MUHASEEN

Chapter 20

by @maryamstar248

Last page

Tsugunnawa a gabanta matuƙin motar ya yi tare da soma faɗin.

"Baiwar Allah lafiyarki ƙalau kuwa, Innalillahi wa'inna ilaihi raju'u."

Sai kuma ya tashi tsaye tare da soma zagaye wajen yana dube-dube ko zai iya ganin ɗan uwanta wataƙila hatsari suka yi a mota, amma har ya ƙaraci dube-duben shi bai ga kowa ba kuma bai ga wata alama da ke nuni da anyi hatsari akan hanyar ba.

Dama haka ya ke, ya yi sabo da ganin tashin hankula iri-iri sannan shi mutum ne me tsananin tausayi baya tsoro ko shakkar za'a iya cutar da shi garin taimako, dan haka sai ya koma wajen ta ya ciciɓe ta ya saka a mota ya bawa motar wuta cike da warewa yaci gaba da tuƙi, kasancewar lokacin dare ne sai ya samu damar sharara gudu yanda ya ke so yana yi yana hangen ta ganin bata motsa ba amma kuma tana numfashi a wahalce.

Sai gab da subahi suka ida cikin garin Legos kai tsaye ya wuce wata unguwa wacce mutane keta hada-hadarsu kamar rama, a daidai wani ɗan surƙuƙin gida ya ci burki tare da matsa horn da ƙarfi, nan take wata mata ita da wasu yara suka firfito daga ciki fuskokinsu cike da fara'a suka shiga yi ma shi barka da hanya, sai de ganin yanayin fuskar shi da alamu damuwa da kuma buɗe bayan ragwargwaɓaɓɓiyar motar da ya yi wata mata ta bayyana a kwance ya saka su kallon juna da alamun tambaya.

"Uwale zo ku kama ku shiga da ita ciki."

Ya faɗa yana gudawa daga wajen motar, babu musu Uwale da waɗanan ƴan matan suka kama ta zuwa ciki, sai de kuma yanzu numfashinta na fita da wani irin sauti me kamar nishi irinna azaba ko fita a hayyaci, basu kula da sun kama ƙafarta me ciwo ba sai da suka kai ta cikin gidan suka shimfiɗe hasken aci balbal ya haske ta a nanne wata budurwa ta saki ƙara ganin yanda ƙafar ta haye ta kumbura suntum.

"Innalillahi Kawu Mamman kalli yanda ƙafarta ta ji ciwo."

Da ya matsa kusa da ita sosai nan take ya hango gocewar da ƙashin ƙafarta ya yi, bai kuma yi jinkiri ba ya dire kofin ruwan da aka bashi ya soma tattaɓa ƙafar.

"Uwale kawo min jakar aikina."

Da hanzari wacce ya kira da Uwale ta tashi tare da shiga wani ɗaki babu jimawa ta fito hannunta ɗauke da jakar, a ladabce ta miƙa ma shi jakar.

Babu ɓata lokaci ya soma gyara mata ƙafar, in banda nishi babu abin da take yi sai kuma ruwan hawaye da ke zirara daga cikin idanuwanta.

WASHE GARI

A hankali ta soma buɗe idanuwanta har ta yi nasarar buɗe su gaba ɗaya ta shiga yawo da su a ɗakin tana kallon wasu baƙin abubuwa da sam bata san da su ba, kuma har mutanen gidan suka shiga tare da jiranta mata sannu da jiki, bata amsa suba sai kallon rashin sani da ta ke bin su da shi, haka suka zagaye ta suna taɓa fira a tsakaninsu ita dai sai aikin bin su da ido da take yi tana hango tarin banbancin da ke tsakanin ta da su duk kuwa data mance wacece ita a lokaci.

