MUGUWAR MACE

PAGE 7

by @1239900

A gajiye Aabid ya fito daga wanka ɗaure da towel a jikinsa ya haye gado ya kwanta yana lumshe idanuwansa. Yunwar da ta fara neman agaji a tumbinsa ce ta sanya shi jan dogon tsaki ya yi juyi tare da ɗakko wayarsa da ya ajiye a bakin gado tun a lokacin da ya shiga ɗakin. Zuciyarsa na suya saboda tinanin abinda zai iya tararwa a cikin wayar ya buɗe password ya shiga TikTok,kai tsaye sunan account ɗin Aabidah mai suna Aaby142 ya shiga. Wani irin yawu ya haɗiye mai tsananin ɗaci saboda ganin sabon posting ɗinta da ta yi ita da yaron shagonta Mai suna Isuhu. Ransa ne yayi bala'in ɓaci ya sake shiga video na gaba yana jin ransa na ƙara ɓaci. Aabidah ce ke tafe tana rausaya mazaunanta da ƙirjinta sanye da ɗaya daga cikin sababbin kayayyakin da ta yi order tana tallata wa mutane tare da yin juyi da fari kamar wadda bata da igiyoyin auren kowa akanta. A haka suka dinga zagaye plaza ɗin tana ci gaba da nuna wa mutane irin kayayyakin da take siyarwa. Videos ɗin su na baya ya koma yana sake gani cike da ɓacin rai. Jin kansa na yi masa matsanancin ciwo ne ya sanya shi tashi da ƙyar ya shiga wajen da kayansa suke ya samu na bacci masu santsi ya saka. Sai da ya feshe jikinsa da turaruka masu daɗin ƙamshi sannan ya sauka ƙasa ya nufi wajen dinning table, ya na zuwa ya buɗe ya ga babu fiye da rabin naman dake saman wajen. Murmushi ya saki kawai ya girgiza kai,cike da sanyin murya ya ce.

"Hajiya Innaji kenan."

Zama yayi ya haɗa wa kansa shayi mai kauri ya buɗe mazubin dambun nama da cincin ya ci ya ƙoshi sannan ya jingina da kujerar yana jiran ya ɗan faɗa masa sannan ya je ya ɗora sassauƙan abincin da gimbiyar tasa za ta ci idan ta dawo. Ƙarar da wayarsa ta yi ne ya sanya shi miƙa hannu ya ɗauka. Notification ɗin da ya gani ya girgiza shi sosai,cikin sauri ya samu waje ya zauna da kyau yana ƙara gwale idonsa yana kallon sabon videon da Aabidah ta ɗora a shafinta. Wani irin yawu ya haɗiya mai ɗaci kafin ya ce.

"Me yasa Baby take zubar min da mutunci ne a garin nan? Babu wanda bai san ta a matsayin matata ba amma take mu'amala da irin matan nan marasa kamun kai da sunan abokan business. Ko ina ta baro abun tatar kokon da take yafawa a matsayin mayafi kuma?"

Sake kallon fancy restaurant ɗin da suka je ya yi. Waje ne da ya amsa sunan sa wajen cin abinci mai tsananin tsada a cikin garin Kano, waje ne da a ƙalla kafin mutum ya barshi sai ya kashe dubunnan ɗaruruwa. Aabid bai gama tsinkewa da lamarin Aabidah ba har sai da ya ji a cikin videon tana faɗin.

'Kowa yayi order ɗin abinda zai ci its on me.'

Kirari matan da take tare da su suka hau yi mata su na jinjina mata tare da sake nuna mata ita ɗin ta kai inda kowacce mace wayayyiya kuma mai aji ta kai. Fari kawai ta yi da idanuwanta masu tsananin kyau sannan ta gyara zamanta tana latsa wayarta. Ajiyar zuciya mai ƙarfi Aabid ya sauke sannan ya wuce sama ya haye gado ya kwanta,domin ya tabbata ko yayi girkin ma ba ci za ta yi ba,dan haka sai ya rage hasken fitilar ɗakin kawai ya rintse ido yana fatan bacci ya ɗauke shi;ko gajiyar da ya kwaso za ta yi masa sauƙi. A hankali ya rungume pillow yana sauke numfashi cike da ƙunar rai,cikin sanyin murya ya ce.

