Page 4
by @1239900
Da sauri ta girgiza Kan ta, tare da tashi ta zauna da kyau a fili ta ke fad'in,
" kaiii inaa da kunya na je ina cewa Mama ta nema min magani na haihu, kaii ba zan iya ba ma, to ya zata kalle ni ma? Ai se ta ce bani da kunya ma"
Tana nan zune har qarfe hudu na rana ta buga ga kiraye kirayen sallar la'asar nan dik ya karad'e ko Ina, gani ta yi zaman ba zai yi mata maganin komai ba ga lokacin sallah ya yi kawai se ta fad'a bathroom ta dauro alwala ta fito ta zira doguwar riga da hijabi ta tada sallah, ta dade tana addu'ar neman gafarar Allah, da yiwa mijin ta da iyayen ta addu'a sannan taiwa dikkan musulmi addu'a kafin ta yi wa kan ta ta neman haihuwa me albarka ta dad'e sosai cikin sujjadar ta ta na maimaita addu'ar ta, sannan ta d'ago tai tahiya ta yi sallama, tana idarwa ta faɗa kitchen ta haɗa masu abinci dan qarfe shida Adnan ke dawowa, tana girki tana qara gyara gidan, ta je toilet din shi ta qara wankewa, ta fidda masa kayan da zai saka in ya dawo, sannan ta fito,bayan ta kammala girkin ne da gyare gyaren ta koma d'akin ta ta cire kayan ta ta d'aura towel ta shige bathroom dan yin wanka, had'a ruwan wankan ta yi cikin kwamin wanka ta zuba dik wasu abubuwa da take amfani da su wajen wanka, ta d'aga qafarta kenan zata shiga ta ji motsi alamar Adnan ya dawo kenan,Murmushi ta yi na farin cikin dawowar mijin nata ta qarasa shiga, kafin ta zauna ya bud'e qofar ya shiga, da sauri ta zauna ta na dariya, dan Sakeenah mace ce Mai kunya,har yanzu bata Iya bari Adnan ya gan ta ba kaya, se dai ta na saka qananan kayan da za a ce da su da babu dik d'aya ne, to ta fi son haka akan ta zauna ya gan ta ba komai a jikin ta, Murmushi ya yi Shima ya qarasa shiga bathroom din ya hau cire riga, se ni Kuma Hamidatuwa na jaaawo musu gambu na koma Ina jiran su a parlour.
Ina zaune na ji dariyar su tare da maganar Sakeenah ta na fad'in,
" Zaka fara ko? ko wanne kyau na yi a hakan, bayan ka dawo da wuri, ni da na so se na tsara kwalliya irin ta 'yan gayu se ka dawo"
"Tabb ashe kin shirya sumar da bawan Allah marayan Allah se Kuma Allah ya dube ni ya dawo da ni akan Kari, Sakeenah ni Adnan zan iya rantsuwa da Allah ban tab'a ganin macen da ta min kyau Kuma take min kyau a kowanne yanayi take ba sama da ke, ko kin yi wanka, ko baki wanka ba ke Mai kyau ce, ki dinga godewa Allah domin kuwa se a tara mata dubu kafin a samu irin ki goma"
Idan Adnan na kod'a kyan ta se ta dinga Jin ta kamar ta fi kowacce mace a dik duniya kyau da kyakkyawan hali, saboda ba ya barin wata kafa ta jikin ta ko ta halayyar ta ba tare da ya yaba ba,
" hmmm na gode" shine kawai abinda ta Iya furtawa ta na Wani tsadadden murmushin da ta San ya na sake rikita shi, su na cin abinci a saman dinning ma Adnan be shiru ba, ci gaba ya yi da ziga ta da yaba dad'in girkin da had'uwar shi,
"Mine ka dena sa wa Ina Jin kaina kamar zai fashe dan girma, wannan irin yabo haka? Ai dik yanda na zama a gidannan Kai ma ka na da babban kaso a Kan hakan, saboda mace na zama ta kirki ne a wasu lokutan gwargwadon irin adalci da kulawar mijin ta a gare ta, kenan ka ga Kai ya fi cancanta a yi wa yabon da ka ke min"
