Page 7
by @1239900
Kafin washegarin ranar aman da ta yi ya fi uku, duk ta fita hayyacin ta, da asuba sallah kawai Adnan ya yi ya kwashe ta sai asibiti, suna zuwa aka hau duba ta, nan take suka gane zazzabi ne kawai ke damun ta, saboda damuwa da ta yi mata yawa, qara mata ruwa aka yi saboda ta samu kwarin jikin ta dan aman da ta yi ya galabaitar da ita, se aka had'a mata da magungunan da za su saukar da zazzabin, likita Kuma ya bata shawarwari na ta qoqarta ta yi avoiding duk Wani abu da zai sa ta shiga damuwa saboda kiyaye Kan ta daga kamuwa da cutar hawan jini, daga baya ya ce wa Adnan ya biyo shi office d'in shi ya na so ya yi magana da shi.
A tare suka shiga office din , Dr. Uwais ya zagaya ya zauna a kujerar shi sannan ya wa Adnan nuni da kujerar da ke gaban shi ya ce ya zauna, zama ya yi Suna fuskantar juna likita ya cire gilashin shi ya kalli Adnan ya ce,
"Alhaji Adnan a iya sanin da na Maka na San Kai me kula da lafiyar ka da ta iyalin ka ce, amma garin yaya ka bari wannan ciwo ke qoqarin kama matar ka? Ka sani fa matar ka na gab da kamuwa da hawan jini, binciken mu da Kuma tambayoyin da na mata ya nuna akwai matiqar damuwa a tattare da ita, wataqila akwai abinda kk mata na rashin jin dad'i ya sa hakan ke Shirin faruwa da ita, Wanda in haka ne zan yi matuqar mamaki, Iya sani na da Kai Kai mutum ne Mai kula da dik Wanda ke qarqashin shi ballantana matar da kowa ya shaida kana so Kuma kana kula da ita fiye da Kan ka na sani tsakanin miji da mata sai Allah, amma dai dan Allah ka duba kai qoqari ka gyara, ka dinga faranta mata kamar yanda ka saba, ka ci gaba da kula da amanar da Allah ya baka, in kuma ta wani wajen take samun damuwa ka qoqarta kaga ka toshe mata wannan kafar damuwar, gaba ake gudu,ina fatan ban yi maka katsalandam a harkokin iyalin ka ba,shawara ce a matsayi na na d'an uwan ka Kuma likitan iyalin ka,wadda Ina ganin in kabi a sannu zata samu sauqi da wuri Kuma za a gujewa wannan mugun ciwo na hawan jini,"
kad'a wa likitan kai Adnan ya yi cikin sauri da kuma gamsuwa da bayanan shi,
"Sam Uwais raina be b'aci ba,ta ya zaka bata min raina akan gaskiya? na ji dad'in shawarwarin ka ainun, amma ina mai sanar maka daga yau damuwar ta zata kau da yardar Allah,Kuma Ina so ka sani bana daga cikin silar damuwar ta amma na san musabbabin hakan Kuma zan d'au mataki akai, haba Kai ma ka San yanda nake son Sakeenaah ba zan cutar da ita ba, na gode Uwais in ka je gida ka gaida su Baffah bari na koma wajen ta,Ka wuni lfy"
Uwais cousin d'in Adnan ne, Baban Uwais Yaya ne ga mahaifin Adnan,anan asibitin suke ganin likita, Kuma suke zuwa medical check up.
Sallama suka yi da juna, ya wuce d'akin da aka ajiye ta,ya tarar da ita waje d'aya ta dafe kai,tana ta tinani kala2 bama ta san ya iso ba,
"Kin gani ba, yanzunnan aka maki maganar rage damuwa amma kin zo kin takura kan ki anan, haba Sakeenaah so kk ki kamu da ciwon da ni zai zame wa masifa da bala'i? Tinda sanin Kan ki ne dik halin qunci ko rashin lafiyar da ki ke ciki na fi ki shiga damuwa, in Kuma ba so ki ke ki rasa ni ba gaba d'aya Dan Allah ki Dena shiga damuwa"
Cikin hawaye ta gyada kai,
"To in dai baki son rasa ni ki daina damuwa, komai da ya faru ki d'auka bai faruba ba zan yafewa kaina ba idan wani abu ya same ki,?"
Dr. Uwais be sallame ta ba sai yamma,kafin a sallame tan Adnan be Sanar da kowa halin da suke ciki ba shi da masu aikin su ne sukai ta dawainiya da ita, kama Daga Kan abinci ne da Duk wata kulawa dai da take buqata har aka sallame su da la'asar.
