CHAPTER 6
by @hafnancy
*HARAMTACCIYAR GADA.*
_*{Haɗuwar rayuka da ƙaddara ta tattara wuri guda.*🔥💔}_
*NA*
*HAFSAT MUSTAPHA ('Yar Mutan Naija).*
*SADAUKARWA GA UWARƊAKI NA: HAJIYA ZAINAB AHMAD (Hajiya Mama). Amincin Allah da ni'imominsa su tabbata a gareki Uwata.*
*BOOK 1*
*Page 6.*
" Amm....Ammm mai kika ji nace ne wai ?"
Yallabai Ya furta yana dafe kansa daya ƙara ɗaukan wani caji. Harara Haj. Nafeesa ta watsa masa tana" Rainin hankali kai, Jalal wai ni kake k'ok'arin maida shashasha ? Ka gaya min wacece kake so ta haifa ma baby?"
Salati ya saki cike da mamak'in kansa don yasan ba k'arya tayi ba. Har yaushe ya fita hayyacinsa ne da maganarsa ta fito fili ? Lallai ba karamin so yake wa Jidda ba tunda har take neman zuzuta shi.
"Daddyn Samha Allah yasa dai ba matan banza ka fara bi awaje ba. Duk yarinyar da ta kuskura ta shigo rayuwar ka to ni Nafeesa sai na tabbata na baƙanta mata."
Haj. Nafeesa ta furta zuciyarta na tafarfasa, macece mai bala'in zafin kishi. Ganin tana neman shi da rigima sai kawai ya tashi ya kwashi wayoyinsa zai yi upstairs ba tare daya ce da ita ci kan ki ba.
Hakan ya kara kufular da ita, da hanzari tabi bayan shi ta damki rigarsa da kyau har tana tattare wa tace tana sakin huci na zafin kishi " Jalal ni zaka maida mahaukaciya ? Ina magana kana k'ok'arin bani waje wato in ci kaina? wannan shine karo na k'arshe da zan tambayeka nace wacece kake faɗin kana so ta haifa ma baby ?"
"Ki cika ni kafin na sharara miki marin da sai ya gigitaki. Idan nace ina so in haihu da wata tunda ke bakya so zaki hana ni ne?"
Kafin ta kai ga bashi amsa, Samha ta fad'o falon, ganin iyayenta cikin wannan yanayin ya d'aga hankalin ta. Da sauri ta nufe su tana" A'uzubillahi haba Mummy meye haka ? Me zan gani haka ? Devil is a liar ba'a gidan nan ba please mummy cika shi wannan disrespectful act ne."
Bata yi jayayya ba ta cika shi tana jero tsaki da wurga masa harara kamar idanunta zasu fad'o. Tana sakin shi ya waigo yana nuna ta da 'yar yatsa ransa a matuk'ar b'ace, cikin borin kunya yace" Idan kika kuskura kika sake maimaita irin cakumar da kika min a yanzu sai nasa kin yi nadamar sani na arayuwar ki. Ki sani ni d'in mijin mace hud'u ne, in na so ina iya cike sunnah ke kin sani kudi ba matsala na bane, amma bana ra'ayi ne don haka kar kiyi tunanin ko tsoron haukar ki nake. Abin da kika ga ya faru zancen zuci ne ya fito fili. Nafeesa ina da bukatar haihuwa, ina bukatar ya'yan da zasu min biyayya, ya'yan da zan hana su abu kuma su hanu, masu tausayi na da kuma jin kaina. Tsayawa kina tambayar ko wacece nake so ta haifan min baby bazai fishe ki ba, shawara zan baki ki zauna ki gyara rayuwar ki dana 'yar ki kafin lokaci ya kure muku shine abunda kawai zan iya cewa."
Yana gama jawabinsa yayi hayewarsa sama. Hannu bibbiyu Hajiya Nafeesa ta ɗora akai tana "Shikenan Samha mun shiga uku, wata tsinanniyar tana k'ok'arin kwace min mahaifin ki, wayyyoo Allah shegiya tana neman shiga tsakaninmu."
