Page 2
by @1239900
A hankali Sakeenaa ta fuskanci irin qiyayyar da 'yar uwar ta ke mata, ba qaramin baqin ciki ta yi da ta gano hakan ba,ta yi kuka sosai akan baqin ciki, ita dai ta san tana matuqar son yayar ta ta, bata son duk wani b'acin ranta, a baya ta zaci kawai haka halin ta yake yawan kushe abun wasu da son ta burge mutane, ta zaci kowa ma haka take masa, bata tab'a tunanin wai hassada take mata ba me qarfi haka.
Duk sanda Sakeenah zata kai mata ziyara kuwa sai ta debi abubuwa sosai ta kai mata, kama daga dangin abinci, sutura ,abin sha,da dai sauran su ta Kai ta na Mai nuna wa yayar tata abinda ta mallaka nata ne ba banbanci dik dan ta sa ta dena nuna mata qiyayya a zahiri, amma inaaa sam basa burge Rasheedah ita dai so take ta zama Sakeenah, Sakeenan ta koma ita, dan haka ta na kawo mata kayayyakin nan za ta mata tatas, ta yi mata rashin mutunci,Kuma ta karb'e tare da fad'in raba arne da makami ai ibada ne, kalmar nan na matuqar qona ran Sakeenah wato ma ita ce arniyar.
Abinda ya faru kenan a yau da Sakeenah ta kawowa 'yar uwar tata ziyara, domin a cewar ta Bata son zumuncin su ya lalace koma mene ne ita ce qarama dole ta bi yayar ta Dan sada zumunci.
Sanye ta ke da wani leshi Mai sauqin kud'i saboda gudun kar ta saka Mai tsada 'yar uwar ta ta ce ta je nuna mata azziqin tufafi, haka zalika takalmi da jakar da ta d'auka dik masu sauqin kud'i ne Wanda ta siya na musamman saboda zuwa wajen Rasheedah, Adnan ya Kai ta da Kan shi har qofar gidan ya ajiye ta, ya fitar mata da kayayyakin da zata Kai wa Rasheeda, kudi ya qara mata ya ce ta Kai wa Sakeenan, sannan ta gaishe su in ta gama ta kira shi ya Maida ta gida.
Dubu goma ne ya bata ya ce ta ja jari, sallamad su ka yi ya wuce, shigar ta ke da wuya ta tarar da Raheedah tana hura murhu zata dora abincin rana, aje maficin ta yi tana yatsina fuska ta ce,
" A'a kaga matan alhazawa matan da suka ci suka tada kai,ku ne a tafe cikin rana haka?"
Murmushi Sakeenaa ta yi sannan ta shige parlour dan ta san sarai magana ta fad mata, zama ta yi tare da cire hijab din ta da niqab, sallama Rasheedah tayi ciki ciki ta shiga, tare da dage labulen sakamakon duhun da wajen ke da shi in ba wuta, gaishe da ita Sakeena ta yi cike da farin ciki tace,
" Rasheedah ga Apple na kawo maki dan na kula mun samu dan baba, na san zaki so shi Allah ya raba ku lafiya ya bada mai albarka," tana maganar ta na bud'e ledar da ta sako fruits ciki.
