Chapter 21:RDBG
RAUNIN DA BA A GANI
Meefat ink ✍️ writers
“ Ammie, ammie” hudace ke Kiran ammie tundaga parlour sai tatashi da gudu tashiga dakin, ammie na ninke kayan huda da ta Wanke sai tashigo da gudu tana cewa “ammie kiga ana bawa adda award awaya” mikawa ammie wayar tayi tana nunamata life video da ake haskawa inda azan yake bawa ruhy award karba tayi tana kallon videon sai huda tace “dama ba tafi excursion dinba kamar yanda adda samha tace da naje naga wannan baturen” hawayene ya taru a idon ammie dan ita batayi tsammanin ruhy zata karbi award ba dukda tasan yar tata nada kwazo sai dai awannan karon yadda take hada sketching da karatu abune mai wahala ace ta samu kyautar girmamawa, tana matukar alfahari da yarta kuma tana addu an Allah yacigabada daurasu a hanya mai kyau sai tasaka musu albarka tana kallon videon, hudace tace “ammie kiban naje na cigabada kallona” kinbata ammie tayi tace “kije kici abinci” “nagama cifa ammie” “toh jeki dauko kibiya kizo natsefe miki wannan kannaki yatsufa dayawa” kwabe fuska huda tayi kamar zata yi kuka tace “adda samha tace intazo zata tsefemin” “nasan agajiya zasuzo dan haka maza kitashi ki kawomin kar ranki yabace” kuka tafara ganin ammie dagaske take tamike tafita dan tsaf tasan inhar ammie tatsefe kannan to sai an kisashi”.
Gaisawa sukeyi da manyan baki sai commissioner ya matso kusa bayan sun gaisa sai ya tambayi azan ya mahaifinsa yake sun dade basu haduba kuma yaji cewar baya kasar , amsa yabashida eh baisamu dawowaba saboda wasu ayyuka da suka rikeshi amma ya aiko da sakon gaisuwarsa,bayan sun gama gaisuwan sai suka cigaba da tafiya zuwa inda motarsu take pake, hango wasu yanmata yayi suna hoto sai idanunsa ya sauka akanta stiff yayi yana kallon yanda take dariya cikeda farinciki bai san lokacinda murmushi ya subuce mishiba, shi Jay riyya ce takira shi sai yadan yi gefe yayi excusing azan batareda yalura da abokinnasa ba, dan juyawa tayi sai suka hada ido, alama yamata da tazo sai ta nuna kanta alamun nii sai taga ya gyada kai, shiru tayi tana kallon samha da ta lura sai tace da samhan “wai yace nazo” “kije mana kiji menene” ahankali tazame daga cikin kawayennata ta iso ahankali kanta akasa zuciyarta yana bugawa da sauri da sauri, shiru tayi bayan ta karaso jin shurun yayi yawa sai ta dago da niyyan kodai baya wajenne dukda tana jin kamashin turarensa, hada ido sukayi sai tamayar da kannata da sauri sai yayi gyaran murya yafara mgn ahankali cikin sanyin murya “congratulations once again ruhaina” ai bata san lokacinda tadaga kai takalleshi da mamakin kiran sunanta da yayi bai mantaba sai yayi murmushi yace “I want to ask you something sai dai like u are not comfortable so inaganin kibani damama wani lokacin” shuru tayi takasa cewa komai sai ta tsinci kanta da gyada masa kai sai shima ya gyada kannasa yace “am can i have your digit if u don't mind sai nayi miki tambayar via phone” still tayi ita atunaninta zai mika wayar sai tasaka number sai taga akasin hakan dan ita Allah Allah take ya sallameta dan taga kamar idon mutane sun fara zuwa kansu ganin bai mika wayar ba sai tadago takalleshi Shima kallonnata yake yana jiran tafada number “am kada kiga kamar takurawa inanufin inbazaki iyabada wabazaki iya bawa ko kawarkine sai ta gayamin” girgiza kai tayi tace “to a ina zan saka maka number” “am kifada inaji” fadamasa number tayi sai ya gyada kai yace “thanks for your time, zaki iya komawa” juyawa tayi tafara tafiya ahankali yana kallonta har ta karasa wajen kawayenta, sai shima ya juya ganin Jay yayi gaba amma still waya kare akunnensa sai shima yabiyoshi abaya.
Hira suke ahankali acikin motan sai Jay dake driving yace “gida zamuwuce koh dan two days mom tace baku gaisaba” murmushi azan yayi yashafa kansa yace “I thought namu gidan zamu wuce” “nope gaskiya muwuce mana sai ku gaisa da mom haana” “yeah zanzo mata na musamman nayini ko dadaddare ne” “alright then” dahaka yawuce yayi sauke Jay agidansu sannan yawuce.