SHI SO DABAN YAKE

Babi na goma sha huÉ—u

by @dijensy

SHI SO DABAN YAKE🌸




By Khadija Ado Ahmad(dijensy)




14




Jidda wani irin sanyi jikinta yayi tana kallon yanayin Hassan bata taɓa ganinsa a irin wannan yanayin ba ba ɗaure fuska yayi ba amma fuskarsa ƙarara takeda disappointment “Mai ne wannan Jidda?maganin mene kike sha?”Ya tambaya a tausashe ta fara wasa da yatsun hannunta tana tsuru tsuru da ido kamar wacce bakinta ke nauyi.


“Birth control”Ta amsashi bata iya ɗagowa sun haɗa ido ba yana riƙe da tablet ɗin maganin ya tako inda ta ke a tsaye ya kamo hannunta ya buɗe tafin hannunta ya ɗora mata ya rufe kafin ta ga ya wuce cikin ɗakinsu gwiwa ba ƙwari ta ke takawa ta ɗauki jakar tata ta komo ɗakin sif ya buɗe agogon hannunsa ya zare ya ajje yana mai juyawa ba tare da ya kalleta ba ya fita daga ɗakin tana binsa da ido tsakar gida ya fita yana jan wata kujerar zama doguwa da yake zama idan cikin gidan da zafi ya fita ƙofar gida ya zauna yana jingina da jikin bango shi kaɗai yasan irin raɗaɗin da zuciyarsa ke masa yana kallon sararin samaniya a yayinda zuciyarsa ke masa saƙe saƙe ba adadi wanda yake ta iya ƙoƙarin ya nisanta kansa daga jin tasirin duk wata damuwa da zata yo kaikawo a ransa.


     Kayanta ta cire tana shiga wanka ta fito ta saka kayan bacci duk abinda take jiki a sanyaye take yinsa ,fitowa tayi daga É—akin ta shiga kitchen tana tunanin ina ya je ta shiga kitchen É—in ta É—auki tukunya ba abinda ta saba yi bane idan sun dawo tayi girki irin wannan lokacin amma yanzu ta tsiri dafa indomie ta kammala ta zuba a plate ta kai parlour tana tsayawa ta rasa mai zata yi ta shiga shawara tana tunanin yadda zata tunkari Hassan tana wannan tunanin ya dawo ciki ta fito tsakar gidan ta ganshi “Ga abinci na gama kar tayi sanyi indomie na dafa maka”Jidda ta faÉ—a Hassan yace “Na Ć™oshi sallah zan shiga”Ya furta yana yin alwala ya fita sallar isha ya dawo Jidda tana kallo indomie ta sandare  tayi shigewarta É—akin ya fita waya take dannawa amma hankalinta baya kai ta na yi tana kallon Ć™ofar shigowa tana jira ya dawo  sai wajen shaÉ—aya ta ga ya shigo idanunta ta mayar kan wayar tana jinsa ya shiga banÉ—aki yayi wanka ya fito ya sa jallabiya fara.Jakar makaranta ya É—akko yana zama kan darduma inda ya saba zaunawa da fitila yake ta karanta littafinsa daga baya aka dawo da nepa ta tashi ta je ta sa wayarta charge tana ajjeta ta komo kan katifar tana gyara pillow tana satar kallonsa ta kwanta “Karki manta kiyi addua”Ta ji ya furta idanunsa akan littafin da ke gabansa ba tare da ya É—ago ya kalleta ba.


   “Tohm”Jidda ta amsa abinda bata taÉ“a yi ba mamaki ya cikata da taji ya mata magana duk a tunaninta fushi zai hana ya mata magana,ta jima kafin bacci ya É—auketa ,washegari Hassan yana off  kamar yadda ya saba ya rigata tashi ya musu abin kari koda ta fito parlour tana kallon takwas da arbain na safe ta ga Hassan É—in yana parlour kamar yadda ya saba ya jera komai.A sanyaye ta Ć™araso tana kallon yau daban ya zuba nashi bai haÉ—a musu plate É—aya ba shiru tayi batare da tace komai ba ta yi karin safen ya rigata gamawa ya bar parlourn sauri tayi ta kammala ta dawo É—aki ya shiga wanka ya fito ya shirya tana kallonsa cikin dark blue yadi ya gama ya goga turare Jiddan tana zaune ne daman tayi kamar waya take dannawa amma ba abinda take dannawa ta ajje kan katifar cikin sanÉ—a ta taso tana tsayawa gabansa ta shagwaÉ“e fuska ta ga ya Ć™i bari su haÉ—a ido yana mayar da turaren ya ajje zai juya ya fita ta sake taresa haÉ—i da kamo hannunsa É—aya tana riĆ™ewa cikin nata “Hassan “Ta kira tana Ć™oĆ™arin tsara maganar da zata faÉ—a mashi.


