Page 5
by @1239900
Tinda suka je farfajiyar hotel ɗin bakunan su Suwaiba yaqi rufuwa, ganin irin manyan motocin da suke ta gani an parker sai kwadayin arziqi da samun dukiyar su ya ninka na da,basu taɓa ganin manyan motoci haka ba a zahiri sai a American movies, wasu ma basu taba ji ko ganin su ba duk Yawon su da kallace kallacen fina-finan nasu, ( abun ku da masu idon cin nera ga Yawon tsiya gidaje da bukukuwan masu kuɗi) hankalin su ya kai qololuwa wajen kwadayin son suga mahallin su ma'ana wajen da za a kai su ya zama shi ne gidan su.
Sun shiga wajen da ake gabatar da dinner tare da angwayen su da abokan angon da suka masu rakiya, inda suka qarasa wajen hight table din da za su zauna, iyakar ganin idanuwan su iya ganin jajayen hulina da fararen kaya da sirkin ja a jikin farin kayan ne, daga matan har mazan shigar kenan, sune kad'ai suka saka baqin lace da ratsin fari a jiki, mazan su ma farar shadda da jan aiki a jiki da jar hula ne akan su.
Wani mutum babba suka gani a gefe mutane kowa ya shiga sai ya gaida shi, ya hakimce a wata qatuwar kujera, suma tashi suka yi suka kai masa gaisuwa sannan suka koma mazaunin su an fara gudanar da dinner lfy, inda daga baya aka umarci kowa yaje ya yi serving kan shi abin da zai ci a wajen, wajen maza daban wajen mata daban,a bangaren Mazan akwai wani irin nama na daban da aka zo dafawa aka masa dahuwar laushi sosai duk abin mutum ba zai gane na meye ba, matan kuwa kaji ne da sauran tarkace abinci kala2 a wajen har da na qasashen waje, sun ci sun sha, daga baya akai ta rabawa mazan wani ruwa a wata kwalba mai duhun kala, jikin su har rawa yake dan murna, kowa ana bashi yake kafa kai tas zai shanye ya ajiye kwalbar ya na lasar baki.
Bayan an yanka cake ne da sauran bidi'o'i aka tashi daga wajen dinner din,daga nan angwayen suka kama matan su suka shigar mota sannan suka ba su wani ruwa a cups masu kyau da sirkin wani magani a ciki, suna sha take bacci ya dauke su, madadin su yi gidajen su na aure da matan sai naga sun ɗauki wata hanya kamar za a bar garin basu tsaya ba sai a dokar daji, wani katafaren gida ne suka isa mai gate guda uku manya, katangar gidan duk maitar mutum na ya gudu ba zai samu dama ba saboda tsayin su, suna isa wasu qattai ne naga sun fito murdaddu sun sha baqaqen kaya da neck tie red, daukar su Suwaiba suka yi a hannu suka shiga da su gidan, a wani qaton parlour suka aje su kan kujeru suka juya suka fita,angwaye kuwa na tsaye su na jiran fitowar Ogan nasu su ji wanne umarni kuma zai basu, ji suka yi wata qatuwar murya ta yi magana,
"A kai min ko wacce d'aki, a haɗa su a gado daya,"
Ko da na duba sai na ga wannan turmusheshen mutumin ne na wajen dinner ya fito ba riga daga shi sai gajeren wando, nan take tunanin inda aka samu telan da ya iya dinka masa wannan wargajejen wandon ya faɗo rai na, ba karamin qaton mutum bane shi ɗin ,gaba ɗaya ya haɗa komai na zama qato ga tsaho ga qiba, ga tumbi, da sanqo, ga gashin baki, gana hammata nan cunkus, ga idonnan jawur, kamar gauta, ba zan taba iya kwatanta girma da yanda yake ba abin sai wanda ya gani kawai, haka ya tako da fataken qafafun shi ya kalli mazajen sukuma sai suka duqa masa alamun gaisuwa, d'aga masu kai ya yi ya ce,
" kuje sai nan da sati biyu ku dawo,dan ban taba ganin mata masu kyau irin wannan ba," ya qarasa yana lashe baki, d'aga masa kai suka yi suka amsa da,
" Tah oga zaks,"
Suka furta a tare, fita suka yi kowa hankalin shi kwance dan sun san samun su zai rubanyu da yawa, Nicon hotel suka wuce su hole abun su, dan su dama sunyi auren ne dan gudun maganar mutane, amma ba dan sun damu da auren ba, tinda a cewar su mata na nan kamar jamfa a jos.
