HARAMTACCIYAR GADA

CHAPTER 4

by @hafnancy

*HARAMTACCIYAR GADA.*


_*{Haɗuwar rayuka da ƙaddara ta tattara wuri guda.*🔥💔}_


*NA*


*HAFSAT MUSTAPHA ('Yar Mutan Naija).*


*SADAUKARWA GA UWARƊAKI NA: HAJIYA ZAINAB AHMAD (Hajiya Mama). Amincin Allah da ni'imominsa su tabbata a gareki Uwata.*



  *BOOK 1*

    

 *Page 4.*


Bayan isar Jidda gidan Mai aikin Samha ta mata iso a katafaren Falon sannan ta tarbeta da kayan marmari. Hannu ta kai ta dauki jan tufa ta fara sha idanunta kan talabijin.


Kamar minti goma da zamanta sai ga Samha ta fito. Matashiya ce 'yar kimanin shekaru ashirin da takwas. Gata mace har mace amma k'yawun hali ne ya ragewa aya zakinsa. Kuma shekaru uku kacal taba Jidda amma idan ka ga yadda Jiddan da sauran matan ke bata girma sai ka kama baki.


Cike da Izza da Takama ta karaso inda take zaune, Jidda na ganinta ta mik'e da dan rawan jiki tana

"Barkanki da fitowa Ranki shi dade."


"Yauwa Barkanki da isowa Alkhairi na." 


Ta furta tana karewa shigarta kallo tun daga Sama har zuwa kasa tana mai gyad'a kai alamun dai shigar ta gamsar da ita kan tace"Shigar ta miki kyau."


Lallausar murmushi Jidda tayi, sai a yanzu ta gamsu cewa lallai ta fito tunda har uwarɗakinta ta yaba.


"Godiya nake uwata, Ya jikin naki?"


Ta yi tambaya tana satar kallonta amma babu wanda zai fahimci tana da juna biyu saboda cikin ma bai yi wata biyu ba.


Samha ta dubeta cikin zolaya ta ce"Jikina da sauki, sai ki fara shirye-shiryen taran ɗan'uwanki."  


Kunya ya kama Jidda ta ce"Allah ya raba lafiya."


Samha ta amsa da "Ameen." 


Bayan ta zauna kan couch ta tsai da idanunta kan Jidda, wannan karon her face looking serious ta ce"Bari muyi magana agurguje kafin mai gidan ya dawo don ya kirani yake sanar mun da yakusa taso wa daga aiki." 


Jidda bata ce komai ba sai wasa da zoben hannun hagunta take yi ko kallon Samhar ma bata yi ba. Don Allah ya gani kwarjini take mata sosai, tana balain shakkarta.


"Dama kiran dana miki kan abu biyu ne amma bari mu fara ta kan wannan yarinyar Saffy."


Jidda bata yi mamaki ba don already ta riga tasa ma ranta saboda Saffy take son ganinta. 


"Kin san har yau ban sa yarinyar a ido ba, ban san ya kamanninta yake ba sai labarinta da nake ji. Da yawan mazauna gidan ma ban sansu ba amma ita saboda matsalar da takeso ta haifar yasa zancenta ya tsaya min a rai. Ki gaya min ke ko SALA waye a cikinku ya bata wajen zama?"


Cikin faɗiwar gaba Jidda ta ce"SALA ce ta bata waje don lokacin da yarinyar ta shiga gidan bana gari. Yau ma na san da zamanta dalilin rikici da wani."


"To, Jidda na baki assignment kisa ido sosai kan wannan yarinyar saboda idan ta ƙara tayar min da wani ƙura a gida kamar yadda na faɗa zan koreta. Ki zaunar da ita ki gaya mata duk abin da bana so kar in tashi ɗaukar mataki aga laifina."


A sanyaye Jidda ta ce"In sha Allahu daga yau ma ba za a sake samun matsala da ita ba."


