MUGUWAR MACE

PAGE 9

by @1239900

Sai da Innaji ta nisa sannan ta miƙe tsaye ta mayar da zumar da ta ɗakko mazauninta. Cike da mutuwar jiki ta kalli Aabidah dake gunjin kuka ta ce.

"To yanzu ya za ki yi da maganar Boka da ya ce ki janyo wannan yaron Maheer jikinki?"

A hasale Aabidah ta ce.

"Wai ke Innaji me yasa wani lokacin sai ki dinga yin magana ba kya tunani ne? Ni yanzu ina ruwana da wani Maheer? Ai sawun giwa ya take na raƙumi Innaji, yanzu babbar damuwa ta a duniya bata wuce na san inda Khadijatou take ba,ina so na nemo ta da kaina kafin Aabii ya ganta. Ina so na kashe ta har lahira kowa ma ya huta. Wannan karon ba zan yi kuskure ba wajen aikata inda ba za ta dawo cikin rayuwarmu ba har abada."

"Da ace Ɗan Amanarki yana nan har yanzu da ko a mafarki ne kin aika shi ya bemo mana inda Khadijatou take,ko a raye ko amace."

Labule Jauharah ta buɗe ta na kallon su Aabidah. A razane Aabidah ta kai dubanta wajen da ta ji motsi,ido huɗu suka yi da Jauharah da ke a buge sai lumshe idanuwa take yi kamar mai jin bacci. Tsaki Aabidah ta ja mai ƙarfi ta kalli Innaji ta ce.

"Yaushe wannan yarinyar ta dawo gida daga yawon dandin da ta tafi?"

Hannu Innaji ta ware tana kyaɓe baki ta ce.

"Yanda kika ganta haka na ganta,dan ba a gidan nan ta kwana ba. Ai ita da wancan da'un ba za ki taɓa sanin lokacin shigarsu ba ballantana fitar su. Ke! yaushe kika dawo gidan?"

Cikin tafiyar ƴan maye Jauharah ta isa kujera mafi kusa da ita ta zauna tana lumshe idanuwa. Cikin muryarta mai kama da ta matan da suka tsufa suna busa sigari ta ce.

"Yanzu Mine ta ajiye ni ta tafi. Babbar Yayaaa na ji kina wata magana akan waccan mujiyar, a ina take na aika yara a kawar miki da ita cikin sirri? Kin san yanda kike bani farinciki dole ne nima na rama wa kura a niyarta."

Tsaki Aabidah ta ja mai tsawo kafin ta ce.

"A hakan ne za ki yi min abinda zan mora Jauharah? Allah ya wadaran rayuwar da kika jefa kanki a ciki. Ke kan ki baki taimaki kanki ba ballantana ki taimake ni. Na kashe kuɗaɗena a banza akan ku,na ɓata lokaci na da energy na duk akan ku,daga ƙarshe kun zamo marasa amfani. Tashi ki bar nan kafin na huce takaicin dake cikin raina akan ki."

Tsuke baki Jauharah ta yi ta tashi tana tangaɗi ta shige ɗakinta ta rufe ƙofa. Tsaki Aabidah ta ja ta dafe kanta tana ci gaba da kukanta wanda take jin sanyi a ranta a duk saukar hawaye ɗaya daga idanuwanta. A wannan rana a gidansu ta kai azahar saboda tsoron kada ta koma gida Aabid ya sake bijiro da zancen Khadijatou ba ta jin zuciyarta za ta iya ɗaukan jin kalmar sunan babbar maƙiyyarta a bakin mutumin da ta fi so sama da kowa a rayuwarta. A duk bugawar sa'a ta agogo sai gaban Aabidah ya faɗi. Ta kasa ci ta kasa sha saboda damuwa da zullumi. Innaji kuwa Laure ta sa ta dafa mata abinci mai rai da lafiya da naman kaza ta ci ta ƙoshi ta kora da lemo. Ganin yanda Innaji ke warkajaminta ba tare da jimamin halin da Aabidah ke ciki bane ya sanya Aabidahn ɗaukan makullin motarta da mayafinta ta shuri takalmanta babu ko sallama ta bar gidan. Kai tsaye gidan ƙawarta kuma aminiyar cin mushenta ta nufa. Tin daga bakin gate mai gadi ya san yau Hajiya Aabidah bata cikin hayyacinta;duba da irin tuƙin da take yi. A gaggauce ta kashe motarta ta buɗe ta shiga gidan Hajiya Zaitunah. Zaune ta ga Hajiyan ita da yaranta suna kallo. Kallo ɗaya yaran suka yi wa Aabidah suka kawar da kawunansu suka ci gaba da kallon su, yara ne da aka sangarta suke jin kansu,dan haka ko gaisuwa bata haɗa su da kowa sai wanda suka ga dama. Ganin irin halin da Aabidah ke ciki ne ya sanya Hajiya Zaitunah wadda ta girmi Aabidah da shekaru takwas a duniya miƙe wa ta bi bayanta zuwa ɗakinta. Su na shiga Aabidah ta zauna a bakin gado ta rushe da kuka. Cike da matsananciyar damuwa Hajiya Zaitunah ta dafa bayan Aabidah ta ce.

