MUHASEEN

Chapter 19

by @maryamstar248

Hawaye ne suka sulalo daga idanuwanta, sai ta damƙi hannun Umma da ɗan ƙarfi cikin muryar kuka ta ce.

"Umma,,,,,,,,Ummana."

Cike da tausaya mata Umma ta share mata hawayen da suka cika idanuwanta sannan ta ce.

"Na'am ƴata mi ya faru."

"Ummana dama kin ce in dinga neman zaɓin Allah ko?."

Ta yi maganar tana kallon fuskar Ummar ta cikin dishi-dishin hawayen da suka cika idanuwanta.

"Ƙwarai kuwa ana so a komi bawa zai yi ya nemi zaɓin Allah, domin kuwa shi ne kaɗai zai iya zaɓa ma shi abin da zai fi zama alkairi gare shi."

Kwantawa Najla ta yi akan kafaɗar Ummar sannan ta ce.

"To Umma dan Allah ki taya ni da addu'a Allah ya tabbatar da alkairi a rayuwata."

Sosai ta bawa Ummar tausayi sai ta shafi kanta da babu ɗan kwali sannan ta ce.

"In sha Allahu ƴata zan ƙara akan wacce nike yi miki akullum, amma faɗa min mike firgita ki a farci cikin ƴan kwanakinan?."

Ta yi tambayar amma a ƙasan ranta tana tsoro da fargabar tabbatar wani abu, wani abu wanda bata isa ta hana faruwar shi ba idon lokaci ya yi.

Sai da Najla ta ja hanci sannan ta ce.

"Daga shekaran jiya du sanda zan kwanta barci sai na yi mafarki da wasu mutane, suna tsorota ni sosai idan na farka sai inga kamar da gaske ina ganinsu, kuma ba ni kaɗai bace harda wannan Sar....."

Ko mi ta tuna sai kuma ta yi shiru bata ƙarasa ba.

Mummunar dokawa gaban Umma ya yi, yayin da tunaninta ya shallake komi ya isa a mafarkin da ta yi a dare shekaran jiya.

'Gudu ya ke iya ƙarfin sa ga jini tako ina yana zuba a jikin shi daga cikin manyan raunikan da aka ji ma shi, amma sai bai tsaya ba ya dage haiƙan yana gudun ba don ceton ran shi ba sai dan isa ga wani waje inda wata mata me kama da iya ke zaune a saman farin dutsi, yayin da wani yaro ke zaune yana kuka a nesa da ita, hankalin matar ne ya rabu gida biyu a tsakanin wannan me gudun yana son tunkaro ta da kuma wannan yaron da ke kuka har yana ƙoƙarin shiɗewa, da taga ba zata iya ceton su ita kaɗai ba sai kawai ta fashe da kuka me sauti, nan hankali wanda ke kukan ya dawo gareta da saurin shi ya taso tare da isa inda ta ke ya dafata, hakan ya yi daidai da isowar wancan wanda ke gudun wajenta, bai yi wata-wata ba ya faɗa jikinta ya ƙanƙame nan take numfashin shi ya ɗauke gaba ɗaya.'

Da sauri ta rintse idonta lokaci ɗaya jikinta na ɗaukar rawa, nan take ta soma jijjiga da ƙarfi idanuwanta na sauyawa daga haske zuwa launin ja, yayin da baƙar ƙwayar ciki ta soma ɓacewa, cikin ƙanƙanin lokaci ta fita daga kamaninta zuwa wata kamar, jikinta ya yi haske fayau kamar babu jini yayin da gashin kanta ya soma warwarewa daga kitson da aka yi mata, sai da ya warware tas sannan ya kwanta lub a gadon bayanta kafin ta ɓingire ta faɗi a wajen kamar matacciya.

Ba iya Najla da ke kusa da ita ba hatta da Uwale da su Jimmai sai da suka kiɗeme ganin abin da ke faruwa.

"Mun shiga uku mun lalace, shikenan matar mutane da mutu a gidan mu wayyo Allah."

Cewar Jummai data ɗora hannu aka ta shiga kurma ihu tana salati hankali a tashe.

Da sauri Najla ta yunƙura da niyyar ta taɓa jikin Ummar wacce ta faɗi a ƙasa, amma sai wani abu me kama da shokin ya kamata, da sauri ta janye hannunta tana zare ido sai kuma ta sake komawa da niyyar taɓa ta ɗin, wani ja da shokin ya yi mata bata san sanda ta faɗo daga kan gadon tana riƙe hanunta ba, nan take ta fashe da kuka tana kallo sai tin ummar da ke kwance a ƙasa.

"Innalillahi yau mu munga bala'i, ke Salamatu je ki kirawo Mamman ya zo ya ga abin da ke faruwa."