Samha ta ce"Good...abu na gaba shine mahaifina ke niyyar fadad'a kasuwancinsa akasashen dake da bukatar abincinmu na Afrika. To, shine ya samu kwangila a can ƙasar birtaniya. Maganar da nake miki tuni ma har an fara aikin ginin kuma yana k'ok'arin mallaka min ya zama nawa da zarar an kammala amma da sharad'in idan har na amince zan rushe gidan mata. Jidda idan zanyi abu bana yanke shawara kai tsaye ba tare dana ji naki ra'ayin ba. A wasu lokutan, da in yi shawara da uwar data tsugunna ta haife ni har gara in yi da ke saboda kina da zurfin tunani. Don haka ya kike gani ? Don wallahi bana jin zan iya rushe wannan gidan matan sbd ba karamin alheri nake samu dashi ba."


In banda toshewar basira taya har zaka tsaya neman zab'i tsakanin halal da haram ? A fa mallaka maka katafaran gidan abinci a daya daga cikin kasashen da ake ji dasu afadin duniya. Sannan ka wani tsaya kana had'ashi da harkar bariki in ba rud'in shedan ba?


Jidda tace "Amma ranki shi dad'e aganina wannan cigaba ne mai k'yau, ba karamin gata Daddy ke so ya miki ba. Shawarar da zan iya baki shine kawai ki karbi wannan babban k'yautar daya miki karki watsa masa kasa a ido.."


"Dakata...! Kina nufin ke ma kin amince in rushe gidan matan kenan? To ku yi yaya? Bayan mafakar da kuka dogara da ita kenan?"


A dan tsorace tace har muryatta na rawa"Kar ki damu Allah zai bamu wata mafaka kawai ina miki kwaɗayin samun gidan abincin ne. A ganina zaki fi samun tarin alherinsa fiye da gidan mata..."


Wani irin gigitacciyar tsawa ta doka mata "Dalla malama rufemun tsamin bakinki awajen. Ai ban san cewa ke shashasha bace sai yau, dan baki san tarin alherin da nake samu a gidan mata ba shiyasa kike min zab'in wani gidan abinci. Ko don kinga ance kasar masu jajayen kunne ne yasa kike ganin kamar wata duniya ce za'a rika samu ? To, kiji dakyau ina da lissafi ba shashasha bace kamarki."


Jidda taso yi mata gamsasshiyar bayani amma taki bata wannan damar.


"Yi min shiru ki saurare ni! 'Yan matan da nake dasu kema kin san zuwa yanzu sun kusa dosan ɗari. Na basu wajen zama k'yauta. Sannan kowani wata ina wadatasu da kayan abinci, nawa kawai shine duk bayan wata bibbiyu kowacce ta dinga bada dubu hamsin shine kudin harajina. A shekara ya kama dubu dari uku cif-cif, kinga a ƙarshen shekara ina iya tashi da abin da ya kusa miliyan 30."


Tari ya turnuketa saboda ta shaƙa da yawa, da sauri Jidda ta tashi ta zuba mata ruwa a kofi ta bata. Sai data sha rabi sannan ta dire cup ta ci gaba.


"Jidda, kin fi kowa sanin gidan matan dana kafa ba irin wanda aka saba gani ko jin labarinsa bane. Gida ne na matan da suka rasa gatansu da kuma matan da wani dalili ya fitar dasu daga gidajensu. Sai dai kafin ka zauna a gidana dole sai ka yarda daga ni har kai zamu ci ribar juna. Ma'ana kuci arzikina nima inci naku. Amma ke ta musamman ce a wajena kasancewarki 'ya mace ta farko dana fara raino har ta zama abin da nake tsananin alfahari da ita a yau. Dalilin daya sa na dad'e da sauke miki duk wani kudin haraji kenan don ba karamin kokari kike min ba, ke alkhairina ce. To cut it short bana jin zan iya karban tayin Daddy, na fi bukatar rayuwa da ku."  


Jidda bata san sanda hawaye ya cicciko mata idanu ba. Tana jin ina ma ace itace tayi dace da uba irin na Samha? 


Allah ya bata mahaifi mai kaunarta mai kuma son ci gabanta amma ta faɗa gurbataccen hanya.


A sanyaye tace "Allah ya huci zuciyar Uwarɗakina..."


Harara ta watsa mata"Tashi ki tafi naji naki ra'ayin amma ki sani ni bazan amshi tayinsa ba, nafi bukatar gidan mata."


"To, shikenan Uwarɗaki! Allah ya shige miki gaba. Muna godiya da kasancewarki tare damu, na barki lafiya." 