Ta share tsayin kwanaki bata magana, kuma rashin maganarta sosai ya damu mutanen gida, sai de kuma suna bata kulawar data dace, idan lokacin sallah yayi suyi mata alwala suna yawan ɗorata a bayi tayi buƙatunta sam basu nuna gajiyawa da ita, su bata abinci Uwale tayi mata wanka, a hankali ta soma sakin jiki da su saboda basu da matsala ko kaɗan, ta soma sakin jiki da su a sanda aka yi wani taron biki duda ba wani taro sosai aka yi ba iyaka makwota na kusa ne suka leƙo musu aka aurar da ɗaya daga cikin ƴan matan gidan me suna Huwaila, kuma har lokacin basu buƙaci sanin ko ita wacece.

Rayuwa ta tafi da nisa inda har ta shekare a gidan a sannan aka aurar da waccan ɗaya itama gida ya rage daga ita sai Uwale da kuma Mamman, suna zamansu lafiya cike da girmama juna, lokaci bayan lokaci Mamman kan kawo baƙi wasu ƴan gudun hijira wasu kuma marayu ana kawo wasu ana kwashe wasu gidan ya zama na jama'a baya ƙyashin taimakawa mutane da gumin shi, sai da suka shafe shekaru goma sha biyu a tare da ita, kuma har lokacin basu san ita ɗin wacece ba, kuma basu nuna gazawa wajen kulawa da ita ba, a kuma lokacinne Mamman ya kawo wata yarinya wcce b zata fi shekara biyu da haihuwa ba, yarinyar tana da kyau me ɗaukar hankali sai de kuma daga ganinta a cikin wahalar rayuwa ta tashi, dan gaba ɗayanta a firgice ta ke, babu wanda ta yarda da shi a gidan sai ita kaɗai kuma da buɗar bakinta sai kiranta ta yi da sunan Umma yayinda wani abu me kama da ƙaunar uwa da ɗa ta ratsa zuciyarta sannan ta gamsu kuma ta amince da suna Umma ɗari bisa ɗari, yayinda itama ta kira yarinyar da suna Najla kuma ba zata iya faɗar dalilinta na saka mata sunan ba, daga ranar Umma ta soma rainon Najla cikin aminci cike da so da shaƙuwa, sosai hankali Kawu Mamman ya sake ƙwanciya ganin ta soma walwala kuma ta saki jikinta da su.

Umma macece me tsananin ibada duk da ta mance abubuwa masu yawa da suka shafi rayuwarta ta baya, sai de bata manta komi daya danganci addini ba, kuma tun zuwan ta gidan sai ta ƙidaya fitar da ta yi daga cikinshi.

CIGABAN LABARI

Wasu zafafan hawaye ne suka silalo a kuncin Umma yayin da ta buɗe bakinta cikin karkarwar harshe ta furta.

"Na tuna ko wacece ni, na tuna asalina na tuna komi daya dangance ni, kuma ban mance zaman da nayi tare da ku ba tsayin shekaru ashirin da tara."

Kallon juna mutanen ɗakin suka yi sannan Mamman ya furta.

"To Alhamdulillahi na yi matuƙar murna da kika dawo hayyacinki kika kuma tuna ko wacece ke, bazan taɓa manta ranar da na tsince ki ba a bakin titi yashe a ƙasa cikin mawuyacin hali na ɗauko ki na kawo ki nan garin Legos sannan na haɗa ki da matata, a tsayin zaman da muka yi da ke cikin ganganci bamu taɓa cutar da ke ba, haka zalika kema baki taɓa koda kwatanta cutar da mu ba, idan babu damuwa zamu so mu ji asalin labarin ki da kuma asalin ko dan mu sada ki da danginki cikin aminci."

Mamman ya faɗa fuskar shi na washewa da annuri, har ƙasan ran shi ya ji daɗin dawowar Umma hayyacinta sosai matar ke burge shi saboda yanda bata ɗauki duniya a bakin komi ba.

Wasu hawayenne suka sake silalowa a fuskar Umma yayinda ta saka idanuwanta a cikinna Mamman tana karanto kyawun zuciyar shi, haƙiƙa ita ɗin shaida ce akan kyawawan ɗabi'un da yake da su, idan da za'a bincika a faɗin duniya ba lallai a samu masu irin zuciyarsa da yawa ba.

