7
*DUHU BAYAN MURMUSHI*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 7.
Sarac Stars R Pen...✍️
Da safe da wuri mama ta tashi ta shiga kitchen kasancewar monday ce su Nasir suna da makarantar boko, gashi baba ya ce kunu da ƙosai zata yi saboda Inna shi tafi so ta karya da shi ko sauran tuwo, gashi jiya ba tuwon tayi ba dan haka tun daren ta jiƙa gero, da wuri ta wanke shi da wake da Aina'u ta surfa, Zahra da Harris suka kai niƙa, wajen bakwai da mintuna ta gama ta sallami 'yan makaranta suka karya suka tafi, sannan Aina'u ya karya ta fito da wankin kayanta dana Nasir da Harris ta fara yi. Mama kuma tana zaune a tsakar gida tana karyawa, a lokacin ne inna ta fito itama ta zauna saboda bayan sallar asubahi ta ƙara komawa bacci, mama cikin sakin fuska tace.
Inna sannu da fitowa, na leƙa ɗazun mu gaisa sai na tadda kina bacci. Ina kwana ya gajiyar hanya.?
Lafiya lau Alhamdulillahi kuma gajiya tabi lafiya, ya kwananku da yaran gabaɗaya.
Lafiya lau, sun ma tafi makaranta.
Ina kwana Innanmu.
Aina'u wanki kika tashi da shi haka, ba zaki makarantar bane.?
Cewar inna cikin yalwar murmushi.
Ai ta gama ƙaramar Sakandiri, babban zata shi ga kuma sai zancen aure ya taso.
Cewar mama tana kurɓan kunu, Inna ta ɗan buɗe ido cike da nuna mamaki.
Uwale aure kuma bani da labari.? sannan kamar baiyi wuri ba dan naga nan binni bakwa auren yara da wuri sai yarinya ta ƙare sakandari ko.?
Ai inna abun ne yazo bagatatan kuma na zumunci ne shiyasa muka amsa maganar, Idi ne ɗan gidan yayanmu Tijjani suka daidaita kansu, kinga ai tuwona mai na ne ko.
Tabbas hakane amma ke Aina'u zaki iya rayuwar kauye.? sannan ba takura ki aka yi ba kina sonsa.? ina ce Idin yana da mata har da yara.
Inna ta ƙare maganarta ga Aina'u, ita kuma sai murmushi tayi mata dan ba zata iya bata amsa ba a gaban mama tace tayi rashin kunya, Fitowar baba ya katse musu hira ya gyara mazaunin hularsa dan har ya gama shirin fita ya karya a can bedroom da mama ta kai masa. Ya zauna akan tabarman kusa da inna da yake babbane shimfiɗa, ya shiga jera mata sannu bakinsa kamar gonar auduga dan farin ciki.
Innata sai kawai muka ganki baki faɗa min ba, kuma safiyar jiya munyi waya dake fa. Sannu da zuwa da fatan kin zo lafiya ya mutanenmu na can duk kin barosu lafiya.?
Lafiya lau Alhamdulillahi, ai cewa nayi sai dai ku ganni kuma babban dalilin zuwana akan Mujaheed ne dan na kawo masa magani dana amso.
Allah sarki angode Inna, jiya ma Uwale ke faɗa mini, na leƙa mu gaisa na samu kinyi bacci.
To kasan gajiyar mota shiyasa, to wai Babangida sai naji zancen Aina'u, da ban zo ba, da ba zan sani ba ashe.
Inna ai wajibi nayi tattaki naje na sanar miki, dama na jira a tsayar da maganar ne tukuna, gashi abun duk na gida ne.
