KAINE JARUMI

Page 10

by @1239900

Sakeenaah na had'a Ido da Rasheedah ta ji gaban ta ya yi wani irin mugun faduwa, saboda yanda taga tsantsar tsanar ta da qiyayyar ta a fuskar yayar tata, cikin rawar murya ta ce,

"Rashee....."

"Dakata min tsohuwar munafuka, dama had'awa ki ka yi da mijin ki in kunzo ku min wulaqanci gaban iyaye na ku min munafurci da annamimanci? Ku fada masu abubuwan da na maki dan su qara tsanata? Gaki an taba 'yar so Kuma 'yar gwal ko? To bari kiji na fada maki wani abu da wataqila baki sani ba Sakeenaah, ni Rasheeda na yi alqawarin ba zan tab'a son ki ba a rayuwa ta har abada,ko me ki ka zama, ko me zaki zama,ko me ki ka mallaka, ke zuri'ar ki ma ba ni ba su ko da kuwa duniya zaki haifa dan yawa nan gaba ni dasu ba zancen soyayya, na tsane ki ! Na tsane ki !! Na tsane ki !!!"

Numfashin Sakeenaah ne ke mata wahalar shaqa, ido ta lumshe wanda tin da Rasheedah ta fara magana take zubda hawaye, wannan wace irin rayuwa ne,wace iriyar qiyayya ce haka me zafi? Me ta yi mata? Anya Rasheedah bata da aljanu da ke had'a su fad'an ba gaira babu dalili? Dan ita har yanzu bata San menene takamaimai abinda ya janyo wannan mahaukaciyar qiyayyar me zafi ba a tsakanin su, a bayyane take nuna mata tsana, kyashi, hassada, da qiyayya, yau ko kafira ce ita ai se haka,abun takaicin shine tama qi sanar da ita asalin dalilin da yasa ta ke qin ta,dan dalilan da ta sani gani take kamar ba su bane, a wajen ta basu kai wanda za ai mata tsana haka ba, kuka take sosai, ta na nan tsayen ta wani jiri na d'iban ta, ta kuwa tafi luuu zata fadi, Rasheedah da ke saitin wajen kawai se ta buga tsaki ta kauce, ai kuwa ji ka ke  'tiimmm' Sakeenah ta fadi a qasa.

Zagaye Sakeenah Rasheedah ta yi zata shige toilet abun ta,tana gab da shiga toilet din ta ji muryar mahaifiyar su da ta je d'akko wa Rasheedahn hijabi saboda sallah, dan tin da ta shigo take kallon kayan sun yi tsiraici da yawa amma bata mata magana ba, da niyyar zata bata hijabi kalar kayanta ta dinga had'awa da shi, cikin matsanancin kuka ta ce,

"Yanzu ashe irin yarinyar dana haifa kenan ban sani ba? Ina murna ina da yara biyu kyawawa, ashe na yi kuskure, yarinya ta d'aya cekyakkyawa me kyan hali ce, d'ayar kuma baragurbi, yanzu da kan ki kike zayyana wa qanwar ki uwa d'aya uba d'aya wadannan abubuwan? Wace........"

Wani nishi da Sakeenaah ta ja ne ya yi sanadin rugawar Mama da gudu gare ta, tana danna qirjin ta, alamar dawowar su Abbah maman ta ji ta kuwa kwala masu kira a gigice, a firgice suka shigo dan sun ji kiran nata kamar da kuka a ciki, Adnan ne a gaba har yana tuntube da Hijab din da Mama ta kawo wa Rasheedahn, sauran qiris shi din ma ya fadi.

Yana ganin matar shi a kwance a qasa shame shame, ya yi saurin kallon Rasheedah wadda ta nuna ita fa yanayin da Sakeenah ke ciki ko a jikin ta, cikin ran ta da fari ta tsorata, amma daga baya da ta ga yanda hankalin kowa ya tattara ya koma Kan Sakeenaah cikin madaukakiyar damuwa da tashin hankali sai hakan ya qara sa ta jin tsanar Sakeenaah ta ninku a ran ta,wai akan ta ake wannan rawar duwais din, ji harda Abban su, kad'a ido sama ta yi ta ja gajeren tsaki zata shige, Mama ta yi wani kukan kura ta janyo ta, daidai lokacin Abba ya shafawa Sakeenaah ruwa ta dawo normal, kifa mata kyawawan maruka mama ta dingayi ta na kuka, tare da fad'in baqaqen maganganu akan Rasheedahn,ko gezau Rasheedah bata yi ba zuciyar ta ta bushe ta dake da qiyayya da hassadar qanwar ta, Adnan ne ya riqe hannun Mama yana bata hakuri,

