CHAPTER 5
by @hafnancy
*HARAMTACCIYAR GADA.*
_*{Haɗuwar rayuka da ƙaddara ta tattara wuri guda.*🔥💔}_
*NA*
*HAFSAT MUSTAPHA ('Yar Mutan Naija).*
*SADAUKARWA GA UWARƊAKI NA: HAJIYA ZAINAB AHMAD (Hajiya Mama). Amincin Allah da ni'imominsa su tabbata a gareki Uwata.*
*BOOK 1*
*Page 5.*
Haseeb ya ida magana full of bragging yana dukan k'irjinsa, hakan ya dad'a haifar mata da tsananin fad'uwar gaba da sake tabbatar da lallai wanda ke zaune agabanta yake cin zarafinta mijin Uwar ɗakinta ne, wato Samha Jalaludeen Alkaleri.
Haseeb na cikin wanda Hadiza keso tayi amfani da shi wajen haɗa ƙulli. Kuma wannan ƙullin ne yasa take son haɗawa da wata a gidan mata shiyasa take ta bibiyar Jidda.
Dr. Ansar ne ya kada baki yace"Haba Gamawa calm down, meyasa kake daukan zafi ne da yawa haka ? Ka natsu mu bi komai a sannu mana."
A zafafe yace"Gamawa nake don haka ka bari in gama da ita, I can see she's so stupidddd!"
Ita ma cikin zafin rai ta ce"The baby is not your's...so please stay out of thissss."
Da rawar jiki ta mik'e hawaye duk ya gama wanke mata fuska ta dubi Dr. Ansar ta ce" Dr. Ansar ka rubuta ka ajiye in sha Allahu wannan shine karo na karshe da zaka sake ganina cikin asibitinka. Na lura asibitinka baya da sirri da patients d'insa, ko wani silly goose yana iya saka baki cikin maganar sirri."
Da sauri Dr. Ansar ya mik'e tsaye yana bata hakuri cikin rashin jindadinsa yace" Dan girman Allah kiyi hakuri kuskure aka samu amma na miki alkawari hakan bazai sake faruwa ba. Dr. Haseeb Gamawa baya da halin da kike tunani, but I'm so sorry ban tab'a tunanin zai yi haka ba."
Cikin zafin rai ta ce"Bai kamata ya tsoma baki cikin maganar da bai shafe shi ba."
"Ya shafeni saboda da ace zan bada had'in kai a biya miki bukatar ki to gobe kiyama sai Allah ya kirani shaida don agabana akayi kuma dole nima a kamani da laifin kashe Rai."
Kallonsa kawai take ta kasa cewa uffan ganin ya dauki lamarin da zafi. To, ya zai yi idan ya san cewa cikin da take dauke dashi na sirikinsa ne?
Sosai kan Dr. Ansar ya dauki zafi sosai yace" Gamawa look you might be saying just the truth amma inaso ka sani ba haka yakamata ka mata magana ba. Maganganunka sunyi tsauri da yawa, ina rokonka please stay out of this ba huruminka bane."
Mik'ewa yayi yana" Haka kaima zaka ce ko ? Ba hurumina ba ? Well shikenan zan cire bakina amma baka isa ka hanani sauke hakk'in amintaka ba. Ansar kasan halina nasan naka, kai mutum ne mai aiki da ilimi dan haka karka bari wani ya canza maka tunani ka aikata ba daidai ba. Na barka lafiya."
Yana gama magana ya zura gilashinsa sannan ya dauki jakar kwamfutar tafi-da-gidanka wato laptop ya rataye, kallo daya ya mata mai wuyar fassarawa wanda zaka iya rantse kace ya santa ne, kana yabar ofishin ransa duk ba dadi. Dr. Ansar yabi bayansa yana bashi hakuri har inda ya paka motarsa amma ko kallonsa bai yi ba.
Yana ji yana gani yaja motarsa yabar asibitin. " Gamawa akwai saurin hawa ga kuma saurin sauka kamar farashi, Allah ya kyauta."
Ya faɗa cike da rashin jindadi. Koda ya koma ofishin wayam! ya gani babu Jidda babu labarin ganin fitar ta a bakin Nurses. Abin da basu sani ba ashe lokacin data fito sam hankalinsu baya kanta ne har ta fice basu ganta ba.
