SHI SO DABAN YAKE

Babi na goma sha uku

by @dijensy

13



    Jidda har washegari bata sakko ba daga fushin da take dashi Hassan kuwa wani irin kusanci ya sake ji ya shiga tsakaninsu da Jidda haka ya shiga tarereyarta ta wata sigar kulawa ta musamman da bai mata kalarta ba a baya ,gashi tunda ya ɗanɗana zaƙin zumarta wani fitinar sake komawa duniyar da ya tsunduma yake so Jidda maida shi ta ƙi bari tsahon kwana na biyar shi kansa mamakin kansa yake da ya kasa dai daita jikinsa ji yake kamar bashi da lafiya.Yau ta gama shirin kwanciyarta ta ji hannunsa yana lalubenta ta shiga tureshi tana ƙoƙarin tashi ya danneta da nauyin jikinsa yana marairaice mata yana fuskantarta  ta yi ƙasa da ido “Jiddahtuna kinsan da bansan ina raye ba sai da kika sabunta ni naji ashe da ba a cikakkiyar rayuwa nake ba ,kamar rubutune fa ba wasali Jiddana na”Jidda bata shirya ba murmushi ya suɓuce mata tana mamakun yadda Ustaz Hassan duk akan wannan abun yake mata magiya haka  kamar zai kuka,ya sake haɗe jikinsu yana fara yawo da hannunsa a sassan jikinta ta lumshe ido wani irin saƙonni suna shigarta a hankali “Mai kike so ki faɗa min zan siya maki”.Ya tambaya da wani irin salon magana Jidda ta ɗago idanunta suna sarƙafewa da nashi  dukda ba haske ɗakin amma ana gani kaɗan da farin hasken wata “iphone”.Ta furta “I promise”Hassan ya saurin faɗa yana cigaba da mata wasanni sai nishi nishi take tana ɗan jin tsoro  rigarta ya cire mata ya cigaba da romancing nata yana gangarawa da hannunsa ƙasa bata yi tsamnani ba ta ji yatsansa a cikin jikinta tayi ‘yar ƙara gam ta riƙe masa hannu tana maƙale jiki ta turo baki a shagwaɓe “A hankula Allah”Ta faɗa ya nodding kai a buƙace yake jinsa yayi ƙoƙarin binta a hankali amma duk da haka sai da ta mashi kuka ya shiga lallashinta bayan da komai ya lafa ƙaunar Jidda na ƙara hauhawa a zuciyarsa yau tare sukai wanka ta fito sai haɗe masa rai take da harara shikuwa wani shauqi na sonta na ɗibansa.



        Wani irin so da ƙauna Hassan yake nunawa Jidda duk sanda zai kusanceta sai ta sa yayi alkawarin siya mata abu shine zata yarda shikuwa sai ya ƙuƙuta ya saya mata haka ya sayo mata felleliyar iphone irin wacce aka sace mata ta maida masa da samsung ɗin tasa bayan ta kwashe komai na ciki iya abinda ta samesa dashi ta bari,Jidda bata fasa karɓar kuɗi ba  ta mayar da yin hakan kamar sana’ar gida  balle da jikinta ya fara karɓa yanzu bata jin zafi irin farko farko ko kuɗin ta karɓe masa duk a abin banza take ƙararwa , watanni sun shuɗe bikin yaya ibrahim ya matso kusa duk wani shigar da ta yi niyya sai da ta mallaka Anty baby har mamakin yadda take fantamawa take da ƙyar Baba ya barta tayi kwana ɗaya shima don Hassan ɗin yayi magana dashi ya roƙa mat Baba  ne amma niyyarta tayi kwana uku ko huɗu.Washegarin biki tana haɗa kayanta zata tafi kowa ya watse tana jin idon Anty baby kanta kafin ta ce “Jidda nawa kika sayi takalminnan ?”Ta tambayeta don a saninta ya kai 38k zuwa sama ta kalli Anty baby “Hassan ya siya min a wajen wata gurin aikinsu nima bansan nawa bane”Tayi ƙarya “Sannu matar mijinta yaushe zaki tafi to?”


