MUHASEEN

Chapter 13

by @maryamstar248

Addu'a abace da ta jima tana yi, musamman akan cikar burukanta, bayan ta yi addu'ar tana tsayuwa da yaƙini akan Allah zai amsata ko ba lokacin ba, ta tsayu akan komi daren daɗewa addu'arta zata karɓu.

Kamar dai yanzu da ta ke jin cewa babbar addu'ar da ta ɗauki tsayin lokaci tana yi tun bayan data mallaki hankalin kanta ta amsu, sai de kuma idanuwanta da take alfahari da su akoda yaushe, takanyi godiya ga Allah idan ta gansu a jikin madubi, sannan tana alfahari da lafiyar da Allah ya wadata idanuwanta da ita, ciwon ido cuta ce da iya saninta bata taɓa yin ta, sai de idonta na sauya launi lokaci bayan lokaci musamman idan ta shiga yanayi.

A yanzu da idanwanta suka zama shamaki wajen kallon cikar burinta, sai ta ji wani sanyi ya baibayeta nan take ta yi ƙasa da kanta idonta na cika da hawaye, ɗisar farin ruwa me sulki da launin jah a saman ƙafarshi ya saka tsigogin jikinshi mimmiƙewa suna matsewa tare da fitar da ruwan gumi, da kyar ya danne ajiyar zuciyar da ke son kwace ma shi, ya sake maida hankali wajen kallon gaban motar.

Hawaye ta ci gaba da saki ko zata samu nauyin da zuciyarta ta yi ya ragu, wataƙila idanuwanta ma daga yau sun daina, taɓe-taɓe ba halinta bane takanga abu ya burge ta amma bata fiye kai hannu da sunan ta taɓa ba, amma a yau a kuma yanzu sai ta ji tana so ta taɓa, badan komi ba sai dan tabbatarwa, bata tsaya shawara da kwanyarta ba ta biyewa zuciyarta ya aika abin da bata yi ba, yayin da alƙalin ƙaddara ya rubuta ƙaddaruwarsa tun kafin wanzuwarta a duniya.

Yam...yam...yam, tsigar jikinshi ya shiga mimmiƙewa, ya yinda wani ɗumi me shige da irin ɗumin da mutum ke kasancewa bayan saukar zazzaɓi daga jikinsa ya baibaye shi nan take.

A lokacin da ɗumin tattausan tafin hannunta ya sauka akan hannunsa, rintse ido ya yi da ƙarfi yana ƙoƙarin saita kanshi, kafin ya lalubo abin yi, ya sake tsinkayar ɗumin lallausan hannunta na yawo a hannunsa tana gaba tana baya da shi, da mugun gudu ya yi nasarar kwato kansa ya dawo hayyacinsa, ba tare da sanin abin da zai biyo baya ba ya saka nashi hannun tare da dakatar da ita, sai kawai ya tsinci kanshi da matse hannunta gam a cikin nashi hannun.

Bayan lokaci me tsayi yau shi Muhaseen ne riƙe da hannun wa ta, wa ta macce wacce sam baida alaƙa da ita ta kusa ko ta nesa, mu'amala da mata ba ɗabi'arsa bace hasalima ko wajen aiki bai fiye yin aiki da su ba, ba kuma dan babu su a companys ɗin shi ba, sai dan yana nesanta kansa da su saboda wani dalili na daban.

Ko da shine bai da lafiya bai fiye shiga asibiti ba, koda ta kama ya shiga to Saleem ne ke bayani akan abin da ke damunsa ko da kuwa ba hakan bane yakan yi shiru yana saurarensu baya cewa komi, shiyasa ya fi so akira ma shi Doctor har gida ya duba shi, amma yanzu bayan isarsu da kanshi ya ja hannunta daya matse a cikin na shi bai tsaya ko inaba sai a gaban kwararen Doctor wanda ake ji da shi a asibitin, sai ya tsinkayo muryashi na jawabi akan abin da ya faru, kuma ya yi tsayin daka har aka gyara mata buguwar da gefen kanta ya yi tare da yin dresing ɗin ƙananun raunukan da ta ji a gefen idonta.

Iya shirun da ta yi kawai bata ce ko kanzil ba tun bayan afkuwar lamarin, abin ya shiga zuciyarshi da wani abu, wani abu wanda ba zai fassara shi nan take ba tare da ya nutsu ya yi nazari ba.

Ko bayan daya tabbatar da komi ya tafi daidai, bai so ya tafi ya barta ba amma babu yanda zaya yi aiyukan da ke gabanshi kaɗai sun ishe shi, ga kiran gaugawa da aka yi ma shi daga Company na ƙirar ƙarafuna, hakan ya saka ya tafi yana jin kewar wani abu wanda ke tattare da ita.

Kallon gefe da gefe na unguwar ta su ta yi tana Allah-Allah akan wani ya leƙo ya ganta ba dan komi ba sai dan ya zame mata shaidar gani da ido idan ta je gida ta bayar da labarin aka ƙaryata ta.

Sai de bata samu kowa ba sai mutanen da ke hada-hadarsu a wajen hakan ya saka ta saɓi ledar da aka shaƙe mata da fruit da kuma magunguna ta yi lungun gidansu kamar zata kifa.

Kamar kullum yau ma tana zaune ita kaɗai tana sana'ar data sabarwa kanta wato tazbihi, ihun da Najla ta kwalla tare da ɗanewa jikinta ne ya zaburar da ita, a kiɗime ta soma faɗin.