"Ah ah Ƙawata lafiya kike irin wannan kukan? Me ya samu Aabii ɗin naki? Ina fatan dai ba sakin...."

"Allah Ya kiyaye Aabii ya sake ni. Ai ni da shi mutuwa ce za ta raba mu,walau ya binne ni ko kuma ni na binne shi. Ƙawata matsala ce mai girma ta taso min wadda muka jima da haƙa rami mai zurfi muka binne. Sai kuma gashi ta ɓullo a lokacin da bamu yi zato ko tsammani ba."

Waro ido Hajiya Zaitunah ta yi tare da dafe ƙirji ta ce.

"Kar dai ki ce min wannan mayyar ta dawo cikin rayuwarku?"

"Wai ke me yasa ba kya faɗan alkhairi ne? In dai boka na raye na yi imanin Khadijatou ba za ta taɓa dawowa cikin rayuwarmu ba."

"To meye zai ɗaga miki hankali haka bayan kin san ba dawowa za ta yi ba? Ko dai kema kin fara fuskantar irin matsalar da nake fuskanta ne?"

Ajiyar zuciya Aabidah ta sauke tare da goge majinar da ke shirin gangarowa a hancinta da tissue ɗin dake gefen gadon Hajiya Zaitunah. Cike da damuwa ta labarta wa ƙawar tata abinda ke faruwa. Salati Hajiya Zaitunah ta yi sannan ta ce.

"To ai wannan maganar taki daidai take da dawowar Khadijatou cikin rayuwarku Aabidah. Abu ne fa da muka riga muka sani amma muke take sanin,shi asiri lokaci ne da shi komai daɗewarsa a jikin bawa. Idan har kika ga bai karye ba to fa mutumin da aka yi wa asirin ya mutu,ballantana Khadijatoun da na sani mai taurin rai ce da kafiya,kada fa ki manta abubuwan da muka ƙulla mata  a baya. Dan haka ni dai shawarar da zan baki shine,ki koma wajen Boka ya sake maimaita sihirin da aka yi a can baya,ni kuma na yi miki alƙawarin raka ki duk inda kika sanya ƙafa.."

Hawaye ne suka zubo wa Aabidah a karo na babu adadi. Muryarta na rawa ta ce.

"Wannan lissafin naki duk ba mai yuwa bane inji Boka. Domin kuwa da faɗa ma muka rabu,dubi nan ɗina,shi ne ya shaƙe ni ya buga da jikin gini har sai da wajen ya kwaile."

"Da dikkan alamu hannunsa ya fara yin sanyi gaskiya shi yasa lamuranmu ke ta taɓarɓarewa. Yanzu ina so ki shirya zuwa jibi zan kai ki wajen wani sabon boka da na ji labari wajen su Zinariya dan ni ma ina buƙatar a sabunta min aikina,gaba ɗaya cikin kwanakin nan bana gane kan Dad...."

Da ƙarfi aka buɗe murfin ƙofar ɗakin da su Aabidah ke ciki. Wani ƙaƙƙarfan mutum ne ya shiga ya tsaya a bakin ƙofa yana kallon su cikin tsananin ɓacin rai. Hannu ya ɗaga yana nuna Aabidah da ta yi sororo tana kallon yanda jikin Hajiya Zaitunah ke rawa. Kallon mutumin Aabida ta sake yi wanda a baya suke sakawa aiki har da ɗebo musu ruwan sha ta ga yanda yake huci kamar wani zaki,nan da nan jikinta yayi sanyi ta miƙe ta saɓa jakarta a kafaɗa ta bar ɗakin. Kai tsaye motarta ta nufa ta faɗa tana sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi kamar wadda ta yi tseren gudu. Tana tada motar ta mai gadi ya wangale mata gate ta bar gidan a guje. A hanya babu abinda take tunawa da ya wuce sauyin da ta gani a gidan Hajiya Zaitunah. Nan take tsoro da fargabar dake cikin ranta suka nunku. Murya na rawa ta ce.