Dan gajeran tsaki Rasheedah ta ja sannan ta ce,
"Hmmm dake an fada maki talaucin namu ya kai yanda in nayi sha'awar ta ba za a siyo min ba ko,"
Sakeena ta hadiye rashin Jin dad'in Kalaman yayar ta se ta yi dariya ta ce,
"Niii ina na isa na fara wannan tinanin ma, kawai dai tawa gudummawar na kawo dan dana ko 'yata su fara cin abun auntyn su, amma ai Yayah Auwal na iya qoqarin shi,"
Kauda kai ta yi ta yatsina fuska, talaucin Auwal ba qaramin damun ta yake ba,
"Ke dalla can wane qoqari ya iya banda qoqarin yi min ciki ba kayan da zasu qara min kuzari, kullum cikin wahala, duba fa ki gani kamar ni ace ina hura murhu, gaba d'aya na yi baqi, haskena ya dishe, kamata ya yi ace yanda nake da cikin nan na qara haske da kyau amma jibi yanda na qare na lalace,"
Cikin kuwa zuba mata Ido kawai ta yi ta na kallon ta,rashin godiyar yayar ta ta ta kullum da alama gaba yake ba baya ba, bud'e baki tayi dan ta mata nasiha amma sai ta dakatar da ita ta miqe ta ce ta na zuwa,kayan miyan da ya kawo ta dakko ta baje a qasa ta hau ware wa, ledar nama ta aje a gefe ta gyara ta dora tafashen nama, sannan ta yi jajjage, ta soya kayan miyan ,ta tsaida ruwan dafa dikan taliya, sannan ta dakko tafasasshen naman ta zuba ta saka maggi da dan kayan qamshi ta rufe sannan ta dawo, duk abinda take a kan idon qanwar ta ta,
"Uhumm ina jin ki,"
"Abinda nake son fada maki Rasheedah shine ki godewa Allah, akan abinda ya baki, ki fa diba ki gani taliya zaki dafa, sannan ki gani ba zallan ta bane haka nan har da naman miya, da damar mutane suna cikin matsalar rashin abin da zasu ci, amma ke kin samu kina kai qarar Allah akan bai baki ba wajen bayin shi, in a rayuwa kk ce ba zaki duba na qasa dake ki godewa Allah ba, to kuwa in kina kallon na saman ki sai dai ki butulcewa Allah, kuma Rash......."
"Ke dakata in wa'azi zaki min riqe abun ki, ba zan qara fada maki damuwa ta ba, akan wane dalili zaki saka ni gaba ki ta faman min wa'azin da kk san na dauka zan ba, meye aibun abinda nace? Bayan komai na fada gaskiya ne, ko dan ke kinga Allah ya baki shine ni dan na fadi halin danake ciki ya zama laifi?"
Sakeenah hadiye bacin ranta ta yi dan tabbas yanda tai mata maganganun cikin daga murya da tsantsar rashin mutunci da wata ce sai ta mayar mata ba dad'i, amma sai ta miqe ta dauki hijabin ta da niqabin ta ta dakko dubu goman ta aje mata akan kayan ta tace mata,
" Allah ya baki akuri ba niyyata na zo na bata ranki ba, gaishe ki na zo yi tinda na gaida ki zan wuce, Allah ya raba ku lfy, ya qara arziqi,"
Cikin halin rashin kulawa tace,
"Tafiya zaki bazaki ci abincin talakawa ba ko, hhhh ai na sani , ki gaida gida , sai munzo cin arziqi gidan masu da shi,"
Bata ce mata komai ba ta fita,a soron gidan ta hango motar shi, yana mata murmushi, take ta ji baqin cikin ta ya ragu, qarasawa ta yi tana masa murmushi dik da niqabin dake fuskar ta bai gaza gane me take mai ba, amma a hakan sai da ya gano zuciyar ta ba dadi a lokacin da ta shiga motar, saurin d'auke niqab din ya yi yace
"Me ta maki yau kuma, na kula kullum kk zo gidannan sai ta bata maki rai ke kuma baki son fad'a min, a gaskiya zaki daina zuwa in haka ne, ita ta dinga neman ki ba shikenan ba,"
"Sam ba za ai haka ba, in banje wajen yayata ba wajen wa zani? Kuma ni ban ce maka ta min wani abu ba ai ko? Ina son yayata ina qaunar ta, kome zata min yayata ce , komai zatai man ba zai taba canja wani abu daga son da nake mata ba,"
Ta qarasa muryar ta na rawa, idon ta taf kwallah,bata son ta kuma cewa komai sai ta jingina kanta a kujera bayan ta maida niqab din ta, jan motar ya yi yana hararar gidan Rasheedan, daidai lokacin da mijin ta ya ke qoqarin shiga gidan, ya na shiga kuwa ta miqe ta karb'e ledar hannun shi ta ce,
"Meye wannan a ledar?"