Kuka take sosai mai tab'a zuciya tana sakin surutai kamar wata tab'abbiya. Ita kanta Samha maganganun Daddyn nata ba ƙaramin sosa ranta yayi ba, babu abin da yafi ci mata tuwo a ƙwarya kamar batun haihuwa.
Hawayen da suka ziraro mata masu dumi tasa tafin hannu tana sharewa tace"Yanzu a idanun Daddy ni ba 'ya bace da har yake son ƙarin haihuwa da wata?Kuma nufin sa ni bana masa biyayya? Na lura tunda na buɗe Gidan Mata daddy ya bar gani na a matsayin 'yarsa. Mummy ki gaya min abin da kike ganin ya dace in yi da zan birge Daddy har na koma matsayin da nake dashi a wajensa."
Ta ɗan numfasa sannan ta ci gaba:
"Ko in hakura in rushe Gidan matan ne sannan in karbi kyautar da ya yi min na Gidan abincinsa na k'asar birtaniya? Kin ga takaddun ma har yanzu ban sa hannu ba dama kin hana in sa. Gashi na dawo mishi dasu amma maganar da Daddy yayi yasa jikina sanyi, zuciyata ta karaya, mummy ina so in faranta ran mahaifi na. Ina ganin kawai zan rushe Gidan Mata sannan in karbi tayin Gidan abincin Daddy."
Haj. Nafeesa ta manta damuwar da take ciki tace tana girgiza kai" Ahir dinki! Sai in a bayan raina ne zaki yi wannan rashin lissafin. Ke shashashan ina ce zaki yadda ki rushe Gidan matan ki dake jawo mana mahaukatan kudad'e akan wani gidan abinci ? Samha ni ki bar komai a hannuna ki zuba ido ki sha kallo muna nan dake zaki ga Gidan abincin nan ya dawo hannun ki ba tare da kin rushe gidan mata ba."
Cikin rashin gamsu wa ta ce" Mummy how ? Ta yaya zai dawo hannu na bayan kin kwana da sanin cewa zaɓi ɗaya kawai ya bani. GIDAN MATA ko GIDAN ABINCI ? duk wanda na zaɓa aciki to hakan na nufin zan rasa ɗayan ne. Daddy yace is impossible ya bari in mallaki duka biyun if not ai nima zan fi so ace ina da Gidan Mata kuma ina da gidan abinci duka mallaki na."
Kafaɗar ta Haj. Nafeesa ta dafa tana sakin wani irin murmushin da ita kadai ta san manufarsa tace"Kar ki manta nina haife ki kuma inna ci alwashin abu sai na cimma nasara akai. Zan sa ya mallaka min GIDAN ABINCIN, In yaso daga baya sai in damƙa miki komai ahannu ki rika tafiyar da kasuwancin ba tare da saninsa ba. Kai na tabbata koya sanin ma babu abin da zai iya yi sai dai kawai ya kallemu kuma ya ƙyalemu."
"Yanzu ki duba ki gani za muyi ta samun alkhairi mai tarin yawa daga ɓangare biyu. GIDAN MATA da kuma GIDAN ABINCI. 'Ya'ya mata jari ne dan haka bai kamata muyi wasa da damar da muka samu ba. Haka zalika akwai samu a gidan abinci tunda ana da bukatar abinci don gudanar da rayuwa ta yau da kullum."
Haj. Nafeesa ta ɗauki lokaci sosai tana hure wa 'yar ta kunne kamar yadda ta saba akodayaushe. Sam bata banbance mata tsakanin fari da baƙi, shiyasa samha take ganin duk abin da take yi daidai ne.
Abin da basu sani ba shine, Daddy bai shige daki ba yana jin duk tattaunawar su. Ransa ya kara b'aci sosai yana mai nadamar auran mace Jahila mai son abun duniya kamar Nafeesa.