**
Jidda na fita bata yi tunanin zuwa wani asibitin domin zubar da cikin ba, kawai d'an sahu ta nema ya kaita gida. Tun tana cikin asibitin Yallabai ya matsa mata da kiraye-kirayen waya amma ta kasa dagawa don ba karamin haushinsa take ji ba. Aganinta shine ummul'aba'isin shigar ta masifar data tsinci kanta ayau.
Ganin takurar tayi yawa yasa ta d'aga wayar ta kange a kunne ranta na bala'in suya tace"Mu haɗu a gida ina kan hanya ne." Ta katse wayar.
Hankalinsa tashe ya dire wayar yana salati domin jin tashin hankalin da ke muryarta ya tabbatar masa da ba ƙalau ba. Dama fitowarsa daga wanka kenan ko kaya bai sa ba ya dauki waya ya k'irata.
A gurguje ya nemi k'ananan kaya ya zura ko tsaya shafa mai bai yi ba balle ayi batun feshe turare, kodayake kullum cikin kamshi yake abunka ga ɗan gayu baya tab'a tsallake zuba turaren wanka acikin ruwa muddin ya tashi wanka, kuma dik wannan aikin Jidda ne, ita ta koya masa son kamshi, na musamman take musu odan kayan kamshin jiki daga Maiduguri.
Wayoyinsa ya kwashe ya zuba a aljihu kana ya fito dakin zuwa babban falon daya wadatu da kayan alatu na more rayuwa. Haj. Nafeesat ne hakimce kan kujera tasha ado itama cikin k'ananan tana jiran fitowarsa.
Bai bi ta kanta ba ya kwashe makullin mota dake saman centre table yayi kofa yana fad'in "Ni Zan fita saina dawo."
Zaburowa tayi tace"Fita kuma ? Kamanta cewa kayi alk'awarin kasancewa tare dani agida yau ?"
Ba tare daya waigo ba yace"Yi hakuri Feey, Alkhairi ne tayi k'ira kuma dole in yi biyayya."
Tsaki ta ja ta bishi da" Ni fa wallahi mutane na shiga haƙƙina da yawa, haba kasuwanci sai kace akan ka aka fara ? Sam baka da lokaci na saina mutane, wannan wani irin rayuwa ne haka ?"
A tunaninta nemansa ake da abin alheri, bata san da cewa Alkhairinsa ce tayi k'ira ba wato JIDDATULKHAIR. Kawai maidata shashasha ya yi tunda bata san rayuwar sirrin daya kafa ba.
Jidda ce kadai macen data hargitsa tunaninsa da lissafinsa. Macen da yake wa mahaukacin so, macen da yake ganin shigowar ta rayuwarsa Alheri ne, hakan yasa yake k'iranta kai tsaye da ALKHAIRINA....
K'ofar wani madaidaicin gida mai tangamemen gate d'an sahu ya sauketa yayi gaba. Ga unguwan shiru shiru kamar babu mutane, makulli ta ciro ta buɗe gidan ta afka ciki jiki duk ba kwari.
Gidan Yallabai ne, nan suka kafa rayuwar sirri da babu wanda ya sani sai Allah. 2 bedroom flat ne, tsakar gidan kuma madaidaici sai kuma parking space. A kan wata doguwar three sitter ta zub'e tana sauke ajiyar zuciya.
Tunanin abin daya faru tsakaninta da Haseeb ya fara barazanar tarwatsa k'wak'walwarta. Muddin ta rufe ido ta bud'e babu hoton wanda take gani daya wuce Haseeb.
Bata tab'a ganinsa a mutum ba sai yau, a hoto kawai ta san shi kuma ta dalilin zuwanta gidan Samha ne. Hotunansa dana Samha da suka dauka suna fara'a, wani kuma ita kadai, wani kuma hotonsa ne an daukeshi sanye cikin kayansu na likitoci.
A takaice dai an k'awata katafaren falon ne da photo frames na hotunansu hakan ya taimaka mata wajen saurin shaida shi a nan asibitin.
Abin da yake bata mamak'i shine yanda Haseeb ya dauki zafi sosai akan lamarinta yadda kasan akanta ne za'a fara zubar da ciki. Ɓacin ran daya nuna k'arara ya bata tabbacin har ransa ya ji zafin barnar da take shirin aikatawa kamar wanda ya san cikin na surikinsa ne.
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun"
Ta furta ayayin da sabbin hawaye ya shiga tsere saman fuskarta yana sauka a dokin wuyanta.
Babu abin da yafi d'aga mata hankali kamar tunawa da ƙullin da Hadiza take so ta haɗa wanda ita a tunaninta shine zai gyara komai.