"Shin me yake faruwa a rayuwarmu ne? Lallai dole ne na samarwa kaina mafita,domin kuwa ba zan taɓa yarda Aabii ya dawo cikin hayyacinsa ba kamar yanda mijin Hajiya Zee ya dawo cikin hayyacinsa."

Tana isa gida ta hau dannawa mai gadi horn,da gudu ya ajiye abincin da yake ci ya buɗe mata gate yana yi mata sannu da dawowa. Ko ta kansa Aabidah bata bi ba ta ajiye motarta ta kalli motar Aabid da ya yi mata wani irin mugun parking. Jiki a mace ta shige cikin gidan tana ɗari-ɗari dan bata san me za ta tarar a ciki ba. Ta na murɗa ƙofar shiga parlourn ƙasa ta ci karo da wajen kamar yanda ta barshi,sai ma takalmin Aabid da ke yashe a tsakiyar parlourn kamar wanda ya yadda shi da gayya. A hankali ta ci gaba da takawa har ta haura sama,kai tsaye ɗakinta ta nufa ta watsa ruwa kafin ta tsantsara kwalliya cikin ƙananan kayan da Aabid ke mutuwar so. Ɗakinsa ta shiga ta tarar da fitilar a kashe;sai dim light da ya kunna,karatun ƙur'anin da aka yi shekara da shekaru ba a saurara ko karanta ba a cikin gidan ke tashi a wayarsa. Kwance yake ya na kallon sama da idanuwansa da suka kaɗa suka yi jawur. Babban abinda ke damunsa shine cushewar tunani da rikicewar ƙwaƙwalwa,sai wani irin matsanancin ciwon kai da faɗuwar gaba da yake ji. Ƙamshin jikin Aabidah ne ya sanya shi lumshe idanuwansa hawayen dake kwance a cikinsu suka gangara gefen idonsa suka yi wa kansu masauki a kunnuwansa. Ba tare da ya damu da share wa ba ya sauke jajayen idanuwansa a saman fuskar Aabidah dake zaune a gefensa ta kasa furta komai saboda tsananin tsoron abinda zai je ya zo. Jin ta take yi kamar wata baƙuwa ko wata sabuwar halitta. Hannu Aabid ya miƙa mata cike da kulawa,ta na ganin haka ta isa gare shi da sauri ta kwanta a jikinsa tana mai rushewa da kuka. Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi ya hau shafa bayanta da sigar lallashi. Duk yanda ya so ya buɗe baki yayi mata magana ya kasa. A haka Aabidah ta samu baccin da bata yi ba ya ɗauke ta cike da mugayen mafarkan da ta dinga fatan ta farka ta buɗe ido dan ta dena ganinsu,amma inaaa gaba ɗaya duniyar mummunan mafarki ta yi mata ƙawanya.

Haka rayuwar gidan Aabid ta koma cike da shiru da tsoro tare da fargaba,ɗimuwa da kuma damuwa. Gaba ɗaya ya dena fara'a,ya dena duk wasu ayyukan da yake yi mata a baya,ko kamfaninsa ya dena fita,lokuta da dama yana ganin kira daga kamfanin zai ƙi ɗagawa har ya katse. Sanin cewa asirin da ta yi masa yana ta barin jikinsa a hankali shi yasa ko da wasa bata yi masa tsawa ko hantararsa ballanta ta saka shi yayi mata wani aiki,tana ji tana gani zai kunna karatun ƙur'ani bata da halin kashewa. A haka Aabidah ke lallaɓawa ta yi musu girkin da suke kasa ci daga ƙarshe sai dai ta kai wa mai gadi,shi kuwa mai gadi sai ya tsince naman ya cinye ya zuba wa karen maƙota abincin. Bayan kwana biyu Aabid ya tashi yana jinsa kamar sabon mutum,kewar Hajiyansa da ƴar'uwarsa ce ta mamaye zuciyarsa dan haka sai ya shirya tsaf cikin shaddarsa gezna ya saka hularsa sabuwa dal da takalmi mai tsada da ya dace da kayan jikinsa. Aabidah na ganinsa da irin wannan shigar hankalinta ya tashi,cikin kissa da kisisina ta dinga bugun cikinsa dan ta ji inda zai je,amma Aabid ya yi shiru bai bata amsa ba. Cike da shagwaɓa Aabidah ta kwantar da kanta a jikinsa ta ce.

