BARA A KUFAI

Page 13.

by @zeeykumurya

*BARA A KUFAI*



*13.*



Alwala kawai Uncle Aminu ya yi ya sakko ƙasa, Laila na biye da shi tana faɗin. "Jaan ka yi mata magana da kanka ko za ta fi ji, ta zo mu je na kai ta ɗakinta ma ta ƙi." Kallon tsanaki ya bi Hasina da shi ya ce. "Ba zan ji daɗi ba idan ina ganin ki a haka, idan ba kya son zama a nan ɗin bari na yi sallah na dawo na mayar da ke gida." Saurin girgiza kai ta yi tare da faɗin. "Ba haka ba ne Uncle, in sha Allah zan saki jikina kamar yadda kake so." Ta ƙarashe maganar tana ƙaƙalo murmushi. Cikin jin daɗi ya ce. "Yawwa ko ke fa, ta so mu je na kai ki ɗakin da za ki zauna da kaina." Ko gama rufe baki bai yi ba ta miƙe, don ta san idan ya tafi Laila ba kai ta za ta yi ba. Da kansa ya ɗauki ledar kayanta ya yi gaba ta bi shi a baya. Laila ta raka ta da mugun kallo tare da jan ƙwafa a ranta, abin da ya ƙara ƙona mata rai ɗakin da ƙannenta suke sauka idan suka zo gidan nan ya kai Hasina.

Farincikin da Hasina ta tsinci kanta da ta ga ɗakin da za ta dinga kwana ba zai misaltu ba, ko sallah ba ta yi ba sai da ta fara yin video a gaban mudubi ta saka a status, a ranta ta ƙudurce duk kora da halin da Laila za ta yi mata ba za ta bar gidan nan kusa ba, don ta ga guri, da rawar jiki ta yi wa Tasneem ƙawarta voice note ta sanar mata za ta iya zuwa gidansu yanzu, da ma abin da ya sa a baya ba ta bari ta zo ba suna shirye-shiryen tashi su bar waccan unguwar ne, amma yanzu sun dawo sabon gidansu duk lokacin da ta shirya ta zo kawai za ta tura mata address. 

Zuwan Laila biyu ɗakin kafin ta idar da Sallah, hakan ya sa tana idarwa ta fita parlour ta same ta.

"Mu je kitchen aiki za mu yi." Ta faɗa a yanƙwane.

Sosai Hasina ta bautu, don kusan sakar mata ragamar komai ta yi, ga yunwa tana ji, amma haka ta daure har suka kammala, tare suka yi dinner duka a dinning, yaran sai gudunta suke ita kuma tana yi musu wasa. 
Irin gidan da ta so a haifo ta kenan, inda za a dinga cin abinci a dinning, rayuwar da ta daɗe tana fata da buri, ita kam ko yankar naman jikinta Laila za ta dinga yi ba za ta bar gidan nan ba, ko don irin wannan abincin mai kaza da kayan alatu, ga sassanyan leman kwali da gwangwani kala-kala. Sai da ta cika cikinta dam sannan ta koma ɗakin da aka sauke ta, missed call ɗin Amma ta tarar har huɗu, maimakon ta kira ta sai ta shiga gyara fuska don sake yin wasu videos ɗin ta yaɗa a duniya. 

****** ******

Cike da gajiyar zuci da ta gangar jiki Juraij ya koma gida, kamar yadda yake ƙa'ida a gare shi sai da ya fara zuwa ya duba jikin Daddy sannan ya sauko, Ramlah ta taimaka masa ya yi wanka ya ci abinci, bayan ya kammala komai ya yi sallah ya koma Master bedroom ɗinsa, inda yake kaɗaicewa idan zai yi wani abu da ba ya buƙatar kowa a kusa da shi. 