Goge hawayenta ta yi sannan ta ce.

"Yanzu kuwa zaka ji ko wacece ni Kawun Najla."

Kusan kowa da ke ɗakin sai da ya ɗan murmusa domin faɗar Kawun Najla da ta yi ya hasko musu irib dambarwar da suke kwasa a tsakaninsu.

Miƙe ƙafafuwanta ta yi tare da soma magana cike da nutsuwa.

"Sunan Gimbiya kuma Saraunita Aishatu, ni ƴa ce ga Sarkin Katsina Kabir Umar, na yi aure a masarautar garin Kano inda na auri aminin mahaifina me martaba Sarkin Kano me suna Muhusin Salis wanda a lokacin shi ke akaragar mulki, ba ni bace babba a cikin matansa ba amma ni ce na zama tauraruwa a cikin matansa duda kasancewata yarinya a cikinsu.

Mai martaba Muhusin Salis adalin Sarki ne wanda al'umarsa ke farinciki da mulkinsa kasancewarsa me adalci ga al'umma, Allah ya jarabce shi da rashin samun haihuwa tun daga kan matansa na aure har ƙwarƙwarorin da aka ba shi babu wacce ta taɓa haihuwa, hakan na matuƙar damun shi, shi yasa lokaci bayan lokaci yake shiryawa ya zo har Katsina wajen mahaifina domin ya raka shi zuwa duba kafiyarsa da suke zuwa a sirrance ba tare da sanin kowa ba, sai de abin da ke ɗaure musu kai bai wuce yanda duk inda suka je ake tabbatar musu da yana da cikakkiyar kafiyar da zai haihu lokacine kawai bai yi ba.

Babban dalilin sarki Muhusin na neman haihuwa ido rufe bai wuce yanda yake gudun subucewar mulki daga gidan su ba, domin dai ta tabbata muddin bai da kwai a duniya to sarauta zata juya gidanau waziri me ci a lokacin, ba dan wata manufa yake gudun juyawar mulkin ba sai dan tsoron irin baƙin mulkin zaluncin da za'a gabatar muddin ahalin Waziri suka amshi sarautar.

Ko ba dan hawa karagar mulki ba ya kasance mutum me tsananin son ƴaƴa, yara ba ɗaya daga cikin abubuwan da ke bala'in burge shi, yana aje sarautar shi a gefe idan yaga yara ya zauna har ya yi wasa da su cike da soyayya.

Matar Sarki Muhsin ta farko ita ce Sarauniya Zainaba itama babbar ƴar sarkin Gwanbe ce ita ce mace ta farko da Sarki Muhusin ya soma aura tun iyayensa na da rayuwa, ita ɗin macece me ji da mulki haɗe da izza, sam bata ɗaukar kuskure ko ya yake tana da zafi sosai sannan bata yafiya, itama ta jima tana yawon neman haihuwa domin ta zama ita ce mace ɗaya da zata rayu a gidan Sarki sannan ta cika shi da tarin zuri'ar ta yanda mulki zai dawwama a tsatsonta, sai de kuma tana tata Allah na tashi, bayan kwashe shekaru biyu ko ɓatan wata bata taɓa yi ba hakan ya saka a lokacin Marigayi tsohon Sarki ya sake nemawa Me martaba auren ɗiyar wani abokin shi, shima Sarki ne a lokacin ya nada ƴaƴa mata su biyar, da Marigayi me martaba ya nemi iri a wajensa sai ya bada ƴar shi me suna Sarauniya Husna.

Sarauniya Husna ita ce ta zama mace ta biyu a wajen Sarki Muhusin, inda tun tana amarya bayan tarewarta suka soma gaba da junansu ita da Gimbiya Zainaba, inda ko waccensu ke ganin tana sama da ƴar uwarta, sam basa ga maciji kullum cikin jifar junansu suke da shairi.

