Matukar Ina Raye 16
by @mrsisham12
MATUƘAR INA RAYE
(As long as I’m alive)
Writer — MRS ISHAM
*** WhatsApp
Page 16
Murmushi ta yi ta ce,
“Ni kaɗai nake rayuwata. Ba ni da aure, kuma babu wani nawa a nan.”
Buɗe baki Waheeda ta kuma yi da niyyar yi mata wata tambayar, amma Husna ta yi saurin dakatar da ita.
“Kin ga waɗannan tambayoyi naki kamar wacce ta karanci aikin jarida sun ishe ni haka. Karasa shan tea ɗin ki, ki tashi mu je in raka ki gida.”
“To,” kawai ta faɗa tana ajiye kofin da guntun shayin da ya rage ciki. “Na gama, Malama.”
Da suka fita daga gidan, Husna ta tara abin hawa, tare da jagorancin Waheeda suka isa gidan. A nan suka samu Ummah na zaune tana magana ita da Salma. Jin sallamarsu ya sa suka ɗago suka dube su da mamaki.
Ummah ta miƙe ganin Waheeda da wata baƙuwar fuska wacce suke kai ɗaya da Salma.
Cikin mutuntawa ta tsuguna tana gaishe da Ummah. Fuska da ’yar fara’a ta amsa mata, tana mata bismillah zuwa cikin ɗakinta, tana kallon kayan da ke jikin Waheeda.
Bayan sun shiga ciki, nan ne ta sanar da Ummah abin da ya faru na al’adar da Waheeda ta fara yau, amma ko kusa ba ta sanar da ita komai dangane da gane-ganen da Waheeda ta fara ba.
Sosai Ummah ta yi mata godiya da kuma yabawa da hankalinta. Ko da za ta tashi tafiya, dari biyar Ummah ta ba ta akan ta yi kuɗin abin hawa, amma sam ta ƙi karɓa ta ce ai tana da kuɗi a hannunta.
Salma Ummah ta sanya ta raka ta, tare da umartar ta da ta tabbatar ta samu abin hawa kafin ta dawo gida.
Sai da suka fita kafin Ummah ta dawo da kallanta kan Waheeda dake kwance akan gado, ta ba ta baya.
“Uwata, tashi mu yi magana.”
“Ummah, bacci nake ji.”
Sa hannu ta yi ta ɗagata zaune, sannan ta riƙe hannayenta duka biyu.
“Mamana, kina jina ko? Yanzu ke ba yarinya ba ce, kin ƙara girma. Duk macen da ta soma ganin al’adarta, to ta tashi daga yarinya ta koma ’yan mata. Kina jina kam ko?”
Kai ta gyada mata tana kallon Ummah, cikin maida hankalinta gaba ɗaya a kanta.
Ummah ta ci gaba ganin tana fahimtar ta.
“Da kyau. Abin da nake so ki sani shi ne, yanzu ba kowane namiji za ki dinga magana da shi ko kuma ki dinga taɓa shi ba.”
Cikin katse mata hanzari ta furta,
“To Ummah, me yasa?”
“Saboda kin ga wannan tafin hannun naki?”
Ta faɗa tana ɗago tafin hannunta sama kaɗan, ta daura yar yatsarta a saman tafin hannunta, sannan ta ci gaba da faɗin,
“Saboda duk namijin da kika bari ya riƙe miki hannu kamar haka, to za ki ɗauki ciki. Ki haihu.”
Da wani irin sauri ta fisge hannunta daga na Ummah.
“Ciki kuma irin wanda ake haifo yara?”
Ta faɗa tana zazzare ido.
Cikin son ƙara tsoratar da ita, Ummah ta gyada kai tana faɗin,
“Kwarai, da gaske.”
Narai-narai ta yi da idanu, ta koma kalar tausayi ta ce,
“Ni dai babu ruwana. Ba zan taɓa barin namiji ya taɓa ni ba, har da Baba Ƙarami da Yaya Ado.”
Dariya ta yi da jin abin da ta faɗa.
“Su ai ’yan uwanki ne. Waɗanda suka kasance bare a gare ki nake magana, amma banda yayyunki maza.”