"Ka barni kan ta kashen yarinya mai yi mana biyayya da son mu da kulawa da lamarin mu gwanda ni na kashe ta, ban tab'a sanin haka Rasheedah ki ke da baqar zuciya ba, a zato na d'an kishin nan ne dake tsakanin 'yan uwa Saqo da saqo,ashe ke kina nan kin gina zuciyar ki akan mummunar qiyayya me zafi haka,mu kuwa me za mu yi da mai halayya irin taki? Ta ina na gaza a baku tarbiyya ni da mahaifin ku har kk deb'o wannan mummunan halayen bamu sani ba? Wannan wacce irin yarinya na haifa? anya bata da  mugayen aljanu a tattare da ita kuwa?"

Abba ne ya zaunar da Maman a gefen bakin gadon d'akin, ya rungume ta ya na lallashin ta,

"Zubar hawayen ki a gurin ta masifa ne,zai sa ta qara lalacewa ne kawai, ki kwantar da hankalin ki da izinin Allah zata so Sakeenaah, kwatankwacin yanda iyaye za su so 'ya'yan su, ki basu lokaci, ke Kuma Rasheedah mu na Mai baki hakuri akan dikkan abinda ki ke ganin mun aikata maki ba daidai ba da ya ja ki ka tsani qanwar ki da ku ka fito ciki d'aya har haka"

Sakeenaah da ta jingina da pillow, a hankali tace zata sha ruwa, ruwan Adnan ya bata, yana mata kallon so,qauna da tausayawa, kallon ta ya ci gaba da yi ya ga yanda take kallon Rasheedah, takaici duk ya ishe shi, a hankali ta Maida kallon ta zuwa ga Adnan ta ga yanda ya damu akan ta, shi Kuma bin ta yake da kallo tare da maganar zuci,

'Baki da wayo my love har yanzu ya Kamata  ki farka ki gane wannan ba zata taba son ki ba,'

A hankali Sakeenah ta furta

" Rasheedah kiyi hakuri da dikkan abinda na miki, wanda na sani da wanda ban sani ba, ko menene shi ki wa girman Allah ki yafe min, rayuwar nan ta duniya ba komai cikin ta face rud'in shaid'an , ni ina son ki,ina son ki, ina son ki,ke yayata ce, bayan iyayen mu banda kowa bayan ke, sai mijina, in baki so na ya zanyi?"

Kuka ne yaci qarfin ta, haushin ta yanzu Adnan ya ke ji, na farko kenan ma baya list din masoyan ta na fari wannan banzar da bata son ta ta ma fishi matsayi, sannan ga shi sai wahala yake da ita amma ko kallo bai ishe ta ba, tari ne ya sarqe ta ta kasa qarasa maganganun da take yi,tsaki Rasheedah ta yi ta d'au gyalen ta da jakar ta ta bar dakin, parlor ta je ta tadda yaran ta duk sunyi bacci, goya Sulaiman ta yi ta dau Yousuf a hannu, ta yi waje, ranta baqiqqirin, da kulawar da ake bawa Sakeenaah, bayan ta manta itace silar koma me ya sami Sakeenahn har ake bata kulawar.

Abun nasu ya zama wata iriyar jarabawa, Allah ya jarabci Sakeenah da tsananin son yayar ta ta, ita Kuma Rasheedah na tsananin qin qanwar ta ta.

(Dama haka Kan faru, sanda Wani yake tsananin son Wani, to shi wannan da ake so sai a yi rashin sa'a lokacin yake tsananin qin Mai son nashi)

Mai adaidaita Sahu ta tsare ta hau ta yi gida,Su kuma suka fito da Sakeenaah dan kai ta asibiti, suna zuwa likitoci suka karb'e ta suka kwantar aka gwada Bp din ta ya hau sosai, sannan aka d'ebi jinin ta suka yi gwaje gwaje, matsalar hawan jinin ta suka hau dubawa dan shine yafi, a haka Mama, Abba,da Adnan, suka shiga jinyar Sakeenaa,har kusan kwana sha d'aya a asibiti, Sakeenah ta d'ashe ta yi haske sosai, kusan kullum cikin amai da zazzabi take,amma kullum idon ta rufe taqi budewa kome ake tana ji tana sane, amma bata son yin magana, tinanin tin da ta fara wayo, zuwa 'yammatancin su take, har ranar auren su, ko akwai abinda ta yi wa yayar ta mara kyau da ya ja mata mummunar qiyayyar nan? Amma ta rasa,dawowar Abba daga kasuwa kenan ya biyo, ya na tambayar jikin Sakeenah a wajen Mama da Adnan da tinda Sakeenah ta kwanta be je ko Ina ba, dik abinda ake da buqatar shi ko signing ko ganin Wani file d'in se dai a kawo masa nan ya yi a mayar, tattauna wa suke akan matsalar musamman jinin ta da ya qi daidaita sai su ka ga hawaye na zuba ta gefen idon ta, Adnan da Abba har suna rige2n zuwa gare ta,Adnan ya kama hannun ta ya ce,