Bayan kwashe shekara biyu da aure Sarauniya Husna itama shiru shine fa aka sake aurawa Me martaba aure da Aishatu.

Duk da kasancewar bana son shi a lokacin umarnin mahaifina na bi amma bai hana na yi ma shi biyaya bakin iyawata ba, a tsarina ni sam bana son sarauta dan na san shairinta ya fi alkairinta yawa hakan ya saka lokacin da ina karatu na haɗu da wani saurayi muka fara soyayya, koda maganar aurena ta taso haƙuri kawai na bashi domin bazan iya tsallake maganar mahaifina ba, dukda na shiga damuwa a farko amma da Fulani mahaifiyata ta ja ni a jiki tare da nasiha me ratsa jiki sai na fawwalawa Allah lamurana na rungumi ƙaddarata.

Ban jima da tarewa a gidan Sarkin Kano Muhusin Salis ba na gama kanainaye zuciyar shi, yayin da na yi baya-baya da matan shi da sauran munafukai irinna gidan sarauta, na maida hankalina wajen kulawa da mijina tare da soma renon soyayyar shi da ta soma ɗarsuwa a cikin zuciyata.

In taice muku labari cikin ƙanƙanin lokaci na zama Giwar Sarki kuma shalelen shi, domin kuwa na amsa sunana Sarauniya kuma ƴar sarki bayan watanni kaɗan da soma zuwa turaka Allah ya azurta ni da samun juna biyu, juna biyun daya zama makulin buɗe ƙofofin ƙaddarar da suka jima a kulle suna jiran ranar buɗewarsu.

Ba sai na ɓata baki wajen sanar da ku irin murna da farincikin da marsarauta ta yi a lokacin ba, yayin da aka shiga yin sadaka gami da manyan kyaututtuka tare da ƴantar da bayi, gaba ɗaya Me martaba da sauran muƙarrabansa masoya na kusa dana nesa duk sai da suka nuna farinciki da jin daɗinsu, yayinda kuma aka haskawa masu mugun nufi da mubafukai fitila suka gane zahirin abin da ke wakana, ba sai na tsaya fayyace muku irin ƙiyayyar da sauran matan sarki suke nuna min a fili ba, ɓullowar wannan cikin kuma ya sake haska musu wata hanya wacce basu hanga ba daga farko, nan suka tattare komi suka aje suka juyo kai na.

Kwatsam a rana tsaka ciwo ya turnuƙe ni bayan cikina ya soma ƙwaru, ciwon da aka gaza gane gaba bare bayan sa, ganin zan rasa rayuwata Me martaba ya bada umarnin a cire cikin tun da shine matsalar, dukda ya shiga matsananciyar damuwa amma kuma yayi farinciki a ƙalla ya ji ance ya matar shi ta taɓa samun ciki amma ya lalace.

Sai da nasha doguwar jinya har sai da aka koma da ni can masarautar gida domin samun lafiya, na ɗauki tsayin lokaci sannan na dawo daidai daga jinya, nan Me martaba sarkin Katsina ya sake bani addu'o'in tsari sannan ya ƙara min hadimai mata masu gaskiya da amana, cikin mutunci aka dawo da ni masarautar Kano inda acanma Me martaba Sarki ya saka aka shirya gagarumar walima domin tarbata, anyi budiri sosai an ci an sha anyi wasanin gargajiya da al'adun hausa abi sai wanda ya gani sosai aka nishaɗantu.

Yayin da hakan ya ƙara ruruta wutar tsana gami da ƙiyayyata me muni a idanuwan sauran matan Me martaba, musamman Gimbiya Zainaba wacce ko haɗuwa na yi da ita a turaka ko fadar cikin gida gabana ke yankewa yana faɗuwa, kallon kykakyawar fuskarta kawai na jefa ni a ɗimuwa bare kuma aje ga batun ta yi min magana cikin kissar da ta saba amfani da ita, nan da nan nike fita a hayyacina tsoro ya cika duniyata.