Ko kadan Samha bata yi dacen Uwa ta gari ba hakan yasa a wasu lokutan yake matuƙar tausayin ta yake kuma yi mata uzuri don laifin duk na mahaifiyar ta ne.
Samha ce tayi dinning ta buɗe kulan breakfast ɗin Daddy daya kasa ci. Avocado toast ne with poached eggs wanda yaji salad cream da timatur. "Wow my favorite mummy."
Ta furta cike da farin ciki ta kai hannu ta dauki slice daya takai baki. Santi ne ya biyo bayan jin ɗanɗanon sa abakin ta, tace" Da jin wannan ɗanɗanon kasan hannun mahaifi na ne yayi girkin nan da kansa...My Dad is just the world best cook."
Harara Mummy ta watsa mata tace" Wato har ma ya fi ni iyawa kenan ko?"
"Haba mummy what are you saying ? Ke ma kin san da gaske Daddy ya fiki iya girki, infact ni Daddyna yafi kowa iyawa. Mummy wallahi cima ɗin nan tayi daɗi sosai."
Mummy tace" To, sarkin santi ba shi yayi ba, kuku ne yayi girkin." Samha tace" ban yi mamaki ba tunda kowa yasan awajen daddy ya koya amma da'ace hannun daddy ne daya fi haka ɗanɗano. Mummy ai kun k'yauta da kuka tarɓeni da Favorite ɗina."
Murmushin yaƙe tayi tace" Da kika kira kike faɗa min zuwan safe zaki yi shine nasa aka yi tunda nasan kina son shi. Sai dai ga kulan ki can amma kin take na Daddyn ki."
Dariyan jindadi tayi tana kallon kulan ta dake ajiye agefe, ita ɗin mai gida biyu ne, muddin ta sanar zata kawo ziyara gida to kulan abincin ta na musamman ne.
Tace" To ai ga nawa nan idan ya shirya break sai ya ci nawa."
Tsaki Haj. Nafeesa ta ja tace" Shi ne zai ci miki abincin bayan a idonki aka gaya wa juna ba daɗi ?"
Samha ta ce"Hmm mummy wai da gaske Daddy So yake ki ƙara haihuwa at this ur age ko kuwa so yake ya ƙaro aure ne sannan wata tazo ta haihun don ni kaina ya ɗaure wlh."
Cike da takaici tace" Kaina yafi naki ɗaurewa Samha, wani irin baƙon al'amari nake gani attatare dashi kuma maganar haihuwa kamar shine abin da yafi tsaya masa arai. Amma koma menene mu bi komai a hankali zan bincika kuma idan na tabbatar da yana tarayya ne da wata a waje to wlh kamar yadda na faɗa sai na saɓanta rayuwarta."
"Mummy ki kwantar da hankalin ki, babu wata 'yar mace data isa ta shigo gidan nan ta haɗa kafaɗa da mazauni dake, ki sa ido sosai akan Daddy muddin kika tabbatar da abunda muke hasashe gaskiya ne, kiyi maza ki sanar dani mu gaggauta ɗaukan mataki tun wuri kafin mu zo muna cizon ɗan yatsa."
Sai da suka gama hure wa juna kunne sannan Samha tayi sama wajen Daddyn nata don ta damƙa mashi takaddun da taki sa hannu. Dama agreement papers ne wanda akeso in har ta amince tana son wannan gidan abincin to ya zama dole ta yi watsi da gidan Mata.
Samun shi tayi akishingiɗe akan sofar dakinsa idanunsa alumshe kamar mai bacci amma ba baccin yake ba. Har ta murɗa hannun kofa zata koma taji yace cikin sanyin murya" Ya akayi ne ?"
Jin muryarsa yasa ta juyo da sauri tana fara'ar dole"laa Daddy ashe ba bacci kake ba."
"uhm.." kawai ya ya ce sannan ya miƙe ya zauna jiki duk ba kwari.