Hotunan sign ɗin da ya ɗauka a jikin gawar Sheikh Adnan da ƴan boarding school ɗin da aka ƙwaƙulewa ido da wasu na baya ya haɗe guri ɗaya ya zuba musu ido, babu wani banbanci ko na ɗigo a jikin alamomin, gabaɗayansu iri ɗaya ne, tabbacin hasashensa ya zama gaskiya kenan. Lumshe idonsa ya yi cikin son tuna inda ya taɓa ganin alamar, don tabbas ya san ta a jikin wani ko wata tun kafin ya fara ankarewa da ita a inda duk aka aikata munanan ayyukan zalunci, rashin gano ko a gurin waye ya sa ya miƙe ya ɗauko wata wayarsa da ba ya amfani da ita, ya lalubo wasu hotuna a ciki ya zuba musu ido cikin kewa da rauni, a hankali ya shafi kan screen ɗin yana sauraren bugun zuciyarsa da ya sauya, a duk lokacin da abubuwa suka yi masa yawa ya ji kansa kamar zai yi bindiga da ya kalli hotunan yake jin wani irin sanyi da salama na ziyartar zuciyarsa, su saukar masa da nutsuwa a dukkan jini da tsokarsa, a gefe guda kuma suna fama masa wani tabo da bai san ranar warkewar shi ba. 

Ringing ɗin wayarsa mai bayyana sunan wanda yake kira ne ya dawo da shi daga duniyar da ya lula, ya sauke numfashi tare da mayar da wayar ma'ajiyarta, sai da ya kashe laptop ɗin da ya yi amfani da ita sannan ya kwashi wayoyinsa ya bar ɗakin, Tahir ne ya kira shi, duk da bai ɗaga ba ya san sun ƙaraso gidan ne. 

Da sauri Ramlah ta bar jikin window inda take leƙen shi ta yi hanyar ɗakinta, zuciyarta cike da son sanin abin da yake gani a cikin wannan wayar a kullum, da kuma dalilin da ya sa yanayinsa yake sauyawa a duk lokacin da ya kalla.

***** ******

Kansu Aliyu ya ɗauki zafi da shirin fara exam, musamman shi da ba ya nan ba ya can a yi wa mutane toturial,  yau da yamma ya kira Amma, bayan sun gaisa ya sanar mata gobe za su fara exam ta taya su da addu'a, ya sha addu'oi sosai kafin suka yi sallama yana jin wani irin daɗi da nishaɗi na jin muryar mahaifiya. 

Misalin ƙarfe biyar suna gaban class ɗinsu yana koya wa wasu mata calculation Monitor ɗinsu ya zo ya kira shi. 

"Tun safe Dr. Dubiya ta aiko aka kira ni na je office ɗinta, ta ba ni list na wasu Reg. Numbers ta ce mini na tura mata su su same ta a office around 5:30, na ga kana cikinsu, sai ka yi hanzari ka je kar time ya ƙure, don ka san halin matar nan ba ta da kyau."

Cikin mamaki Aliyu ya ce. "To! Me muka yi mu kuma?" Dafa kafaɗarsa Monitor ya yi ya ce. "Easy Ƙwaro, ba wani abu ba ne na sani, na tarar tana ta recording C.A may be akan haka ne." 

"To ai ni na yi mata komai, na yi test na yi mata assignment." 

"Ka je dai ka ji, Khairan in sha Allah." 

Calculator ɗin hannunsa ya ajiye cikin sanyin jiki ya tafi, ya tarar da wasu students ɗin da yawa, da ƴan class ɗinsu da wasu, sai da ya jira wanda suka riga shi suka shiga suka fito sannan shi ma ya shiga yana karanto addu'ar da shi kansa bai san dalili ba, yana fatan dai su rabu lafiya don kowa ya san ƙiris take jira ta kayar da mutum course ɗinta. 

Da sallama ya shiga, ya tarar da ita a ɗuke tana duba wasu papers da glasses sanye a idonta, ɗago kai ta yi ta dube shi, da sauri ya yi ƙasa da kansa don ji ya yi gabansa ya faɗi. Ba yabo ba fallasa ta nuna masa kujerar gaban table ɗinta ta ce. "Have a seat." 

"Thank you Ma." 

Ya faɗa tare da zama a ɗarare.

"Your name?" 

"Aliyu Lawan Abdullahi." 

"Reg.no." 

Ya faɗa mata full yadda za ta gane daga department ɗin da yake.