Babu ko kallabi Salamatu ta fice a guje dan zuwa kirawo Mamman.

Tsaye ya ke a gaban wani baro da aka shaƙe tab da kayan gwangwan suna ta tafka ciki, kamar daga sama ya hango Salamatu ta taho a guje, ɓata fuska ya yi a daidai sanda take gab da ƙarasowa wajen ya tare da ta faɗin.

"Ke dan Ubanki bana hana ki fitowa a haka ba, jibe ki kamar mahaukaci kai ko kallabi babu."

Cikin shesheƙar gudun da ta yi ta ce.

"Baba ka zo gida ba lafiya, Umma ce ta faɗi tanata wani abu na ban tsoro."

Salati ya rafka tare da kiran wani yaro ya ce da shi ya zo suyi ciniki zai je ya dawo.

A hanzarce ya bi bayan Salamatu sai zabga sauri ya ke kamar zai tashi sama, ga gaban shi da ke ta faɗuwa.

Yanda Salamatu ta barta haka ta isketa yashe a ƙasa, isowar Mamman babu jimawa ko gama shiga ɗakin bai yi ba kan shi ya sara da wani irin ƙarfi nan take ya durƙushe a ƙasa sannan cikin wata iriyar murya wacce sam bata yi kama da tashi ba aka soma faɗin.

"Allah ya ja zamanin Gimbiya kuma Sarauniya, takawar ki lafiya giwar Amale, ambuga da ke am barki kece a gaba kece a baya maƙiyanki fadawanki."

Haka aka ci gaba da jeranto kirari ga Umma da ke kwance har lokacin, yayin da Mamman ke gurfane kan shi a ƙasa.

Gaba ɗaya sai mutanen ɗakin suka sha jinin jikin su, domin dai sun fara fahimtar abin da ke faruwa da alama Umma nada iskokai kuma sune suka tashi yanzu haka.

Fitsari ne kawai ya rage Uwale taba yi ba dan tana da mugun tsoron Aljannu, bugu da ƙari kuma wata ƙara da suka soma jiyowa na tashi daga saman ɗakin busa ce irinta algaita da kuma ƙarar takun dawakai harma da haniniyarsu, gaba ɗaya ƙarar kamar a cikin ɗakin ake yin ta, sai da suka toshe kunnuwansu da sautin ke shiga sosai har yana ƙoƙarin saka musu ciwon kai.

BAYAN MINTUNA ARBA'IN.

Sannu a hankula Umma ta shiga buɗe idanuwanta a hankula, yayin da haske ranar da ya soma shigowa ɗakin ya yi jagora wajen sukar idanuwanta, da sauri ta sake kulle su tana jin yanda hasken ya shiga cikin su kai tsaye, mitsa ƙafarta ta soma yi wacce ta ji kamar an kunce ta daga ɗaurin gwaggwaɓar sarƙa, sai kuma ta ɗaga hannunta da shima ya yi mata nauyi sosai, tambayar zuciyarta ta soma yi.

'Shin mike faruwa da ita.'

Sannan ta yunƙura tare da tashi zaune ɗangwara gwas, ware fararen idanuwanta ta yi tare da bin mutanen da suka baibayeta da kallo irinna, 'Mi kuke yi a nan.'

Bama kallon da suke yi mata bane abin ɗaure kai sannun da suke jeranta mata gamu da fatan sauƙi shi yafi komi dagula lissafinta.

Tana so ta buɗe baki ta yi magana amma ƙarfin jini irinna Sarauta da ke yawo a sassan jiki da jijiyoyinta ha hana faruwar hakan, dafe kanta ta yi da ƙarfi kafin ta ce cikin rarrabewar harshe.

"Mi nike yi anan, su waye ku."

Tsit masarrafar tunanin Najla wacce ke durƙushe a gaban Ummar ta tsaya cak da aiki lokacin da Ummar ta jefo wannan tambayar, ba wai bata san Ummar ba ɗaya daga cikin ahalin gidan ba ce, sarai ta san da hakan kuma bata manta ba sai de a yanayin yanda Ummar ta yi maganar sai ta ruɗar da ita, sau uku tana buɗe baki zata yi magana amma kuma sai hakan ya gagara, ga wani kwarjinin Ummar da ya cika lakin gaba ɗaya.

"Ummana."

Najla ta ƙwato maganar daga can ƙasan numfashin ta dake barazanar ɗaukewa a ko wanne lokaci.