Miqa mata ya yi ya koma ya zauna a gajiye, aikin gini yake, gaba d'aya ya gaji, tsaki ta ja sosai sannan ta kalle shi,
"Yanzu Auwal meye wannan tsakani da Allah? Ya zaka kawon wani zogale sai kace tsohuwa? Ga abubuwan kwadayi da qarin jini nan da masu ciki ke ci amma ni ka ban wannan?"
Cike da takaici ya kalle ta, se kawai ya mata shiru dan in ya biye mata sai ya faffalla mata maruka, miqewa ya yi ya kewaye ta ya fita tsakar gida dan wanke hannu da qafa, sanin halin shi ne yasa tayi gum da bakin ta da ta ga ya miqe, se da ya fita ta dauki zogalen ta na mita ta kwadanta yawun ta har zuba yake ta yi maza ta goge da bayan hannun ta,ta zauna zata ci kenan ya fito, dariya ya barke da ita,sannann ya yi maza ya karb'e kwanon daidai lokacin da zata zira hannu dan diba ya kama hannun nata da qarfi ya sid'e , cikin kuka ta fizge hannun ta shi kuma ya shige d'aki da shi ya rufe qofar, ihu ta saka tana kiran ya bata ta ci amma ya qi ya na ta dariya ya ce
"Ba zan bayar ba ai ina kallon ki, jira dama nake ki gama had'a min tinda ke ba so kk ba, kin raina abinda na baki saboda kin fi qarfin shi ko? To ni da ban fi qarfin shi ba bari na ci abuna"
Cikin kuka take masa magiya shi kuwa ya yi kamar be ji ba, se kwasar zogalen ya ke ya na kaiwa baki, tare da lumshe idanun shi, hannun da ya sid'e ta kalla ta ga akwai saura se ta hau sid'e hannun nata,Wani irin dad'i ne ya gauraye mata baki har tsakiyar kan ta ta ji shi.
" Auwal kai min rai ka bani na ci, cikinnan zai iya zubewa in ban ci abinnan ba,"
"Wa ya yi cikin da izinin Allah? Ba dai Allah ni ya bawa ikon dura abubuwan da cikin ya samu ba? Kar ki damu ya zube na qara maki wani,"
kuka ta zube a wajen tana yi,dan tabbas ta san ba zai tab'a bata ba, sai da ya gama tass d'an burbudin kwanon ya dangwara a gaban ta ya yi wajen taliyar da ta dahu har ta dan fara qauri, saukewa ya yi ya d'iba ya dawo parlorn ya na ci , kallon shi ta yi cike da harara da tsiwa, ranta na suya dan ba qaramin b'ata ranta ya yi ba daya cinye,
" Allah sai ya saka min Mugu azzalumi kawai tinda ai ka san sarai ina da buqatar irin wadannan abubuwan a jiki na tin da ciki gar..,"
Kan ta rufe baki ta ji ya bige mata baki da bayan hannun shi, nan take kuwa ta buga ihu ta Kai hannun ta baki se ga jini, qara rikicewa ta yi da kuka, shi Kuma ya miqe ya na nuna ta da yatsa ya ce,
"Ni kk zagi ki ke had'awa da Allah?dan ma kin samu ina maki qoqari ko? za ki ga iskanci kuwa ganin idon ki mun d'aura daga yau, tin da qoqarin da nake a ban da shi kin raina muje zuwa da Auwal kk magana,"
Wajen tukunyar ya nufa ya kwashe sauran naman tass ya wuce uwar d'aki ya zauna ya sa gaba yana ci, wani yunquri ta yi da sauri dan ta je ta ci itama,Wani mugun kallo ya wurga mata se da hanjin ta ya kada, qunquni take ta na ja masa Allah ya Isa kamar wata qaramar yarinya,Auwal na ganin haka ya janye kwanon zai miqe ta kwasa waje da gudu,
"Da ki tsaya mana qaramar mara kunya, kwatakwata baki da hankali baki San me duniya take ciki ba, zan koya maki zaman duniya ne, shashasha kawai"
