MUGUWAR MACE

PAGE 8

by @1239900

Aabid yayi matuƙar mamakin ganin Aabidah cikin shirin fita tin kafin ya farka. Kallon da take binsa da shi ne ya saka shi a ruɗani,domin kuwa kallo ne da ya kasa fassara abinda yake maƙale a cikin zuciyarta. Ba tare da ta ce masa ci kanka ba ta gegare shi ta fice daga ɗakinta riƙe da jakarta da makullin motarta. Cikin sauri ya bi bayanta suka hau sauka daga saman bene; bakinsa har rawa yake yi wajen tambayarta dalilin fitar ta da sassafe kuma cikin gaggawa. Tsayawa ta yi cak ta shaƙi iska sosai a huhunta kafin ta fesar ta ce.

"Fita a daidai wannan lokacin ta zame mini dole Aabii. Ban sani ba ashe ni ina can ina dukan taiki na bar jaki a gefe yana cin karansa babu babbaka. Amma daga yau zan gyara duk wani abu da ke neman lalace min. Sai na dawo."

Cike da ruɗani Aabid ya buɗe baki zai yi magana;Aabidah ta ɗaga hannunta tare da wurga masa kallon gargaɗi. Kan dole Aabid ya shanye maganarsa ya bi bayanta ya raka ta har jikin motarta yana yi mata ƙorafin ko karyawa bata tsaya ta yi ba. Ba tare da ta ce masa komai ba ta ja motarta mai gadi ya buɗe mata gate ta fita daga gidan. Ajiyar zuciya Aabid ya sauke mai ƙarfi sannan ya koma cikin gidansa yana safa da marwa,tin daren jiya yake jin wasu sauye-sauye a cikin jikinsa wanda ya rasa dalilin faruwarsu,sai dai kawai abinda ya sani shine ƙwaƙwalwa da zuciyarsa suna tuna masa wani abu mai matuƙar muhimmanci a rayuwarsa. Waje ya samu ya zauna a saman kujera tare da lumshe kyawawan idanuwansa. Hoton kyakkyawar fuskar da ya jima bai gani ba;kuma bai ji muryarta ba ce ta gilma a idanuwansa. Cikin sauri ya buɗe idanuwansa yana sauraron ƙarar bugun zuciyarsa da ya cika kunnuwansa. Muryarta ya ke ji tana ratsa cikin kunnuwansa kamar a wannan lokacin ne ta yi masa magiya da roƙon ya kula da maraicinta kada ya fitar da ita daga rayuwarsa. Cikin sauri ya miƙe tsaye ya hau sama da sauri. Kai tsaye makullin motarsa ya ɗauka ba tare da ya sauya kayan jikinsa ba ya fita daga gidan ya faɗa motarsa.

*Aabidah.*

Tun kafin ta isa gidan nasu take kiran Innaji wadda ta shirya cikin atamparta riga da zani da mayafi ta tsaya a bakin gate tana jiran isowar gudan jinin nata. Aabidah na tsayar da mota Innaji ta faɗa suka rankaya gidan Bokansu wanda suka bawa yarda da imaninsu gaba ɗaya. Su na zuwa suka tarar da shi zaune yana jiransu. Kuka Aabidah ta fashe da shi kamar ranta zai fita ta ce.

"Me yasa? Me yasa hannun agogo ke neman koma mana baya? A zato na ka gama kawar mana da matsalar Khadijatou har abada,me yasa Aabii ya ke tuna ta bayan tsawon lokacin nan da aka ɗauka? Ya kai Bokan da ke share min duk wani ɗigon hawayena da yake zuba ka sani idan har Dijah ta dawo cikin rayuwarmu tawa ta ƙare. Bana jin Aabii zai sake kallo na da gashi ballantana har ya bani soyayyarsa da kulawarsa. Na tsani kishiya,bana ƙaunarta,bana son duk wata mace da za ta raɓi mijina ko da kuwa mahaifiyarsa ce. Ya mai share min kukana ka yi wani abu akan wannan matsalar da ta ke neman hana rayuwata sukuni."

Wani irin gurnani Boka yayi sannan ya kafe kwaryar dake gabansa da ido,nan take ruwa ya cika ƙwaryar ba tare da su Aabidah sun ga lokacin da ake zuba ruwan ba. Cike da ƙwarewa a harkar tsafi boka ya yi siddabarun da ƙwaryar ta isa gaban su Aabidah da kanta. Cikin wata iriyar murya ya ce musu.

