Chapter 22:RDBG
RAUNIN DA BA A GANI
Meefat ink ✍️ writers
Mamace zaune adakinta waya kare akunnenta dagani waya mai muhimmanci take “eh naji, aa kada kadamu, kacigabada abinda nace maka idan lokaci yayi zansake tuntubanka” sai takashe wayar, adaidai lokacin adamu yayi sallama ta amsa tana gyara zamanta akan gadon, dago kai tayi ta kallesa sai tace “lafiya dai ko” ciro wayarsa yayi a aljihu ya kunna wani video yamika mata yana cewa “mama kiga videon nan” karba tayi tana kallo bayan tagama ta mikamasa batareda tace komai ba “ wallahi mama abinnan yadameni har yanzu ban daina mamakiba tayaya za ace azan ne zai wakilci daddy a'irin wannan taron"sai yafara tafiya acikin dakin cikin tsantsar takaici “munanan fa mama nida hamis mune manyan y'ay'an daddy, mu yakamata mutane su sani mu yakamata mu wakilceshi amma tunda wannan yaron yazu kullum shi da wannan jabir din” sai ya danyi shuru sannan yace cikin karin takaici “kuma Jay dinnan fa ba dansa bane amma koda yaushe yana cikin family affairs dinmu kamar wani dan gidan”mama dai tayi shuru tana sauraronsa sai yacigaba “daga companies zuwa manyan al’amura kullum Jay da azan mu kuma kamar bama cikin gidan"mama tadanyi murmushin takaici takalli dannata tace “da ace dan uwanka bai aikata abinda ya aikataba dana tabbata yanzu ku kuke jan ragamar komai na yola holdings, na tabbatar da cewa har yanzu mahaifinku na fushi daku dan da ace dagaske yayafe da yabarku kuncigaba kamar da” shuru yayi har tagama kafin yace “to me zamuyi yanzu mama” “ka tuna abinda nagaya maka kwana kin baya” sai ya gyada kai, sai tace “ba kowani abu bane ake warwareshi cikin gaggawa” sai ta danyi shuru kafin tace “inada abinda nake shiryawa, idan nagama” sai ta danyi murmushi “sai mu koma kan shi” “kin tabbata mama” “na tabbata dan haka ka kwantar da hankalinka kabar komai a hannuna” sai ya sauke nunfashi ahankali ya mike yamata sallama ya tafi. Komawa tayi tazauna ta kalli wayar hannunta sai tace “banyi tunanin zuwan me jajayen kunnuwannan zai kawomin cikas ba amma zanyi maganinka dan shi jabir karamin kwarone” sai ta ajiye wayar zuciyarta cikeda shirin da aganinta shine karewar komai.
Isowaarsa direct sashensa yanufa dan yasauya kayan jikinsa, yana gamawa yafito tsaf dashi cikin kananan kaya yawuce direct masallacin kusa dasu yayi sallan azahar sannan yakoma, tunuwa dayayi yamanta wayarshi adaki yasa yakoma missed calls yagani wasu daga company bai saya bita kansuba yadauka zai fita sai kiran Jay ya shigo “ hey man” sai azan cikin tsokana yace “wai har kayi missing dina” tsaki Jay yaja azan yaware ido yace “wato daga zuwanka har ka koyi wannan abun koh” “grand ma dinka ce takoyamin” dariya sukayi sai Jay yace “ motocin fa sun iso man” da mamaki azan yace “which cars” “The rolls-royce i booked few weeks back toh dazu jax yakira yace sun iso” sai azan yace “umm that's good” “yeah and it's for both of us” sai yafita a parlourn yana nufan side din mamy “both of us kuma” sabida har ga Allah yamanta wani booking na mota da sukayi sai Jay yace “u remember time dinda nake booking, har kace bakada sha’awar irin motarnan i though u were joking so sai nayi booking biyu” sai azan ya girgiza kai yace “ ok then i will use it idan naga dama idan kuma banga daman ba I will just give it to someone else”.
Mamy na zaune a parlournta tana waya da kanwarta dake can turkey, sai tafara murmushi data hangosa yana shigowa.