Wata takarda ta ɗauko ta miƙa masa tare da faɗin. "Check your name." 

"Ok Ma." Ya faɗa tare da karɓa ya duba ya nuna mata, karɓa ta yi tana bin shi da kallo ta ce. "Me ya sa ba ka taɓa attending class ɗina ba?" A ɗan ruɗe ya waro ido waje ya ce. "Wallahi Ma ban taɓa fashi ko sau ɗaya ba tun daga farkon semestern nan har kika yi covering." Glasses ɗin idonta ta zare, ba ta ce komai ba. Hakan ya sa ya ci gaba da yi mata bayani cikin fatan ta yarda da shi, ya fara tuttuno mata wasu abubuwan da suka faru a lokutan da take yi musu lectures, ba ta katse shi ba har ya kammala, takardar ta sake miƙa masa ta ce. "To ga dai abin da na gani ni, C.A ɗinku ne gabaɗaya na shigar, ka duba da kyau za ka ga babu sunanka a gurin attendence." Hannunsa har karkarwa yake gurin karɓa, gabaɗaya jikinsa ya yi sanyi har ya ji kamar yawun bakinsa ya ƙafe. Ya ci burin yadda ya fara karatu lafiya ba C.O ya ƙare a haka, ko don ya koma ya tunkari ɗinkinsa ya fara taimakar Amma, ya kuma fita da kwali mai kyau da za ta yi alfahari da shi, amma a yanzu ya ji duk ya sare, don ya san wannan rashin attendence ɗin zai iya janyo masa spill a wannan course ɗin.

"Ga wasu papers can, je ka duba su a tsanake ko yaran da na ba wa su shigar mini da marks ɗin ne suka yi mistake, in har da gaske kana attending class ɗina za ka gani." Ta yi maganar cikin ƙasaitar da ta zame mata jiki kamar ba ta so.

Da azarɓaɓi ya je ya duba, cikin sa'a ya gano sunansa ya kawo mata ta duba, jinjina kai ta yi ta ce. "Ga inda problem ɗin yake, shi ya sa nake kiran ku don ku duba da kanku." Ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ya sauke yana ƙara jinjina ƙa'ida irin tata, komai nata a tsare daki-daki. Da hannu ta nuna masa ƙofa bayan ta shigar masa da marks ɗinsa, godiya ya yi mata ya fice da sauri yana hamdala ga Allah. 

Da wani irin kallo ta bi shi tare da sakin guntun murmushi, wayarta ta latsa ta kara a kunne, bayan an ɗaga ta ce. "Shi ne! Na ƙara confirming yanzu." Ta yi shiru na wasu sakanni sannan ta saki dariya ta ce. "Sai mun kuma magana, bye." Daga haka ta sauke wayar ta kashe tana maimaita full name ɗin Aliyu a cikin ranta.

***** *****

Da daddare da Baba ya dawo Inno ta kira shi ɗakinta, bayan ya dubi ko'ina baki a washe ya ce. "Gaskiya Lauratu tana gatanta ki, a duk lokacin da na shigo ɗakin nan naki sai na ji kamar kar na fita, haske ta ko'ina ga iskar fankar na kaɗawa, ga ko'ina tsaf sai ƙamshi ke tashi." Haɗe rai Inno ta yi ta ce. "Yaya kiran ka na yi akan matakin da ka ce za ka ɗauka akan waccan munafukar yarinyar, na ji shiru ba ka ce komai ba kuma a gabanka suka dawo, idan kuma ɓacin ranmu ni da Laure ba naka ba ne to na sani." Hangame baki Baba ya yi ya ce. "Kul! Kar ki sake furta haka, ɗazun da suka dawo ina ta sauri ne sai na sha'afa, amma yanzu za a yi ta ta ƙare, ai duk duniya babu mai taɓa ku ya zauna lafiya bare kuma wanda yake a ƙarƙashina, Laure fa ƴar albarka, ai mataki zan ɗauka tsatstsaura da zai firgita su daga shegiyar ƴar har uwar tata, in ma ta kama sai ta bar gidan gabaɗaya." Da sauri Inno ta ce. "A'a kar ka kore ta, ka bar ta, ka ɗauki matakin da ya dace kawai."