"Kalli nan ki gani. Wannan shine babban dalilin da ya sa aikin da muka yi miki ya warware. Kada ki manta maƙabartar da muka yi amfani da gawar cikinta mai kimanin shekaru ɗari a binne a cikin ƙasa tsohuwar maƙabarta ce. Wasu garuruwan sukan siyar da irin tsofaffin maƙabartun nan zuwa ga gwamnati ko wata ƙungiyar ko kuma wasu ɗaiɗaikun mutanen. Wannan dalilin ne ya sa aka samu wata ƙungiya mai zaman kanta da take gina makarantun islama da masallatai tare da gidajen marayu ta siyi maƙabarta ta gyara;ta gina Makarantar Islamiyya a wajen. Yawan karanta ƙur'ani da addu'o'in da ake yi a wajen ne yayi tasirin karya sihirin da duk wani boka ko matsafi yayi a cikin wannan maƙabartar ciki kuwa har da namu."

"Wayyoo ni Aabidah na shiga uku na lalace,shikenan Innaji rayuwata ta zo ƙarshe,na tabbata a yanzu ko Aabii bai rabu da ni ba to fa tabbas zai nemo wannan mayyar yarinyar ne a duk inda take."

"Ko kuma ta dawo da kanta ba. Kada ki manta da kanta ta bar gidan cikin tursasawa da kuma turen shaiɗanun aljanun da muka yi mata,kin ga kenan dawowarta gidan mijinta ko haɗuwarsu da komawar aurensu zai iya faruwa ta kowacce hanya."

A hasale Aabidah ta kalli Boka ta ce.

"Kenan kana nufin za ka bari su sake haɗuwa a waje ɗaya su ci gaba da rayuwa a inuwa ɗaya? Meye amfanin maƙudan kuɗaɗen da nake kashewa akan ayyukan da kake ikirarin kana yi min? Na ra...."

Wata iriyar shaƙa Aabidah ta ji an yi wa wuyanta kamar za a raba ta da numfashinta,Innaji na ganin haka ta zube guiwowinta a gaban Boka ta hau bashi haƙuri. Ransa a matuƙar ɓace ya sauko daga wajen da ya maƙale a sama ya na nuna Aabidah ya ce.

"Shi yasa na fi ƙaunar rayuwa da aljanu,domin su in dai za ka dinga yi musu abinda suke so za su yi maka hidima,kai ko da ba za ka musu abinda suke so ba matsawar za su ci su sha to fa za su iya zama tare da kai ba tare da sun yi maka butulci ba. Kin manta irin taimakon da na yi miki a baya? Kin manta irin tudu da gangaren da na ratsa saboda biyan buƙatarki? Me yasa ku bil'adama kuke da mantuwa da butulci?"

Wurgi yayi da Aabidah ta faɗi ƙasa ta buga kanta a jikin gini,kuka ta fashe da shi tare da zubewa a saman guiwowinta tana kuka tana bawa Boka haƙuri. Cike da matsanancin fushi ya ce.

"Ku tashi ku bani waje marasa godiya kawai,maza ku tashi kafin na sa aljanu su shanye min ƙafafuwanku."

Cikin sauri Innaji ta saɓi jakarta sannan ta ɗauki jakar Aabidah ta riƙe a hannunta. Mayafinta na zamewa kamar zai faɗi amma ko ta kansa bata bi ba ta kama Aabidah da gefen kanta ya kurje yayi fari tas ko ɗigon jini babu a wajen. A dudduƙe suka fita suna bawa Boka haƙuri. Cikin tsawa ya ce.

"Ku tafi ku jira har sai na neme ku da kai na. Ku da kanku kun sani da ni da ku duk akan ɓata muke,idan Allah Ya hukunta faruwar abu to fa dole sai ya faru. Dama ce kawai yake ara mana muke yin abinda muke so,dan haka ku tafi ku bani lokaci na yi bincike na samo mafita."

Da jin haka sai hankalin Aabidah ya kwanta. Godiya suka dinga yi wa bokan sannan suka tafi cike da tarin damuwa da tsamin jiki. Sun jima a cikin mota Aabidah na saka tissue ta na goge ciwonta da ya fara tsattsafo da wani ruwan azaba. Da ƙyar ta iya tada motarta suka bar gidan Bokan suka nufi cikin gari. Suna tafiya Boka ya hau bincike akan Aabid,nan ya gano yana daf da isa gidan Maheer,cikin sauri ya hau yin wani irin tsafi akan Aabid. Ya na gamawa ya shafe ruwan hoton Aabid ya ɓace.