A ranar da aka raka ni turaka bayan dawowata a ranar na tantance irin girman da soyayya ta tayi a zuciyar Me martaba, domin dai ni kaina sai da na fayyace irin yanda nike matuƙar ƙaunarsa, daga ranar muka sake curewa muka zama abu ɗaya muka shiga farantawa junanmu duk sanda kwanana ya zagayo, har ƴan fada sai da suka tantance sanda nike da Me gida, domin kuwa ya dinga shige da fice kenan ko zaman kirki baya yi a fada, yakan leƙa cikin gida sau babu adadi.

Yayin da a gefe ƴan gulma da munafukai suka shaidawa sauran Matan Sarki abin da ke faruwa, nan take suka sake ɗaura lamara suka yi shirin yaƙin sunƙuru a kaina.

Bayan shekara ɗaya da lalacewar cikina Allah ya sake azurta ni da samun wani cikin, sai de a lokacin ban bar wata alama ko ɗaya da zata iya bayyana cikin jikina ba, hatta da Me martaba sai da na ɓoyewa ina da juna biyu, duk kuwa da yanda yake liƙe da ni, hatta da turaka sai da na nemi alfarma akan yayi min lamani ina fama da lalura, amma ban amice ya sanarda kowa ba dan sirrina ne, da yake yana da fahimta sosai kuma yana bawa komi da ya dangace ni muhimmanci, sai bai sake ɗaga maganar ba, duk kuwa da yana cutuwa da rashina, daga baya har kwarkwarori aka tanada ma shi waɗanda zasu taimakawa sauran matan shi ɗaukar ɗawainiyar shi, yayin da Gimbiya Zainaba da Sarauniya Husna suka shiga yi min dariyar wai amfanina ya ƙare an gama ɗaukina yanzu a turaka gashi nan yanzu har da ƙwarƙwara Me martaba yake da, ko kaɗan ban damu ba dan nasan ina da dalilina na yin hakan.

Kwatsam a waya rana ina kulle a can cikin ƙuryar ɗakina bayan na bada umarnin kar wacce ta koda leƙo ƙofar ɗakin bare kuma ta shiga, ko minene a jira ni ina zuwa, cire alkyabar jikina na yi tare da ɗage ƙatuwar rigata data taimaka sosai wajen ɓoye girman da cikina ya soma yi, ɗaura hannuwa na na yi duka biyu akan cikina tare da lumshe ido ina shafar cikin, farinciki gami da ɗaukin ranar da zan haife shi na baibaye ni domin ina matuƙar son naga na haihu da Me martaba, na shagala sosai da abin da nike yi ban ankare ba kuma bansan sanda wani ya shigo ɗakin ba abin da na sani na riga da na kulle ko ina kuma na rufe tagogi, amma sai na tsinci muryar mutum a kuda da ni, a kiɗeme na juya ina firfito da duka girman idanuwana cike da razani.

Kallon cikin kwayar idon shi da tayi jazur na yi tare da soma ja baya ina girgiza kai kuka na kwace min me.

Bina ya soma yi duk inda na yi da haka har muka dangane da jikin bango sai kawai na rintse idanuwa ina fashewa da kuka, durƙusawa ya yi akan gwuiwoyinsa tare da daka hannayensa ya tallabe cikin, sai kawai shima ya fashe da kukan muka dinga yi a tare babu me rarrashin ɗan uwansa, ni ina kuka akan hukunci da zai yi min na ɓoye ma shi wannan al'amari me girma yayin da shi kuma ya ke kukan farinciki ganin wani cikin a jikina.

Bayan mun tsagaita da kukanne ya tallabe ni a hankali ya zaunar abakin gado sannan cikin laushin murya ya ce da ni.

"Tauraruwata tun yaushe kike ɓoye min wannan lamarin, watansa nawa yanzu.?

Ya faɗa idon shi a kaina yana jiran ya ji abin da za faɗa.