Ta mik'e tana k'ok'arin barin gidan.


"And that reminds me, better take me serious ki ja wa yarinyar nan kunne sosai, idan bata shirya zama ba tabar mun gida kar mu samu matsala da ita. Sannan kuma ki ƙara jan kunnen 'yan gida kar wata ta sake shigo da wani koda ɗan'uwa ne saboda bana so a sa min ido."


Samha ta ida magana fuskarta babu alamar wasa ko kadan.


Jidda tace"In sha Allahu za'a kiyaye."


"Good....karbi k'ya hau mota da wannan."


Ta mik'a mata dunkulen kudi akalla zai kai dubu goma.


Murmushi tayi tace"laaa! Uwarɗaki da kin barshi ina da kudin komawa."


Samha tace"Ki dai karba ki ƙara ai na san kina da shi don na fahimci sabon kamun da kika yi yafi nada maiko." 


Gaban Jidda sai daya faɗi amma bata ce komai ba tasa hannu biyu ta karba ta mata godiya sannan ta fice da hanzari.


Sai data bar gidan ta girgiza kai ta furta a hankali"Ai babban kamun da nayi shine mahaifin naki. Kuma soyayyar da nake miki yasa nake so ya miki gatan da zai cetoki daga halaka. Taimakon da nake so in miki shine nake ganin mafi alheri a gareki amma ba wannan ƙullin da Aunty Hadiza take so ayi ba."


Tunda ta bar gidan ta koma gida, tunane-tunane ya addabi ranta.


'Ina makomarta?'


'Ya za ayi ta samu cikar burinta kan Samha kafin Aunty Hadiza ta ɓata komai?'


'Ya kuma za tayi da alak'arta da Yallabai? Shin haka zasu cigaba da rayuwa a sirrince?'


Saffy fa ? Wani taimako zata yi na ganin ta tsiratar da yar'uwata daga faɗawa halaka ? Don ga dukkan alamu har yanzu sabuwar hannu ce bata kai ga fara harkan ba. Sabida haka ya kamata tayi saurin yiwa tufkar hanci.


'Ta ina zata fara?'


Ji take kamar kanta zai tarwatse tsabar ciwon kai, kafin wani lokaci zazzab'i mai k'arfi ya rufeta da ko d'an yatsarta ma bata iya d'agawa.


Haka ta kwana cikin wani hali, ga kiraye-kiraye da ake ta mata amma bata iya d'agawa ba. Adaddafe ta mik'e tayi sallar asuba, tana idarwa ta jawo wayarta tana dubawa, yawancin missed calls d'in daga Yallabai ne. Ta sani sarai yana cikin wani hali yanzu haka muddin bai ji daga gareta ba to hankalinsa ba zai tab'a kwanciya ba.


Maida wayar tayi zata ajiye don ba iya kiransa za tayi ba don mutum ne mai iyali. Kiransa a wannan lokacin na iya haifar masa da matsala.


Bata kai ga direwa ba sai ga kiran nasa yana sake shigowa, babu bata lokaci ta daga tana "Yallabai barka da safiya." Cikin wani siga na jan hankali.


Wani sassanyar ajiyar zuciya ya sauke yana"Haba Alkhairi kin jefani cikin wani hali meya faru ne aka kasa daga wayata tun daren jiya ko laifi nayi ban sani ba ?"


Wani abin da ke bata mamaki shine daga shi har 'yarsa Alkhairi suke kiranta. Sai dai kowanne da alherinta a gareshi.


"Yallabai wallahi zazzab'i ne ya rufeni ina ma tunanin in gari yayi haske zanje asibiti adubani ."


Hankalinsa ne ya tashi ainun don aduniyarsa ya tsani duk wani abin da zai takura Jidda, don ba karamin jinta yake arai ba.


"Subhanallah abun har ya kai ga haka ? Alkhairi please ki kokarta kije asibiti a dubamin ke. Don baki so ne a san da alakar da ke tsakaninmu da yanzun nan zan bada mota azo har inda kike a ɗaukeki a kai min ke asibiti.


Da sauri tace"A'a ba sai ka turo kowa ba zan je da kaina da zarar gari ya ƙara haske."