Acikin wannan yanayi na sake-saken Yallabai ya shigo ya sameta. Tun daga yanayin yadda ta amsa mishi sallama yasan cewa yau babu lafiya.
Jan jikinsa ya yi da yake jinsa kamar ba nasa ba ya karasa gabanta ya durkusa yana"Alkhairi wai mai yake faruwa ne ? Ko jikin ne ? Wallahi Hawayen nan da kike zubar wa ciwonsa nake ji a raina. Please ki fad'a min ko ɓata ranki aka yi. Na miki alk'awari na baƙanta ma wanda ya saki zubar hawaye koda kuwa Samha ce."
Ganin taki magana ya sake cewa arud'e yana tuhumar kansa"Ko dai ni ne mai laifin ?"
Cikin tashin hankali kawai tace" Ciki gareni har na tsawon sati shidda."
Kukan da take ta danne wa yaci mugun k'arfinta, bata yi aune ba kawai taji ta sama ya d'agata yana yawo sai k'yak'yalar dariya yake yana "Good news Jidda Na...Rabon da in yi farin ciki irin haka tun lokacin da aka haifa min SAMHA. Jidda na fad'a miki ke ɗin ALKHAIRI NA ce , ina matuƙar alfahari dake. Wannan dadad'ar albishirin ya cancanci k'yauta mai tsoka daga gareni kuma ayanzu ne zamu fito kowa ya ganmu domin shimfiɗa rayuwar aure mai ban sha'awa. A yanzu ne zaki fara ganin tsantsar soyayya sabida kina dauke da gudan jinina. JIDDA wallahi ina bala'in sonki kin sani farin cikin da ban san yadda zan iya kwatanta miki shi ba"
Kuka ne yaci k'arfinsa hadda hawayensa ya durkusa k'asa da ita ahannu, amaimakon taji tausayinsa sai fizgar jikinta tayi ta mik'e ita ma kukan ta fashe dashi tana"Yau ga ranar da nake gudun zuwansa yazo. Dama na san hakan zai faru muddin na bari na dauki cikinka to babu makawa sai asirinmu ya tonu. Auren sirrin da muka yi dole zaka so ka bayyanawa duniya. Ka yi wa Allah ka yi wa annabi, ka kuma duba abin da zai je ya zo muddin muka bari na haifi ɗan ciki na. Jayman ina matuk'ar k'aunarka amma don girman Allah ka bari mu zubar da cikin nan."
A tsananin fusace ya mik'e yakai hannu zai wanka mata bari sai kuma ya tuna matsayinta agareshi hakan yasa ya maida hannun ya dunkule muryarsa na mugun rawa yace"Cikin nawa za a zubar? Wallahi baki isa ba ina son cikina! kuma zaki haifa min shi."
Ya ida magana cikin zafin ran da bai taɓa nunawa ba.
"Yanzu na gane dalilin daya sa na iskeki cikin damuwa. Haihuwa ne baƙya son yi dani amma kike fakewa da wasu dalilan ki marasa kan gado."
Runtse ido tayi tana girgiza kai hawaye na zuba tace" Jayman ka kasa fahimtata, ina sonka amma ina tsoron Samha ta gano na ci amana na auren mahaifinta da nayi."
"Wallahi idan kika fusata ni zan kira Abba Habibu ya san halin da ake ciki."
Bata san sanda ta ce"Don Allah kayi hakuri karka shigo da Abba Habibu cikin zancen nan."
Sai data bari ya ɗan sassauta fushinsa sannan ta ci gaba da magana cikin kwantar da murya.
"Kar ka manta kai mahaifin Samha ne, matsayinta a gareni abu ne da bazan iya kwatanta maka ba. Samha ta nuna min gata a lokacin da duniya ta ƙwaye min baya. Da na tashi saka mata sai muka yi auren sirri da mahaifinta kuma gashi yanzu ina dauke da cikinsa. Ka gaya min ko zaka ji dad'in ganin halin da za ta shiga muddin ta samu labarin nan?"
"Ke kike tsoron abin da zai je yazo amma ni ko a jikina tunda nasan da cewa ke matata ce sannan gudan jinina da kike dauke dashi d'an sunnah ne ba ta hanyar banza muka sameshi ba, to me zai sa hankalina ya tashi ? Tun farko ke kika so ayi auren sirrin nan wanda ni ba haka naso ba . So nayi muyi aure ayi shela dashi agari kamar yanda kowa ke yin nasa amma kika nuna rashin yardan ki. Auren ma sai da kyar na samu na shawo kanki kika bari aka ɗaura bayan kinji tsoron jefani a halaka, haka ne ko ba haka ba?"
