MUGUWAR MACE

PAGE 2

by @1239900

Karkata kan motarsa yayi ya ɗauki hanyar unguwar Ƴankaba. A daidai ƙofar wani gida na masu matsakaicin ƙarfi ya tsaya. Ya jima sosai a cikin motar kafin ya fito tare da zaro wayarsa da ke cikin aljihunsa ya hau latsawa. Jiki a mace ya kara wayar a kunnensa,ko sallama bai yi wa wanda ya kira ba ya ce.

"Ka same ni a ƙofar gidanka yanzu."

Kashewa yayi ya jingina da jikin motarsa yana jin ƙafafuwansa sun masa nauyi kamar ba zai iya ci gaba da tsayuwa ba. Cikin abinda bai fi minti biyu ba wani siririn dattijo ya fito daga gidansa ya na saɓa tsohuwar babbar rigarsa a kafaɗarsa,kaki yayi ya zubar sannan ya ƙarasa wajen Aabid dake tsaye. Sallama yayi wa Aabid tare da naɗe hannuwansa a cikin babbar rigarsa ya duƙar da kansa ya ce.

"Ranka ya daɗe lafiya dai ko na ga ka zo har gida ba ka kira ni can kamfani ba."

Ajiyar zuciya mai ƙarfi Aabid ya sauke kafin ya ce.

"Lafiya ƙalaou Malam Sallau. Na zo ne akan maganar nan da muka taɓa yi da kai da jimawa daga baya kuma na ce na fasa. To yanzu ina so ka sake tuntuɓar mutumin ka ji if he is still interested i am willing to...."

Cikin hanzari Malam Sallau ya katse Aabid ta hanyar washe baki ya ce.

"Ai Alhaji ko yanzu muka je na san zai amince. Wannan mutumin ai kusan sana'arsa kenan,dan haka duk lokacin da ka shirya kawai zuwa za mu yi mu same shi har gida a daddale magana."

"Ok idan dai haka ne kawai mu je yanzu."

Har Malam Sallau ya kama hannun motar Aabid ya buɗe zai shiga,sai kuma ya ja ya tsaya. Cike da sanyi tare da mutuwar jiki ya ce.

"Ranka ya daɗe ba zan ce maka ban ji daɗin wannan harƙalla da za a ƙulla ba,saboda ko babu komai ta nan nake samun nawa abincin da wasu buga-bugar. Amma kuma ina ganin kamar abinda za ka aikata bai dace ba,kada ka manta fa...."

Hannu Aabid ya ɗaga wa Malam Sallau rai a ɓace ya ce.

"Za ka kai ni ne ko na samo wani?"

Da sauri Malam Sallau ya saka hannunsa guda biyu ya zuge laɓɓansa sannan ya faɗa mota ya zauna. Cikin ƙiftawar Ido Aabid ya bar unguwar su Malam Sallau suka nufi unguwar Ɗanladi na Sidi. Da kwatance Aabid ya kai su gidan Alhaji Kabiru Mai Tumbin Nera. Gida ne kadaran kadahan domin kuwa gaba ɗaya unguwar shi ne gidan da bashi da gate da kyawun sifa kamar sauran manyan gidajen dake jere a unguwar reras gwanin ban sha'awa. Malam Sallau ne ya fita ya je ƙofar gidan ya dinga kwaɗa sallama. Babu jimawa wata yarinya ƙarama ta leƙa tana tambayar waye. Washe baki Sallau yayi ya ce mata.

"Ki ce wa gyatuminki yayi manyan baƙi ya hanzarta ya fito kada ya ɓata wa Alhaji lokaci."

Da gudu yarinyar ta koma cikin gidan ta sanar da zuwan su Malam Sallau ga mahaifinta wanda ke tsaye yana sanya takalmansa tare da tura uban tumbi gaba yana nishi tsabar ƙiba. Kai kawai ya gyaɗa mata ya nufi waje. A tsaye ya tarar da su Aabid ya miƙa musu hannu suka gaisa. Babu ɓata lokaci Sallau ya kora masa bayani akan dalilin zuwan su. Murmushi Alhaji Kabiru Mai Tumbin Nera yayi sannan ya ce.

"Yanzu ake buƙatar kuɗin ko yaushe? Domin ni a shirye nake da na bada kuɗi,a bani takardu tare da kafa shaidu."

"Idan ka shirya ni ma a shirye nake."