"Ba Zaki gane matsayin da ki ke da shi a zuciya ta ba ne, ke dai Allah ya qara min lafiya da arziqi na ci gaba da Baki kulawa kamar sarauniya "
"Ameeen, Ina son ka mijin Sakeenah,"
"Ina son ki matar Adnan"
Murmushi ta yi kafin su miqe Daga saman dinning din su yi masauki a kujera Mai cin mutum biyu, kunna TV ya yi ya Kai NTA, kwantawa ta yi a jikin shi ta na shafa qirjin shi sannan ta ce,
"Yauwaa my love dan Allah bana muje hajji mana, kaga sai mu samu mu yi ibada kuma mu yi addu'ar da muke da buqata akai ko"
Lakace hancin ta ya yi sannan ya sumbaci tsinin hancin nata ya ce,
" kamar kin karanci zuciya ta,anya baki min leqen asiri a zuciya ta ba?wannan na cikin tsari na a shekarar nan inshaa Allahu zamu koma hajji ni, ke, Abba da Mama ma duk zamu da su, dan ba zamu tafi ba muje da iyayen mu ba ko,"
Wani irin dad'i ne ya kama ta ta miqe ta kwanta rubda ciki a kan shi, tana facing din shi tare da rungume shi sosai, shi Kuma sai dariya yake fitarwa a hankali ba abinda ke bashi farin ciki sama da ya ga Sakeenah na farin ciki a rayuwa, kallon shi ta ke cike da tsananin so da qaunar shi da suka ninku a zuciyar ta, d'an qaramin leben ta na qasa ta ciza a hankali cikin kashe murya da kashe Ido ta ce,
"Bani da bakin da zan Maka godiya mine sai dai na ce Allah ya jiqan iyayen mu da suka gabata ya kyautata makwancin su ya sa su yi alfahari da samun ka a matsayin d'a na gari Ameen"
"Dama ai ba godiya nake so ba, Dan nima iyaye na ne, addu'ar ki kawai nake buqata Dan kuwa addu'ar ki a gare ni haske ce, Kuma alkhairi ce, Dan tinda na had'u Dake alkhairai kala kala ke bibiyata wadannan addu'o'in naki na daga cikin abinda ke qara min ci gaba a rayuwa, kin ga kuwa ni ne ma zan maki godiya ko?"
Lips din shi ta kama da yatsan ta ta Dan ja, ta miqe ta gudu d'aki, da qarfi ya furta,
"Invitation aka bani in zo kenan? To Gani nan zuwa" da sauri ya bi ta d'akin suka rufe qofar abin su, Bai fito ba sai da aka kira magariba, ya wuce masallaci.
Sallah ta gabatar da azkar ta sake gyara abubuwan da suka b'ata, ta Dan watsa ruwa ta saka rigar baccin ta Mai kyau, ga tirarukan da ta Sanya masu sanyin qamshi, sai ta Dora hijabin ta ta na jiran a yi isha'i, bayan ta idar da sallar isha'in ne ta shiga kitchen ta sama masu fruit salad da chicken and potatoes salad sai Dan abun sha da ta had'a na abarba qarfe tara na dare ya shigo, ya na hamma,
"Wai kin San ana idar da sallar isha'i kawai se bacci ya dauke ni, maqocin mu ne da zai tafi ya tashen shine muka taho"
"Ai dole bacci ya dauke ka, ka wuni aiki, ka dawo ban barka ka huta ba, I am sorry mine"
Kamo ta ya yi ya na Murmushi ya ce,
"Ni fa da na gan ki da qaton hijabi haka na San akwai wata harkar a qasa, zo nan in gani ba wata I am sorry,"
Guduwa ta yi suka hau zagaye kujerun Suna dariya, da kyar ya kama ta suka zube a kujera su na dariya,
"Dan Allah zo mu je mu ci abinci yunwa nake ji, na San kaima yunwa ka ke ji"
Da kyar ya barta suka jera ya na riqe da qugun ta, sai da ya fara ja mata kujera ta zauna sannan ya zauna Shima, ta zuba musu abinci suka fara ci.