Nan ya warware mata komai ya tabbar mata da Aina'u tana son auren ba dole aka yi mata ba, kuma zata cigaba da karatunta kamar yadda suka yi masa alƙawari, sannan ga ɗinki tana koya wanda zai siya mata sabon keke da zata tafi dashi gidan aurenta, Inna taji daɗin bayanin da ya yi mata, dama ita kar ya zamana an takura yarinyar, kuma zaman kauye kamar za a cutar da ita ne, amma jin zata zama tamkar futila mai haskawa ne a garin Magami sai zuciyarta tayi amanna da auren tare dayin addu'a akan lamarin. Sun jima suna hira da baba sai wajen takwas da rabi kafin ya miƙe ya bawa mama kuɗin cefane yace ayi tuwo miyar buɓewa ɗanya, sai ya wuce kasuwa. A lokacin mama ta shiga kitchen da ɗaukowa Inna abun kari, kunu a jug rabin kofi sai ƙosai guda bakwai duk da ta yi su da girma amma sunyi kaɗan ace ta bawa Inna ƙirgaggun ƙosai, koda ta aje mata sai ta shige ɗaki, inna kuma ta buɗe kofin ta shiga juya kunun wlh ko a ido ta raina, dan yadda take kaunar kunu iya gejinta shi ne a cika mata wannan jug ɗin, idan ta shanye ko ba ƙosai ya isheta ta yini a haka, ta sauke ɓoyayyen ajiyar zuciya kafin ta duba kwanon ƙosai da ya gama ƙandarewa, guda bakwai kamar zata bawa dan autanta Nasir, wanda ko shi ba zai ci ƙosai bakwai yace yayi masa ba, ta girgiza kai kawai ta soma kurɓan kunun, babban abunda ya shayar da inna mamaki shi ne babu sugar a ciki, ita ba ciwon sugar ba taya za a horar da ita da shan kunu ba sugar, ai tana da labarin ko masu ciwon sugar ana basu damar shan Mazarkwaila ko kuma wani sugar nasu na musamman na masu ciwon, sai ta kalli Aina'u da take ta aikin wanki.
Aina'u idan kuna da sauran sugar a gidan nan ɗauko mini na ƙata akunun nan.
To Inna.
Aina'u ta faɗa tana miƙewa tare da ɗauraye hannunta da ruwa mai kyau ta shiga kitchen ta ɗauro robar sugar wacce mama ta ware dan shi, kusan sugarn dake ciki zai yi loka biyu in bai fi ba, Inna ta sauke ajiyar zuciyar mamaki ta ɗauki ludayin dake cikin sugar ta saka sai ta ce Aina'u ta mayar wannan ya isheta, ta juya ta cigaba da karyawa tana tunanin mama ba zata bata tsiren jiya da baba yace ta ware mata ba, to wacce aka bawa kunu ba sugar ita taga bakin cin tsire, haka ta kammala ta miƙe, da kanta ta kai mata kayan kitchen ta dawo ta zauna a shimfidar ita kaɗai tana hira da Aina'u wanda duk akan Mujaheed ne, shi kuma yana ɗaki yana ta bacci dan bai farka da wuri ba.
Tunda mama ta shiga ɗaki ashe kwanciya tayi har bacci ya ɗauke ta, har Aina'u ta gama wanki, inna ta saka ta dafa mata ruwan wanka, da yayi zafi ta surka mata ta kai mata bayi sai taje tayi, bayan ta fito ta koma ɗaki ta sauya kaya ta aje wanda ta cire sai ta samu kan katifarsu Aina'u ta kwanta ba jimawa tayi bacci. Ko da Aina'u ta gama shara wanke-wanke tayi kafin ta ɗaura sanwar wake da mama ta faɗa mata dan shinkafa da wake zasu yi da rana, zuwa dare ne zata yi tuwon da baba yace saboda Inna. A lokacin Mujaheed ya fito yana miƙa, Aina'u ta dube shi fuska a sake.
A kwana a hantse sai kyakkyawa, yayanmu kasha bacci bari na kawo maka abun kari, duk ma yayi sanyi.
Tana gama faɗar haka ta shiga kitchen dan ta san ba magana zai yi mata ba, ko da ta kawo bai wanke baki ba ya zauna ya karya, yana gamawa ya koma ɗaki ya cire kayan jikinsa ya mayar da ƙananan kaya riga mai guntun hannu da wando jins, duk da masu datti ne amma sunfi wanda ya cire dama-dama, sai ya ɗauko rigar sanyi mai hula baƙa ya saka, ba dan yana jin sanyi ba sai dan abunda kwakwarwarsa kenan ta kitsa masa, ya fice daga gidan wanda kuma sai an ganshi.