"In sha Allahu rabbi, yanzu ma kuwa." Ya yi maganar yana miƙewa, har ya fara tafiya ya dakata ya ce. "Kamar ƙamshin ƙwai nake ji fa tunda na shigo." Husna da ke soyawa a wani ɗan lungu da ke parloun ta zumɓura baki tare da faɗin. "Wannan mutumin akwai jarabar kwaɗayi, don masifa sai da ya jiyo ƙamshi duk yadda nake addu'ar Allah ya sa kar ya ji." Inno kuwa cikin takaici ta ce. "Husna ce take dafa indomie da ƙwai, ka je idan ta gama zan dafa maka kai ma." Baki ya washe kamar gonar auduga ya ce. "Da kuwa kin kyauta, don a yunwace matuƙa gaya na dawo." Ba ta tanka masa ba har ya fice, don ita kanta wani lokacin rasa inda Baban ya nufa take yi, akwai shi da azababben kwaɗayi da son cin daɗi, indai za ka dinga ba shi abu to zai ta bin ka yana nane maka da yi ma fadanci, gefe guda kuma akwai son nuna shi wani ne a wajen mutane, musamman waɗanda ba su da shi, yanzu zai ta yi musu fariya da nuna shi wani hamshaƙi ne.

Cikin hargagi Baba ya shiga ƙwala wa Umma kira a tsakar gida, ta fito a guje ɗankwali a hannu ta tsugunna a gabansa, takaici ya sa Ummi jan tsaki, don ta tsani wannan rawar jikin da Umma take a kan Baba, Ahayan kuwa runtse idonta ta yi don a duniya ba abin da ta tsana kamar yadda Baba yake wulaƙanta Umma a gaban kowa.

"Yanzu Karima har wuyanku ya yi kaurin da Laure za ta yi wa waccan ƴar'iskar ƴar taki hukunci ku kai ta ƙara gurin Adam?"

Dafe ƙirji Umma ta yi ta ce. "Ni! Wallahi Malam ban kai ƙara ba, ban faɗa masa komai ba, kawai....."

"Dalla rufe mini baki, Zulan da ta faɗa mini za ta yi miki ƙarya ne? To ki buɗe kunnuwanki ki saurare ni da kyau, daga yau sai yau kar a ƙara girki a gidan nan a ba ta ko daidai da ƙwayar shinkafa ɗaya ne, tunda ita ba ta da mutunci ba ta san shi ba, tana agola saboda ita ce uwar tsaurin ido shi ne za ta kai ƙarar ƴar masu gida, wadda ita ce ƙarfin ci da gidan nan, saboda ita butulu ce ba ta san halacci ba." 

Girgiza kai Umma ta shiga yi a gigice ta ce. "Don girman Allah da darajar iyayenka ka yi haƙuri Malam, idan aka daina ba ta abinci ban san ina zan samu na dinga ba ta tana ci ba, ka yi ha..." 

"Ke! Na gama magana, idan kuma kika ƙi ji kika sake ba ta abincina ko na wani a gidan nan a bakin aurenki!" Ya katse Umma a tsawace da faɗin haka, tare da barin tsakar gidan fuuuu kamar zai tashi sama. 

Lumshe ido kawai Ahayan ta yi, hawaye masu zafi suka kwaranyo ta gefen idonta. 

Haɓa Ummi ta kama ta dubi Raudah ta ce. "Tabdijan!"

Cikin yarinta Sabira ta ce. "Ko Baba ya daina ba ki abinci Allah zai ba ki Aunty Ahayan, na aljanna ma in sha Allah!" 

Jiki a mace Umma ta janyo ƙafa ta dawo ɗaki ta zauna ta rafka tagumi, yaran duk suka zuba mata ido ba su ce komai ba.

Sosai hukuncin da Baba ya yanke ya yi wa Inno daɗi, don ba ta taɓa tunanin matakin da zai ɗauka ba kenan, ta san watan tagayyarar Ahayan ne ya tsaya, da ma ita burinta kenan, saboda wata irin tsana take wa Ahayan da a kullum burinta ta ga ta ƙasƙanta.