"Innalillahi Najla mi ke faruwa ne, lafiya?."

Ta yi tambayar tana riƙe Najlar da kyau tare da raba idanuwanta a bakin ƙofa tana jiran ta ga shigowar abin da ya biyota.

Cikin shehseƙar murya Najla ta ce.

"Sarki,,,, Sarki Umma Sarki na gani a yau kuma a yanzu."

Ta yi maganar tana damƙar hannun Ummar da iya ƙarfinta gaba ɗaya ta ruɗe ta fita a hayyacinta.

Wani abu me ƙama da mashi ne ya caki zuciyar Umma, yayinda itama jikinta ya hau rawa ba gaira ba dalili, wani abu data daɗe da yiwa zuzzurfan rami ta bizne a can ƙasar zuciyarta ya shiga buɗewa da tsananin ƙarfi, sake damƙe Najla ta yi suka soma jijjiga atare.

"Ikon Me sama sai kallo, ke dai Najla baki gakiya da shirme da shashanci, yo shashanci mana idan ba shashanci ba minene hakan kike yi, kin zo kin ruɗa mata tana zamanta lafiya, Allah ya yaye ma ki wannan cutar, wataƙila Sarkin Aljannu ne ya ke wasa da hankalinki."

Ta faɗa ta na yin gaba ta barsu a nan, tallafar fuskar Najla Umma ta yi a cikin tafukan hannayenta, wasu hawaye na kwanciya a cikin idanuwanta cikin sarƙewar murya ta ce.

"Ma sha Allah, ina taya ki murna ƴata na cikar burinki da kikaga muradinki a yau, ina me adduar Allah ya amsa ya zama mijinki, Allah ya tabbatar da alkairinsa a tsakaninku."

Da ace Umma tasan cewar addu'ar da ta yi kamar tayiwa kanta ne, da bata yarda ta tsaya iya nan ba, da ta haɗa da kanta a ciki wataƙila hakan ya zama mukulin buɗe ƙofofin da suka jima a datse.

Kwanciya Najla ta yi a jikin Umma tare da ƙanƙameta tana jin yanda jikinta ke rawa har lokacin, tana jin kanta daban ga wani dunƙulallen farinciki daya dunƙule mata waje ɗaya a ƙasan zuciyarta.

A ranar zance da ta wuni bayar da labarinsa kenan, ko kulawa da ciwonta da ke mata zafi bata yi ba, illa sake maimaita labarin da ta ke yi ga du wanda ya shigo gidan, bakinta ko gajiya baya yi wajen bayar da labarin hasalima ko kalma ɗaya bata tsallakewa, sannan lokaci bayan lokaci tana kai hannunta a saitin hancinta ta shinshina ko zata ji mayen ƙarshin ya ragu, sai de yana nan daram ya kame a jikinta.

Tun tasowarta bata taɓa riskar rana me ɗumbin farinciki a gareta irin wannan ranar ba, saboda muhimmancin da ta bawa ranar ya saka ta nufi madafa ta samu tsinke ta saka a cikin wuta sai da ya yi zafi sosai sannan ta buɗe farar cinyarta ta rubuta date ɗin, sam bata ji zafin wutar ba sai ma buɗe wajen da ta ke yi ta kalla du bayan lokaci fuskarta ɗauke da murmushi me zurfi.

MUHASEEN

Tun zamanshi a kujerar da aka tanada don yin meeting ya kasa taɓuka komi, sai faman shan ruwan da aka aje a gabansa da ya ke lokaci zuwa lokaci, gaba ɗaya hankalinsa baya wajen yana can wani waje, wani waje wanda shi kanshi bai san ko ina ne ba, yayinda idonshi ke kallon lallausan hannunsa da ya nannaɗe hannun rigar izuwa sama, har lokacin yana jin ɗumin tafin hannunta me laushi na ratsa wajen yana bi ta jijiyon jikinsa yana isa har zuwa can cikin zuciyarsa.

Har aka gama dogon meeting ɗin bai ce komi ba daga ƙarshe sai Saleem ne ya tashi ya yi jawabi a madadinsa, daga nan kuma basu wuce ko ina ba sai wajen da aka gama loda kaya ana ƙirga kwantenonin da za'a dita da su daga company, nan ma bin mutanen wajen ya dinga yi da ido ba kuma dan hankalinsa na kansu ba, sai dan fuskar da ya ke gani kwance akan fuskokin mutanen wajen.....✍🏻

MARYAM STAR⭐ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪.

Follow the MARYAM UMAR HAUSA NOVELS BOOKS LIBRARY 📚📚 channel on WhatsApp: ***

🌹𝙈𝙐𝙃𝘼𝙎𝙀𝙀𝙉🌹

(𝐿𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑧𝑢𝑐𝑖𝑦𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑘𝑢𝑛𝑐𝑖, 𝑟𝑎𝑦𝑢𝑤𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑘𝑎𝑙𝑢𝑏𝑎𝑙𝑒😔.)

𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀 𝘽𝙔

𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐.

💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍,𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪

✊ 𝙏𝙃𝙀 𝙎𝙃𝙄𝘿𝙊𝙍𝙄𝘼 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝙏𝙀𝘼𝙈🤝

***

𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙆

𝙎𝙀𝘼𝙎𝙊𝙉 𝙊𝙉𝙀