*****
Safiyya.
A daren ranar da suka dawo ta kasa bacci saboda daren tsawo yayi mata, ta shiga tsantsar kewar Jabir, ta saba da yin bacci tare da shi tana maƙale a jikinsa, sai take jin kamar in babu shi ba zata rayu ba, tabbas tasan Allah ya jarabceta da rabuwa da shi ne domin ya gwada Imaninta. A daren da kyar ta samu bacci ya ɗauketa wajen ƙarfe biyu shima carbi ta riƙe ta riƙa salati Annabi s.a.w wanda hakan ya ɗauke mata tunani har baccin yayi nasarar ɗaukarta. Da safe ta saba tana tashi zata shiga kitchen ta ɗaura musu abun kari ta fito ta fara gyaran gida, amma sai gashi gari ya waye tana naɗe a gado ta riƙe waya tana kallon tiktok, shigowar Hafsa da kofi da plate yasa ta ɗago kai suka kalli juna tare da sakarwa juna murmushi.
Anty Fiyya Ina kwana.
Lafiya lau auta, har kun gama abun kari.?
Ai da wuri muke aikin saboda makaranta, yanzu ma zamu wuce.
Allah ya bada sa'a.
Yauwa Mamanmu tace ki zo falon Baffa in kin gama.
To tace mata kafin Hafsa ta fita, Safiya ta sauko daga gadon ta duba abun karin kunun tsamiya ne da ƙosai, nan take taji zuciyarta tayi mata baƙi, duk da tana son kunu amma kosai bai dame ta ba, hasalima in ba Azumi ba bata yin kunu a gidanta saboda daga ita har Jabir sun fi gane tea da kayan turawa, ta saba ta fasa kwai biyar taci ita kaɗai da tea, tabbas wannan shima ƙalubale ne, Jabir ya saba mata da daɗi.
Shi yasa yake tunanin dole zan dawo masa.
Tayi maganar a zuciya, kuma tasan tabbas yasan dalilai da yawa da yake ganin ba zata jure zaman gidansu ba zata dawo masa. Amma kuma zata nuna mata itama mutum ce da zuciya a ƙirjinta, zata jure duk wuya duk runtsi har sai ya sauko daga wannan ƙudurin nashi ya yarda da nata burin kafin su daidaita su koma inuwa ɗaya. Sai ta sauke a jiyar zuciya ta shiga bayi ta wanke baki kafin ta dawo ta karya, bayan ta gama ta fito falo ta samu babu kowa sai ta wuce sashin Baffa, a nan ta samu duk iyayensu suna zaune suna magana, shigowarta ne ya katse su ta zauna a carpet ta yi musu sannu dan ta gaishesu tun asubahi su duka, Baffa ya faɗaɗa murmushinsa.
Zo nan Safiyya, ya kwanan baƙunta.? dan ke yanzu baƙuwa ce a gidan, amma babu wata matsala ko.?
Alhamdulillahi Baffanmu, kuma babu komai.
To madalla, batun kayan ki na nan Kano suma za a kwaso su In Sha Allah, da fatan ba zaki bani kunya ba akan wannan mara miki baya dana yi, Safiyya gabaɗayanku dana aurar daku wlh bana fatan ace kun dawo gida da sunan saki, amma ke naki babban al-amari ne da dole sai mun tsaya mun jajirce wajen kwato miki haƙƙinki, kuma tun farko daga ke har shi kun saka son zuciya shiyasa Allah ya jarabce ku, dan haka abun da ya faru sai ya zama babban darasi a gare ki, ki kuma ɗauki niyyar gyarawa. A yanzu zaki cigaba da zama a nan har muga abunda Allah ya tsara miki, idan Jabiru ya gyara zaki koma, in kuma ya nuna ko-in-kula to magana ta ƙare sai dai muyi miki fatan Allah ya zaɓa miki abunda yafi zama alkhairi a rayuwarki.
Amin Baffa nagode.