"Wannan haka yake."
Ta bashi amsa jiki a sanyaye.
Amshinta ya bashi ƙwarin gwiwa ya ci gaba"Haka bayan auren ma na biye miki kika cigaba da tafiyar wa Samha da kasuwancin ta ba don komai ba sai kawai don ina k'auanarki. Duk abin da ranki ke son yi bana hanaki yinsa koda ba so nake ba. Muna sauka gari shekaranjiya kika nuna zaki gidan da kika taso amma haka nayi hakuri don kawai in faranta miki rai. Zama ba zai yiwu a haka ba kina ji ko? Dole ne ki zaɓa tsakanin ni ko Samha."
Saurin katse shi ta yi "Jayman please..........."
Da hanzari ya ɗaga mata hannu"Idan har kina sona dole sai kin zaɓeni! Kuma idan kina son zama dani sai kin bar cikin jikinki don ina son haihuwa. Ina murna zan samu karuwa saboda Samha ce kaɗai 'yar da Allah ya bani, daga haihuwarta bai sake azurtani da wani rabon ba sai yanzu. After 28yrs sai gashi ubangiji ya sake yi min wata ni'ima abin da na dad'e ina mafarkin samu sannan ke kice zaki kawo min cikas ga cikar burina ? No Jidda baki isa ba wallahi."
Ya ida magana yana girgiza kai ransa a mugun b'ace, idanun nan sun kada sunyi jawur dasu. Jidda bata tab'a ganinsa cikin irin yanayin nan ba sai yau. Amma bata tsorata ba ta d'aga murya tace" ya zama dole in zubar da cikin nan don shine kawai rufin asiri na."
Shi ma cikin d'aga murya yace"Kina nufin kin zab'i Samha kenan a kaina? To shikenan amma zan ara miki lokaci ki zauna kiyi nazari dak'yau ki zab'i tsakanin ni da ita. In kin zab'i aure to hakan na nufin kina tare dani sannan kuma kin shirya yin watsi da komai ki fara bautar ubangijin ki. In kuma kika zab'i bautar da babu riba a ciki to ki sani hakan na nufin kina tare da Samha. Kuma kin shirya rabuwa dani rabuwa ta har abada kuma wallahi tallahi i mean it. Jidda in kika bari na juya miki baya shikenan ni da ke har abada na yadda son naki ya zama ajali na."
Ya karashe maganarsa cike da damuwa dafe da k'irjinsa da yake ji tamk'ar zuciyarsa za ta tsage.
Gabanta ne yayi mummunar fad'iwa da jin furucin daya fito daga bakin mafi soyuwar halitta agareta. Bata tab'a tsammanin Yallabai zai iya mata barazanar rabuwa ba.
Da sauri ta matsa da nufin kwantar masa da hankali sai gani tayi ya dakatar da ita da hannu"Kar ki tab'ani har sai kin yi making choice ɗinki. Zan baki kwana uku kiyi nazarin abin da kike ganin ya dace da rayuwar ki. A kwana na hudu zan dawo gare ki in ji hukuncin da kika zartar akan mu duka."
Tana ji tana gani ya fice daga gidan ba tare data sake yunkurin dakatar dashi ba.
Wani kukan kura tayi tabi bayan shi amma ko kafin taje ya tada mota yabar k'ofar gida. Haka ta dawo ciki tana nadama, wannan kuskuren da take neman tafkawa na rabuwa da Yallabai da gaske yana iya zama silar bankwana da farin cikin ta.
Bata san ya rayuwarta zata kasance mata ba idan ta kuskura ta rabu da Yallabai. Gashi har ya tafi bata gaya masa komai daya danganci had'uwarta da sirikinsa Haseeb ba.
***
*ƁANGAREN HASEEB.*
Bayan ya bar asibitin ya koma inda yake aiki, abin kirki bai iya tabuka wa ba saboda tashin hankali. Lokacin tashiwarsa ma bai yi ba ya koma gida, Samha nata mamak'i don da wuya ka gansa ya dawo gida da rana tsaka, sai ce mata yayi kawai baya jindadin jikinsa ne.