Bayan sun dawo gida wanka ya mata da ruwa mai dumi sosai jikin ta ya gasu sosai, ta ji dad'in wankan, shima yayi, qananan kaya suka saka dan su sha iska daga nan se suka koma parlor,amfani ya yi da comb ya hau taje mata gashin ta suna ta hira ya na bata labarai na abun dariya, ita Kuma ta na ta sheqa dariya abunta kamar bata da wata sauran damuwa a duniya,da kanta ta sa band ta daure Kan nata ya dawo gaban ta ya kalle ta ya qara ya ga yanda ta yi kyau se qamshi take budawa,rungume ta ya yi ta na mishi dariyar yanda yake ta yabon kyan ta daga baya ya sake ta ya je ya kunna mata kallo ya sunkuya ya sumbaci goshin ta sannan ya wuce kitchen,bayan shi ta bi da kallo ta na yi masa addu'a a zuciyar ta,murmushin ta mai kyau dake bayyanar da hushiryar ta ta saki,ya na juyawa suka had'a Ido kuwa ,ya ji dad'in ganin wannan tsadadden murmushin nata, hakan na nuna masa ta fara warewa kenan, a qasan ranta tana qoqarin mantawa da komai, daga zancen haihuwar har abinda yayar ta ta ke mata,so take ta fifita farin cikin mijin ta da ita Kan ta akan kowa yanzu,yanda Adnan ya damu da halin da take ciki ya na bata tausayi sosai dan har 'yar rama ya yi a dare d'aya, tana wannan tinanin ya iso dauke da faranti babba a hannun shi, tarkacen kwalamar ta da ta Saba ci ya deb'o mata dan kawai ranta ya yi fari, dangin su Chocolate da biscuit ne da ice cream, sai Apple,shi dai kawai ya lodo komai da ya Kan ga ta na ci dan bai san me zai fi faranta mata ba a yanzun da bata da lafiya,aiko tana gani ta hau masa dariya, dan ta fuskanci gaba daya bai ma san me zai kawo mata ba,
"Ko kina son wani abu da ban saka ba ne a cikin nan? ko banana kk so, ko kina son juice ? Aikuwa kin ga na manta ban dakko ba bari na kawo miki,"
Miqewa ta yi ta amshi farantin ta aje a center table, ta je gare shi, d'afe shi ta yi kamar wata mage haka ta shige jikin shi, ya d'aga ta da kyau ita ko ta saqale qafafun ta a qugun shi,ta kwantar da fuskar ta a wuyan shi, a hankali, numfashin ta na dukan wuyan nashi, kama ta ya yi da kyau sannan ya samu waje ya musu masauki a kujera, a hankali ta ke masa rad'a a kunnen shi,
"Ina son ka mijina,ina qaunar ka, Allah ya faranta maka yanda kk faranta min, Allah ya jiqan iyayen ka ya sanya su a aljanna,Allah ya kyautata makwancin su, kafin a samu namiji kamar ka a wannan zamanin sai an sha wahala, KAI NE JARUMI na ni Sakeenah Allah ya barmu tare har abada, Allah ya bani iKon kyautata Maka sama da ya da ka ke kyautata min"
Wani irin dad'i addu'o'in ta ke masa tare da narkar da zuciyar shi a kogin qaunar ta da girmama ta,lumshe Ido kawai yake ya na bin ta da kallon qauna,Sakeenah na kashe masa gab'ob'in jiki da addu'ar da take wa iyayen shi iyayen shi shi kad'ai suka haifa amma samuwar Sakeenah a rayuwar shi ya sa Yana Jin kamar su biyu suka bari a duniya, bata gajiya da yi musu addu'o'i a kowacce Rana ta duniya ko Mai ya mata in ta ji dad'i sai ta musu kyakkyawar addu'a,ya tallabo fuskar ta ya dago ta sosai suka fuskanci juna,magana yake son yi ya kasa furta komai, ji ya yi ta ce masa
"Dauke ni mu je d'aki miji na"
Murmushi ya saki ya manna fuskar shi a jikin ta, ba musu Adnan ya sungume ta sukai d'aka abun su Suna dariya, tin a hanya ta fara gigita shi, dana ga haka nace tabbas ba wani rahoto daidai ni bari na cinye kwalamar ta ta☹
(To jama'atul musulmi Dan mace na period ba shi zai hana ta shiga aza room da mijin ta ba, saduwa ce take haramun, dik abinda za su yi da be sab'awa Allah ba suna Iya abun su Dan faranta ran junan su)
***************************
Rasheedah ce ke ta sharar baccin ta tin daren jiyan bata farka ba balle ta yi wankan tsarki ta yi sallah, ko kuka yaron ta ya yi Auwal ke Kara shi jikin Nono ya sha ya koma bacci se kace wadda tai aikin qarfi,ta na nan kwance har sai da Yousuf ya tada ta ya yi kashi a poo ya na so a wanke masa sannan ta miqe, ta je ta wanke masa ta yo wanka ta sa kaya ta tada sallah rana na kallon ta gatso gatso,a hanzarce ta jejjefa sallar ta ninke sallaya ta zo ta dafa masu taliya, da manja da yaji, ta duba kayan da aka kawo mata jiyan, wasu qananan kaya ne masu matuqar kyau riga da wando kalar orange, masu matuqar kyau da tsada ta dauka har zata saka, can wata zuciyar ta ce mata
'ke me zaki saka kayan qanwar bayan ki kiyi da su? Kawai kije ki siyar ki sai wasu sauran kudin kin kashe wata hidimar da su'
Ta yi amanna da shawarar kuwa dan haka ba b'ata lokaci ta samu Sulaiman ta masa kwaskwarima Yousuf ma ta masa,ta saka masu wasu kayan ta dau wad'anda take ganin zata siyar suka rufe gida su ka yi gaba, suna fita wani babban shago ta je a layin nasu da suke saida yan kayyaki haka,taje ta masu bayanin kawo mata akai jiya ita kuma ba ta son sawa tace bari ta saida, aiko yana gani shima dan son banza ya hau d'aga wa ya na kalla, wasu riga da wando ne suka dauki hankalin shi ya riqe wandon ya na kallo, tambayar ta ya yi nawa zata siyar masa wandon, ta ce ko nawa ne ya bata dan ba sanin kud'in su ta yi ba,iya wandon dake mahad'in rigar zaiyi k, amma haka ya hada dika da rigar da wandon ya bata 4k, sauran ma haka ya yi ta musu siyan wulaqanci, a haka ta tashi da 37k dad'i ne ya kama ta kamar ta suma, kasuwa ta wuce daga nan ta siyo atampopi uku, ta saiwa yaran suma yan kayan da ba Wani tsada gare su ko quality ba, ta hado kan sauran canjin ta ta yi cefane har da kaji biyu, tayo gida.