****** *****


Manyan mutane ne su biyu zaune a wani madaidaicin parlour wanda babu wadatar haske a cikinsa suna fuskantar juna. A hankali mai ƙibar ciki ya nisa ya yi ya ce. "Ka tabbatar za mu iya duk tattaunawar da za mu yi ta sirri a nan ba tare da wani ya ji ko ya gani ba?" Murmushi Siririn ya yi ya ce. "Ba ka da matsala fa mutumina na faɗa maka, ka saki jikinka mu yi abin da za mu yi kawai, ka san ba mu da lokaci, akwai meeting na ƙungiya anjima." Gyara babbar rigar jikinsa ya yi ya ce. "Batu ne nake tafe da shi mai matuƙar muhimmanci da zai amfane mu ni da kai idan har ka ba ni haɗin kai." Tattara dukkan hankali da nutsuwa Siririn ya yi a gare shi ya ce. "Ina sauraren ka, kuma a shirye nake na bi duk hanyar da ka zo mana da ita indai mai ɓullewa ce." 

"Good! So nake mu haɗa ƙarfi da ƙarfe, mu yi iya yin mu, mu tashi tsaye mu jajirce mu nemo duk inda wannan goɗiyar da Ƙanzula take faɗa a duk inda take mu kai mata ita a ƙasa da wata ɗaya, domin mu samu mu haye karagar shugabancin dakarun ƙungiya, ya zama sai abin da muke so Ƙanzula za ta yi, mu samu damar mallakar dukkanin ƙasashen nahiyar nan da ma wasu na ƙetare, kowa da kowa zai zamto yana ƙasanmu ne, tun daga kan masu mulki da sarakai da hukumomin tsaro zuwa al'umma bakiɗaya, masu kuɗi da masu masana'antu za su dinga bibiyarmu kamar yadda ƙuda yake bin alawa domin mu saka musu hannun jari, duk wata yarjejeniya da kasashen ƙetare za su gindaya ta hannunmu za ta biyo, za mu juya kowa da kowa kamar waina a cikin tanda, mutane za su zamo tamkar bayinmu saboda sai abin da muka tsara, sai yadda muka so haka za a yi, kowa da komai zai kasance a tafi hannunmu." 

Gajeren murmushi Siririn ya yi ya ce. "Yanzun ma ai akan wannan matsayin duk wani badakare na ƙungiya yake." Cikin tarar numfashi mai ƙibar ya ce. "Akwai bambanci, saboda wancan tsarin zai kasance iya mu biyu ne kacal ba mu bakwai ba." Jinjina kai Siririn ya yi ya ce. "Na fahimta, amma ka sani wannan tsari ne mai hatsari, tsari ne da ya saɓa wa dokar ƙungiya, tsari ne da idan aka samu akasi komai zai iya lalacewa, ciki har da wahalar da muke shafe shekaru muna yi na bautawa ƙungiya da gina ta." 

"Hakan ba zai taɓa faruwa ba matuƙar za mu dage da zubar da jini a doron ƙasa, saboda haka idan ka amince mu tafi step na gaba." 

"Na amince." 

Ya faɗa idonsa ƙyam a kansa.

"Good! Step na farko da za mu fara takawa shi ne gano inda za mu samu goɗiyar nan." 

"Ta yaya? A ina za mu same ta, shekaru masu yawa fa ana maganarta amma har yanzu shiru ba wani labari, abin da bai taɓa faruwa ba tun kafuwar Ƙungiya, anya kuwa tana nahiyar nan tamu?" 

"Tana nan, a kusa da ɗayanmu, ka fi kowa sanin Ƙanzula ba ta faɗar abin da babu shi, don haka dole mu zage damtse mu nemo ta a duk inda take! Ko ma waye take tare da shi yake ɓoye ta mu za mu binciko ta mu raba shi da ita!" 



Hannu ya dunƙule ya miƙa masa, shi ma dunƙule nasa ya yi suka haɗe suka bubbuga tare da kecewa da wata irin dariya da ta amsa kuwwa a gabaɗaya falon.