"Dijahna ina kike? Ina kewar ki sosai,ki dawo wajen masoyinki mai ƙaunarki da gaskiya,na yi alƙawari ba zan sake barin ki matsa daga inda nake ba ko da da ƙiftawar ido ne....."

Cike da sambatu na tsananin ƙauna,kewa da bege Aabid yayi bacci. A ɓangaren Aabidah kuwa bata dawo gida ba sai sha ɗaya da rabi na dare. Ta na dawowa ta wuce ɗakinta ta cire kayanta ta watsar a ƙasa ta shige wanka. Kai tsaye kayan bacci ta saka ta fesa turarukanta sannan ta saka hula a kanta ta nufi ɗakin Aabid. Kwance ta ganshi yana bacci rungume da pillow yana murmushi kamar ƙaramin yaron da yake mafarkin kansa a ɗakin alewa. Murmushi ta saki tana jin wani irin son sa da ƙaunarsa na sake ratsa zuciyarta. Sosai take son Aabid da kishinsa shi yasa ta tsaya tsayin daka ta raba shi da kowa da kuma duk abinda take ganin zai kawo mata tsaiko ko ya zamo kishiyarta a zuciyarsa. Tsaki ta yi da ta tina har a wannan lokacin ta kasa raba tsakaninsa da Maheer. Cike da takun ƙasaita da jin kai ta nufi saman gadon Aabid ta haye,sai da ta zame rigar dake saman kayan baccinta sannan ta zare masa pillown da ya rungume ta maye gurbin pillown da jikinta. Cikin magagin bacci Aabid ya rungume ta ya manna ta da jikinsa ya ce.

"I love you so much Dijahna.."

Wani irin juyi Aabida ta yi ta miƙe zaune tana kallon Aabid cike da matsanancin tashin hankali a cikin manyan idanuwanta da ta waro waje. Ƙirjinta dake barazanar fashewa ta sanya hannu ta dafe tare da janyo hularta da ta ajiye a gefe ta hau firfita da ita. Wata iriyar dariya ta ji Aabid ya saki ya na kara hannu a fuskarsa tare da kiran sunan matar da ta tsana sama da kowa a duniya. Jinin jikinta ne ya hau tafarfasa,nan da nan jikinta ya hau rawa ta hau tsiyayar da zufa. Hankali a tashe ta sauka daga gadon Aabid ta nufi ɗakinta cike da matsananciyar damuwa. Ta na shiga ɗakin ta kulle ƙofa ta cire wayarta da ta sanya a caji ta hau nemo lamabar wayar Innaji. Cike da magagin bacci Innaji ta amsa wayar tana faɗin.

'Wai ke sau nawa zan faɗa miki idan kika dawo daga yawonki ki dena tashi na? Ki na da makullinki amma dan ɗaukan alhaki....'

"Innaji ni ce Aabidah buɗe idonki da kyau ki kuma buɗe zuciyarki saboda ki fahimci abinda zan sanar da ke."

Da jin kalaman Aabidah sai Innaji ta wartsake daga magagin baccin da take yi;ta tashi ta zauna da kyau tana sake manna wayar a kunnenta kamar mai tsoron kada kalma ɗaya da Aabidah za ta sanar da ita ta kufce mata. Cike da damuwa Aabidah ta mayar da hawayen dake barazanar zubo mata daga idanuwanta zuwa saman kuncinta ta ce.

"Innaji na shiga uku na lalace,rayuwata na gab da ƙare wa..."

'Aabidah boka ya duba maki na kusa mutuwa ne na ji kina irin waɗannan kalaman?'

"Yo Innaji idan mutuwa kika kusa yi ai lokacinki ne yayi. Tashin hankalin da nake ciki ya ninka zancen mutuwa Innaji."

