PAGE 4
by @1239900
Motar kamfanin Aabid ta gani ta ɗiban hatsi tsaye a ƙofar gidan ɗauke da kaya,sai direba dake tsaye yana yi mata bayanin daga inda kayan suka fito tare da sanar da ita saƙon Alhaji Maheer. Gyaɗa kai kawai ta yi ta matsa ta basu waje. A gaban idanuwanta suka shigar da kayan ɗakin da ta gama gyarawa sannan suka yi mata sallama suka wuce. Kanta ya ɗaure sosai da wannan sabon lamarin da ta kasa yi wa suna. Shin me yake faruwa ne? Rashin samun amsar tambayarta ne ya sanya ta shige wa ɗakin ta duba kayan da yanda suka jera komai a inda ya dace. A hankali ta ja ƙofar ta rufe sannan ta koma sashenta ta zauna. Tagumi ta zabga tana hasaso abubuwa da dama da za su iya sanya Yah Maheer gyara ɗakin nan kamar wanda za a saka wata amaryar a ciki. Kasa cin abincin da ta dafa ta yi;duk kuwa da irin yunwar da take ji na kartar tumbinta. Kwanciya ta yi a saman doguwar kujera tana hawaye,a haka bacci mai cike da mafarkin Yah Maheer ɗinta ya ƙara sabon aure har ya tare da amaryarsa.
Kiran sallar magariba ne ya tada ita daga nannauyan baccin da ta sha,a gaggauce ta faɗa banɗaki ta yi brush ta ɗaura alwala sannan ta wuce ɗakinta ta tada sallah. Kaya ta sauya zuwa ƙanana masu kyau sannan ta ƙara feshe jikinta da turare,daga nan sai ta wuce parlour ta kunna turaren wutanta mai daɗin ƙamshi,nan da nan gidan ya kiɗime da ƙamshi kamar a Sudan. Sai da ta tabbatar ko ina ya ɗauki ƙamshin sannan ta wuce ɗakin tsakar gida ta kunna turaren wutan ta zauna tana jiran ya gama ta ɗauke.
Har Mahreen ta kammala duk wani abu da za ta yi ta zauna,shiru Yah Maheer bai dawo ba bai kuma kira ta a waya ba kamar yanda ya saba. Jin shirun yayi yawa ne ya sanya ta ɗaukan wayarta ta kira shi. Haka wayar ta karaci ringing bai ɗauka ba,jikinta ne yayi sanyi sosai ta sanya hannunta a baki tana cizon farcenta ta ce.
"Ni fa wannan sabon lamarin dake faruwa ya fara bani tsoro,ina mijina ya tafi tun safe har yanzu bai dawo ba;kuma bai kira ni a waya ba?"
Tsaye ta miƙe ta hau sintiri a parlourn tana jin yanda cikinta ke kukan yunwa amma ta bawa banza a jiyarsa. Duk yanda Mahreen ta so ta daure kasawa ta yi,cike da damuwa ta hau rubutawa Yah Maheer saƙo. Kafin ta tura ta ji horn ɗin motarsa,wurgi ta yi da wayar tata ta fita da gudu zuwa tsakar gidan sanye da hijabi a jikinta. Gate ta buɗe masa tana ta washe baki saboda farincikin dawowarsa. Sai da ya parker motar a inda yake ajiye wa sannan ta kula da Hajiyanta da Samhah a baya. Cikin sauri ta ƙarasa rufe gate ɗin ta nufe su,a daidai wannan lokacin Yah Maheer ya riƙo hannun Hajiya yana taimaka mata ta fito daga motar. Damuwa kwance a fuskar Mahreen ta hau jero musu tambayoyin da suka sanya Hajiya sakin murmushin baƙinciki. Yah Maheer ne ya kalli Mahreen dake a cikin ruɗani ya ce mata.
"Baby ki yi haƙuri mana mu shiga ciki sai na baki amsar tambayoyinki. Yanzu kafin nan maza ki je ki haɗa wa Hajiya ruwan wanka da abinci."
Da sauri ta wuce sashenta ta ɗora ruwan zafi a gas zuciyar ta cike fal da tarin tambayoyi. Ruwan na tafasa ta juye a bokiti ta sirka ta kai banɗakinta,ta na kai wa Hajiya ta tashi da ƙyar Samhana riƙe da hannunta Mahreen ta isa wajensu ta kama Hajiyan suka kai ta banɗaki,cike da kulawa Mahreen ta ce.
"Ko na tsaya na taya ki wankan?"