Yace"To shikenan amma fa wallahi ke kike tsoro, ni kam ko a jikina tunda na san Allah ne ya ƙaddarta tarayya tsakanina da ke domin ya zama darasi ga 'yata. Ai ni kin ƙara min sonki ne tun lokacin da kika faɗa min kina zaune a gidan da 'yata take alfahari da shi. Kuma ina addu'ar Allah yasa hasashen da nake a kanki ya tabbata gaskiya bayan kin je asibiti, idan yaso duk wani rufa-rufan da ake yi yazo k'arshe In sha Allah." 


A tsorace tace" In sha Allahu hakan bazai tabbata ba Yallabai ka bar tsoratani please." 


Tuni hawaye ya mata sharr! A fuska.


Ajiyar zuciya ya sauke yana"To shikenan Allah ya kara lafiya, kidai yi kokari kije asibitin a dubamin ke, sai na kira inji yadda ake ciki.....Allah baki lafiya I love you ALKHAIRI." 


Kit! Ya kashe wayar ba tare daya jira amsarta ba. 


Kayataccen murmushi ta saki, tana son yanda yake kiranta 'ALKHAIRI'


Kulawar da kuma yake nuna mata abun ba'a cewa komai, ga salo na soyayya da wani matashin ma sai dai ya koya masa. Allah ya sani tana kaunar Chef Jalal sosai kuma tana ƙwadayin kasancewa dashi har ƙarshen rayuwarta amma bata da ƙwarin gwiwan tunkarar abunda zai biyo baya.


Misalin takwas da rabi na safiya ta shirya don zuwa asibiti ahakan ma sai da Yallabai ya matsa mata, adolenta ta shirya da wuri ta fice. 


Garkuwa hospital shine asibitin data saba zuwa duk sanda bata da lafiya. Bayan wasu 'yan gwaje gwaje aka gano tana dauke da juna biyu na tsawon sati shidda.


Salati ta saki tace da Nurse d'in" Don Allah zaki iya taimakawa ki zubar mun dashi ?" Cike da mamaki Nurse Zahra tace"Wa'iyazubillah zubad da ciki kuma ? Gaskiya mu bama zubar da ciki anan asibitin infact in Dr. Ansar ya ji labarin na aikata danyen aikin nan zan iya rasa aikina don haka ki rufamin asiri, amma meyasa kikeson zubarwa ? Bakya son cikin ne ?"


"Wannan ba damuwarki bane, Nidai kawai ki taimaka ki zubar mun dashi ko nawa ne zan biyaki."


Jidda tayi magana kamar zata saki dan marayan kuka wanda hakan ya kitsawa Nurse Zahra bahaguwar tunani akanta, ba mamaki cikin shege ne, ta raya hakan aranta.


Ajiyar zuciya ta sauke tana"Ki addana kudinki bani bukatarsu, Ni dai iya gaskiyata na fad'a miki, bazan iya zubar miki da ciki a sirrince ba tare da kwakkwaran dalili ba. Kuma koda naji kwakkwaran dalilin dole sai da sanin mai asibitin, kai tsaye ba ma aikata irin wannan aikin mai had'ari ba tare da izininsa ba...."


Da rawan murya tace"Tohh Tohh naji had'ani dashi inda hali sai ni in nemi izininsa please...." 


Sosai ta shayar da Nurse d'in mamaki amma ganin ta dage sai taga babban likitan yasa taje ta nemo mata izininsa adaidai lokacin yana ofis tare da wani abokinsa likita daya kawo masa ziyara.


"What?? Zubar da ciki acikin asibitina ? Wacece wannan ina son ganinta inji dalilinta first." Dr. Ansar ya furta a hasale.


Dan duk'awa Nurse din tayi alamun girmamawa tana"Ok sir bari in mata iso." Ta juyo ta fice.


"Kana maganar dalili, dalili ya wuce rabon dan titi ne aka samu shine ake k'ok'arin halaka shi ?" Abokin nasa ya furta fuskarsa dauke da damuwa.


Dr. Ansar yace"Nima abin da nake tunani kenan, amma kar muyi saurin yanke hukunci bari ta shigo muji..."