Shigar Oga Zaks dakin keda wuya ya isa gaban gadon, yana lashe baki, kashe wutar ya yi ya kunna bed side lamp, cire masu kaya ya yi ya dakko wani magani ya shaqa masu, maganin bacci ne, wanda zai kai su kwana bakwai cif suna bacci ba tashi, ina ganin zai zame rugegen gajeren wandonnan nai gaba da gudu, ba dani za ai kallon tashin hankali ba.
Oga Zaks ba shi ya fito daga dakin nan ba tin daren sai qarfe tara na safe hamma yake yana miqa ya wani bangare ya shiga wani daki, waya ya yi naji yana,
" ku shigo, "
Sannan ya aje wayar ya shiga wanka, wasu mata ne dattijai suka shigo, dakin da su Suwaiba suke nan suka shiga, suna gyara su suna tausaya masu, ɗaya daga cikin matan ne tace,
"Hmmmm wama ya sani ko garin shegen son abun duniyar su ne suka haɗu da su, ai kinga ban ga laifin mazan da suka kawo su ba kwadayi mabudin wahala"
Jikin ajiyar zuciya d'ayar ta furta,
"Haka ne kuma Allah dai ya kyauta"
Bayan sun gama shirya su ne suka tafi suka bar su suna ta shaqar bacci, a palour suka haɗu da Oga Zaks yana zaune, ya baza uban tumbi yana kwasar girki,cikin qatuwar muryar shi ya furta,
" Daga yau duk wata shegiyar tsohuwa a cikin ku da ta qara gulma akan matan da suke shigowa gidannan sai na mai da ita matata kuma ta inda baku tsammata ba tanan zan na amfani da ita, munafukan banza da wofi ku bace min da gani,"
Jiki na rawa baki na kyarma suka hau bashi hakuri, korar su ya yi ya barke da wata mahaukaciyar dariya.
**************************
Salma kuwa matar Alhaji me saida motoci,wani qaton gida ya kaita a wata unguwa a gwarinpa, gidan ya haɗu iyakar haɗuwa dan kuwa tun daga baƙin gate d'in gidan za ka san cewa nera ta zauna, bayan ya tsaida motar a bakin gate d'in ne ya fita da kan shi ya je ya bude gate sannan ya koma ya shigar da motar cikin harabar gidan,a tare suka fito daga motar sannan ya daga ya riqe ta a jikin shi, bayan sun shiga cikin gidan ne Salma ta hau zare ido dan ganin uwar dukiyar dake gidan.
Wani d'aki ya kaita mai kyau, suna shiga ba tare da aikata komai da ya kamata amarya da ango sun gabatar ba a daren su na farko ya ja ta gare shi ya fara aika mata saqonnin shi da ya jima ya na jiran irin wannan ranar ya isar da su gare ta, dan kuwa shi dama bai wani more ta ba sosai, kuma babu laifi Salma bata yi irin wayewar su Suwaiba ba ko ya je soyayyar tasu bata wuce kiss da shafe shafe bata taɓa bashi dama ya kusance ta ba,haka angon Salma ya fara qoqarin cika burin shi a kan ta babu sallah ba salati ba godiya ga Allah na daren farko na ma'aurata ba adduar komai haka ya maida ita cikakkiyar mace,ai kuwa yasha kuka da zagi a wajen Salma, dan ashar sai wanda ta manta, bayan sun kammala komai ne ya yi ta rarrashin ta,a qasan zuciyar shi yana ayyana,
'Zakici uban ki ne wannan zagin da dukan da kk mun duk sai na rama na fanshe abuna, yar me kwadayin tsiya'
A zahiri kuwa wani irin lelen ta yake kamar kwai, a cikin sati dayan nan ya nuna mata gata sosai, wanda ta dinga hango gidan su tana ayyanawa a ranta
'Dama haka rayuwar Abuja take da daɗi, ga miji gangariya na samu, ga kayan alatu na ci na sha na kwanta miji namin hidima, tab amma an bar Juwairiyyah a baya ina tausaya ma rayuwar ta, dan kuwa haka zata qare ta cikin talauci da babu'
Shafa gefen fuskar ta Alhajin nata ya yi tare da fad'in,
"Tinanin me kike yi haka ?"