"Allah ya taimake ka ka gafarce ni ban yi hakan da wata manufa ba na yi hakanne dan kawarda idon masharanta, kuma ina da burin sanar da kai amma kuma wasu abubuwa da suke faruwa da ni ya saka na kasa sanar maka."

A ɗimauce ya soma tambayata abubuwanda ke faruwa, nu kuma ban ɓoye masa ba na sanar da shi.

"Allah ya taimake ka haƙiƙa ina fuskantar barazana akan wannan cikin, ga shi ina yawan yin mugayen mafarkai da kuma firgita, abin yana tsorata ni sosai shi yasa na kasa sanar da kai banaso ka sake ƙwallafa ranka akan ciki kuma daga baya muzo shima mu rasa shi."

"Tabbas kin aikata laifi me girma na ɓoye min abin da ke faruwa da ke, kuma tabbas kin cancanci hukunci saboda haka na yanke hukunci za ki je can Masarautar Katsina ki raini cikin a can, zaki tafi da kyautar dawakai biyar shanu goma tare da ɗanyar gorl wannan masoni ne na hukuncin gagarumin laifin da kika aikata."

Faɗawa jikin shi na yi tare da jeranto godiya sinƙi-sinƙi farinciki fal raina.

Kamar yanda ya faɗa hakan ce ta faru, kai tsaye a washe gari aka tashi da labarin zuwana Katsina, bayan na yu sallama na tafi ne labarin ina da shigar ciki ya baibaye Masarauta, labarin daya ɗimauta zukatan munafukai da kuma azzalumai, daga ciki akwai babbar azzaluma wacce sam babu Allah a ranta wato Gimbiya Zainaba, idan ana neman ƴan tawagar shailan na kurkusa to a sakata a sahun farko, domin zaluncinta na shallake gaban kwatance.

Daga ranar da labarin ya risketa bata sake barci cikin salama ba, inda ta dinga shiga tana fita wajen ganin ta kassara min rayuwa, a ɗa can tana zuwarmin a mafarki amma a ɓoye, amma a yanzu a zahiri nike ganinta kuma a siffar ban tsoro ga shi yanzu tsoratar da ni da ake yi abin ya ninka na baya, dan ma dai na duƙufa da addu'a sannan a gidana kullum cikin taya ni suke, takanas ake dafa abinci sutura harma da kuɗaɗe aka dinga sadaka da niyyar Allah ya kare ni da abin da ke cikina.

Cikin ikon Ubangiji mabuwayi me rahama da jin ƙan bayinsa a ranar wata juma'a bayan cikina ya shiga watan haihuwa, kuma a ranar na samu baƙuncin Me martaba da ke zuwa duba ni duk ƙarshen mako, muna zaune muna gaisawa ciwo ya ci ƙarfina, dama dauriya kawai nike yi, nan take aka yi asibitin masarautarmu da ni.

Mutane ko ta ina antaru anata addu'ar Allah ya sauke ni lafiya, yayinda na kasance tare da Me martaba Sarki a ɗakin haihuwa inda kusan a tare muke yin gumurzun ni da shi.

Bayan awanni huɗu ƙwarara Allah ya sauke ni lafiya, bayan na haifi santalelen yaro namiji da ƴan mintuwa wata naƙudar ta sake taso min gadan-gadan ba'a rufe mintuna a shirin ba ana sake direwa Me martaba wani yaron.

Bazan iya misilta muku murna da farincikin da garuruwa guda biyu suke ciki ba, Me martaba kuwa ba'a magana ko gyara yaran ba'a gama yi ba ya ɗauke su cikin jini ya rungume yana kukan farin ciki tare da jeranta kirari da godiya ga Allah."

Nisawa Umma ta yi tare da kallon fuskar Mamman da ta sauya da wani yanayi me kama da al'ajabi, sai kuma ta karkata kanta zuwa wajen da Najla wacce ta yi mutuwar zaune ta ke sai ta share hawayen idonta sannan ta janyo hannun Najla zuwa kuda da ita, Najla wacce gaba ɗaya tasha jinin jikinta lokacin da Umma ta janyo ta sai ta lumshe idon ta wasu hawaye na tsinke mata.

