Y'AN ABUJA

Page 6

by @1239900

Talle ne ya qarasa fitowa Yana gyara wandon shi, rigar shi kuwa na yafe a kafadar shi, d'aurin qirjin gado ne a jikin Marka lokacin da ta fito daga d'akin nata ta na wata miqa , bakinnan na ta na ta fidda wani wari kamar an bude shaddar gidan haya, hammatar ta har wani kore2 brown2 take, qafar nan fururu da ita kan ya danqare, ba a qanin tsagar kitson ma, kuma gashi ita mace ce mai cika da tsahon gashi amma ba gyara ,yawu ne cike a bakin Talle na kyankyamin Marka ya je ya zubar yana masifa.

" ke ba a binda ki ka iya sai aukin son a kwanta da ke, in ba ai maki yanda ki ke so ba ki tara wa mutane jama'a ba ki kunyar Idon kowa,a dai biya maki buqata kawai,gaki nan ne kawai baki san ya ake gyara ba sannan in na nema a wani wajen ki fi kowa kishi da nuna jin zafi, to bari ki ji ba zai yu ba, ko ki canja hali ko wannan karon inna tafi sai na yi wata shida ban dawo ba"

" ka yi hakuri Talle amma dai kasan ba laifi na bane ko, kana ganin baka bar mana komai ka ke tsallake mu ka yi tafiyar ka, ni ke wa kai na komai a gidannan ba mai taimaka mana,a hakan dai nake samun abinda nake yi wa nawa yaran da na haifa da ciki na,sannan ga wadannan shegun 'ya'yan da iyayen su ba sa nan, duk a kaina, yaushe nake da lokacin gyara? Kawai hakuri za kai, in ka gyara kaga gyara, in baka gyara ba ka ga dan gundun uban qazanta a gidan ka ah toh,ko 'yan iskan da ka ke bi ai kai ka ke kahye musu kuɗi suke yin gyaran ko kuma wasu 'yan iskan su kahye musu kuɗi su gyara ka tsinci dami akala"

Ta qarasa maganar ta tare da murguda baki ta wuce tana kada manyan duwaiwakan ta, tsaki Tallen ya yi sannan ya ce,

" Ga mace dai a nan har mace da mutum zai huta amma an kashe waje da qazanta Allah wadaran naka ya lalace jakin dawa ya ga na gida"

Zubda yawu ya qara yi har zai fita ya tina da salma, leqawa ya yi yaga tana kwance har lokacin sai kuka take, dakin ta ya tura qofa ya shiga sannan ya hau gadon ya sa hannu ya d'ago ta, saka ta ya yi a cinyar shi da niyyar ya lallashe ta, nan take wani irin wari ya kai wa hancin ta ziyara, yunqurin  amai ne ya taso mata, da gudu ta fita waje ta hau kakarin amai amma kuma ta kasa aman ga wahala duk ta ishe ta saboda yunquri, kuka ta fashe da shi na takaici, cikin ɓacin rai Talle ya biyo ta ya tsaya a kan ta babu ko digon tausayawa a tattare da shi ya ce,

" Ke dan uwar ku mai shegen kwadayin tsiya ni zaki wa iskanci? Ni zaki fito kina toshewa hanci kina qoqarin haras wa? Yau zaki ci uban ki kan na tafi kuwa"

Janta ya yi da qarfi ya yi d'akin nata da ita yaran nashi manyan suna labe suna jiyo kukan ta, ya wurga ta gado ya cire kaya ya hau kusantar ta da dattin jikin shi da warin da najasar da ya gama saduwa da Marka,Salma kuwa da ta ji azaba kuka take tana kakarin amai amma saboda yunwa ba komai a cikin ta sai aman ya qi fitowa banda wahala babu abinda take kwasa, cikin kuka da nunfashin wahala ta ke fad'in,