“To shikenan, Ummah.”
Bayan sun gama wannan tattaunawar ne Ummah ta ƙara mata da karatun yadda za ta dinga kula da kanta da yadda za ta yi wanka bayan gama al’ada da dai sauransu, haka har Salma ta dawo daga rakiya.
Washegari ta shirya da wuri saboda jarabawar da suke da ita da ƙarfe 8 na safe, kuma ga shi ita kaɗai za ta tafi. Su Iklima sun yi hutu, su ne kaɗai masu zuwa saboda jarabawar da suke yi.
“Ummah, na tafi, sai na dawo.”
Ummah da ta gama zuba kosai a leda ne ta ɗago ta ce,
“Allah ya taimaka. Ga wannan kosan, ki miƙa gidan Mai Dawah. Daga can ki wuce makarantar.”
Ɓata rai ta yi ta soma buga kafa, don ba ta san abin da zai sa ta yi late ba.
“Ki ba Yaya Salma mana, ta kai ni fa sauri nake yi, kar na makara. Shi sa ko karyawa bazan tsaya yi ba.”
“Ai na san da ita, nace ke ki kai. Na ga dai duk hanyar za ki bi?”
Tana tura baki ta sa hannu ta karɓi ledar, ta soma tafiya tana kunkuni, wai ga Salma nan, ita ba za a aike ta ba, sai ita da take saurin zuwa zana jarabawa.
Wurga mata harara Ummah ta yi tana faɗin,
“In kin gama zagin nawa, sai ki zo ki rufe ni da duka, kin ji?”
Uffan ba ta ce ba, ta bar gidan.
Ganin gate ɗin gidan a wangale ne ya sa ta sa kai ta shige gidan. Mutane ta gani a tsaye a hanyar mashigar falon, suna cikin shiga ta alfarma, sannan uwa uba ga fuskar wanda take yawan gani ana nunawa a TV, kan cewa shi ne Sarkin su na jihar Gombe, sai wasu samari masu kama da BK da ta gani tsaye a gefensu.
Ko da ta iso kusa da su, kanta a ƙasa ta gaishe su, sannan ta wuce ciki. Da kallo su Ya Abdul-Samad suka bi bayanta.
Yau dai ba ta samu haɗuwa da Nini ba. Zanaya ta tarar a kan kujera, hakan ya sa ta nufe ta tare da faɗin,
“Sannunki, wai ga kosan ku in ji Ummanmu.”
Murmushi Zanaya ta sakar mata tare da miƙa hannu da nufin karɓan ledar. Nan ne hannunsu ya gogi na juna. Wani irin azabar shocking ta ji ya kamata a lokacin da hannunsu suka haɗu. Ta ji wani irin abu mai zafi, tamkar barkono a idanunta.
Da sauri ta sakar mata ledar ta ja baya, ta ɗan fitar da sautin azaba tana rufe idanunta da hannu.
Zanaya da ta ga haka, sai ta miƙe tana tambayar ta abin da ya same ta, cike da damuwa, amma Waheeda ta kasa ba ta amsa.
BK da Zannor da suke saukowa a tare ne suka yi saurin isowa falon ganin abin da yake faruwa.
“Me ya same ki?”
Cewar BK cikin sauri, yana kallon Waheeda wadda ta dafe idanunta da hannaye, hawaye na ƙoƙarin zubowa daga cikin idanunta.
Zannor ya nufi Zanaya da sauri.
“Me ya faru?”
“Ban sani ba. Muna tsaye ne kawai, zan karɓi kosai, nan take ta saki ledar ta ja baya tana cewa wani abu ya shiga mata idanu.”
BK ya sake kallon Waheeda.
“Waheeda.”
Ba ta amsa ba, hakan ya sa ya furta,
“Besty, ki buɗe idanunki.”
A hankali ta cire hannayenta daga idanunta, amma take buɗe su sam.
Cikin rawar murya ta furta,
“Ba wannan ba ce ta watsa min barkono a idanuna. Tana son makantar da ni.”
Kallon juna suka yi, musamman Zanaya wadda ta cika da mamakin abin da ya fito daga bakin Waheeda.