Cike da kulawa tace" Daddy bana son ganin ka cikin damuwa please kayi hakuri komai mai wucewa ne in sha Allah. RAYUWA da KADDARA atare suke tafiya tamkar ƴan'uwan juna ne, kamar yadda RABO da KADDARA ba'a guje musu arayuwa. Daddy Ka sani Duk abinda kasamu arayuwa to Allah ya kaddara naka ne haka duk abinda ka rasa Allah bai nufeshi da zama naka ba, kayi hakuri ka zauna lafiya da mummy kuma kayi hakuri ka cigaba da min kallon 'ya agareka."
Ta karashe magana cikin rauni har tana zubar hawaye. Duk da maganganun nata sunyi matuƙar tasiri akansa, sai bai bari hakan ya sauya ra'ayinsa ya dangane da hukuncin daya zartar ba. Babu ja da baya sai ya aiwatar da kudirin da ke ransa.
Ɗago wa yayi yana kallon ta yace"Hmm Samha waya ce na bar kallon ki amatsayin 'ya ta ? Sabida baƙya min biyayya shine zai sa in bar ganinki a 'yata? ai ki sani hannunka baya tab'a rub'ewa ka jefar. Samha look You are 28years don haka kin yi wayon da zaki san abunda ya dace da rayuwar ki. Maganar haihuwa kuma da kika ji ina yi in nace ina son k'arin wasu ya'yan bayan ke ai ba laifi bane koko laifi ne ?"
A sanyaye tace"A'a ba laifi bane amma Daddy ka duba mummy bata da wani k'arfi na k'ara haihuwa ayanzu, ina tsammanin ma jim kadan haihuwa na iya tsaya mata."
Da sauri yace" Wai lallai sai Mummyn taki ce zata haifa min su?"
Tana k'ok'arin magana yayi hanzarin d'aga mata hannu" Kin ga Samha ban shiga rayuwar ki ba don haka kema kar ki kuskura kiyi kasalandan acikin nawa. Kowa yayi abunda yake ganin daidai ne, ban shiga haƙƙin ki ba, na sakar miki 'yancin kina wataya wa yadda kika dama so please nima ki rabu dani in yi nawa rayuwar. Yanzu dai ya maganar agreement papers ? Have you finally made your choice?"
Wani nannauyar Ajiyar zuciya ta sauke cike da fargaban abin da zai biyo baya tace" Gasu nan ahannu na dama dalilin zuwana kenan in mayar maka dasu."
Farin medicated glasses ɗinsa ya maƙala a ido sannan yace" miƙo min."
Jiki na rawa ta Isa ta mik'a mishi. Buɗe wa yayi yana duddubawa. Ko kadan bai yi mamakin ganin bata sa hannu ba. Ya tsammaci hakan sai dai kuma amatsayin sa na mahaifi dole ya ji zafi ace baya da ikon juya ƴar cikinsa ta mishi abin da ransa yake so.
Glasses ɗinsa ya zare yace cikin rauni" Shikenan samha jeki naga choice naki, na miki babban ƙyauta ke kuma kika mayar min da hannun ƙyauta baya. Ina fatar baza kizo kina cizon ɗan yatsa daga baya ba ?"
Shiru ta masa tana tunani, har zai sake magana sai ya ji tace" Dad I'm sorry amma ba zan iya rushe Gidan Mata ba akwai alot of benefits acikinsa. Amma ina neman alfarman daka mallaka wa mummy, da kai da kayan duk mallakan wuya ne."
A fusace yace" Ba ke ce zaki gayamin wanda ya dace na mallaka wa ba. Assest ɗina ne bana uban kowa ba don haka I'm entitled to determine who will benefit from it. Ki tafi abin ki ni nasan in da yafi cancanta da in sadaukar da wannan k'yauta. I promise you Samha I'll do what i think is the best."
Kuka ta fasa mai tab'a zuciya tana"Dadd......."
Da sauri ya tari numfashin ta " Samha please take ur leave....My Assest My choice perioddd."