 “Gajiya kukai dani?da yamma zai zo mu tafi”.Ta furta tana tashi ta fita tsakar gida ta kira Abdallah dubu biyu ta bashi ya je ya siyo mata nama ta komo ɗaki ta ƙarasa haɗa kan kayanta ta ruwan wankan da Umma ta jona a heater ta ɗakko bokiti ta juye ta shiga wanka.

              

          

                            *****


      

          Dawowarta gida da kwana biyu Husna ƙanwar Hassan ta zo daga Jos da yaronta ɗaya tun ana gobe ya faɗa mata zata zo a gidan zata sauka Anty Ruƙayya an mata rasuwa taje jigawa yayar mahaifiyarta ta rasu.Ba wani abun arziƙi tayi mata na tarba ba shinkafa da wake kawai tayi kaɗan taci itama don ta yi order chips da nama har ta hallaka shi a cikinta.Husnah da kwatance da tambaya ta gane gidan shima da hassan sukai waya Jidda ta ƙarar da charge wayarta har ta mutu taji an ƙwanƙwaso ta ƙarasa ƙofar ta buɗe tana kallon Husna riƙe da yaronta a hannu tayi murmushi Jidda ba yabo ba fallasa take kallonta kafin  ta matsa “Sannu da zuwa”Ta faɗa tana kalle Husna  dake shigowa suna kama da Hassan musamman murmushinsu ta rufe ƙofar tana shiga parlour Husna na biye a bayanta a gajiye take don daga bakin titi a ƙafa ta shigo ga kaya ga yaro a goye yake saukesa tayi sabida gajiya Husna ta gaisheta “Lafiya lau ya hanya?”Murmushi Husna tayi tana amsawa “Lafiya lau ba a taɓa haɗuwa ba sai ysu Allah ya nufa ya taro yace min kunyi biki ko ? da ai satin baya zan zo yace kuna biki”.Jidda ta giɗa kai tace lafiya lau yaron hannunta nata  kokawa a sauke shi ƙasan kujera tayi murmushi “Arif ,zaka je gurin Anty ?”Jidda  ƙemadagas ko karar ta miƙa hannu ta ɗaukesa bata yi ba shiru ya ratsa parlourn Arif ya ƙware Jidda still ta zuba masa ido Husna nata jijjigasa ba sannu daga bakinta tana kallon Husna ta kwantar dashi ta bashi nono Jidda ta tashi kitchen ta shiga ta ɗakko musu shinkafa da wake a warmer ta kawo mai da yaji ta ajje da cokali.Hijab ta saka ta fita bayan da tace mata zata karɓo charge power bank Husna ta buɗe kwano ta ga shinkafa da wake a tunaninta dan bowl din miya ce ciki ta ga man gyada  suna  da rufun asiri ita shinkafa da wake ma bata iya ci a haka sai dai da miya da kayan ganye su da suke da vegetable dayawa  a garinsu waken ta dan matse ta sa ma Arif a baki ya dawo dashi gashi ita kanta yunwa take ji balle ta bashi nono ya sha ya koshi Jidda ta dawo Husna ta tashi ta ce mata zata yi alwala Jidda ta nuna mata banɗakin dake tsakar gida ta shiga Arif yana kwance tana binsa da kallo ta leƙa ta ga akwai alamar pampers jikinsa ta tafi ɗaki ta jona wayarta a jikin power bank din kwanciyarta tayi tana danna wayar ganin karan charge  goma ya hau a parlour ta bar Husna tayi sallah ta idar haka ta ja plate ta caski shinkafar nan ko rabi ta kasa ci ta rife zuciyarta tana ta saƙe saƙe kowa da irin sa idan Anty Ruƙayya ce tab abinci na musamman zata mata da tuni ma yaran sun kewayeta suna hira ga faraa gurin Anty Ruƙayya.Jidda ta shantake tana ta duba tiktok har yamma tayi Hassan ya dawo ya shigo parlour yana sallama Husna ta amsa fuskarta dauke da murmushi cikeda faraa ya zauna gefen kujera suna gaisawa ya karbi Arif yana ta yan kananun kuka “Kwiya yake Husna kin koya masa halinki?”Dariya tayi “Baya fa kwiya wallahi watakila bacci yake ji ya gaji”.