A qofar gida ta ganshi ya cika ya yi fam,sai a sannann gabanta ya fadi, dan kwata2 ta manta da shi, salati ta hau yi, kan ta iso qofar gidan itama ta dake ta b'ata rai sosai kamar yanda ta ga ya yi, yana ganin ta ya Isa gaban ta ya miqa mata hannu, makulli ta zaro ta bashi, ya bude gidan, ya wuce bai tanka ta ba, sai ta yi dariya tace,
"ka isa yanda na b'ata rannan ka tanka ni dama humm da ka ga ruwan rashin mutunci mtseww" karaf a kunnen Auwal kuwa.
Tana aje Sulaiman a gado Yousuf ya haye kujera ya hau baccin wahala dan ba kad'an ta wahalar da yaran nan ba, ga rana ana kod'awa, juyowar nan da za ta yi ya kifa mata mari guda uku kyawawa, tsabar gigicewa matse qafa ta yi saboda matse fitsarin da ya taho mata ba shiri,daka mata tsawa ya yi ya ce,
"Fita waje ! In ki ka min fitsari anan se kin gwammace kid'a da karatu, mahaukaciya da bata San ciwon Kan ta ba"
Da gudu ta yi waje kafin ta Isa band'aki fitsari ya kufce mata, anan tsakar gidan ta gama shi ya na gama zuba kuwa ta rushe da matsanancin kuka, tana zage2 akan me zai dake ta? Me ta masa in ba cin zali ba Allah ya isan ta ,kamar Jira kuwa ya ke ya fita a sukwane ya hau jibgar ta, Yousuf da ya farka tin a tsawar da aka daka mata ne ya tafi da gudu ya na kuka ya tsaya a tsakanin su ya kalli wannan ya kalli wancan , Sulaiman ma da ya farka ganin ana ta koke2 se ya saki nashi,nan fa gida ya rikice da koke koke kamar gidan makoki, shigewa daki Auwal ya yi yana tinanin hali irin nata, ta na nan ta na sharar bacci bata basu abun karyawa ba, ya na tinanin in Yara suka tashi me za su ci Kan a yi girki? Shi ne dalilin da ya sa ya tafi siyo masu indomie da d'an kwai tinda jiya Adnan ya basu kud'i,ya na dawowa ya gan ta da qatuwar leda ta nufi shagon da ke unguwar su ta na magana ana d'aga kayan, daga nan ya fahimci me take yi, a gaban idon shi ta hau machine da yaran shi dika ta bar unguwar, ya na nan zaman jiran ta, Kuma dan ta raina masa hankali ta dawo tana Wani cin magani tana fad'in maganganun rainin hankali akan shi ita gawurtacciya ko? Shiru Auwal ya yi ya dor'a hannun shi a Kan shi da yake Jin yana sara masa ga yunwa da ke mugun cin shi,tsaki ya ja Mai qarfi ya kalli sauran kayan da ta barbaza wasu a akwatin wasu a qasa,yanzu tsabar hauka ace ta sai da kaya masu daraja da tsada ta shigo da tarkace a madadin su,haushi kam ya shashi har ya rasa wajen aje saura, addu'ar shiriya ya mata ya miqe ya fita dan nemawa kan shi abinda zai ci da d'an shi, kwance ya ganta kan kujera tana ta kuka, tausayin ta ne ya kama shi domin ba duka qanqani ya mata ba, banza ya yi da ita ya fita, har ga Allah yana son matar shi, amma bata da hali mai kyau, qyashi da hassada, da baqin ciki sun wa rayuwar ta yawa shi Kuma ba matar da ya zaci ya aura ba kenan......
Wanda ya sai rariya ya San zata zubda ruwa ai ko?
[6/10, 5:43 AM] HAERMEEBRAERH❤️: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*****
*****