Da shigarsa ɗaki ya kwaɓe kayan jikinsa ya faɗa banɗaki ya watsa ruwa. Bayan ya fito ko abincin kirki bai iya ci ba, kansa kamar zaya fashe tsabar azababben ciwon daya saukar masa.
Shi kansa tunanin abin da ya shiga tsakaninsa da Jidda ne ke neman birkita masa k'wak'wala. Tabbas ayanzu ne yake ganin cin mutuncin da ya mata bai k'yauta ba. Da gaske ne He went too far!
Bayan yayi sallar azahar yasha magani ya nemi lafiyar gado. A wannan ranar zan iya cewa daga kan Jidda, Yallabai har zuwa kan Haseeb babu wanda ya ji daɗin yinin. Jidda da Yallabai ma kwanan k'unci suka yi musamman Yallabai da ke jin gaba ɗaya duniyar jinta yake tana juya masa.
Ganin bacci ya gagareshi yasa ya tashi misalin k'arfe uku na dare ya dauro alwala ya hau saman sallaya ya hau jero nafilfili.
A sujjadarsa ta k'arshe ne ya fara gaya wa Allah damuwarsa a fili muryar sa na rawa ayayin da hawaye masu d'umi ke kwaranyo masa yace"Ya Allah ina rokon zab'inka game da rayuwa da Jiddatulkhair. Ya hayyu ya qayyum in har akwai alkhairi a ci gaba da zama da Jiddatulkhair ina rokon ka daidaita mu. Ka saukaka mana tashin hankalin da ke jiranmu saboda mu samu mu shimfiɗa rayuwa mai tsafta, Allah mun tub'a ka yafemu. Ya Allah kasan ina matuƙar k'aunar Jidda da abun cikin ta amma in dukansu bazasu zame mun alkhairi ba to ya Allah na rokeka ka kawo mana sauk'in rabuwa da juna."
Ya daɗe da goshinsa akasa yana kai wa Allah kukan sa ita kam Haj. Nafeesa bata ma san wainar da ake toyawa ba, baccin ta take kwasa hankali kwance babu abin da ya dami duniyar ta.
Tunda Jidda ta shiga wannan gidan tun bayan dawowar ta daga asibiti bata sake saka kafafunta awaje ba har washegari tana nan bata fita ba. Cikin ikon Allah babu wanda ya nemeta hatta Samha sai dai Saffy data bi ta addabeta da kira.
Ta ma sha'afa cewa sun ajje magana kan zasu had'u a jiya a Alkaleri's kitchen domin samun damar tattaunawa. Tashin hankalin data tsinci kanta yasa tana ganin calls ɗinta amma ta shareta.
Ganin kar hankalinta ya tashi yasa kawai ta aika mata da saƙo a daren jiya tace tayi hakuri tafiyar gaggawa ya sameta amma in ta dawo zata nemeta.
A daddafe aka yi kwana hud'u babu wanda ya san inda Jidda take. Shi ma gogan ko zuwa wajenta bai yi ba wai ala dole fushi yake kuma ya bata lokaci ta shawarta da kanta.
A yau ne ya kamata yaje gareta yaji hukuncin data zartar akansu. Sai dai tunda ya tashi gabaki daya yake jin tsananin fad'uwar gaba, jikinsa sam ba kuzari kamar wanda k'wai ya fashewa ajiki.
Haj. Nafeesa ta lura da yanayinsa don ko breakfast ma ya kasa tab'awa tunda ya zauna akan dinning har kuku ya gama jera abinci ya tafi ko kallonsa bai yi ba balle abincin. Gaba daya yayi nisa a duniyar tunanin makomar sa a yau wajen wacce yake ganin alkhairinsa ce.
Haj. Nafeesa ce tayi gyaran murya tace"Daddyn Samha wai meke damunka ne ?"
Bai ma san tana yi ba sai data tab'o shi asannan yayi firgigit! Ya dawo hayyacinsa yana"Don girman Allah karki banni....Ina sonki kuma ina son babyna ki yi hakuri ki haifa min shi."
Hankali a tsananin tashe Haj. Nafeesa ta mik'e har jikinta na wani irin k'yarma tace"Jar uban nan.....wacece wannan da kake son ta haifa ma baby?"
A daidai lokacin Samha ta sawo hancin motarta cikin gidan......
**Auren Jidda da Yallabai zai koyar da darasi ga matan da ke da hali irin na SAMHA🤣**
* My Arewa fan's ya kuka ji fejin nan?…..
Drop your comment.