 “A mashi wanka mana toh”Ya faɗa sai a sannan ma ya lura da ƙaramar akwatun kayansu da tana gefen kujera bai ga ɗuriyar Jidda ba ya tashi ɗaki ya shiga ya tarar da ita ta yi ruf da jiki tana ta latsa wayarta ya zare earpiec ɗin kunnen nata a hankali ta waiwayo tana kallonsa ta mike zaune “Yaushe ka shigo?”Ta tambaya ya kalleta “Yanzunnan ”.Ya amsa yana juyawa ya buɗe sif ya ciro makullin ɗakin waje ya fita  sai da ya share ɗakin bayan ya buɗe ba komai ciki sai leda da katifa yar karama da yasa daga baya ,Husna ya kira bayan ya ɗakko mata akwatun kayan ya ajje ta shiga ta zauna“Wanka yakamata ai ki masa Husna bai saba da garin Kano ba bai ma taɓa zuwa ba inaga ko?”Murmushi tayi Hassan ya koma ɗaki ya ɗakko blanket ya dawo ta karɓa tana godiya .”Bara na shiga masalallaci”Ya faɗa yana ficewa da yaji ana kiran sallah bayan ya sha ruwa dashi yayi buɗa baki yana idar da sallah Hassan ya fita yar siyayya ya siyo Rufaida,fruit sai tsire da ya kusa ƙarasowa ya tsaya shago ya sayi bread da madara  ya dawo  Arif sai kuka yake ya kawo flask da ruwa ciki  ya wanke banɗakin tsakar gidan ya zuba ruwa dukda da akwai a fanfo wani ruwan ya sake haɗawa ya zuba a flask Jidda ta fito kitchen ɗin tana kallonsa ya buɗe warmer da ta sa mashi shinkafar kayan shayi da bread  ya dauka ya kai wa Husna da flask na ruwan zafi da cokali da kofuna ruwan bunu yasha Hassan ya haɗa da tea yaci shinkafar da Jidda ta ajje masa Husna kuwa ta sauri ta haɗawa arif shayi ta na haɗa masa da tsomen bread ya na wawura.Shayi ta haɗa itama ta sha taci da bread ɗin ta haɗa da nama ta ɗan ji dama dama Hassan ya shiga parlour ya ajjewa Jidda nata naman ya duba ɗaki ta shiga banɗaki a lokacin koma wajen Husna ya zauna a ɗan gefe ya karɓi Arif sai yanzu yake ‘bangala masa dariya yana masa wasa ,sun jima suna hira da Husna har yaron yayi bacci a kafaɗarsa ya tashi yana mata sai da safe ta kwantar da yaron ya fita bayan ya kwashe kofunan da suka sha shayi ya dauraye ya shiga ɗakinsu hakimar tana kan katifa aikin da ta saba danna waya sau ɗaya ta ɗago ta kalli hassan ta ajje wayar ta tashi tana shiga wanka ta fito  tana jin idanunsa kanta har ta sa kayanta na barci ya tako zuwa inda take ta ji ya zagayo da hannayensa daga bayanta zuwa cikinta ya rungumeta ta baya “Amiraty  na daɗe?kinsan mun daɗe bamu haɗu da ƙanwar tamu ba”.Ya faɗa don a tunaninsa ko lefi yayi.


  “Ni nace ma kewarka nake ?”Murmushi yayi Hassan yana mata cakul kuli “Tohm ni nayi sosai sosai”.Kafaɗa ta maƙale yana mata sunba a wuya ta juyo tana kicin kicin da fuska “Ka bari mana na gaji”.