"My love pls ki yi magana mana ki fad'i abinda ke ran ki ki cire damuwar ran ki ko zamu samu ki ji sauqi, nasan kina jinmu ba wanda yace ki tsani yayar ki, amma baki ganin sata arai har ki samu matsala haka babbar illa ce ga rayuwar mu? Kin sani in Wani abu ya same ki ba zan rayu ba, ke kad'ai nake da a duniyar nan, ki yi hakuri ko dan  abinda ke cikin ki?"

Da sauri ta bud'e ido tana kallon shi, dan duk abinda su keyi tana ji amma meyasa bata ji zancen ciki a jikin ta ba? Gyada mata kai ya yi idon shi tab hawaye,

" Eh ciki, jiya likita ya tabbatar mana kina dauke da qaramin ciki"

Sunkuyawa ya yi daidai kunnen ta nima ko na kai nawa naji me zaice amma inaaa ya iya qusqus banji komai ba☹ murmushi ta saki ta rufe idon ta, sai kuma ta saki kukan farin ciki, da kyar suka lallashe ta ta yi shiru, murna a wajen ta ba a magana,banda hamdala ba abinda ta ke maimaitawa, tini damuwar da take ciki ta Kau ta maye gurbin damuwar da farin ciki, roqon shi ta yi daya d'aga ta ta je toilet, alwala ta yi tazo ta yi sallah raka'a biyu ta godewa Allah da ya amsa addu'ar ta a wannan lokacin.

Se da suka qara kwana biyu aka tabbatar da lafiyar ta sannan aka sallame su, gidan su suka wuce, Mama da Abba ma suka wuce nasu, cike da farin ciki.

Makaranta ba sai na fad'a maku irin lelen da Sakeenaa ke sha ba wajen Adnan kai har ma da Mama da Abba ba, kullum cikin shagwaba ta suke, komai tace tana so sai sun bata, kan kuce me Sakeenaah ta zama Masha Allah barakallah, ta yi 'yar qiba me kyau ta masu ciki, jikin ta kamar ba ita ba, ta yi haske akan baqin ta se kalar ta ta zama Mai d'aukan hankali da idanun Mai kallo, Adnan in yasata a gaba da kallo, har sai ta soma shagwabar kallon ya yi yawa. Wani abu dake qara burge Adnan kuma shine her demand of sex increases, duk a harkar cikin wannan bangaren ya fi burge shi, kusan kullum ba fashi sai anyi wataran har sau uku,kai wataran har hudu ma, ba qaramin morewa yake ba,ji yake kamar ta tabbata haka ko bayan haihuwa, ita kuma in an gama sai ta hau bashi hakuri tana kuka, akan tasan tana takura masa, amma ba yanda zata yi ne, ya yi hakuri data haihu zasu koma normal, kawai sai ya gyada kai, a ranshi ko yace ba amin ba Allah sa a dawwama a haka mu na morar juna.

Lokacin da cikin Sakeenaah ya kai wata bakwai, Adnan ya na yawan ganin ta tana rubuce2, in ya yi qoqarin gani,ta saka kukan shagwaba akan yana mata leqe, haka zai hakura ya je ya hau yin wani abun ya barta, a girman cikin da take da shi haka take ci gaba da dukkan ayyukan da muka san ta da shi, sai dai kawai wannan karon akwai sauyi, in kasala ta rufe ta sai ta hakura sai ta ji normal sannan ta tashi ta yi ayyukan ta.

Cikin ta na wata takwas ta shirya ba da sanin Adnan ba ta tafi gidan Rasheedah.......

*Kai ni ku ban madoki na tsane Sakeenaar nan, me ya kaita kuma zuwa gidan Rasheedah, mara zuciya kawai😡*

[6/11, 9:49 PM] HAERMEEBRAERH❤️: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼

WRITTEN  BY HAERMEEBRAERH