Ɗaura kanta Umma ta yi a saman cinyarta tare da shaga kanta sannan ta ci gaba daga inda ta tsaya.

"Bayan na farfaɗo ya dawo hayyacina na riski lafiyayyun kyawawan tagwayen yarana, waɗanda suka saka ni zubarda hawaye ina godiya ga Allah da yayi nufin zuwansu duniya duk da irin ƙalubalen gami da tsoron dana shiga lokacin da nike ɗauke da su a cikina.

Matsowa Me martaba ya yi tare da ɗaga min gadon na ɗan yi sama, sannan ya ɗauko yaran gaba ɗayansu ya saka min a gefe da gefe na, fuskar shi ƙunshe da yalwatacciyar fara'a.

Lokacin da ɗumin su ya ratsa ni sai da na lumshe idanuwana sannan na ɗaura idona akan ɗaya daga cikin yara.

Idon shi a buɗe tar yana ɗan kyaftasu yana kallon fuskar Me martaba, nima kallon Me martabar na yi kamar zan yi magana sai ya riga ni da faɗin.

"Hhhhh wannan ai shine Magaji, domin tun zuwan shi duniya ya fara sanin mahaifi sa, bara ki gani in kauce zai rufe idon shi ne."

Kamar wasa ya kauce zuwa ƙasa sai ga yaron ya yamutse fuska gami da maida idon shi ya rufe, dariya muka yi gaba ɗayanmu mutanen da ke cikin ɗakin muna al'ajabin wannan yaro, Me martaba na ɗagowa yaron ya sake buɗe idon shi.

Kwanana ɗaya a asibiti aka sallame ni domin ina cikin ƙoshi kafiya ni da yarana, kwana ɗaya na ƙara a Katsina muka tattara muka koma Masarauta dan Me martaba ya matsa akan mu koma, sosai aka haɗa shagali wajen tarbarmu, a ranar na sake gasgata irin soyayyar da Me martaba ke yi min, nan aka dinga tururuwa dangi da ƴan uwa harma da sauran manya ana zuwa ganin yara, kuma duk wanda ya zo ba zai zo hannu biyu ba da gagarumar kyautar da za'a yiwa yaran, tun zuwan su duniya Me martaba yayi musu huɗuba da suna Hassan da Husaini, sai de an ɓoye sunan aka saka musu inkiya Muhaseen da Suhail, haihuwar yarannan ya sake buɗe min ƙofofin arziƙi, yayinda nima ba'a barni a baya ba wajen samun manyan kyaututtuka daga jama'a na tayani murna.

A ranar suna kuwa shagalin da aka sha ba zai misaltuba, dan kuwa anci uban nera a ranar, kowa da ke garin Kano sai da yasan da ansamu ƙaruwar yara a gidan Me martaba sarki Muhusin Salis.

Bayan anyi taron suna ni da sauran dangina muka yi zaman ƙirga abin da na samu, sai da na girgiza lokacin da aka lissafa min miloyoyin dana samu, da kuma wanda yarana suka samu, iya tsabar kuɗaɗe kenan banda gonaki da kuma shanaye da raƙumma, harma da kaji na hausa da akuyoyi, ji nayi lissafin yafi ƙarfin kaina dan haka sai na kirayi Me martaba ya zo, nace zan raba komi biyu zan ba shi rabi, ni da yarana sai mu ɗauki sauran rabin, amma fafur yaƙi amincewa, sai ma bada shawarar fara kasuwanci me gwaɓi da yayi min tayi, domin juya dukiyata ta ƙara bunƙasa, sosai sauran ƴan uwana suka yi na'am da hakan, basu koma ba sai da aka gama tsara komi aka kasafta dukiyar, inda aka zuba mana hannayen jari a manyan kamfanonin da ke ƙasarnan harma da sayranƙasashe, yayi da na yi rubutu da saka hannu akan na damƙa hagorancin gaba ɗaya dukiyar ga babban ɗana Muhaseen, ko bayan bana raye ya ci gaba da kulawa da dukiyar kar ya raba tashi data ɗan uwansa, a lokacin dariya mutanen da ke wajen suka yi min, ganin yaron da ke da ƴan ƙwanaki a duniya amma har na fara ɗira ma shi nauyu, sai da na ware waɗanda zan kyautar ga sauran jama'ar gidan da kuma wanda na fitar domin ayi sadaka da abin da zai taimaki sauran jama'ar gari, sannan muka tattara muka koma Katsina.