Sai maganar fita, gaskiya ba zaki riƙa fita ba sai da babban dalili, ki natsu guri guda banda zaman kaɗaici, ki fito tsakar gida a yi ayyuka da ke.
In Sha Allah nagode.
Batun lafiyarki in an kwana biyu Aliyu zai kai ki asibiti a duba ki.
Allah ya kaimu.
Cewar Safiyya, iyayen suka amsa da amin, sai mama ƙarama tace.
Amma Baffa me zai hana a nima mata aiki ta fara dan ba zata ji daɗin zama guri ɗaya ba.
Baraka wani irin gaggawa ne wannan, mu da muke fatan wannan yaro ya zo a daidaita ta koma ɗakinta, idan kuma aka samu aikin ta koma Abuja ya za a yi.?
Ba sai tayi zamanta anan ba cikin 'yan uwanta tunda yana da gida anan, sai ya riƙa zuwa mata duk bayan mako ɗaya ko biyu, nifa ina ganin koda za a daidaita a nuna masa ba zai yuwu ta koma Abuja ba dan a ga kamun ludayinsa, a can ya barta a ƙaton gida ita kaɗai ga kaɗaici ga ciwo ga damuwa, shiyasa abun yayi mata yawa, gata nan duk ta lalace ana ganinta am san tana cikin tashin hankali.
Hakane Baraka, amma kuma mu bari muga abunda Ubangiji ya tsara. Safiyya zaki iya tafiya kuma duk abunda kike buƙata ki zo ki sanar dani ko ki faɗawa iyayenki su faɗa min, babu abunda zai gagare ni na hidimarki In Sha Allah.
Allah ya ƙara buɗi Baffa nagode.
Ta faɗa kamin ta miƙe ta wuce zuwa tsakar gida ta samu Kausar tana wanke-wanke, ta isa wajen taja ƙaramar kujera ta zauna suka shiga hira tana tambayarta makaranta, Kausar tace mata tana jiran sakamako ne da zata shiga jami'a, haka ta ɓata lokaci a gurin, bayan Kausar ta gama suka ciga ɗakinsu dake nan tsakar gida wanda yake na su, Safiyya ta kwanta a katifar ɗakin ba jimawa bacci ya ɗauketa.
Haƙiƙa zaman gida idan ya wuce mace to ya wuce ta sai dai in ƙaddara ya dawo da ita zata zauna dole, amma kuma zata fuskanci ƙalubale, musamman ga rayuwar wasu iyayen sai a sakar wa mace Tarbiyyar kanta ba a kwaɓa mata a ganinsu ta wuce a yi mata faɗa, hatta abinci bata isa a bata ci uku a rana ba, batun sabulun wanke ko omo da sauran abun buƙata babu mai bata sai dai in ta fita ta roro ta yiwa kanta hidima, a irin wannan yanayin kesa wasu matan bin maza in sun rasa yadda zasu yi, In kuma mai tunani ne ba tada kwaɗayi sai ta fara aikatau ko buga-buga, babban sauƙin mace shi ne in Allah ya sa tana da sana'a to ta tsallake, in kuma tayi karatu sai ta nima aiki ta cigaba da kula da kanta da yaranta in ta zo da su gidan. Wannan matsalar ko da ace miji ne ya mutu ya bar mace da yara idan bai bar musu komai ba ta dawo zaman gidansu, to fa tun ana tausaya mata na kwanaki daga baya za a sakar mata komai hatta yaran ita ce zata nima abunda zata basu babu bai taimaka mata sai Allah, shiyasa yana da kyau koda kina gidan aurenki ki kama sana'a wacce zata riƙa taimaka miki wajen samun rufin asiri saboda mazan wannan lokacin basa iya ɗaukar nauyin mace gabaɗaya sai ɗai-ɗai, haka ma idan aure ya mutu ko miji ya rasu kina da abun yi ko sana'ar da zata taimaka miki, to tabbas kin tsallake daga wani damuwar, domin wannan lokacin kina cikin wani siraɗi ne da babu mai duba lamarin ki sai Allah.
Rahma ce.