Cikin ƙanƙanin lokaci su Aabid suka gama duk abinda ya kawo su suka yi sallama da Alhaji Kabiru suka tafi. Godiya sosai Malam Sallau ya dinga yi kamar zai kwanta wa Aabid a ƙasa. A haka Aabid ya sauke shi a daidai wajen da zai samu mota ya koma gida shi kuma ya wuce gidansu dake cikin unguwar Ɗanladi na Sidin. A waje ya ajiye motarsa ya shiga cikin katafaren gidan nasu wanda da wayonsa mahaifinsa ya siyi gidan a hannun gwamnati ya rushe shi ya sake ƙera kalar wanda yake so. Gida ne da ya amsa sunansa gida mai part uku da manyan filayen da aka yi shuke-shuken ƴaƴan itatuwa da flowers domin ƙayata wajen. Gefe ɗaya kuma ƙaton waje ne da aka yi kitchen irin na gargajiya tare da ɗakuna uku na masu aiki. Zagaye Aabid ya dinga yi a gidan yana kallon kowanne lungu da saƙo na gidan yana tuna memories masu daɗi da marasa daɗi da suka faru a gidan. A ƙofar ɗaya daga cikin sassan da ke cikin gidan ya tsaya yana bin ƙofar da kallo. Wani irin abu ya ji ya daki zuciyarsa har sai da ya sanya hannu ya dafe ƙirjinsa.

"Dijahna"

Shi ne sunan da ya ambata kafin ya tura ƙofar ya sanya ƙafarsa ta dama a ciki. Nan take hotunan rayuwar da yayi a baya ta hau gilmawa a idanuwansa. Kansa ya ji yana sara masa kamar zai tsage. Babu shiri ya fita daga sashen ya ja ƙofar ya rufe. Da sassarfa ya nufi sashen Hajiya wadda ke kwance ita kaɗai a parlourn ta da ya koma kamar kango tana firfita. Kallonta yayi fuska a haɗe kamar bai taɓa dariya ba ya ce.

"Ina wannan yarinyar take na ganki ke kaɗai?"

Da sauri Hajiya ta tashi zaune daga kishingiɗar da ta yi ta kalli Aabid cike da so da ƙauna irin na ɗa da mahaifiya. Murmushi ɗauke a saman fuskarta ta ce.

"Samha? Ta fita samo mana gawayi mu ɗan ɗora ruwan koko a samu a karya tinda gari ya waye."

Rintse idonsa yayi yana jin jiri na ɗibansa. Mahaifiyarsa ce fa,matar da ko Custard za ta sha sai ya koma fari fat saboda madarar da take zabga masa,ta saka ta ruwa sannan ta ƙara da ta gari,ita ce yau take neman gawayin da za ta dama koko. Mahaifiyarsa wadda take rayuwa kamar sarauniya komai sai an yi mata saboda dukiya da gatan da mahaifinsa da shi kansa suke bata. Kyaɓe baki yayi sannan ya zaro dubu biyu ya ajiye a nesa da ita ya kurɗa kansa cikin ɗakinta,da wani irin farinciki Hajiyan ta ɗauki dubu biyun tana jin kuɗin kamar dubu ɗari biyu a wajenta,yaushe rabon Aabid ya zo gare ta? Yaushe rabon ta samu arziƙin samun wani abu daga gare shi? Lallai wannan babbar nasara ce a gare ta wadda take fatan watarana komai ya koma kamar yanda yake a baya. Bincike yayi sosai kafin ya samu abinda yake so sannan ya fito yana zufa kamar wanda yayi wani aikin wahalar. Kai tsaye ya fice ya bar gidan ba tare da ya ce mata kanzil ba ya faɗa motarsa ya fige ta. A hanya ya haɗu da Samhah hannunta riƙe da tarkacen itacen da ta yo da kanta saboda rashin samun gawayin da bata yi ba. A gabanta ya tsayar da motarsa ya kalle ta ya ce.

"Ke wannan yayin haukan da kika ɗebo fa na meye?"

Cike da jin tsoronsa bakinta ya hau rawa,tsawa ya daka mata tare da sake tambayarta abinda ke hannunta na meye. Cikin rawar murya ta kalle shi ta ce.

"Ƙirare ne na samo dan mu yi amfani da shi."

"Ina gawayin da kika je siyowa?"

"Ban samo ba."

Tsaki ya ja mai tsawo sannan ya ja motarsa ya bar wajen a guje kamar zai tashi sama. A hankali ta waiga ta kalli ƙurar da motar ke tadawa sannan ta girgiza kanta ta wuce gida.

Washegari da sassafe ko tashi daga bacci su Hajiya basu yi ba suka ji ana buga gate ɗin gidan nasu da ko arziƙin mai gadi babu. Hajiya da kanta ta sanya mayafinta ta nufi ƙofar gidan da makulli a hannunta tana tambayar waye. Wata murya ta ji wadda bata waye da ita ba tana faɗin.