Cike da shagwab'a ta kwanta a jikin shi ta ce,
"Ba komai, ina tinanin ka ne kawai"
Ta qarasa maganar ta tana wani karairaya tare da qarasa haye cinyar shi,
" karki damu ai gani kome kk so naki ne, nema kawai zaki a baki baby"
Dariya ta yi tana shafa jikin shi tana limshe ido, sannan ta kashe murya ta furta,
"Da gaske Alhaji na?"
Da gaske mana tambayi ki ga aiki da cikawa"
"Hmmm ni dama dubu dari biyu kawai nake so zan je na dan siyo kayan sawa na gida, dan na ga ba a kawon kayana nan ba, kace a bari inna zo gidan ka akwai amma ka hana ni shiga dakuna ukun can, sannan kuma in da nake ba wasu kayan kirki na saka wa"
' Yarinya wannan lokacin nake jira da zaki nemi wani abu a wajena'
A zahiri Kuma sai ya ce,
"Sorry my love ki yi haƙuri,maza shirya muje na kaiki ki siyo kayan da duk ki ke buqata, menene wani dubu ɗari biyu kuma? Ai ba abinda ba zan kashe maki ba in dai ina da shi"
Da sauri ta sauka tana murna ta saka kaya ta dauki jakar da tazo da ita ta fito ta na jiran su tafi shopping,tsaf ta ganshi a tsaye Shima ya fito yana mata wani irin shegen murmushi, fita suka yi suka dauki hanya, suna ta tafiya, sai ta ga suna barin gari suna ta wuce shaguna da super markets, kasa jurewa ta yi cikin kissa ta ce,
"Ina zamu ne haka sweety?"
Idanun sa na saman hanya ya furta,
"Wani waje zan kai ki na musamman in kk ga wajen zaki ji daɗi sosai"
"Wooow Sweety u ar so romantic , i love u"
"I love u more dear"
kiss ya yi wa hannun ta, a haka yana tuqi ta yi bacci, bata bude ido ba sai a wani qauyen da bata san ina bane, wani gidan qasa ne mai girman gaske, ko ta ina mata da yara qauyawa ne a ciki sai wasu dattijai a gefen wata bishiya, sina cin wani tuwo baqi miyar koriya sharrr da ita, da sauri ta miqe ta fara murza ido, a zaton ta mafarki take yi,cikin tsananin razana ta furta,
"Babe ina ne nan? Me muke yi anan? Ko mafarki nake yi ne?"
" Hhhhhhhh ba mafarki ki ke yi ba Salame, nan shine ya dace da ke, kuma nan ne gidan ki, na asali, can gidan gidan oga na ne daya karban auren ki, anyway sun yi tafiya shine na kai ku mu ci amarcin mu, karki damu bangaren ki yafi na dika gidan kyau, da taimakon ogana, harda TV an sa maki, tin da ko gidan uwale da ubale ai babu su ko?"
Ya faɗa yana wani shu'umin murmushi, ita ko ta dad'e da fara kuka harda majina, kuka take tana bashi hakuri ya maida ita wa Goggon ta ita ta fasa auren nashi in dai a nan zai ajiye ta, wanka mata mari ya yi mai lafiya sannan cikin fushi ya ce,
" Dan uwar ki mai kwadayin nan an gaya maki wawa ne ni? Na kashe maki yan kudaden nawa kice na maida ki gida, ai ke da gida sai kin haifi biyar a qalla, sai dangin ki sun manta dake , ba dai Abuja kk so ba, to ai nan ma Abuja ce, dan haka baki da damuwa,inna fita ki tabbatar kin biyo ni in ba haka ba a gaban su zan fara ballaki, danni ba sabon abu bane wajena dukan mace"
D'aga kai ta yi ta na kallon shi cike da tsoro da mamaki,dan yanzu wani irin tsoron shi take ji ba kadan ba, hankailin ta kuwa idan ya yi dubu to ya tafi yawo, musamman da ta shiga ta ga daki daya ne dakin nata da wata yar TV da kayan kallo, sai gado qarami da kujeru biyu, da yan kwanika da ledar tsakar d'aki, kai abun dai kamar wata mara gata, haka ta shiga tana kuka kamar ta suma take ji dan baqin cikin da ke ran ta, biyo ta ya yi yace ta biyo shi d'aki mai kallon nata, amsawa ta yi ta bishi kamar raquma, wani d'aki ta shiga mai cike da tarkace da tsohon gado, sai wata uwar datti da aka tara a gefe na kayan wanki, ga poo din kashin yaro ba a zubar ba qazanta dai ta qarshen qarni kawai, wasu yammata ne a gefe an ci mai an yi fari ta fuska an d'ashe har fuskar ta yi wani kampala kampala, ba kyaun gani, sun sha bra ta dame su anyi daurin qirji da yan wayoyi a hannun su, manyan 'ya'yan Alhaji Talle ne, a qauyen nasu duk da Talle aka san shi, ko kuma a ce masa Tallen marka wato matar shi uwar 'ya'yan shi manyan kenan.