Da gudu ta bar dakin tana rusar kuka kamar ranta zai fita. Bata tab'a ganin b'acin ran Yallabai kamar na yau ba.
An ya bata tafka babban kuskure ba ? Ga dukkan alamu ta ida ruguza ɗan guntun soyayyar daya saura tsakanin ta da mahaifin ta.
Bayan fitar ta yasa hankici yana sharar hawayen bak'in cikin daya wanke masa fuska. Bai tab'a yin nadamar samun Samha amatsayin 'ya ba kamar yau.
'Ashe shi ɗin banza ne awajenta bai sani ba?'
'Har tana iya zuwa ta dubeshi tace bata son zab'in shi nata take so?'
Dama Jidda ce ta kawo shawara kan ya mallaka mata gidan abincin. A tunaninsu muddin ya sadaukar mata da babban project ɗinsa na gidan abincin da ake ƙerawa a kasar birtaniya zai yi nasarar rinjayar ta daga halakar da take neman jefa kanta tare da 'ya'yan mutane. Sai dai kuma ga dukkan alamu ba za ayi nasara ba.
"Samha zan baki mamaki. Sai dai ina guje miki ranar da zaki sa tafin hannunki ki tari ruwan hawaye a sanadin GIDAN MATA. Allah ya baki ƙwarin gwiwan tunkarar baƙar kaddarar dake tunkaro ki."
Maida glashinsa ya yi sannan ya kalli agogo , sha ɗaya saura ya saukar da ajiyar zuciya yace" Its about time JIDDAH, ya zama dole ayau ki zab'a ko Ni ko SAMHA ? ko UBA ko 'YA ? ko AURE ko BARIKI ? "
Bai sake bin takan Haj. Nafeesa da 'yar ta ba duk da sun so sake d'aga masa hankali amma bai biye musu ba ya bar gida.
**
A ɓangaren Jidda haka ta tashi sukuku da ita, babu abunda ta iya sa wa aciki sai tea. Acikin kwana ukun nan adaddafe tayi shi kamar ba zata kai labari ba, damuwa da fargaba suna neman kai ta wurin da in an je ba'a dawowa.
Sai ta yi kamar zata kira Yallabai sai kuma ta fasa, yau dai ta san za'a yi ta ta ƙare. Tana nan zaune a falo, ta kafe jemammun idanunta a TV da suka rine tsabar kukan da ta sha. Amma a zahiri hankalin ta ba'a nan yake ba, tayi nisa sosai cikin tunani. Kamar daga sama ta ji wayar ta na burari yana neman agaji.
Firgigit! Ta dawo Hayyacin ta ta jawo wayar tana haki kamar wanda yaci Uban Gudu. A tunaninta Yallabai ne ke k'iranta sai kuma taga akasin hakan.
'UWATA' shine sunan data ga yana yawo akan allon wayar. Gabanta ne ya tsananta bugu ganin Samha ke k'iranta. Sai daya kusan tsinkewa sannan ta ari mayafin natsuwa ta ɗaga gami da rangaɗa sallama tamƙar ba wacce take cikin kogin damuwa ba.
Samha bata jira sunyi wata gaisawa ba don ita kanta cikin damuwar take, tace"Jidda ga masu kawo kayan abinci nan tafe sun k'ira ni wai suna kan hanyar zuwa gidan mata, so please ki shirya inspecting, kin san yanda abubuwa suke ba sai na batar da yawu ina kara miki bayani ba, ki dudduba ki tabbatar komai ya cika, duk abunda kika ga babu kiyi maza ki sanar dani da wuri."
Rasa abun cewa Jidda tayi don Allah ya gani bazata iya zuwa gidan mata ahalin da take ciki a yanzu ba.
"Hello Jidda Ko baki ji abunda nace bane?"