Kai Hajiya ta gyaɗa alamar eh,dan haka Samhah sai ta fita ta basu waje. Wanka mai kyau Mahreen ta yi wa Hajiya wanda ya bata ƙarfin jiki suka fito. Kai tsaye saman dinning table ta zaunar da Hajiya ta hau zuba mata abinci ta fara bata a baki,ganin ƙwalla a idon Hajiya sai ya karya zuciyar Mahreen. Cike da kulawa ta sanya hannu ta share mata wadda ta gangaro saman kuncinta. A haka Yah Maheer ya tarar da su shima ya zauna ya zuba abincin ya fara ci. Samhah na fitowa daga wanka itama ta zauna ta ci nata. Kallon Mahreen Yah Maheer yayi ya haɗe fuska ya ce.
"Me yasa baki ci abinci ba yau?"
Tura baki ta yi ta ce.
"Ba kai bane ka ɗaga min hankali? Ka fita tun safe babu waya babu saƙo,sannan baka yi min bayanin abinda ke faruwa ba."
Murmushi yayi sannan ya ce.
"Wannan halin naki na yawan shiga damuwa akan abu ƙalilan shi yasa na ƙi sanar dake abinda yake faruwa. Yanzu dai ki tabbata kin zuba abinci kin ci kin ƙoshi. Idan kin gama sai mu raka Hajiya ɗakinta ta huta."
"Dama Hajiya ka gyarawa wancan ɗakin?"
Mahreen ta faɗa cike da farinciki maɗaukaki. Kai Yah Maheer ya gyaɗa mata yana murmushi,tsallen murna ta daka ta rungume Hajiya dake kusa da ita tana murmushi. Zama Mahreen ta yi ta hau cin abinci tana zuba musu surutu suna amsa mata. Tana gamawa suka raka Hajiya sabon ɗakinta sannan Yah Maheer ya tsaya a gaban idonsa aka bata magungunanta ta sha ta kwanta tana ta zuba masa godiya da sanya albarka. Sai da bacci ya fara ɗaukanta sannan suka yi wa Samhah sallama suka koma nasu sashen.
Duk yanda Mahreen ta so ta ji dalilin dawowar Hajiyanta gidan Yah Maheer ya ƙi sanar da ita gaskiyar lamarin. Kan dole ta haƙura ta kwanta ranta fal murnar dawowar Hajiyanta kusa da ita kamar yanda take fata a koda yaushe.
A ɓangaren Yah Maheer kuwa yanda ya ga rana haka ya ga dare,domin kuwa hankalinsa a matuƙar tashe yake,yana jiye wa Aabid tsoron yin mummunan ƙarshe sakamakon wulaƙanta mahaifiyarsa da yake yi a rayuwa. Babbar damuwarsa bai wuce a ce har a wannan lokacin Aabid bai kirasa ya sanar da shi abinda ya aikata ba,sannan bai nemi ya san ina Hajiyansa ta shiga ba. Me yake tunani da ya siyar da gidansu na gado ba tare da sanin kowa ba? Ko babu komai Mahreen na da haƙƙi akan dukiyar mahaifinta. Me zai yi da maƙudan kuɗaɗen da ya siyar da gidan? Shin ko dai Aabid yana cikin wata matsalar rashin kuɗi ne? Kansa ya shafa zuwa fuskarsa tare da furzar da wani irin zazzafan huci. Zama yayi a kujerar dake cikin ɗakin nasu ya furta.
"Kamfaninsa na samun riba mai tarin yawa,ban ga dalilin da zai sa ya aikata wannan mummunan abun ba ba tare da yayi shawara da ni ba."
Jingina yayi a kujerar yana ci gaba da jera wa ƙwaƙwalwarsa tambayoyin da ya tabbatar da babu mai amsa masa su face Aabid da kansa. Da wannan tunanin ya miƙe ya buɗe ƙofa ya leƙa su Hajiya,jin shiru babu motsin komai ya tabbatar da bacci suke yi,sai ya koma ɗakinsa yana tunanin sanya musu solar a gidan ko dan matsalar wuta da ake fama da ita,ga kuma tsananin zafi da ake zubawa,sannan Hajiya ta saba da solar saboda yanayin jikinta bata son zafi.
Ɗakinsu ya koma ya shiga banɗaki ya ɗaura alwala ya fito. Abun sallah ya shimfiɗa ya hau ya tada sallah,ya jima yana jera nafilfilu kafin ya zauna yayi addu'a. Yana idarwa ya hau gado ya rintse ido yana fatan ya samu bacci ya ɗauke shi ko babu yawa. A hankali ya furta.
"Ya Allah ka bani ikon samun sallar asuba akan lokaci kada na makara sakamakon jimawa da na yi ban rintsa ba."
Yana gama faɗin haka ya runtse idonsa,sai dai tunanin dake cikin kansa ya hana shi samun abinda yake so. A haka aka yi kiran farko yana ta tasbihi a cikin ransa.