 â€śKaga dai fushi ba halinka bane,nasan nayi laifi amma kayi haĆ™uri tun a jiyan ma na zubar Allah karka faÉ—awa Baba dan Allah”.Hassan sai yanzu ya sauke idanunsa ya kalleta ta zuba masa ido tana kallonsa cikin ido “I am sorry”.Ta sake faÉ—a “Ban kwana da fushinki ba Jidda”.Cewar Hassan “Amma meyasa kaki cin abincina jiya?”


“baki son haihuwa dani meyasa zaki so cin abinci dani?”


  “Fushi É—in kenan ai ,ka haĆ™ura yanzu?bazaka faÉ—awa baba ba?”


Kai ya girgiza “Har abada bazan taÉ“a kai Ć™ararki ba ,ba kuma naji zafi ba sabuda kaina ke nake jiyewa bakisan zai iya zama cutuwa gareki ba?da kin min magana akwai dabaru ai ba sai ta wannan hanyar ba duk lokacin dakika shirya ni bazan matsa maki haihuwa yanxu  ba amma shan maganin zai iya haifa maki matsala wa ma ya baki?”Sakin hannunsa tayi “Ai na yar dashi bazan sake shaba ba sai ka sani ba”.Ta faÉ—a sai da kyar  ya roĆ™eta ta faÉ—a masa makociyarta ta karÉ“a gunta tana kan tsarin maganin haihusa sai ta canja zuwa allura ita kuma shine take neman kai dashi jidda ta karÉ“a a gurinta tace mata tana sha ta Ć™arÉ“o da ya Ć™are ne ta sake siyo wani shine ya ganshi a jakar.Hassan ya rasa ma mai zece mata a shagwaÉ“e ta kallesa “Har yanzu kana jin haushi?”


  Kai ya girgiza mata “Bazan taÉ“a jin haushinki ba Jiddahty,kin san matsayinki anan?”Ya faÉ—a yana kamo hannunta ya dora a kirjinsa saitin zuciya yana kallonta “Ina Ć™aunarki ,ina Ć™aunarki Jidddaaa”.Ya Ć™are da jan sunan cikin wata siga mai nuna zallar Ć™auna Jidda kawai tana kallonsa bazata iya relating da abinda take ji a zuciyarta ba akansa ya shafa gefen fuskarta “Ba sai kin biyani da komai ba kawai roĆ™onĆ™i nake ki kula min da kanki a kodayaushe ,bana son abinda zai cutar dake”.Jidda tayi Ć™asa da idanunta a lokacin da ya sunbaci goshinta ya riĆ™o hannunta “Ɗalibanmu zasu je musabaqa zan je can makaranta ta can zamu wuce”.


   “Sai kun dawo Allah taimaka”Ta furta yana kallonta murmushi a fuskarta kafin ya cire wayarsa a charge ya sa a aljihu ya fita.Kan katifa ta zauna tana mai É—aukan wayarta ta kira Anty Baby sukayi waya sun É—an daÉ—e kafin suyi sallama ta ajje wayarta gefe ta kwanta har ranta bata zata Hassan zai É—auki abin da sauĆ™i haka ba da tunane tunane bacci ya É—auketa bayan ta tashi da azahar tayi sallah ta shiga kitchen yau tayi abin arziki shinkafa da miya ta girka mai rai ta saka a warmer ,tana da zoÉ“o da Umma ta kawo mata ta tafasa ta haÉ—a ta aika aka siyo mata Ć™anĆ™ara ta sa a cooler ta koma É—aki ta kunna kallo a waya.Hassan sai bayan isha ya dawo gida Parlour ta kawo abincin ta ajje tana masa mita zoÉ“on ba sanyi sosai tun É—azu take sa ran dawowarshi hassan yayi murmushi yana zaunawa ya tankwashe Ć™afa “Duk a yadda kika bani nasan zai min daÉ—i Amiraty kada ki damu”.Baki ta taÉ“e ya buÉ—e abincin ya zuba ba Ć™aramin yaji tayi ba miyar amma haka ya daure ya cinye ga zoÉ“o ya Ć™ara yajin a harsheshi amma dukda haka Hassan bai nuna ba ko yayi Ć™orafi sai ma faÉ—a mata yake yaji daÉ—in abincin tana kallonsa kawai.Wajen Ć™arfe tara da rabi tana zaune kan kujerar ya zo ya zauna daga gefe wayarta take ta latsawa ta ji ya kwanta da jikinsa yana mai É—ora kanshi a cinyarta ta kallesa tana turo baki bata son ya takura mata fuskarsa É—auke da murmushi yatsa yasa shafa  mata lips  ta doke hannunsa ya na mata dariya mara sauti ta hararesa komim yadda zai kai da bata haushi kyawun murmushi da dariyarsa bata kuÉ“ucewa daga ganinta.