 “Ina da maganin gajiyar fa”Ya faɗa ta hararesa ta san me yake nufi ta canja maganar da tambayarsa mai ya siyowa baƙuwar tashi ba tare da ya kaeo komai ba ya faɗa mata duk abinda ya siyo ɗin ta giɗa kai tana faɗawa kan katifar ya bita da kallo zuciyarsa cikeda ƙaunarta.Washegari da safe yana gida yau yana off da wuri ya tashi ya fereye doya ya ɗora a gas doya da ƙwai zai musu Jidda baccinta tasha ta farka taga ya kammala komai ya kaiwa Husna tun ɗazu sun gaisa tayi masa godiya ya shigo parlour ya tarar Jidda na zaune a plate ɗaya ya xuba musu ya haɗa mata shayin.Jidda ba abinda ya  shafeta da wata Husna idan banda Husna ta shigo parlour sun gaisa da bazata je wajenta ba ,Husna waya ta sake yi da Anty Ruƙayya ta tambaya yaushe zata dawo ta faɗa mata gobe.Kwana biyunnan da Husna tayi sai da ta fuskanci hali na Jidda gabaɗaya yanayin zaman yayanta da Jidda bai mata ba ta fuskanci ba iya baƙi takewa ba hatta mijin bai kaucewa raini da wulaƙanci na Jidda ba ranta ba daɗi haka ta tafi da yammaci sai da ya dawo ya raka Husna har gidan Anty Ruƙayya ya fahimci ita kanta bata sake a gidansa ba yasa bai takura sai dole ta zauna wajensa ba ,bayan ya rakata gidan ya wuce makarantar darensu.Jidda suna tafiya  ta ji ta sakata ta wala da duk a takure take jinta kamar a kanta suka zauna,yau daman tana son ‘yan chanji a gurinsa da biyu ta ja hankalinsa tasa shi sai da suka raya dare ta karɓe matsabbanta.


  Husna washegari da safe ta kasa ɓoyewa Anty Ruƙayya sai da ta faɗa mata abinda Jidda ta mata tayi dariya “Matar yayan naki yarinya ce kinsan sai a hankula yana haƙuri da abarsa zata gyara yau da gobe”.Anty Ruƙayya ta faɗa dan ita mutum ce me kyautata zato ita dai Husna bata ga alamar gyarawa ba ,yau da ta kwana a nan ɗin  wani daɗi taji tamkar yayarta haka ta ke jin Anty Ruƙayya Arif yana hannun yaran sai wasa suke.Husna sati ɗaya tayi ta tashi komawa Jos tazo dai tayiwa Jidda sallama goma ta arziƙi ya haɗata dashi Hassan hakan ma aljihunsa yayi ƙasa don na musamnan ya yi cefane ya ke kaiwa Anty Ruƙayya sabida zuwan Husna har ta tafi.Jidda kam a haka sai da ta ji haushi a ranar sai da ta masa ƙorafi datarta ta ƙare bai tura mata ba ko ya bata kuɗin kati ta shiga mita ya cire dubu uku ya bata.Indai kuɗi ne ta san salon karɓe masa amma bacin haka ba wani abu da ta iya duk sanda bashida kuɗi haka tayi ta fushi kenan kwanciyar raya sunnar auren ma bai isa ya yi kyauta ba ko kunya bata ji don a kan hakan ma ta sabar masa.Akwai wani wata sai da ta sa shi cin bashi da ƙyar ya samu ya biya  haka take chajarsa ba tsoron Allah sai da wasu yan kuɗin allowance na wajen aiki ne ya biya bashin ba don haka ba sai dai bashin ya ta binsa.


    

  Yau tana kwance kan katifar ya shigo wajen sha biyu yayi sallama ta amsa batare da ta juyo ba “Jidda ,ɗalibaina sun zo suna parlour ki taimaka ki fito ku gaisa”Hassan ya roƙeta don fushi take dashi jiya ta tambayesa abu yace mata sai ya samu kuɗi.


 “Ni na sa su kwaso ƙafa su zo?ba inda zan fito”.Ta faɗa cikeda tsiwa yace “Jidda please kinji”.


 “Indai na fito to wallahi sai ka bani kuɗin ankona”.Ta furta don bikin wata cousin ɗinta za ai kuma ankon ya kai dubu talatin ga kuɗin ɗinki.