"Ni ka daga ni kaje kai wanka kasan ba zan qi ka ba, wannan warin zai kashe ni in baka tashi ba,nimfashina kamar zai dauke haka nake ji "

Mari ya sakar mata ya ci gaba yana cewa,

" kema sai kin shaqa dan uwar ki niba a haka aka sani na yi har sau biyu ba ban tsinci komai ba? Dan haka dole na sauke akanki dan inna tafi ban san randa zaku ganni ba"

A haka ya gama abinda zai ya tashi gajiya fal jikin shi, ba wankan tsarki balle na daud'ar daya kwasa haka ya fice ya sa kai ya yi cikin garin Abuja,inda ya tafi ya Salma a nan kamar matacciya, ita kuma Marka ana can gabam murhu anyi goho ana hura wuta, Itan ma ko wanka bata damu da ta je ta yi ba, gaba daya murna ce fal cikin ta, yau Talle ya biya ta bashin da take bin shi, hankalin ta kwance take ayyukan ta dan kuwa ta sani talle ba qaramin gwarzon maza bane, ya qi tsayawa ne kawai ya kula da ita da iyalin shi dika, ga girma na kama su, dan shi zai yi shekara 47, ita kuma zata yi 38,  lokaci ne da ya kamata su zauna su mori rayuwar su kafin tsufa ya rufe su,amma inaaa kowa da nashi matsalar, tin asali ita ta bazama shi neman mata saboda muguwar qazantar ta da rashin sanin ya kamatan ta, shine sanadin kwadayin matan waje da yake yi a Koda yaushe musamman in ya gansu fes da su a cikin gari, daya shigo dan ya sauke buqatar shi sai ya ganta duqun2n kamar jakka, ai kuwa nan take haushi zai kama shi ya ji kamar ya rufe ta da duka, a hankali ya fara da marin ta in ta cika masa ciki, sai duka ya biyo baya, a haka har halayen shi suka munana, lokacin da take son ya gyara lokacin shi kuma idon shi ya buɗe da matan waje, still ita kuma bata gyara ba, ita ba ma ta ganin wai laifin daga gare ta ne balle ma ta ɗauki matakin gyarawar,ga yaran su da suka lalace duk a sanadin muguwar tarbiyyar iyayen na su, tinda in suka tashi kusantar juna ba ruwan su da yaran za su ji ko baza su ji su ba,kawai zasu yi abun su kamar dabbobi su fito suna zagin juna ko yabon juna a gabam yaran, ta haka Huwaila babbar yar su ta fara miqawa Baban gida cousin din su jikin ta yana lalubewa, domin so take itama ta ji me Marka kewa ihu tana nuna jin daɗin ta akai, ana haka Badamasi shima ya ke jan Jummala su yi nasu, kafin kace me yara idon su ya buɗe, Haule ce kawai Allah ya sawa nutsuwa a yaran Talle kaf, dan ita har makaranta take zuwa, kuma mamar ta daban a gidan,bata san ta ba, shi kanshi bayace ga uwar ta bama, tinda ya saki uwar ta da za ta tafi ta ajiye masa Haulen ba ta sake juyowa ba, dan gani suke gidan shi ba abin son haɗa zuria bane ba sam qaddara da tsautsayi ne ya sa auren su ya qullu shi yasa ta yafe masa 'yar ta cire ta a ran ta ta qara gaba.

Kullum haka rayuwar gidan Talle take, gidan babban gida ne na gado tare yake da yayun da wato  iyayen su Badamasi da Baban gida, iyayen su sun rasu,  suma Su Badamasin Mahaifiyar su bata da rai sai mahaifin su, watan ta shida da rasuwa, sun rasu ita da jaririn ta da tazo haihuwa, dan haka daga su sai uban su da yaqi aure sai bin 'Ya'yan jama'a sa'annin su Jummala, gidan su Talle gida ne na marasa da'a da tarbiyya, ko kadan ba mai kwab'a a gidan balle ya tsawatar akan abinda ake aikata wa mara kyau.

