Y'AN ABUJA

Page 2

by @1239900

Juwairiyyah bata b'ata lokaci ba wajen isar da saqon Abbahn nasu a wajen Goggo, da kyar ta amsa mata sannan Juwairiyyah ta koma bangaren su,da isa da qasaita Goggo Sarai ta shiga parlourn Mama,hakan ne ya sanya Abban murmusawa duk da cewa ranshi na matuqar quna  game da abubuwan da take yi mishi.

"Sarauta kenan yi ki qaraso mu yi abinda zamu yi na fita sallah ko?"

Qarasa shiga ta yi tana hura hanci ta zauna a gefen hannun shi na dama, inda Mama Bilki kuma ke zaune a gefen shi na hagu, cikin wani irin yanayi mara misaltuwa ya buɗe baki ya fara magana,

"Da farko dai zan ma Allah godiya daya kawo min wannan rana da nake ta buri, duk da cewa ta zo min a bazata kuma ba a yanda na so zuwan ta ba, amma dai Alhamdulillah,a yau ne manema auren yaran nan su Suwaiba, Saudat da Salma suka zo, kuma mun karbe su a gidan Yaya Balarabe cikin aminci da mutunci, inda suka damqa mana dukiyar auren yaran, Suwaiba kudin sadakin ta da na gani ina so da kudin da zata hada lefe dika, an bamu million huɗu da dubu ɗari biyu, sai na Saudat Ita kuma Million biyu da dubu ɗari bakwai, a gaskiya na so na qi karba saboda kudin sunyi yawa, kamar wasu wanda zamu saida 'ya'yan?....... "

A hargitse cikin damuwa da jimami Goggo Sarai ta ce,

"Abban su ina fatan dai baka yi mana baqin ciki irin na iyayen zamani ka sa an rage kudin nan ba?"

Cikin ɓacin rai Abbah ya kalle ta ya ce,

" Amma dai na rasa me yasa baki da d'a'a Sarai? Ya ina magana ban qarasa ba zaki katse ni? Har kina ikirarin zan ma 'ya'yana baqin cikin iyayen zamani? Anya rayuwar da kk ɗora yaran nan akai za ta ɓulle da ku kuwa? Gaba ɗaya kin sa tarbiyyar yarana ta zamo a lalace? Kin raina ni baki ganina da qima da mutunci? Kedai harka in ba ta kudi ba baki san komai ba? Na gode Allah da yasa ina iyakar qoqarin riqe gidana ni  Baballiya da ke kam na san da karuwanci zaki saka 'ya'yana yi su na kawo maki kudi, haba, bai ishe ki misali ba akan Balki da 'yar ta guda ɗaya tilo? 'Yarta ɗaya amma ta tsaya wajen bata ilimin addini dana zamani daidai iyawar ta, ke kuwa in ba Salma ba da ta yi sauka yarannan biyu ba zasu iya bude qur'ani su yi karatu mai kyau ba, Salman ma gashi nan ne dai kawai, to ina mai maki nasiha da kiji tsoron Allah akan abinda kk yi, ina jiye maki ranar kuka, ranar dana sani, ranar ni 'yasu,........ "

Da sauri ta d'aga masa hannu ta na yatsine ta ce,

"A'a faaaa, bafa zaka sani a gaba ba kana min mugun fata da kuma maganganu na nuna baqin ciki qarara a wannan al'amari ba, 'Ya'ya dai nawa ne, nice na yi naqudar su na haifa abina, ba wanda ya taya ni lokacin da nake qafa ɗaya a lahira, d'aya a duniya ko akwai? Dan haka sai wanda naga damar su aura sannan zasu aura, nifa takura ce bana so tammm, yanzu ka bamu kuɗin lefen da na sadakin dan musulunci bai yarda kowa ya taba dukiyar auren yara ba sai su ehe"

"Hmmmmm Sarai kenan, ke kaɗai  ai ki ka yi cikin su ki ka haife su ba da ni ba dole ki ce yaran ki ne ke kaɗai,to bari kiji iya kuɗin lefe zan baku, sauran kuwa sai sanda akai auren su zan baki su,wai da ke a taki qaramar kwakwalwar sai na dauki wannan maqudan kudin na baki dika? Haka kawai aje wani abu ya faru bana fata ba ai aure ba ku barni da biya da tashin hankali? To bazai yu ba"