A can naci gaba da rainon ƴaƴana cike da kulawa, bani na koma Kano ba sai da suka yi wayo sosai, ko bayan dana koma munci gaba da rayuwarmu cikin kwanciyar hankali sam bana fuskantar matsalar komi daga wajen mijina, ga ƴaƴana da suke wuni a faɗa musamman Muhaseen da sam bashi da rigima, saɓanin Suhail da ke da ƙallafar uwa, ko fita aka yi da shi baya jimawa ake dawo da shi in shayar da shi (Yanzu na gane wani abu, shin masu karatu kuma kun gane ko kuwa🤔).

Rayuwa ta miƙa sosai, abubuwa masu daɗi da marasa daɗi sun faru, masu daɗin sun fi yawa akan marasa daɗin, marasa daɗin basu wuce yanda nike fuskantar barazana ni da yarana ba daga wajen abokan zamana, ga shi na gagara sanar da kowa damuwata, mugayen mafarkai gami da gane-gane babu wanda bana yi har tsoro nike dare yayi ace zan kwanta.

Ba zan mance ranar data zama rana mafi muni a gare ni ba, ranar Muhaseen da Suhail suka cika shekaru biyu da watanni, mun zauna a turaka ni da Me martaba muna lissafin ribar da ake samu a kasuwancina, sai ya ke bani shawara akan mu kafa kamanoni a kudu, ana samun alkairi sosai, ban ha da nisa ba na amince nace ma shi ko bayan bana raye yayi abin da ya dace kawai, ashe duk abin da muke yi Gimbiya Zainaba na laɓe tana jinmu, domin ranar ita zata amshi turaka, kuma lokacin fitata ya yi, ban ƙara jimawa ba na yi ma shi sallama na tashi da yarana na fice, ɗan turus na yi lokacin dana ganta a baki ƙofa tana jefami mugun kallo, amma ban ce komi ba na raɓata na fice gabana na faɗuwa.

Bazan mance ba a ranar ne naji ana kiran sunana lokacin nayi shirin barci ni da yarana ina musu wasa barci ya ɗauke ni, a ranar ne naji zan iya mutuwa idan ban fita daga Masarautar Kano ba, hankalina ya gushe tunanina yayi ƙaura na gagara gane komi illa bin umarnin da ake bani ta hanyar kiran sunana, ban san abin da ya faru daga nan ba kawai de na farka na ganni a wannan gidan, idan ban manta ba."

Ta kai ƙarshen maganar tana gashewa da kukan kewar yaranta data tuna a yanzu, tare da damƙar gashi kan Najla a cikin hannunta tana murzawa....✍🏻

Alhamdulillahi a yau Allah ya nufe ni da gama MUHASEEN littafi na ɗaya, zamu ɗora a littafi na biyu wanda ya kasance littafin kuɗi ne.

Ƴar uwa idan har kina so mu warware zaren cakwakiyar wannan libari tare da ke to ki garzaya ki biya kuɗin wannan labbarin naira 500 kacal kema ki mallaki na ki

9136291920

MARYAM UMAR

OPAY.

Shaidar biya a wannan layin.

***

Karku bari a barku a baya ni ce taku har kullum me son ganin farin cikinku.

MARYAM STAR⭐⭐

SAI MUN HAƊU A LITTAFU NA GABA 2