 â€śBaki taÉ“a faÉ—amin ba”


 â€śMe?”Ta tambaya tana kallon screen na wayarta a yayinda Hassan ya ke kallon fuskarta ya rungume hannayensa a kirjinsa.


 â€śMai ne mafarkinki na rayuwa? misali kafin aurenmu”.


  Sauke idanunta tayi ta kallesa bata shiryawa tambayar tasa ba ,ta sauke wayar tana É—an nazari “Babbar yar jarida  har na kai matakin da za a ganni a bbc ,ko wata barrister haka na dai yi suna in ga an san da ni meyasa ma kake tambayata?”Ta Ć™are da faÉ—a tana kallonsa yayi faffaÉ—an murmushi “Mene?”Ta tambaya ganin har lokacin bai ce komai ba murmushi kawai yake.


  “Kai yanzu ma idan nace zan koma makaranta É—in tsakani da Allah nasan ma ba bari zakai ba kai da kake ustaz  haram ne ko?”Hassan  ya zuba mata ido yana cigaba da murmushi “Mai yasa kika faÉ—i haka?”


“Sabida haka kake”.Ta amsa kai tsaye ya numfasa “Bazan hana ki karatu ba Jidda ,yanzu ke ce mafarkina duk wani mafarkina ya tattara akanki idan banda hali nan rayuwa bana son mu fara abinda bazan iya gama maki shi ba ,ba don hakan ba da tuni na sama maki admission yanzun ma ina da wannan niyyar shiyasa na zo maki da tambayar ,indai har na samu promotion ɗina na wajen aiki ya tabbata nayi maki alƙawari zaki cigaba da karatu ƙarƙashin abinda kike so ɗin ,ina alfahari da ke kuma nasani nan gaba ma zanyi a duk sanda na kalleki ina hango ki a wani babban mataki zaki yi farinciki a rayuwa zaki ji daɗi kullum ina addua in sha Allah bazan yi disappointing naki ba zaki tuna na faɗa maki ,ina son na zama silar farincikinki da cikar burin rayuwarki ta duniya da lahira da izinin Allah i will lead you to that dream”.


  Jidda ta kallesa “Toh kai baka da dream?”


 â€śMafarkina yana dunqule waje guda da naki ,happy wife happy husband ko ba haka ba?”Ta giÉ—a kai wayarta ta É—auka tana cigaba da latsawa Hassan ya rufe idaninsa har sannan yana kan cinyarta shiru ya ratsa parlourn  ,ta shagala da wayarta bata san ma yayi bacci ba sai da taji Ć™afarta ta mata tsami ta ajje wayar tana motsawa tana kallonsa yana baccinsa hankali kwance ta Ć™urama masa ido a iya zamanta da mutane da ta sani bata taÉ“a ganin mai haĆ™uri irin Hassan ba ko baba a sanin da ta masa don wani sain yana tsawatarwa itace daman ba ya mata amma daga baya ya saketa shikuwa hassan ga kowa yake yiwa hakurinnan.Hannunta ta tsinta da taÉ“a gashin kansa da ke kwance ganin ya É—an motsa ta saurin janye hannun tayi tapping kafaÉ—arsa “Bacci zanyi ka tashi”Ta furta ta ga ya buÉ—e idanunsa murmushi ya sakar mata yana tashi zaune “Kafata tayi tsami”Ta furta ta matsa Ć™afar.


 â€śHaba mugani”Ya faÉ—a yana Ć™oĆ™arin duba mata ta ture hannunsa tana tashi “Allah ban bari ka sake É—ora min kanka akwai nauyi”.Yayi dariya “Nima ki kwanta min to”Tafiyarta tayi É—aki tana barinsa tayi shirin kwanciya tana gyara pillow taji ya matso kusa da ita yana jawota jikinsa “FaÉ—a min yaushe ne kike son baby kinga sai na kiyaye”.Makale kafaÉ—a tayi yana Ć™anĆ™ameta a jikinsa “FaÉ—a min”.


   “Nan da wasu shekaru tukun”.Ta furta ya É—ora haÉ“arshi a gefen kafaÉ—arta daga bayan “Kamar shekara nawa kenan?”


 â€śBiyar”Ta amsa “Bai yawa ba?”Ta girgiza kai tana jin hannunsa na yawo a jikinta “Yadda kika ce zan fara kiyayewa daga yau”Ya furta yana juyo da ita suka haÉ—a ido yana binta da wani kallo me wuyar fassaruwa zallar shauqi da Ć™aunarta ne a cikinsu saĆ™onnin dayake aika mata a hankula suke shigarta saÉ“anin koyaushe yau gabaki É—aya ta sakar masa jikinta suna lulawa duniyar maaurata…….