Bayan sun kammala a tare suka gyara waje Wanda suka rage suka saka a fridge ya taya ta wanke kwanukan, suka kashe kayan kallo suka wuce d'aki, ni dai ban bi su ba dan lamarin su Adnan in kana binbini se ka ji kunya.
Bayan ya tafi aiki da safe ita Kuma da hantsi ta shirya ta ja motar ta ta yi gidan su ta sanar da iyayen su game da tafiyar da Adnan ya ce za su yi zuwa Hajji, ba qaramin murna suka yi ba, cikin tsananin farin ciki Mama ta sa waya ta kira Rasheedah ta Sanar da ita abin farin cikin da ya same su dan ta taya su murna,wayyo Allah, Rasheedah ji ta yi kamar ta mutu dan baqin cikin daya kama ta, tana kashe wayar ta hau kuka, Auwal ne ya riqe ta yana tambayar waya mutu cikin tashin hankali, banza ta yi da shi sai da tai kukan ya ishe ta sannan tace,
"Wannan banzar yarinyar ce zata makka,da su Mama, zan so ace ni na fara kai su, ba ita ba, amma dubi yanzu sabida auren talaka qanwar bayana ita zata kai iyayen mu makka,"
Ta qarasa cikin kuka, wani haushin ta ne ya kama shi kamar ya shaqe ta, ya na mamakin yanda bata Iya b'oye baqin ciki da hassadar ta har se ta yi kuka,anya Rasheedah ba 'yar tsuntuwa bace a gidan? Dan shi yanzu ba safai ya ke Jin haushin zagin da take masa na talauci ba, Cikin Jin haushin maganganun ta ya yi tsaki ya fice daga d'akin, d'aga kan ta ta yi ta kalle shi ta murguda baki tare da hararar shi, sannan ta ce
"Ni ba dan son da nake maka ba na rantse da tini na bar gidan ka na auri mai kudi, haba namiji ace yau ko atampa super ko Holland din nan ba ka tab'a siya ka ce na Kai gida ba, balle shadda me d'an maiqo, kamar Kai ka kawo talauci duniya"
Yousuf ne ya shigo yana kuka yayi kashi, wani haushi ne ya qara kamata kamar ta kama yaron ta yi ta duka, da mai kud'i ta aura yanzu ai da tana da masu aiki, ga Sakeenah nan masu aikin ta kusan biyar, wai a haka ma bata son masu girki, gyara parlourn ta guda uku da sauran dakuna kawai ake mata se kula da tsakar gidan da fulawowi da wankin su da sauran abubuwa, amma dik wata hidimar Adnan da kanta take yi,cikin fushi ta miqewa ta daka masa tsawa akan ya bar mata kuka kan ta doke shi, aiko qara b'are baki ya yi, tako kama shi da jibga,ba ta yi aune ba ta ji maruka masu lafiya ta kowanne gefen fuskar ta, ihu ta kurma ta hau bori,
"Dan iskanci kina nan kina shashanci da muguwar hassada yaro ya dakko po zai hau ya kasa cire wando har yayi a jiki shine zaki hau d'a da duka,ke wa ya dake ki a jakancin da kike wa mutane",( makaranta kuji fa har jaka mijin ta ke kiran ta sabida tana mai halayen su) kuka ta ke sosai, ga baqin cikin da ke cin ta in ta tina tafiyar su Sakeenah,ga duka taci a hannun miji,sannan ya sata gaba ta wanke kashin dole,ta na kuka take wanke masa ta shirya shi, ta koma ta kwanta, tinanin wannan tafiyar da zasu yi take ta yi anyaa zata bari a yi tafiyar nan kuwa?...........
*Readers barkan mu da safiya, anya Rasheedah na da head kuwa?*
[5/16, 2:43 PM] HAERMEEBRAERH❤️: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*****
*****