A tsakar gida ta ja ta tsaya, can Kuma ta qarasa ta ja tukunyar taliyar ta hau cin abinci tana kuka, ko gamawa bata yi ba ta tuna da abubuwan da Sakeenah ta Kai mata, da sauri ta nufi parlour ta dauki ledojin ta hau bubbud'ewa,da soyayyan nama ta fara yin karo se fruits da fresh milk,sannan kud'in da ta aje mata, d'aya ledar Kuma rigar bacci ce da turare da man shafawa se d'ankunne, kyabe baki ta yi tace,
" Ko banza na mora, duk da ba haka na so ace wai qanwata ke min ba, ai kyanta ace ni ce zan dinga bata ta na karb'a ba wai ni ta dinga kawon ba"
Ci ta hau yi ba ko bismillah, ko me ta tina oho, se ta miqe ta shiga daki ta zauna gaban Auwal tana ci tana waqe2n habaici, ko kula ta bai ba, dan ya san wa ya kawo, shi a nashi b'angaren dik da yasan ya mata qarya wajen auro ta, amma yana tsananin son ta, sannan in ta bishi a sannu zasu zauna lfy, kuma iya qoqarin shi zai mata duk abinda ya sawwaqa tinda harkar gini watarana a samu me yawa ne watarana kad'an amma ita inaaa bata San wannan ba, sai da suka yi aure duk wasu halayen ta da bai ma san ta da shi ba musamman na tsanar qanwar ta da duk wani wanda ya fita qumbar susa suka fito masa fili se ya dauki hakan a matsayin Allah ne ya tura shi wajen ta dan ya yi maganin ta, halayen munana bai rage masa son ta ba sam, sai ma qaruwa da yake, dan ko ba komai yana morar ta ta wani wajen.
***************************
Cikin dare Sakeenah ta miqe tana safa da marwa a d'aki, juyi Adnan ya yi se ya ji bata jikin shi,idon shi ya bud'e kad'an da magagin bacci ya kalli gefe ya ga ko ta mirgina gefe ne ya jawo ta jikin shi se ya ga bata nan, sun riga sun Saba wa junan su kwana a manne da juna,rashin ganin ta a gadon ne ya bashi damar bud'e ido sosai a tsaye ya gan ta tana safa da marwa, cikin damuwa ya sauke qafafun shi tare da zira takalmin shi ya riqe kafad'ar ta ya ce,
" My love lafiya ki ke kuwa? Me ya same ki, ko na maki wani abu ne da ya b'ata ran ki ban sani ba?"
Da sauri ta fada jikin shi tana kuka sosai,
"Mine abun nan na damuna sosai, ka duba ka ga qawayena da akai auren su bayan namu duk da ciki, Rasheedah da aka mana aure rana d'aya ciki ne da ita ba wai baqin ciki nake ba ko Wani abu makamancin haka ka fahimce ni kawai nima na so ace Ina da shi amma shiru har yanzu,"
Ta qarasa maganar cikin matsanancin kuka, sake baki ya yi da farko yana kallon ta, sannan daga baya ya yi murmushi ya kamo ta ya dora kan cinyar shi,
"Habaa my love, yanzu ina ilimin ki ya tafi, ki dinga zance irin na Wanda suka manta Allah na yin yanda ya so a lokacin da ya so Kuma akan Wanda ya so? Habaa gaskiya ban ji dad'in Jin haka daga gare ki ba, ke da na sani ki na da tawakkali da aiki da ilimin ki na addinin da na boko ma, Ina hankalin ki ya tafi ?habaa kar kina saka wannan a ran ki, Kuma dai na ga ni ban ma gama cin amarci na ba"
Ya na fad'a yana sunsunar wuyan ta, yana shafa bayan ta, sannan ya yi amfani da d'ayan hannun shi yana qoqarin janye mata rigar dake jikin ta, itama cikin zaquwa da abinda mijin nata yake mata ta juya ta bashi hankalin ta dika, wasanni suke kamar zasu cinye juna, ina ganin haka nace tooooo Haermee an zo wajen manya fece🏃🏻♀🏃🏻♀🏃🏻♀
[5/16, 2:42 PM] HAERMEEBRAERH❤️: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*****
*****