***** ***** 


A ranar da Nas ya zo gurin Saudat da daddare ragowar baƙin gidan duk suka tafi, har su Shamsiyya da Yaya Mardiyya, duk wanda zai tafi sai ya gwaɓa wa Saudat magana ya ce saura ita, murmushi kawai take yi wanda ya fi kuka ciwo. Sai da ta tsaftace gidan sannan ta kwanta. 

Washegari da suka tashi gidan tsit kamar ba shi ne kwana biyu da suka wuce yake cikin hayaniya ba, Mama tana bacci Saudat ta yi duk ayyukan gidan, ta tafasa musu ruwan tea ta soya dankali da ƙwai, bayan ta gama ta ci ta adana wa Mama nata a kan dinning, ta koma ɗaki ta shirya a gurguje don tafiya Tahfiz, da ma hidimar biki ce ta saka ta fashi a wancan satin, don kullum take zuwa, Saturday to Wednesday, ƙarfe tara zuwa shabiyu da rabi, ta yi hadda tun a shekarun baya, yanzu tana tisa ta biyu, burinsu kenan ita da Abba ta zama mahaddaciyar alƙur'ani, ba wani abu da yake saka ta a cikin farinciki a yanzu face zuwa Islamiyyarta, tana jin daɗin karatun sosai da yadda Malaman suke son ta da girmama ta. Tara da mintuna ta fito cikin dogon hijab ɗinta, hannunta riƙe da niƙaf da jaka, ta tarar Mama ta fito tana zaune tana waya, zaunawa ta yi a kan carpet ta jira ta kammala.

"Saudat! Me nake gani haka? Ina za ki je?" Mama ta tambaya tana bin ta da ido bayan ta katse wayar.

"Islamiyya zan je, zan koma yau saboda bana son fashina ya yi yawa." 

Gyara zama Mama ta yi ta ce. "To ki koma ki cire uniform ɗin nan, saboda kin daina zuwa makarantar daga rana irinta yau, karatun da kika yi a baya ya wadatar Allah ya amfana, a nan gidan dai ya isa haka, sai dai idan kin je gidan mijinki idan zai bar ki ki ci gaba." A raunane ta ce. "Amma me ya sa haka Mama?" 

"Saboda nan da wata biyu muke son a yi bikinku da Nasir, jiya bayan kin yi bacci Baba Gali da kansa ya kira ni har ya je ya faɗa masa, don haka za ki zauna a gida a fara gyara miki wannan dusar fatar kafin lokacin, a koya miki gayu da kwalliya don ba za ki je gida mai daraja da ƙima irin wannan a wannan dinkumen da kike ba." 

"Amma Mama...." 

"Ba shawararki na nema ba don na riga na gama yanke hukunci, tashi ki ba ni guri, kin san bana son musu." 

Gwiwa a mace ta miƙe idanunta cike da ƙwalla, da jan ƙafa ta ƙarasa ɗakinta ta zube a kan katifa, anya za ta yarda da wannan auren kuwa? Tana son ta yi wa Mama biyayya ko don ta samu kulawarta irin wadda ta daɗe tana fatan samu, amma burikanta fa? Burin zama shahararriyar mai rera karatun alƙur'ani tartilan, burin samun zaunanniyar hadda da koyar da karatu a Islamiyyu sadaƙatul jariya ga Abbanta, a yadda ta ga Nas bai yi kala da waɗanda za su bari ta cika burikanta ba, abubuwan da Aunty Hindu ta faɗa mata ne suka faɗo mata a rai, da sauri ta shiga girgiza kai tare da faɗin. "No! Ba zan iya rayuwa da Nasir ba, ba irin mijin da nake fata da addu'ar samu ba ne, Allah ka shiga lamarina ka kawo mini ɗauki, ka zaɓa mini abin da ya fi zama alkhairi a gare ni."

Ta ƙarashe maganar tare da miƙewa ta zare hijab ɗin jikinta da ta ji tamkar ta haɗa da ɗan ragowar farincikin rayuwarta ta zare su a tare, muddin auren Nas yana cikin ƙaddarorinta!



*#Zeey Kumurya*
*#****