Bala'i ta miqe tana zazzagawa son ranta ita sai an bata kudin, tashi ya yi ya kad'e rigar shi ya fice dika a gidan, daidai lokacin da Mama Balki ke cewa,

" Ubangiji ya sanya alkairi da albarka, Allah ya kare dukkan abinqi ya basu zaman lfy"

"Hahaiiiiiiiii Cassssss, ni zaki wa bariki Balki? Zuciyar ki cike da baqin ciki amma wai kk addu'a mai daɗi irin haka,to dama dai ba daga bakin ki ta fito ba dana ce ameen"

Sa kai ta yi ta fice ta shiga madafin su ta hau aikace2, tana yi tana masifa kamar wadda ta zautu, yaran ne suka dawo daga yawon tazubar din su da sunan Islamiyya suka tarar ta na masifa, tambayar ta Saudat ta yi da cewa,

"Wai Goggo me ke faruwa ne gaba daya muryar ki har qofar gida ana jiyowa"

"Ba ni da wannan sallamammen uban naku ba ne, an kawo kudin auren ku sun riqe shida Balarabe, to ni ba zasu nuna min isa da iko ba, sai sun kawo kudin nan dika"

Cikin qasa da murya Suwaibah ta ce,

"Goggo kwantar da hankalin ki tashi mu shiga ciki ki gani"

D'aki suka shiga ta d'akko mata maqudan kudi a jakar ta ta zube mata su a saman gado, tsabar razana da ganin yawan su se da Goggo tai baya dafe da qirji ta na zaro ido,

"Suwaibah waya baki wannan kudi haka me yawa?"

Fari ta yi farrrr da idanun ta kafin ta ce,

" Alhaji Salihu mai tumbin Nera  kk ji Goggo, cewa ya yi ga su ko zan qara wasu abubuwa a lefe yaso bayar wa a can wajen karbar sadakin se ya fuskanci za a iya cewa sun yi yawa, shi kuma yana ganin ko nawa ne zai iya kashewa ya samu yar zumar shi"

( Sunan da yakan kirata kenan lokacin watsewar su) dariya Saudat ta yi ta ce,

"Aaaaa kice Adda Suwaiba Alhaji ya ji zuma yau"

Dariya suka yi dika har uwar tasu suka tafa, baqin cikin ma da take ciki tuni ta manta da shi, ba sallah ba salati suna nan zaune ana maida yanda akai da yanda za ayi.

**************************

Washegari Juwaiirah  ce zaune saman sallaya da goshin asuba ta na ta ibada, kamar wata babbar mata, Maman ta ta saba mata da tashin dare, dan ta sanar da ita cewar duk abinda bawa ke so ya roqi Allah da ikhlasi da yaqinin Allah zai biya masa buqatar shi to fa ba makawa Allah zai biya masa buqatar shi musamman in bawan nan ya yi addu'ar a lokutan karbar addu'a, wanda qarfe uku zuwa asuba ko huɗu zuwa asuba Allah na amsa addu'ar bayin shi dan lokaci ne mai mahimmanci ga bayin Allah, sannan ba a son mutum mumini ya zage ya dinga kwasar bacci daga farkon dare har zuwa qarshen dare ba tare da ya farka ya yi nafila ko da raka'a biyu bane,mu ke da buqata a wajen Allah Allah ba shi da buqatar mu, ya na daga cikin cikar imanin mutum ya dinga rokar Allah ya bashi ikon ganawa da shi a cikin dare ko da ya na jin kiwar yin hakan da kan kan shi ,to sai Allah ya bashi ikon tashi ɗin.

Hannu ta daga sama cikin qasqantar da kan ta a gaban mahaliccin ta ta ce,

" Ya Allah kai ne masanin abin da ke zuciya ta Allah ka biya min dikkan buqatu na na alkairi Ka sa Yaya Jabeer ya zama shine mafi alkairi a rayuwa ta duniya da lahira....."

Wannan addu'ar ce tafi daukan hankali na, nace tooooo waye kuma Yaya Jabeer? Addu'ar ta ta ci gaba bayan ta gama ta yi wa iyayen ta da yan uwan ta da dikkan muslmi, bayan ta idar ne ta hau karanta Qur'ani da zazzaqar muryar ta, har aka kira sallah ta gabatar da sallar asuba ta dora da azkar da karatu har gari ya waye, a sannan ne ta samu ta dan koma bacci zuwa qarfe takwas ta tashi, ta fara taya Maman ta aiki, bayan ta gama gyara gidan dan ba su ke girki ba balle ta taya ta aikin girki, wanka ta shiga ta fito,haka nan taji tana son yin kwalliya yau dan ita ba ma'abociyar yin kwalliya bane  a koda yaushe,sai lokaci lokaci ta kan dan taɓa ,ta na gama  sheqa kwalliyar ta me kyau ta buɗe akwatin ta ta dakko wata rigar ta doguwa ta atampa ,rigar na da fadi ta qasa ta sama kuma an dan tsuke ta da dogon hannu ,jujjuya rigar ta yi ta kara ta a jikin ta kafin daga baya cikin murmushi ta saka rigar,yanda rigar ta zauna mata abin kallo ne domin Juwairah  akwai shape mai kyau, gyara gashin kanta ta yi da kyar dan yawan shi da tsahon shi ke wahal da ita wajen kula da shi, bayan ta gama ne ta kafa dauri me kyau, ta samu tiraren ta da Mama ta bata ta fesa, tana gamawa ta je wajen Maman ta ta na wani yanga ta na nuna mata yau fa Allah ya yarda 'yar ta ta yi kwalliya, ta duqa zata dau Ammar, cikin tsokana irin na tsakanin 'ya da uwar da suka shaqu da juna Mama ta ce,

" A'a kaga Juwairere saraunuyar mata,Juwairere  diyar Mamanta gaye ne aka sha haka yau, to ko dai suruki na ne zai zo?"

Cike da shagwaba da nuna jin kunyar Maman nata Juwairiyyah ta ce,

"Haba Mama wanne irin suruki kuma,kawai dai na yi sha'awar na yi kwalliya ne yau, kuma ni mama na ce maki bana son Juwairere  Allah dariya qawayena suke min in suka zo sukaji kina fada musamman Nafeesa"

Cikin 'yar dariya Mama ta ce,

"To in banda abinki Nafi ai qanwar ki ce kin fa bata kwana bakwai masu kyau dan haka data tsokane ki sai ki yi murmushi irin na manyan yayu saboda yarinta ce ba wani abu ba"

Dariya suka saka a tare, sosai suke dariya abun su gwanin sha'awa,Goggo Sarai ce ta ja dogon tsaki ta ci gaba da aikin ta,a tunanin ta Mama Balkin na tsokanar ta ne kawai su na yi ne dan su bata haushi , ba tare da sun ji sallama ba Juwairiyyah ta ji an kama hancin ta, muryar da ta ke tsakanin buri da muradin ji ce ta ce mata,

"Wannan dariyar taku Mama ba zata bari kuji komai ba , musamman wannan Juwaireren da ta buɗe wannan qaramin bakin nata take cika wa mutane gida da qara da wata Muryar ta se kace ta kanari"

Tsalle ta soma yi na murnar ganin Yayan nata sannan ta kama hannayen shi dika biyun a nata ta na kallon kyakkyawar fuskar shi da ta yi kewa ta ce,

" Yayana, wayyo Yayana kaine da gaske? I missed u so much Yayana, yaushe ka dawo? "

" Oh Juwaiiraah ko zama bai yi ba fa wannan zumud'i da tambayoyi a bari ya ɗan zauna ya huta mana"

"Mama rabu da ita nima ba qaramin Missing din Juwairere na na yi ba, ban ga laifin ta ba dan ta nuna murnar ta na gani na"

Murmushi Mama ta yi sannan ta fita d'ebo masa ɗan ruwa ya sha dan gidan haka suka tashi ko na karyawa ba a miqo masu ba, jawo ta ya yi kusa da shi sannan ya ce,

" Amma da Juwairere kin san na hana kwalliya ko?what if wani ya zo ya gan min kwalliyar mata ta? Ko a aike ki a haka kowa ya kallen min ke? A gaskiya ni dai bana so, ba wannan ba ma dai yanzu ai ta qare tinda ga angon ki nan ya gani kuma ya yaba kwalliya ta yi dari bisa dari"

Duqar da kan ta ta yi qasa wata iriyar  murna da farin ciki na ratsa ta tunda ta ji ya  kira kanshi angon ta, ga hannun ta da yake murzawa a hankali, karɓe hannun ta ta yi ta canja mazauni tana turo baki, ita a dole fushi ta fara,Mama ce ta shigo ɗauke da kofi a hannun ta ta aje masa a gaban shi ta samu wajen zama,

" Mama kin ga wannan yar rigimar ta turo baki, lallai akwai magana a cikin shi"

" A'a ni kam ba ruwana ina gefe ba a shiga tsakanin ku ai ku se mutum ya ji kunya"

komawa ya yi kusa da ita ya d'ago kanta ya na kallon kyakkyawar fuskar ta da ya ke jin zai iya shekara ya na kallon ta ba tare da ya gaji ba,

"Juwairere na me ya faru?"