'To dan ubanki ki yi sauri ki sanar dani abinda yake faruwa kafin jini na ya fi yanda yake hawa.'

"Innaji Aabid ne yake ambaton sunan Dijah a bakinsa. Innaji na shiga uku na lalace rayuwata ta zo ƙarshe."

Ƙirji Innaji ta dafe tare da zaro ido waje ta ce.

'Ke ki bari dan manzo? To garin yaya aka yi ya ke ambaton sunan wannan matsiyaciyar yarinyar? Anya Aabidah baki tone wani ƙullin ba kuwa cikin rashin sani?'

"Haba Innaji ta yaya zan tone abinda na binne domin samun kwanciyar hankali na? Ni dai Innaji don Allah gobe ki shirya mu koma wajen Boka mu ji abinda yake faruwa."

'Aabidah ba fa zai yuwu mu ƙare rayuwarmu a bin....'

Cike da tsawa da rashin kunya Aabidah ta miƙe tsaye ta ce wa mahaifiyarta.

"Bin hanya da gidajen bokaye su ne abinda muka taso muka ga kina yi,dan haka dole ne ki taimaka min na mallaki zuciyar mijina ta yanda ko a bacci ko a zahiri bana son na sake jin sunan ko da kare ne in dai ba nawa ba a bakinsa."

Wani irin yawun takaici Innaji ta shanye tare da sassauta muryarta ta ce.

'Shikenan Aabidah ki shirya daga nan zuwa safiya sai mu koma wajen Boka mu ji. Amma ni dai da zaki haƙura mu ci gaba d...'

"Ke a zamaninki kin yi haƙuri kin zauna da kishiya ne Innaji?"

Kamar Aabidah na ganinta haka Innaji ta girgiza kai ta na so ta lallashi ƴar tata da ta fi so sama da kowa a cikin yaranta. Sai dai kafin ta buɗe baki ta sake cewa wani abu Aabidah ta riga ta da cewa.

"Tom kamar yanda baki haƙura kin zauna da kishiya ba,ni ma babu wani dan iskan da ya isa ya sani zama da kishiya ko da kuwa ta aljanu ce da ba ganinta zan yi ba."

'To na ji, yanzu ki kwantar da hankalinki ki kwanta ki huta;idan yaso da safe sai mu shirya mu je wajen Bokan.'

Kukan da Aabidah ke ta riƙe wa ne ya kuɓuce mata,da ƙarfi ta sake shi ta hau rerawa kamar waƙa,jin yanda take kuka babu mai lallashinta sai ya karya zuciyar Innaji ta kashe wayar ta kwanta tana jin tsanar duk wata macen da ke da kishiya. Ji take yi kamar ta jawo gobe ta gaggauta zuwa domin su je wajen bokan da zai samar musu da maganin matsalarsu. (Subhanallah)

A ɓangaren Aabidah kuwa kuka ta dinga yi har idanuwanta sai da suka kumbura suka yi jawur kamar gauta. A haka baccin wahala ya ɗauke ta ba tare da ta gyara kwanciyarta ba.

Washegari da sassafe.......

MUGUWAR MACE.

NA : HAMIDAH SUNUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️

*Za ku iya fara payment ɗin littafin MUGUWAR MACE da yake akan farashin 1k ta 9031416423,ku tura shaidar biya ta ***.*

*Ƴar'uwa kema kin yi ta shan maganin slimming amma har yau ya ƙi karɓar ki? Matso na zo maki da haɗin da zaki sha ki sauke ƙiba da nauyin jiki cikin sauƙi,Shayi ne mai daɗi da ƙamshin da ba zai baki damar yin ƙiwa ba wajen amfani da shi. Bayan haka akwai slimming oil da zai rage maki kitse a duk gaɓar da kike da buƙata a jikinki;kamar tumbi,damtse,kitsen baya,da cinya.*

*Slimming Tea 6k.* *Slimming oil 3500.* *Body scrub 3500* *Skin oil 2500* *Location Kano.* *Phone No ***.*