Lokuta da dama Marka na leqawa dakin Yayan mijin ta su watse tare ba tare da kowa ya sani ba,sakamakon nesa da mijin na ta ke yi da su,idan ya tafi ya na jimawa bai waiwayi gida ba dan kuwa watarana idan ya sa kai ya yi gaba sai ya yi watanni shida zuwa bakwai bai dawo ba yana can cikin garin Abuja, wannan ta'asar da ake ta tafkawa a gidan gaba ɗaya yaran da manyan gidan duk basu sani ba,domin a fili nunawa suke yi su ko gaisuwa ma basa yi da junan su sun tsani juna, amma da dare yayi in wani na buqatar wani zasu qwanqwasa qofa a bude su shige su gama su fice ba wanda ya sani, wannan shine Gidan Tallesious.

**************************

A bangaren amarya Juwairere kuwa, suna shaqar amarcin su cikin jin daɗi so da amince wa juna tare da girmama junan su, rayuwar ta na yi mata daɗi matuqa dan kuwa ba ta da damuwa ko kaɗan ko kewar gida ta yi Jabeer na kore mata damuwa a gefe d'aya Kuma ga qawar ta kuma 'yar uwar ta Nafeesa itama ta na debe mata kewa sosai, tare  da taya ta aiki in Yah Jabeer ya fita kasuwa wajen saida jakunkunan shi.

A haka rayuwar su ke ci gaba yau da gobe ana cin daɗi saboda garar da aka kai ta da shi, amma bahaushe ya ce zara bata barin dami, sai ibtila'in talauci ya ziyarce su,kasuwa ta kulle sai ya fita Watarana ya gama wunin sa be fi a sai takalmi ɗaya ba ko ya dawo ma Watarana ba a sai komai ba, Juwaira kuwa bata taɓa nuna masa wani sauyi ba sai ma qara masa qwarin gwuiwa da take yi a kullum.

A cikin wannan yanayin da ake ciki ta fara fuskantar canji daga wajen Surukar ta wato Hansai wadda suke kira innarmu, bata nuna mata a fili sai dai a qasan qasa ta yanda ba mai sanin halin gallazawar da take yi wa Juwairiyyah, ga shegen habaici kamar wadda ke tare da kishiyar ta,ta na so ta fito fili ta nuna wa Juwairiyyah qiyayyar da take yi mata amma ta kasa saboda ba qaramin kwarjini Juwaira ke mata ba.

Ba komai ke jawo wa bawa kwarjini ba kaga yana da maqiya amma su rasa ya zasu yi da shi face tasbihi,zikiri , da yawaita hailala da istigfari, komai maqiyin ka zai yi maka sai dai ta bayan Idon ka ba dai ta gaban ka ba domin kuwa Allah zai kare ka ko abun ya same ka ka sani yana daga cikin jarabawar rayuwar ka shiyasa u can not escape it, iya hakurin ka iya lada da daukakar ka,sannan yana sa maqiyan ka su dinga shakkar ka, ga soyayyar Allah da mala'iku da bayin Allah managarta, mu riqe ambaton Allah a koda yaushe, kina tuqa tuwo ne, kina shara ne, kina tafiya ne, kina ma megida wanki ne ko guga, kina ma yara wanka ne, ko zaki sauke tukunya ne, ki yi bismillah, komai zaki ki sa ambaton Allah a ciki rayuwar ki zata zama abin so wajen kowa, sannan Allah zai so ki ya ambace ki a tsakanin mala'ikun shi.

Wannan dalilin ne yasa ta fito da dabarar yi mata zagon qasa wajen Yah Jabeer tunda ta kasa musguna mata gaba da gaba.