Markan ce ta fito daga kicin kamar wata baqar mahaukaciya, futu2 da ita tana goge hanci da bakin zanin ta, ido ya yi mata jawur, da dukkan alamu girki take yi dan kuwa jikin ta sai qauri hayaqi da warin hammata ke tashi, cikin d'aga murya Talle ya ce,
"Dalla malama ki yi sauri yau zan koma ni"
Shiga d'akin ta yi tana bin salma da wani irin mugun kallo,cikin neman qarin bayani ta ce wa Talle,
"Wannan fa Talle?"
"Qanwar ki ce, dama na zo ne na kawo ta zan koma, ki kula da ita in ta bar gidannan kashe ku zan da ke da asararrun yaran ki, kun dai san hali na ai"
Ya na gama maganar shi ya liqe ya sa kai zai fita, Marka ta kama qugu cikin masifa ta ce,
"To ina zaka rabon ka fa da nan wata uku kenan, sannan yau kazo ko kwana ba zaka yi ba zaka wuce"
"Jarababbiya muje na maki ko sau daya ne ba dai jarabar ki in ta motsa har a gaban 'ya'yan ki sai kin nema ba"
Cikin rashin kunya ta furta,
"Eh ɗin na ji muje"
A gaba ta sa shi suka koma d'akin yaran na dariya suna tafawa, ita ko salma qafafun ta ta ja ta yi d'akin da yake nata a yanzu,gado ta faɗa tana kuka mai ban tausayi, ga mijin da take so can da wata qazama yana mu'amalar aure da ita duk suna jiyo wa, ga talaucin da ta hango tsabar shi a gidannan, yau ina zata saka kant ? Kuka take sosai ta ji an banko qofar d'akin nata da ta saya , cikin masifa ta ga wata matashiyar yarinya ta tsaya a kan ta tana fad'in,
" Malama ki je ki qarasa mana abincin tin da baba ya qule daka da marka, yunwa muke ji , dan yanzu kan su fito sai an gan su"
sShewa yaran suka yi suka tafa tare da fad'in ,
"Hahaiiiiiiiiiiii casssssssss "
Miqewa Salma ta yi ido ya yi mata jawur saboda kuka tace,
"Ni na saka uwar taku shigewa d'aki da uban naku da zaku nuna min ku fitsarraru ne?"
"Ni ki ke mayar wa da magana? Yau zamu daga maki qafa ko dan darajar Baba na gari, amma ki kiyaye mu, mu nan da ki ka ganmu zane matan baba muke yi, ki tambaya kiji, sakarai kawai, kema ba zai wuce tarkon baba kika faɗa ba ai kwadayi mabudin wahala ne dama ai,"
Dariya suka saka suka sake tafawa, wata ce a cikin su da bazata wuce shekara 14 ba ta shigo ɗauke da bokiti akan ta na markaden koko, kallon su ta yi ta kauda kai ,
" ke jummala je ki qarasa abinci marka bata kusa,"
" ku me kuke yi tin dazu baku je ba? Ba in da zani sakarkaru kawai"
wucewa zata yi Huwaila ta janyo ta ta kwada mata mari, kuka ta saka tana fad'in,
" Allah ba zan ba mugaye kawai sai dai ku kashe ni, baku da aiki sai dai kuci ku yi wanka in su yaya Baban gida sun zo su yi ta lalibe ku da sunan wasan abokan wasa kuke yi, ko ji kuke ban sani ba ne?"
Shiru suka yi suka sake ta suka kama hanyar shiga madafin nasu, kuka taci gaba da yi, daga baya kuma a hankali ta yi shiru ta daga kai tana kallon Salma, cikin washe baki ta ce,
" laaaaa kece amaryar Baba da za a kawo dama?"
Daga mata kai Salma ta yi ta shige d'akin ta, shigar ta ke da wuya Talle ya fito daga dakin Marka............. [18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼 ' YAN ABUJA 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAEH