta cika fal da farinciki, an samu sauyin ma'aikata yayinda aka sallami wasu, wasu kuma aka ƙara musu matsayi, sannan kuma lokacin tashi bai yi ba aka sallami kowa tare da bayar da hutun kwana biyu, hutun da ya ɗarsa ayoyin tambaya a zukatan ma'aikatan.

Sai da kowa ya gaba ficewa bayan an rufe ko ina ya rage daga su sai masu gadi, sannan jerin motocinsu suka soma firfitowa a jere gwanin sha'awa su na fita daga ma'aikatar.

Runtse tafukan hannayensa ya yi yana jin ɗumin yatsunsa na ɗumama tsokar tafin hannunsa, lokaci ɗaya zuciyarshi ta sauya daga yanayin yanda ta ke dokawa, wani abu kamar tsutsa ya shiga bi ta ciki naman zuciyarshi yana kwaranya a jinin jikinshi a daidai sanda ƙwayar idansa ta yi tozali da ita, yanayin take burkin da driver ya yi da ƙarfi hayan ya saka sai da ya yo gaba sannan ya yo baya, kwata-kwata bai ji wannan ba gaba ɗaya hankalinsa na akanta.

Hannayenta duka biyun a ɗage sama yayinda ta dogara da babban ɗan yatsar ƙafarta, tsoro da firgici ya sanyata jin wani irin juyi, sai hakan ya bada salo me burgewa musamman da doguwar rigar rafae jikinta ta ɗage tare da buɗewa nan ta shiga yin juyi kamar fanka, a zahiro sai hakan ya yi kama da rawa irinta matan india, duda hakan bata gujewa abin da ta ke tsoro ba sai da ƙafarta ta gurɗe ta faɗa akan motar da ƙarfin gefen fuskarta ya daku da gaban motar nan take jini yayo tsalle daga bakinta, hakan ya yi daidai da fitowar Driver sa Saleem yayinda sauran securie suka firfito tare da zagaye wajen cikin shirin ko ta kwana.

Cike da ƙarfin hali ya ɗaga kanta bata tsaida ganinta ako ina ba sai a daidai saitin fiskarsa tada fito raɗau, yunƙurawa ta yi zata tashi amma sai wa ta azaba ta ziyarceta ba shiri ta komar da kanta.

Saleem ne ya soma kamota yana son ya tsaida ita amma sai ta gagara tsayuwa sai tangal-tangal ta ke yi, a ruɗe ya soma jera ma ta sannu yana kallon jinin da ke fita daga bakinta, ɗaga daga cikin motocin gabansu ya nufa da ita.

Ikon mallakar kanshi ne ya ƙwace daga gare shi, fararen idanuwanshi suka soma rikiɗewa su na sauya launi, yayinda ya kafe yatsun hannun Saleem da ke riƙe da ita, shi kanshi bai san abin da yake ji ba domin linzamin ikon mallakar karshi ya suɓuce daga gareshi.

Cike da amo me razanarwa gami da bada umarni a dake ya kira sunan Saleen bayan ya fita ya tsaya akan ƙafafuwansa.

"Sarki za'a wuce da ita hospital tana zubar da ji...."

Saleem bai ƙarasa faɗar abin da zai faɗa ba ganin kallon da Muhaseen ya yi ma shi ba sannan ya koma mota yabar ƙofar a buɗe.

Da sassarfa Saleem ya soma janta zuwa wajen motar ya shigar da ita gidan baya sannan ya koma mazauninya ya juyo da kanshi ta baya yana tambayarta ya jiki.

Gaba ɗaya sautin komi ya ɗauke mata lokacin da ta ji an ambaci kalmar Sarki, tana jin azaba me raɗaɗi amma hakan bai hanata buɗe idanuwanta ba ta kalleshi cikin yanar da ta baibaye idonta, daga kuma sanda ta ji an sake janta zuwa wani wajen daban sai ta soma yin yaƙi da nauyin da ke ƙoƙarin danne ta.....✍🏻

Ku yi following ɗina a arewapen dan samun damar karanta next chapter.

👇👇👇👇👇👇

https://www.arewapen.com/u/maryamstar248

MARYAM STAR

***

https://www.arewapen.com/u/maryamstar248

🌹𝙈𝙐𝙃𝘼𝙎𝙀𝙀𝙉🌹

(𝐿𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑧𝑢𝑐𝑖𝑦𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑘𝑢𝑛𝑐𝑖, 𝑟𝑎𝑦𝑢𝑤𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑘𝑎𝑙𝑢𝑏𝑎𝑙𝑒😔.)

𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀 𝘽𝙔

𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐.

💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍,𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪

✊ 𝙏𝙃𝙀 𝙎𝙃𝙄𝘿𝙊𝙍𝙄𝘼 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝙏𝙀𝘼𝙈🤝

***

𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙆

𝙎𝙀𝘼𝙎𝙊𝙉 𝙊𝙉𝙀