Wata rana Juwairiyyah ta fito daga d'akin ta dan ta yi abinci sai ta fara da share madafin ta ta gyara shi tsaf,sannan ta qara dauraye tukunyar ta , ta haɗa wutar murhu ta dora ruwan zafi,sai ta deb'o waken ta ta fara gyarawa, ta gama gyara waken kenan ta wanke ta zuba sai ta yanka albasa a ciki dan ya yi laushi da qamshi, dama tasan ba su da kayan miya man da za ta yi miyar  kan shi manage za ta yi da shi bashi da yawa, kuma da dikkan alamu in suka ci wannan na dare sai dai ai hakuri, ta kammala dafa waken kenan sai nufi d'akin ta dan dakko shinkafa ta rege sai shinkafa tace ɗauke ni a inda ki ka ajiye,duban duniya Juwairiyyah ta yi amma haka ta nemi shinkafa ta rasa.

Hankalin ta ya tashi sakamakon duba lokaci da ta yi ta ga lokacin dawowar Yah Jabeer da ya kusa, cikin tsananin damuwa ta zauna ta zabga tagumi tare da fad'in,

" Oh ni Juwairah yanzu in ya dawo me zan bashi, ya wuni kasuwa bai ci komai ba, sannan ya bada kuɗin cefane daidai gwargwadon ikon sa a masa girki, kawai sai ya dawo ince shinkafar ta b'ata?"

Tana tsaka da tunani da damuwa ne ta ji muryar Nafee na fad'in,

" kin kusa gama abincin ne ? Dan na fara jin yunwa , Innarmu ma na can tana neman abinci yunwa take ji sosai"

"Na shiga uku ni juwairah, kin ga Nafee anan na aje shinkafar daga kewayawa bayi kan na fito na rege na saka ban ganta ba, na neme ta sama ko wasa na rasa "

Cikin mamaki Nafeesah ta kalli Juwairiyyah ta ce,

"Baki ganta ba fa ki ka ce, to Ina zata ke ita ba qafa ba?"

kuka Juwairah ta fara ta koma daki ta yi tagumi ta rasa abin yi,ta na nan zaune dabara ta faɗo mata, tashi ta yi ta samu wannan waken ta rage masa ruwa sosai, ta samu dan man daya rage masu, da dan wani magi da take da guda uku, sai gishiri ta zuba a ciki ta qara albasa sosai, inda suke shuka alayyahu ta je ta yanko mai yawan gaske ta zauna ta cinke ta gyara ta wanke sosai ta zuba, nan da nan abinci ya haɗu murna ta dinga yi tana godewa Allah da wannan dabarar da ta yi, duk da qarancin shekaru irin nata amma hakan be sa ta tsaida tunanin ta waje ɗaya ba, sai ta faɗad'a tunanin ta ta yanda har sai da ta sama wa kan ta mafita, bayan ta gama ta zubawa kowa ta kai masu, ko da ta shiga d'akin Innarmu bata gan ta ba sai ta yi zaton ko ta na makewayi ne,kawai sai ta ajiye ta yi wa Nafee magana ta wuce sashen ta, kan ta fita daga sashe su Nafeen ne ta ji Innarmu da wani yaro tana ce masa,

"ka siyar shamusu nawa ya baka me shagon?"

Kasa kunne Juwairiyyah ta yi amma bta jin me yaron yace,sai ta sake jin muryar Innamu na fad'in,

" Amma dai bai kyauta ba gaskiya, a fa wajen shi Juwairah ta sai shinkafar amma shine ya rage har nera saba'in ɗan nema mai kan buta kawai sallamamme shi yasa shagon ya qi ci gaba gashi nan jiya iyau"

Kafin ta dawo Juwairiyyah ta bar wajen cike da mamakin da ya  cika mata ciki, dama Innamu ce ta dauke shinkafar? Me hakan yake nufi?dama Innarmu bata qaunar ta? Bata son zaman lafiyar da suke yi da Yah Jabeer?shin me yake faruwa ne? [18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼

WRITTEN BY HAERMEEBRAEH