“Ni kuma? Akan me yasa zan watsa miki barkono a ido? Ya BK, wallahi ban mata komai ba. Iya abin da na faɗa muku shi ne kawai ya faru.”
Alama ya yi mata na ta kwantar da hankalinta. Nan ya riƙe hannunta ya ja ta bakin sink ɗin dake a falon. Ya tara ruwa ya wanke mata fuska kusan sau uku, sai a sannan ya samu ta buɗe idanunta.
Ai kuwa sosai suka rine, suka yi bala’in jajir, alamar sun sha wahala.
Duk suka yi mata sannu. Zanaya ta sake faɗa mata cewa ita ba ta zuba mata komai ba, hasalima babu wani yaji a falon sai iya wanda ta kawo, kuma shi yana cikin kosan a daure, ba yadda za a yi ya shigawa mutum ido.
Ba yadda BK bai yi na su ajiye ta a makaranta ba, amma ta ƙi amincewa. Ta ce ita a kafa za ta yi tafiyarta, don ta san in Ummah ko Baba Ƙarami suka samu labarin ta shiga motar mutane, to ta banu. Hakan ya sa ta yi tafiyarta.
Ana tashi, ba ta tsaya ko ina ba, ta dawo gida. Ta samu ana ta buga gurmi tsakanin Mama Sadiya da ’yan adashe, wai ta cinye musu kuɗin adashe, za su kira mata mutane.
Ummah ce ta shiga tsakanin su, ta dinga ba su haƙuri, amma Mama Jamila kam ko bin ta kan su ba ta yi ba. Ita haka ɗabi’arta take, duk abin da za a yi, inde bai shafe ta ba, da wuya ta saka muku baki.
Waheeda da ta ga yau gidan nasu a rikice yake, kawai ta shige ciki ta yi zamanta. Ta fito da littafin makarantarta ta fara duba abin da za su yi gobe.
“Heedah, yaushe kika shigo?”
Cewar Salma da yanzu shigowarta ɗakin ta tadda ita zaune.
“Ban jima ba. Me ya faru? Na ga gidan haka.”
Taɓe baki ta yi tana zama, ta ce,
“Mama Sadiya ce ta cinye wa mutane kuɗin adashe. Ashe duk burga da nama da girkin da take yi ta kashe mu da ƙamshi, ashe kuɗin jama’a ta tattara tana cinyewa.”
Cike da dariyar ƙeta Waheeda ta ce,
“Kayyasa! Dama an ce rana dubu ta barawo, rana ɗaya ta mai kaya. Shi ne Ummah ta tsaya tana kare ta duk irin rashin mutuncin da suke mata. Lallai kam, na rasa wace irin zuciya ce da ita wallahi.”
“Ki bari kawai. Ya jarabawar taki ta kasance?”
Ta tambayeta tana karɓan littafin hannunta.
“Ni ma fa, da yanzu na san ko ban kammala jami’a ba, da ina gabar ƙarshe.”
Waheeda ta saki murmushi tana kallon ’yar uwarta.
“Kar ki damu, Yaya Salma. In dai karatu ne za ki yi, in sha Allah.”
“Allah ya yarda.”
Sima ce zaune a garden ɗin gidan tana waya. Kallo ɗaya za ka mata ka fahimci tana cikin nishaɗi, sai juya wata ƙaramar kwalba take a hannunta.
Ta furta,
“Na ji daɗi sosai, kawata. Driver ɗin ki ya kawo min maganin, kuma zan yi amfani da shi yadda ya dace. Nan da kwana biyu akwai taron da ’yan gidan za su tafi, amma shi bana tunanin zai je. Kin ga nan ne zan samu damar aikata duk abin da nake so. Matukar ya sha wannan maganin, magana ta kare.”
Murmushi kawai take sakewa tana sauraron ƙawarta da muguwar shawarar da take ba ta.
“Na gode sosai. Ke kam duk yadda ta yi, za ki ji ni. Sai anjima.”
Bayan ta kashe wayar ne ta kalli kwalbar, tana murmushin jin daɗi tare da faɗin,
“BK, my love, daga nan zuwa kwana biyu za ka zama mallakina. Zan jiyar da kai daɗin da ba ka taɓa ji ba.”
Ya Ado ne ya shigo gidan, hannunsa riƙe da baƙaƙen ledoji guda uku ɗauke da kifin ruwa a ciki. Ya raba ne domin ya ba kowane ɗaki nasu, saboda in ya ba Mama Sadiya, akan a dafa duka gida ne, to ba ƙaramin aikinta ba ne. In ta gama, ta hana ɗakin Ummah, sai dai su ji ƙamshi, amma ba su za ta yi ba. Shi yasa tun da ya fahimci in ya samu kuɗi ya sayi abu ya kawo, ba a ba su , sai ya koma yana siya kashi uku.
Waheeda na ganin sa ta nufe shi da gudu tana amshe leda ɗaya, don ta san na su ne, tare da yi masa barka da zuwa, wanda ya kwana biyu bai zo gidan ba.
Girgiza kai kawai Ummah ta yi tana addu’ar Allah ya shiryi Waheeda.
“Barka da rana, Ummah.”
“Sannu Ado, ya ƙoƙari?” Ummah ta tambaya cike da kulawa.
“Alhamdulillah. Ashe auta ta kammala jarabawarta. To, Allah yasa mu ga sakamako mai kyau.”
A tare suka amsa da “Ameen,” amma banda Mama Jamila dake ta wanki.
Zuwaira da Salma kallo suke a waya. Yau babu tallan rana, sun ce yau za su huta.
Duk da yadda babu jituwa a tsakaninsu saboda sun kasance ’ya’yan kishiyoyi, amma fa manyan ƙawaye ne kuma ’yan uwa. Haka za su yi fadan su su shirya, har cikin ransu ba sa son fadan da iyayensu suke yi, musamman Zuwairah, don ta san mahaifiyarta ce mai yawan tada husuma. A hakan ma Ummah ba kulata take yi ba, sai dai Waheeda da Salma ne masu tankawa.
Sallama suka ji a ƙofar gida. Har Ya Ado zai miƙe, Zuwairah ta yi saurin cewa,
“Bari in duba.”
Ta fita ba tare da ta jira amsarsa ba.
Shigowa gidan ta yi da sauri tana zare ido, alamar ta ga abin mamaki.
“Ummah, yaran gidan Mai Dawah ne suke neman izinin shigowa.”
“Mai Dawah kuma? Me suke nema?” Cewar Ya Ado, da shi ma ya cika da mamaki jin sunan su.
Mama Sadiya, jiki na rawa, ta ce wa Zuwairah,
“Maza ce musu su shigo mana. Kin bar su a rana.”
Hijabi Ummah ta sanya a jikinta ganin Zuwairah ta tafi yi musu iso.
Waheeda na a ɗakin Ummah, ba ta ma san me ke faruwa ba, don tunda ta karɓi kifin hannun Ya Ado ta sanya a roba ta shige ciki.
Zannor, BK da Nini ne suka shigo, sai ma’aikatan gidansu suna sanye da uniform ɗin aiki suka shigo da kayan abinci buhu-buhu.
Cikin girmamawa da mutuntawa suka gaisa. Nan suka sanar da su suna raba zakka ne gida-gida, shi ne suka kawo musu.
Tunda suka shigo gidan, Zannor ya zuba wa Salma ido. Duk sanda ta ɗago kai, sai sun haɗa ido, har ta gaji ta murguɗa masa baki. Murmushi kawai ya yi, yana jin wani abu a ransa dangane da ita.
Bai taɓa tsammanin Waheeda tana da ’yar uwa ba sai yanzu da ya ganta. Ganin farko suka yi wa Ummah, suka fahimci ita ce mahaifiyarta saboda suna ɗan kamanni. Ita kuma Salma tana diban kama da Ummah, hakan yasa ya fahimci ’yar uwar Waheeda ce, ciki ɗaya.
Tana kwance akan gado ta ji hayaniya a tsakar gidan, muryoyi da yawa. Hakan ya sa ta miƙe ta fito don ganin su waye a gidan nasu.
Sake baki da hanci ta yi ganin su BK. Tambayar kan ta ta shiga yi, me ya kawo su gidan su.
Da gudu Nini ta nufe ta ta rungumeta tana faɗin,
“Kawata, ina kika shiga? Kwana biyu bana ganin ki.”
Murmushi ta yi ta ce,
“Jarabawa nake yi, shi sa.”
Nini ta dafe goshi tana cewa,
“Wayyo, na manta! Ashe Ya BK ya faɗa min.”
Kai ta ɗaga ta dube shi, ta ga idanunsa na kanta. Murmushi ta sake, ta ɗan motsa lips ɗinta ta furta,
“Barka, Besty na.”
Murmushi ya sakar mata bayan ya karanci motsin labbanta.
“Barka, Zannor,” ta faɗa a fili tana kallansa.
Ummah ce ta ce,
“Auta, har yaushe kika fara kiran babba da sunansa kai tsaye?”
Dariya ta yi tana runtse ido, ta kuma ce,
“Barka, Ya Zannor.”
Sai da ya yi dariya kafin ya amsa yana zolayarta.
Sosai suka yi musu godiya.
“Ummanmu, bari in raka Nini waje.”
Kai kawai ta gyada mata, sannan suka fita suna musu sallama.
Daga waje, ta ƙofar gida suka dakata. Muryarsa ta ji yana tambayarta,
“Ya jarabawar?”
“Babu daɗi fa ko kaɗan, amma dai na ji daɗi da muka gama.”
Ya ɗan gyada kai yana kallonta.
“Allah ya sa kin yi abin da zai sa ki samu sakamako mai kyau.”
“Ameen.”
“Ya idanun naki yanzu sun daina miki zafi ko?”
“Eh, sun daina.”
Zannor da ya gama amsa wayar da yake yi ne ya dawo wajen su, yana kallon su biyun.
“Bestyn BK, shi ne ranar kika ƙi yarda mu kai ki school ko?”
Ta yi saurin girgiza kai tana kyafkyafta idanu.
“Tab! Idan Ummah ko Baba Karami suka ji labarin na shiga motar mutane, na banu. Musamman ma Baba Karami, yankani zai yi.”
A hankali BK ya furta,
“Na ga alama kina tsoron wannan Baba Karamin nan.”
Gyara tsayuwarta ta yi da niyyar fara magana, ta hango shi yana tahowa cikin takunsa na isa da jarumta, kamar yadda ya saba.
“Ɗan halak, ka ƙi ambato.”
Maganar da ta yi a zuciya kenan ta fito fili, hakan yasa suka kai dubansu inda take kallo.
Ko da ya iso, fuskarsa a haɗe, babu yabo babu fallasa. Ya miƙa musu hannu suka gaisa, sannan ya juya kan Waheeda.
“Kin zuba min waɗannan manyan idanun naki, wuce ki shiga gida.”
Ya faɗa yana watsa mata harara. Ko ta kansu BK ba ta bi ba, ta arce cikin gida a saba’in. Ya rufa mata baya.
Kallon juna BK da Zannor suka yi kafin Zannor ya sanya dariya yana faɗin,
“Tabb, wannan yayan nasu ɗan zafin kai ne.”
“Na gani ai,” cewar BK yana ɗan murmushi, sannan suka wuce gida.
Dakatawa ya yi yana kallon tulin kayan abincin da suke baje a tsakar gidan, yana mamakin waɗannan daga ina.
“Wannan fa?” Ya faɗa yana nuna su da hannu.
Nan ne Ya Ado ya sanar cewa waɗanda suka fita su ne suka kawo musu zakka.
Jinjina kai ya yi ya furta,
“An gode.”
Mama Jamila ta ce,
“To yanzu ya za a yi da kayan? Rabawa za a yi ko kuma a ajiye ne, a dinga ɗiba ana girkawa?”
Mama Sadiya, kamar jira take yi, ta yi caraf ta amsa da,
“Ah ah, babu batun a dinga ɗiba ana girkawa. Gwara a raba a ba kowa nasa yawwa.”