Bai gama rufe bakinsa ba sai ganinta suka yi ta shigo dauke da sallama abakinta. Idanunta ne ya fara sauka akan abokinsa. 


Cak! Ta tsaya akofar numfashinta na barazanar daukewa sakamakon wanda idanunta suka yi arba dashi...


"Malama ki karaso ciki mana kin wani tsaya daga bakin kofa kina kallonmu ko daga nan ne zamu yi magana ?" 


Dr.Ansar ya furta ransa amugun ɓace. Sai asannan ta dawo hayyacinta kana ta ari mayafin natsuwa ta yafa. Asanyaye ta tunkari inda suke bayan ta rufe kofar, kanta a ƙasa ayayin da gabanta ke mugun doƙawa.


Shi kam abokin Dr. Ansar tunda ya mata kallo sau daya ya watsar gefe ya cigaba da latse-lasten wayarsa, dan haka sam shi bai ma lura da yanayin data shiga ba adalilin ganinsa da tayi.


"Samu wuri ki zauna abin bana tsayuwa bane, magana za muyi." 


Dr. Ansar ya bata umarni kuma bata ci musu ba ta kame a kujerar dake kallon na bakon likitan da ganinsa gabaki daya ya sauya mata yanayi. 


Shi kam har yanzu hankalinsa akan wayarsa yake. A takure take sosai don gani take ayau kamar asirinta zai tonu ne. 


Sai da Dr. Ansar ya gama nazarinta sosai kan ya cire alkalamin rubutu da yake ta wasa dashi akofar bakinsa ya soma magana" Meke damunki ? Naga duk kin wani sukurkuce daga shigowar ki ? Ko pregnancy dilemma d'in ne ya jefaki cikin wannan yanayin?"


Sake aron mayafin natsuwa tayi akaro na biyu tace" Ban shirya zama Uwa bane ahalin yanzu sabida wasu dalilai shiyasa nake son ataimaka acire min shi." 


A kufule abokinsa ya d'ago ya buga teburin gabansa wanda ba ita kadai ba hatta Dr. Ansar saida ya tsorata. 


Idanunsa ya jefa cikin nata yana "Malama What are your stupid reasons ? Mutane kuna bani mamaki sai kuce baku shirya haihuwa ba amma kuma kuke having affairs, yanayin ki sam bai nuna wacce take fuskantar financial problems ba balle ayi tunanin ko ɗan cikin ne in kun haifa bazaku iya kula dashi ba. Kallo daya mutum zai miki yasan akwai wadata atattare dake sai dai kuma in dama can fake life kike. Amma ni nama fi tunanin kawai kina cikin jerin ire-iren matan nan masu son hutu da tattalin jikinsu ne marasa son haihuwa, wani nanan yana neman haihuwan bai samu ba. Ke Allah ya miki ni'ima amma kike neman butulce masa. Well, I'm sorry to say, sai dai kuma in dayan abin da nake tunani ne Astagfirullah."


"Enough!!!" 


Ta furta ranta na bala'in suya Idanunta aruntse, babu abunda yafi yi mata ciwo kamar kalamansa na karshe, tabbas tasan abunda yake nufi k'ok'arin shegenta abunda ke cikinta yake shirin yi.


Koda ya kasance dagaske shegen ne bazata so aci mata irin wannan zarafin ba. Hawaye ne masu zafi suka shiga wanke mata fuska tace tana girgiza kai "Duk hasashen da zakayi sai dai kayi amma bazaka tab'a jin mutuwar sarki abakina ba. My reasons are personal, wajen Dr. Ansar nazo ba wajenka ba, infact ban sanka ba! Ban tab'a ganinka ba dan haka please keep yourself in order kabar yin kasalandan cikin rayuwar wani.." 


Cikin tsananin bacin rai shima yace" Yes, zaki iya cewa baki tab'a ganina ba amma karya kike kice baki san da zamana acikin garin Kaduna ba. Baby girl hands down, I'm DR. HASEEB ALIYU GAMAWA, the eye doctor king unbeatable and top-notch!"





**Mai son ganin yadda zata kaya tsakanin Jidda da Haseeb ya jira next page**






*NAGODE ALL🙏*



#HaramtacciyarGada

#2026 Novel

#HAFNANCY📚✍️

***/***