*Aabid.*

Tinda ya baro gidansa yake tuna duk wata rayuwarsa da ta gabata kamar wanda aka kai cinema aka kunna wa video yake kallo. Wasu irin zafafan hawaye ke sauka daga kwarmin idanuwansa wanda suka sa har baya iya ganin gabansa. Bugun zuciyarsa da ya tsananta ne ya sanya shi samun waje a bakin titi ya tsayar da motarsa tare da kifa kansa a jikin sitiyarin motar. Hannu ɗaya ya saka a ƙirjinsa ya dafe saitin zuciyarsa dake barazanar tarwatse masa. Ya jima a haka kafin ya samu nutsuwa ta fara ziyartarsa. Cike da matsananciyar kewa tare da kawa zucin ganin mahaifiyarsa da mace mafi soyuwa a ransa ya tayar da motar ya nufi gidan Maheer,domin kuwa shi kaɗai ne wanda zai yi masa jagora domin dawo da faricikin rayuwarsa da ya rasa na tsawon shekaru. Yana isa ƙofar gidan Aabid ya tsayar da motarsa a bakin gate ɗin gidan ya taka ya hau ƙwanƙwasa ƙofar gidan. Yana nan tsaye ya ji wani irin faɗuwar gaba ta kama shi har sai da ya ji kamar jiri na ɗibansa,babu jimawa kansa ya sara masa da ƙarfi, kamar ɗaukewar wutar nepa haka ya nemi tunaninsa na baya ya rasa,nan take ya hau duba kayan jikinsa da wajen da yake tsaye. Cike da matsanancin mamaki ya juya da sauri ya shige motarsa,yana jin muryar Maheer na faɗin.

"Waye?"

Cikin sauri ya tada motarsa ya bar ƙofar gidan da mugun gudu. Ko da Maheer ya fito ya buɗe ƙofar gidan sai bai ga kowa ba,cike da mamakin wanda ya zo yana yi musu bugu kamar zai ɓalle gate ɗin gidan ya koma ciki. Kai tsaye sashen su Hajiya ya nufa ya tarar da Samhah na shanya zannuwan Hajiya a igiya. Murmushi ya sakar mata ya ce.

"Sannu Auta,Allah Ya yi miki albarka."

"Amin Yah Maheer;barka da safiya."

"Barka dai Auta,Ya jikin Hajiya? Ina fatan yau kun samu bacci sosai ko?"

"Eh Alhamdulillah tinda ta sha maganin nan jiya take bacci bata farka ba sai da asuba,ta na idar da sallah ko azkar bata ƙarasa ba bacci ya ɗauke ta."

"Masha Allah. Allah Ya ƙara mata lafiya,ke kuma Allah Ya ƙara baki juriyar ci gaba da kulawa da ita ba tare da gajiyawa ba."

Nan take muryar Salimah ta hau rawa,cike da matsananciyar damuwa ta ce.

"Kula da Hajiya ya zame mini dole Yah Maheer,kada ka manta bani da kowa bani da komai,ku ne gata na,kuma ku ne ahali na da nake gani na ji daɗi a raina."

Jinjina kai kawai Yah Maheer yayi ya wuce cikin sashen su cike da tausayin Samhah a cikin ransa.

*Aabidah.*

Kai tsaye gidan Innaji suka yi wa tsinke. Cike da damuwa Innaji ta ɗakko zuma ta shafa wa Aabidah a ciwonta da ke yi mata zogin azaba. Cikin tsananin damuwa Aabidah ta kau da kanta daga hannun Innaji dake lallaɓata tana bata haƙuri.

"Innaji kada ki damu da ciwon dake kai na,ina so ki mayar da hankali akan warkar min da ciwon dake cikin zuciyata. Innaji bana son Aabii ya rabu da ni,ina son sa ba zan iya ci gaba da rayuwa ba tare da shi ba a duniyar nan."

"Haba Aabidah ya kike magana irin wannan kamar an ce miki ko da Khadijatou ta dawo cikin rayuwar Aabid zai iya rayuwa babu ke? Ina son ki dinga tunawa da mun riga da mun kama Aabid kamu na har abada. Aabid ba zai taɓa ganin Khadijatou ba ballantana tarin sihirin da muka yi musu ya warware. Ke ina mai tabbatar maki da cewa ko da sun tuna da juna ba zamu taɓa yarda su haɗu ba;domin haɗuwarsu tafi tunawa da junansu hatsari a wajen mu."

Wani sabon kuka Aabidah ta rushe da shi sannan ta ce.

"Why me? Why meeee? Me yasa sai da nutsuwa da kwanciyar hankali ta same ni;ariziƙi na ya nunku,ina zaune da mijina lafiya wannan matsalolin za su kunno min kai? Ya Allah ka sake ara min dama ka nesanta Khadijatou da Mijina,Ya Allah ka sake raba tsakaninsu rabuwa ta har abada......

MUGUWAR MACE.

NA: HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️

*Za ku iya fara payment ɗin littafin MUGUWAR MACE da yake akan farashin 1k ta 9031416423,ku tura shaidar biya ta ***.*