A ruɗe tace bayan ta haɗo karyar da zata lafta mata"Uwata kiyi hakuri yau kwana huɗu kenan bana gari wallahi tafiyar gaggawa ne ya kama ni zuwa Abuja. Amma yanzu zan yi waya da SALA tayi abin da ya dace."
A fusace Samha tace" Wai Jidda mai yake damun ki ne ? Kin fara canza min fa ? wai ace yanzu in zakiyi tafiya sai dai kawai in ji bak'ya gari. An bar gani na da muhimmancin da har za'a sanar min za ayi tafiya."
"A'a Uwata ba haka bane kawai jiya ne yazo ya daukeni wai akwai aikin da zasu aiwatar a Abuja kuma kwana biyar zasu yi ba zai iya bai ji ni a kusa dashi ba."
Ta ida magana da rawar murya don bata saba k'arya ba. Cikin tsananin fusata Samha tace"Shi ɗin wa ? Shi ɗin banza ko baki faɗa masa matsayi na bane awajenki ? "
A gigice Jidda tace" Na faɗa masa amma kiyi hakuri."
Samha tace" Babu zancen hakuri! Mutumin nan so yake ya kai ni wuya. Ki turomin lambarsa yanzun nan zan kira in masa kasheɗi da babban murya kar ya kara daukar mun ke kuyi tafiya ba tare da izina na ba. Zama na kike ba zaman uban kowa ba, haka lokacin da kuka yi tafiya kasar waje kuka kwashi watanni uku a can, sai bayan kun bar kasar kika kira kike faɗa min. Na ji zafi amma ban nuna ba, shine yanzu ya daukeki kuka sake tafiya ba tare da sani na ba bayan kin san nafi gane wa aikinki. To, wallahi ki shiga hankalinki ban so in samu matsala da ke. Yanzu ki yi maza ki turo min lambarsa sai na ci mutuncinsa."
Wannan karon kaɗan ya rage Jidda ta saki fitsari a zaune jin ance ta turo lambar waya.
Idan ba Mahaifin Samhar ba wa take dashi ayanzu da har zata tura mata lambarsa ? ai sai dai ta kashe ta amma sam bazata iya ba.
Kawai amsa mata tayi da "To zan turo Allah ya huci zuciyar ki."
"Kit! Ta kashe wayar. Gwalalo idanu Jidda tayi bayan ta farga ta ganta akan toilet seat rigar ta ta jike da fitsari.
'Har yaushe ta shigo toilet bata sani ba?'
Lallai ba karamin ruɗa ta Samha tayi ba. Ga wani uban zufan data haɗa tamƙar wanda aka ciro daga gidan biredi. Ajiye wayar tayi akan wani kujerar tsugunno sannan ta tuɓe kayan ta sakar wa kanta shawa.
Tana wankan tana tunanin yanda zata yi ta fita a tarkon Samha. Bata kammala ba taji tsayuwar mota a kofar gida, da hanzari ta kashe shawa ta jawo towel ta daura ta fice adaidai lokacin da ta ji ana k'ok'arin buɗe gate.
Cikin maɗaukakin tashin hankali tayi saurin isa bakin taga tana leƙe. Yallabai ta gani ya bayyana cikin gidan kasancewar yana da na shi makullin gidan a hannu, ita ma haka. Amma bai san da cewa zai sameta a gidan ba kawai ya yi tunanin tunda sun ajiye magana dole duk inda take zata zo, ko bai ganta ba zai jira ko ya kirata a waya.
Gabanta ne ya tsananta bugu, alokaci daya kuma taji wani hawayen farin ciki sun zubo mata.
A hankali ta furta" Alhamdulillah Jayman na san zaka dawo gareni don bana tunanin kai ma zaka iya rayuwa ba tare da ni ba."
Da sauri ta saki labule ta koma gaban wadrope tana neman kaya masu sauki da zata saka. A yayin da ta fara tunanin makomar aurensu na sirri a yau.......
**A sannu zaku san ta yadda aka ɗaura wannan auren sirrin na Yallabai da Jidda.**