Cikin 'yar kwallar da ta daddage ta taro a idon ta da ya sha kwalli ta ce,

"To ba ga shi nan ba wai Juwairere, ni Allah bana son sunan nan,gaba ɗaya kun sa Nafee na tsokana ta, Kullum ta ganni sai ta hau ce man Juwairere "

Ta qarasa maganar 'yar kwallar ta na qarasa sauka a kuncin ta bakin nan a gaba, dariya ta bashi ba kadan ba wauta da shagwabar ta na burge shi sosai

"Ki kwantar da hankalin ki princess ba zan qara faɗa ba inshaa Allah sai munyi aure"

Hararar wasa ta masa tare da jin kunyar kalmar aure da ya ce, sai kawai ta miqe ta fita a dakin da gudu tai tsakar gid tana dariya, kad'a kai Mama ta yi sannan tace

"Ni Allah dariya kuke bani yaran nan, kun iya wauta da yawa"

Cikin wata iriyar murya jabeer ya ce,

" Mama kenan ba wauta bane da gaske auren ta nake son yi, amma idan Baba zai ban ita, ko ita ɗin ma Abuja za a kai ta? Dan na ji an maida sunan gidan nan wai gidan 'YAN ABUJA saboda yaran gidan a Abuja suke son yin aure su kalar Abuja ne, ina jin haka hankali na ya tashi ina fatan Allah ya sa ba Juwairere na a cikin wannan haukan, dalilin zuwana kenan Mama wato na yad'a manufa ta na son auren Juwairiyyah, na ji a wajen Innar mu wai har an kawo kuɗin Auren wadan can marasa kunyar"

"Hhmmm haka ne Jabeer amma kasan ni ba ruwana da wannan kalmar ta 'YAN ABUJA ko? Duk inda mijin Juwairiyyah yake ina fatan ya kasance miji na gari mai addini wanda zai riqe min ita da amana ,kuma wannan magana ta Abuja su da kan su yaran gidan nan duka qirqirar wa kan su ita wai su  YAN ABUJA NE ba zasu auri kowa ba sai ɗan can, in su suna faɗa kuma sun yarda zasu aure su ni ban faɗa ba, kuma ban ba 'yata izinin kiran kanta da 'YAR ABUJA ba , in da rabon can ne gidan auren ta yake Allah ya zab'a mafi alkairi in ba can bane ni ko ina albarka na ke nema mata kullum"

" Haka ne Mama, Allah ya shige mana gaba"

"Ameeén ya Allah Jabeer"

Jabeer dan gidan Yaya Balarabe ne ya dawo daga bautar qasa inda aka tura shi illorin, ya kammala karatin shi bangaren kasuwanci, to a yanzu haka yana taɓa saida jakunkuna da takalma, ba wani arziqi ne da shi ba, yayun ta sun so matuqa ace me kuɗi ne da sun aure shi ko dan kyawun shi, amma inaaaa talauci a cewar su ya dakushe tauraruwar shi.

A yan kwanakin nan kusan kullum sai ya zo gidan su Juwairiyyah ,ga saurayin Salma mai baqin naci shima kullum ya na tafe, shi ma d'an Abuja ne ya na sana'ar saida motoci, kullum in zai zo zance se ku ga ya baza uwar riga ya shigo mota mai tsada ya zo amma fa baya bata ko sisi, wataran ne ma zai dan samu ya siyo mata yar shawarma kamar mayya tana rawar kai saurayi ya siyo mata abu ta amshe ta shigo gida,itama tini ta bi sahun manyan ta amsar kudin maza da basu jiki ai tabe2 , Alhajin da ke son ta shima in yazo zancen haka yake gama lalube ta ya yi gaba abun shi......... [18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼   YAN ABUJA.  💅🏼

WRITTEN  BY HAERMEEBRAERH