Kalmar Umma kalma ce da tasan ana amfani da ita wajen kiran wacce ta taka matsayin uwa, ko kuma aka raɗa mata wannan sunan, sai de a iya sanin ta sam batada wanda ya taɓa koda kwatanta kiranta da wannan sunan ba, a yanzu kuma da aka kirata da sunan sai ta ji wani abu me nauyi ya faɗo daga zuciyarta ya shiga bajewa a ƙirjinta, yayin da kanta ya sara da ƙarfin gaske nan take shuɗaɗun abubuwa suka shifa dawowa a kwanyar ta daki-daki.

MAFARIN ƘADDARA.

Komi ya faru ne a tsakiyyar daren ranar takata, inda Sarauniya Aishatu ta farka daga barcin da ya ɗauke ba tare data shiryawa hakan ba, idan ba zata manta ba tana kwance ne asaman gadonta na alfarma yayinda tagwayen yaranta ke shimfiɗe a kusa da su, ba zata iya tuna abin da ya sakata mancewa da azkar da kuma alwalar da take yi duk daren duniya musamman idan zata kwanta barci ba, kawai de taji kasala na baibaye ta yayin da Jakadiya ta kawo mata yaranta tagwayen da suka yi marice a fadar Sarki, kafin barci ya ɗauke ta ta kasance cikin yi musu wasanni kamar yanda ta sabar musu duk farkon dare kafin suyi barci, kuma zata tuna yanda ta mulke jikunan su da ruwan addu'ar da aka tanada domin su.

Ta farka a furgice cikin barcin daya kwasheta yayin da ta soma ji ana kiran sunanta ta ko wace kusurwa da ke ɗaƙin, a gigice ta farka cike da razani ta soma juye-juye tana neman wanda ke kiran nata, sai de kuma muryoyi ne mabanbantan data gasa tantancewa, ga wani abu me kama da magana da ke janta zuwa hanyar fita, daga ita sai rigar barcin jikinta ta soma takawa cikin hanzari tana yin hanyar fita daga ɗakin, sai da ta gama ficewa daga manyan falukan gidan ta fita cikin tsakar gida sannan ta kai dubanta gabas da yamma kudu da arewa amma ta rasa hanyar da zata bi ta fice zuwa wajen da ake kiranta, kiran da idan ta ji shi take jin kwanyarta na tafarfasa tana fita daga hayyacinta, idonta ne ya sauka akan dogon ginin katangar wajen, bata yi wata-wata ba ta nufi wajen gaban-gaban ta ɗane katangar tare da doma haurawa har ta samu ta haye da kyar, dira ta yi a ƙasa cikin rashin sa'a sai ta dira akan ƙafarta ta haggu nan ta amsa da tsananin azaba, amma jin ana sake jiranta ya saka ta miƙe tana ɗingisa ƙafar ta soma takawa a wahale, juyawa ta yi tare da kallon bayan ginin masarautar sai kawai taga wuta me tartsatsi na tashi da sauri ta kawar da kanta tare da cigaba da tafiya.

Ba zata iya misilta tsayin lokacin data kwashe tana tafiya ba, sai de zata iya ƙiyasta baƙar azabar da ta ke cikin sha a tafiyar da take yi, gazawa ta risketa ne a daidai lokacin da sautin wannan muryar ta ɗauke gaba ɗaya, nan take ta fice a hayyacinta tare da durƙushewa a ƙasan wajen da bata damu da ko ina bane, nan take ta baje tana dakin numfarfashi, tana iya ganin hasken da ke hasketa tun daga can nesa ta cikin idanuwanta da suka yi biji-biji, kuma tana jin sanda wani abu me ƙara ya ja ya tsaya a kusa da ita, abin da bata tantance ba shine, shin motar ta bi ta kanta koko.?.....✍🏻

ALHAMDULILLAH MUNA GAB DA KAMMALA FREE PAGE ZAMU SHIGA PAID PAGES KU GARZAYA KU BIYA KUƊAƊEN KU DOMIN SAMUN DAMAR KARANTA WANNAN LABARIN TUN DAGA FARKO HAR ƘARSHE.

MARYAM STAR⭐⭐ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS

Follow this link to join my WhatsApp group: ***

🌹𝙈𝙐𝙃𝘼𝙎𝙀𝙀𝙉🌹

(𝐿𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑧𝑢𝑐𝑖𝑦𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑘𝑢𝑛𝑐𝑖, 𝑟𝑎𝑦𝑢𝑤𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑘𝑎𝑙𝑢𝑏𝑎𝑙𝑒😔.)

𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀 𝘽𝙔

𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐.

💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍,𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪

✊ 𝙏𝙃𝙀 𝙎𝙃𝙄𝘿𝙊𝙍𝙄𝘼 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝙏𝙀𝘼𝙈🤝

***

𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙆

𝙎𝙀𝘼𝙎𝙊𝙉 𝙊𝙉𝙀