 “Zan miki yanzu dai ki taimaka ki tashi kinji yar albarka”.Motsawa tayi tana miƙewa ta ajje wayar ta gyara ɗaurinta ya ɗauko mata mayafi ta hararesa kafin ta karɓa ta yafa ta fito tana ganinsu dayawa mata sun ware gefe ɗaya gefen yan maza da ɗan girmansu suka shiga gaisheta ta amsa tana kallonsu ɗaya daga cikin su ya fara jawabi yana kanzaza kirkin mallam hassan da hidimtawa makaranta da yake yasa suka ga ya cancanta su kawo ziyara gidansa su gaisheda matarsa kuma su sa albarka a sabon gidan nashi da ma auren Hassan da faraa a fuskarshi yana kallon jidda da fatan bazatayi wani abun da zai sha kunya ba tana kallon yan matan wasu ma sun fita girma Hassan ya ɗakko musu ruwa ɗalibinsa a ladafce ya karɓi ledar ruwan yana rabawa ɗaliban hassan yana ta rafka musu godiya itama tace angode  daga haka suka tashi suka fita ta koma tana tsaki.Jiransa tayi ya shigo ta kallosa tana miƙa masa tafin hannu “My money”.Ta faɗa ya yi faffaɗan murnushi taga ya ƙaraso wajen taji ya mata sunba a tafin hannu ta sauke hannunta tana hararsa “Kuɗina zaka bani bs bs”.Sai da yayi dariya mai sauti hassan yana tambayarta mene bs bs “Ba sani ba sabo”Ta amsa da sauri ya sani amma so yake yaji ta bakinta “Allah ya miki albarka Amiraty ina ɗaukan salary nayi alkawari yaushe ne bikin?”Ya tambaya.


“Wata ɗaya ya rage”Ta faɗa yace kafin nan.Haka Jidda ta bisa bashin kuɗin yana salary sai da ya bata har da na ɗinkin da bikin ma yazo sai da ta bata gudumowa ta ce zata kai rabi ta bayar ta cinye saura.Ana haka watan ramadan ya shigo Jidda ta sake lanjarewa  bata moruwa yadda ta saba cin abinci azumi yazo ba kaɗan take shan wuya ba in kaga tana shawagi to ansha ruwa haka zai dawo tana sheme sai ya musu abin shan ruwa da ya gane kawai yake siyo musu abin shan ruwa don makara suke wajen buɗa baki hatta kunu sai dai ya siyo ko yi tayi tsinkewa yake tace masa ta daina yi gwara ya siyo,abincin sahur ɗin ma yawanci indomie ce ko taliya sai idan shi ya zage yayi abinci me ɗan nauyi da daddare sai su ci da sahur ga kashe kuɗi tsarabe tsarabe wani abun ma Jidda kasa ci take yi ciki ya cunkushe amma sai ta sa ya siyo har azumin ya wuce ta dawo da jikinta wani lokacin Hassan yata tsokanarta kenan ta hararesa.


*

    

Yau ta je unguwa Hassan bayan ya tashi daga aiki ya biya suka taho tare suna shigowa gidan aka ɗauke wuta magriba ta riga da tayi Jidda ta shiga banɗaki ta kwala masa kira tana faɗin ya kawo mata wayarta ya kunna fitilar wayarsa yana buɗe zip na jakar tata ya ciro wayar hannunsa ya taɓa wani tablet da ke ciki wayar ya kunna fitilar batai masa ƙorafin ciwo ba maganin me ta siyo ?Yayi tunani ko bata da lafiya ne ?Zaro maganin yayi yana juyasa bai gane shi ba kiran da ta sake masa ya sa ya ajje ya shiga ɗaki yana miƙa mata ta buɗe ƙofar banɗakin kaɗan ya koma parlour bai fasa kallon jakar ba zuciyarsa taƙi kwanciya ya sake ciro maganin yana duba bayan rubutun har sannan bai gane na mene ba ya tsinci kansa da ɗauka a hoto yayi browsing take bayanan magungunan suka fito cak ya tsaya yana maimaita karantawa google ya tabbatar masa da na hana haihuwa ne gabaki ɗaya duniyar yaji ta mashi duhu har lokacin ya kasa sarrafa abin a ransa Jidda kuwa koda ta fito daga banɗaki ta tuna jakar tana parlour daman fitsari ne ya korata ta shiga ɗakib da sauri ,fitowa tayi parlour tana kacibis da Hassan da ke riƙe da tab ɗin ya ɗago yana kallonta Jidda tayi sak ta ƙame idanunta na kan tab ɗin kafin ta maida kallonta ga yanayin fuskar Hassan.