"Mu ne."

Gabanta ne ya faɗi har sai da ta dafe ƙirjinta kafin ta ce.

"Ku su wa?"

"Alhaji Aabid bai sanar da ke zuwan mu ba ne? Ina ga zai fi kyau ki kira sa a waya ki tambaye sa su waye za su zo war haka."

Cike da jarumta Hajiya ta buɗe ƙaramar ƙofar gidan ta tsaya tana kallon mutanen da bata taɓa gani ba sai a wannan ranar. A guje Malam Sallau da ya tsaya bawali ya ƙaraso yana gyara wandonsa tare da fyace majina ya ce.

"Barka da safiya Hajjaju."

Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke sannan ta ɗan yi dariya ta ce.

"Malam Sallau ai har na ji tsoro,ashe ku ne ke tafe. Bismillah ku shigo."

Da jin haka sai suka ɗunguma suka shiga cikin gidan gaba ɗaya su na sake gaisawa. Alhaji Kabiru Mai Tumbin Nera kuwa kallon gidan yake yi yana girgiza kai tare da washe baki. Tafe yake yana buɗe duk wani ɗaki ko ƙofa da ya gani kamar gidansa. Cike da mamaki Hajiya ta ke kallon ikon Allah,ba ta katse da lamarin Alhaji Kabiru ba har sai da ta ga ya nufi sashen ya saka hannu zai buɗe ƙofa. Da ƙarfi ta ce.

"Malam lafiya wai naga kana ta buɗe min ƙofofin gida kana kalle-kalle?"

Malam Sallau ne ya sosa ƙeya sannan ya ce.

"Hajiya wai ko dai kina nufin Alhaji Aabid bai sanar dake abinda ke faruwa bane?"

Cike da mamaki Hajiya ta juya tana kallon Malam Sallau sannan ta ce.

"Malam Sallau me ya samu ɗana? Me yake faruwa wanda ba a sanar dani ba?"

"Baki da labarin Alhaji Aabid ya siyar da wannan gidan Hajiya? Ai jiya da yamma ya kai wa Alhaji Kabiru takardu muka je wajen Mai Unguwa aka saka shaidu ya biya kuɗi da ..."

Wani irin duhu ne ya mamaye ganin Hajiya,nan take ta yanke jiki ta faɗi. Alhaji Kabiru na ganin haka ya hau sauri yana son barin gidan,domin shi mutum ne mai tsananin tsoro da kiyaye duk wani abu da zai haɗa shi da hukuma. Banda nishi babu abinda yake yi a haka ya isa waje ya shige motarsa ya zauna yana yarfe zufa.

Sallau kuwa sunan Samhah ya dinga kira ta fito a gigice kanta babu ko ɗanƙwali. Ganin Hajiya a zube a ƙasa ne ya gigitata ta nufi wajen da gudu ta zube a gefen Hajiyan tana jijjiga ta. Hankalin Sallau ba ƙaramin tashi yayi ba dan haka sai ya miƙe ya lalubo wayarsa ya dannawa Aabid kira. Cikin rashin sa'a kiran ya shiga a daidai lokacin da wayar Aabid ɗin take hannun Aabida tana duba mutanen da yayi waya da su a jiya;wanda murnar ganin gingimemen alert ɗin kuɗi ya mantar da ita dubawa. Ɗauka ta yi cike da gadara. A kiɗime Malam Sallau ya labarta mata abinda ke faruwa. Rai a ɓace Aabida ta ce.

"Idan ta faɗi mutuwa ta yi? Malam idan za ku yayyafa mata ruwa ta tashi ku yayyafa mata,idan ba za ku yayyafa mata ba ku kuka sani ku barta ta ƙarasa ai dama ta kwana biyu,babu inda mijina zai fito da sanyin safiyar nan yana hutawa."

Tana gama magana ta katse wayar ta ci gaba da abinda take yi..........

MUGUWAR MACE.

NA: HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH. ✨✍️

*Ƴar'uwa kema kin yi ta shan maganin slimming amma har yau ya ƙi karɓar ki? Matso na zo maki da haɗin da zaki sha ki sauke ƙiba da nauyin jiki cikin sauƙi,Shayi ne mai daɗi da ƙamshin da ba zai baki damar yin ƙiwa ba wajen amfani da shi. Bayan haka akwai slimming oil da zai rage maki kitse a duk gaɓar da kike da buƙata a jikinki;kamar tumbi,damtse,kitsen baya,da cinya.*

*Slimming Tea 6k.* *Slimming oil 3500.* *Body scrub 3500.* *Skin oil 2500.* *Location Kano.* *Phone No ***.*