Da misalin huɗu da arba'in Mahreen ta farka ta shiga banɗaki,brush ta yi ta ɗaura alwala ta fito ta tada nafila. Tana idarwa Yah Maheer yayi shirin masallaci ya tafi. Bayan ta yi sallar asuba ta shiga kitchen ta fara haɗa musu abun karyawa,tana tsaka da aiki Samhah ta shiga ta hau taya ta,nan da nan suka kammala soya doya da ƙwai tare da dama kunun gyaɗa,sai suka gyara gidan. Ta so ta zuba musu anan su ci dika,sai Samhah ta ce.
"Hajiya ta ce na sanar dake,daga yau idan kin yi abinci a dinga kai mana namu can."
"Ohhh Hajiya,to Yah Maheer ɗin baƙonta ne?"
Murmushi kawai Samhah ta yi wanda ya sanya Mahreen ƙure ta da ido tana murmushi,a hankali ta ce.
"Kamanninki da Yah Dijah sai suka bayyana da kika yi murmushin nan."
Ƙwalla ce ta taru a idon Samhah ta miƙe da sauri ta bar sashen. Kai Mahreen ta dafe ta na jin babu daɗi a cikin ranta da ta tuna wa Samhah abinda ita kanta yana damun zuciyarta ballantana Samhah da ta fi ta kusanci da Dijah. Jiki a sanyaye ta kwashe abincin da ta zuba ta kai ɗakin Hajiyar. Rashin ganin Samhah a wajen da kuma ƙarar ruwa da ta jiyo a banɗakin ne ya tabbatar mata da wanka take yi,sai kawai ta zauna ta gaishe da Hajiya ta zuba mata abici ta kai mata gabanta. Godiya Hajiya ta yi mata tare da sanya musu albarka sannan ta ja kunun gyaɗar ta hau sha.
Yah Maheer na dawowa daga masallaci ɗakinsu ya shige ya hau rama baccin da bai samu ba a daren Jiya. Mahreen kuwa ta so ta zauna su yi hira da Hajiya a haka har ta bigi cikinta ta sanar da ita dalilin dawowarsu nan da zama,amma Hajiya ta kora ta wajen mijinta,kan dole ta tafi ba dan taso ba.
*************************
A ɓangaren Aabid kuwa tunda ya siyar da gidansu na gado aka tura wa Aabida kuɗin ta account ɗinta kai tsaye ya samu sauƙin matsin lambar da take yi masa. Wata iriyar soyayya take zuba masa wadda yake jin sa kamar shi kaɗai ne yayi dace da sa'ar macen aure a duniya. A ɓangare ɗaya kuma kullum da tunanin halin da Hajiyansa take ciki zuciyarsa ke kwana ta tashi,sai dai duk da damuwar da yayi da lamarin baya marmarin zuwa ya ga halin da take ciki ballantana ya san a ina take kuma a wanne hali take.
Bayan sati biyu Aabida ta kammala zuba kayan da ta yo order daga ƙasashen waje a sabuwar plazar da ta siya,da kanta ta jagoranci ma'aikatanta suka zuba kayanta da take siyarwa tana ta posting a social media tare da sanar da ƙawayenta Alhajinta ne yayi mata kyautar wajen. Aabid kuwa idan ya ga posting ɗin da ta yi sai ya tsaya yana kallon wajen yana tunani kala-kala a cikin ransa.
Yau ma kamar ko da yaushe tun da asuba da Aabid ya farka bai koma bacci ba. Abun karyawa yayi musu sannan ya haɗa wa gimbiyar tashi ruwan wanka mai cike da kayan gyaran jiki kamar yanda take so. Sai da ya tabbatar komai yayi daidai yanda take so sannan ya haura sama ya taso ta. Miƙa ta yi tana hamma tare da yamutsa fuska kamar wadda ta ga kashi. Da kallo Aabid yake binta yana jin wata iriyar soyayyarta zazzafa na ƙara huda kowanne sashe na jikinsa. Kallon Aabid ta yi daga sama har ƙasa ta ɗaure fuska ta ce..........
MUGUWAR MACE.
NA: HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️
*Ƴar'uwa kema kin yi ta shan maganin slimming amma har yau ya ƙi karɓar ki? Matso na zo maki da haɗin da zaki sha ki sauke ƙiba da nauyin jiki cikin sauƙi,Shayi ne mai daɗi da ƙamshin da ba zai baki damar yin ƙiwa ba wajen amfani da shi. Bayan haka akwai slimming oil da zai rage maki kitse a duk gaɓar da kike da buƙata a jikinki;kamar tumbi,damtse,kitsen baya,da cinya.*
*Slimming Tea 6k.* *Slimming oil 3500.* *Body scrub 3500.* *Skin oil 2500.* *Location Kano.* *Phone No ***.*