Girgiza kai Ya Ado ya yi.
“Haba Mama, duka dai dafa su za a yi. Ba gwara a ajiye ake girkawa ba?”
“Hakane Ado. Hakan ma zai fi. Ban ga amfanin kacancana shi ba, duk da suna da yawa,” cewar Mama Jamila.
Ita Mama Sadiya ba haka ranta ya so ba. Hakan yasa ta taɓe baki. Ta so a ce Ummah ta yi magana ta gaggaya mata maganganu, amma ko ɗago kai ba ta yi ba balle ta sa baki.
Haka shi ma Baba Karami bai ce komai ba. Ya samu wuri ya zauna kusa da Ummah yana daura kansa a kafadarta.
Sai ji ya yi Mama Jamila ta ce,
“Baba Karami, in ya so sai ka cire na gidanka a ciki, kai ma ka huta da cefane na kwana biyu.”
“Kar ki damu. Labiba ba ma iya girki take yi ba, ba sai na ɗiba ba.”
Daga nan shuru ya mamaye gidan. Kowa ya yi shuru. Katse shurun ya yi ta hanyar faɗin,
“Ummah, in ba damuwa, ina so Labiba ta dawo gidan nan. Jikin nata sai ƙara tsauri yake, kuma ita kaɗai a gida. Ni kuma sai dare nake dawowa. Sannan bana son turata gidansu, kin san kishiyoyin babarta ba kaunarta suke yi ba.”
Ummah dama ta fahimci akwai damuwa a tattare da shi, ta ce,
“Ba komai, Babana. Gwara ta dawo nan ɗin saboda ta dinga samun kulawa har Allah ya sauke ta lafiya.”
“Na gode, Ummah.”
“Tsaya-tsaya! Yanzu na fara fahimtar inda wannan labarin na ki ya dosa yanzu, yar uwa. Alaka tsakanin Muhammad BK da ita Waheeda ya fara ƙarfi. Ina ji a jikina wannan ba iya abota ba ce, zai iya juyawa ya koma wata babbar alaka ta musamman.”
Cewar Sani da ya nutsu guri ɗaya a gabanta, suna sauraron labarin da take ba su.
Girgiza kai ta yi, ta yi murmushi na takaici, sannan ta ajiye kofin shayin da yanzu kam sanyi ya yi kalau. Ta duba wayarta, nan ta ga ƙarfe goma sha biyu na dare.
Da hanzari ta miƙe ta sanya takalmanta. Su ma ’yan majalisan majiya labaran da take bayarwa suka miƙe, suna kallonta cike da tsoron kar ta ce tafiya za ta yi ba tare da ta karasa musu labarin Waheeda da Muhammad BK ba.
“Yarinyata, ya na ga kin miƙe? Kar dai tafiya za ki yi.”
Kai ta gyada masa.
“Hakane, Baba. Zan tafi. Lokaci ya kure. Ba zan iya ci gaba da ɓata lokaci ina bayar da labari ba, bayan akwai abubuwa masu muhimmanci da ya kamata in yi.”
“Mun sani, amma don Allah ki yi wa Allah ki karasa mana wannan labarin. In kika bar mu a nan, za ki bar mu da zullumin ya ƙarshen labarin ya kasance.”
Cewar wani mutum a cikinsu. Ya yi maganar ɗauke da damuwa akan fuskarsa.
A taƙaice ta furta,
“Wannan labarin ba shi da ƙarshe. Ni kaina ban san yadda ƙarshensa zai kasance ba, balle in sanar da ku.”
Ya kuma faɗin,
“Na fahimce ki, kuma mun fahimci muna ɓata miki lokaci. Ki ba mu labarin a ɗan taƙaice, inda ya fi muhimmanci a cikin labarin. Daga nan mu kuma mun miki alkawarin tafiya tare da ke domin neman ita wannan Waheedan.”
Ajiyar zuciya ta sauke, alamar ta amince da zancensa, sannan ta koma ta zauna.
Zama suka yi suna jin daɗin amincewarta.
Ci gaban labari…
Follow me for more interesting chapters 🥰🤌🏻