"Wai ni Aabii laifin me na aikata maka ne a cikin gidan nan da ka dena yin hira dani,ka dena kula ni a matsayina na matarka ta sunna,kullum haka za mu kwanta mu tashi da kai  ba tare da wani abu ya shiga tsakaninmu ba,idan na yi maka girki sai dai ka ce a zubar ka yi order a waje ka ci. Ko dai ka dena so na ne Aabii?"

Ta ƙarashe maganarta cike da zubar hawaye da ƙuncin zuciya. Numfashi mai tsawo Aabid ya ja kafin ya fesar ya samu waje ya zaunar da su a kujera. Fuskarta ya ɗaga yana share mata hawayenta kafin ya buɗe baki kamar mai jin tsoron yin magana ya ce.

"Ni kai na ban san me yake damu na ba a cikin kwanakin nan Baby....lokuta da dama sai in dinga jin ƙirjina,kai na da zuciyata suna yi min nauyi.... Aabidah ina ji a jikina akwai wani abu da na rasa mai muhimmanci a rayuwata. Jikina yana bani akwai wani abu da nake so ko yake jirana ko kuma...i just don't know what is happening to me. Ki yi haƙuri da duk wani sauyi da kike gani a waje na,da yardar Allah komai zai dawo kamar yanda yake tun fil azal."

"In Allah Ya yarda babu abinda zai dawo kamar yanda yake tun fil azal...."

Aabidah ta yi suɓucewar baki ta faɗa da ƙarfi. Cikin sauri Aabid ya kalle ta yana mamakin furucinta. Da sauri ta wayance ta hau ƙirƙirar abubuwan da take ganin za su ɗauke masa hankali,sai dai cike da rashin samun nasara Aabid ya kewayeta ya fita daga ɗakin. Kanta ta dafe ta saki ƙara a hankali kafin ta mari kuncinta ta ce.

"Da dikkan alamu idan Boka bai gaggauta samar min mafita a wannan lamarin nawa ba zan haukace saboda damuwa."

*Aabid.*

Ya jima yana maimaita kalaman Aabidah a cikin ransa,amma ya gaza gane inda addu'arta ta dosa. A haka ya dinga tuƙi ya na ratsa gidaje da tituna har ya isa ƙofar gidan mahaifinsa. Ya na zuwa ya ga an sabunta fentin gidan tare da yin shuke-shuke a wuraren da aka bari domin shuka. Murmushi ya saki domin yana da yaƙinin babu mai yin wannan aikin sai Maheer. Wata iriyar kewar Maheer ce ta mamaye shi,sai yake jin kamar ya ɗauki wasu shekaru masu tsawo bai gansa ba. Kai tsaye ya dirfafi gate ɗin gidan da zummar shiga ciki. Sai dai ganin wani mutum sanye da kakin soja a jikinsa ne ya sanya shi tsaya wa yana kallonsa cike da neman ƙarin bayani. Shi ma mutumin kallon Aabid ya ke yi tare da faɗin.

"Kai ina za ka je ne kake ƙoƙarin wuce wa ciki ba tare da neman izini ba?"

Wata kafirar harara Aabid ya banka wa sojan sannan ya ce.

"Gidan uban nawa ne zan nemi izininka dan zan shige shi? Kai ɗin waye?"

Murmushi sojan yayi dan ya fuskanci Aabid bai san cewa an siyar da gidan ba. Dan haka cikin ƙanƙanin lokaci ya bayyana masa cewar ai gidan an siyarwa da ogansa ne;a cikin satin ma suka tare. Baki Aabid ya saki yana mamakin wanda zai siyar da gidansu na gado ba tare da izininsa ba. Gefe ya koma ya zaro wayarsa ya danna kiran Maheer. Ta jima sosai tana ringing tare da katse wa ba a amsa shi ba,shi kuwa Aabid ba tare da gajiya wa ba ya sake kira. A haka har dai Maheer ya gaji da nacin Aabid ya ɗaga wayar a hasale ya ce.

'Wai don Allah wannan wanne irin kira kake yi min ne Aabid?'

Da sauri Aabid ya sauke wayar daga kunnensa ya kalli wayar sannan ya mayar da ita kunnensa ya ce.

"Maheer ni ne fa Aabid."

'Sai aka yi yaya dan kai ne Aabid?'

Cike da mamakin sauyawar halayyar Maheer Aabid ya ce.

"Ohhh yanzu na gane komai,dama kai ne ka zuga Mahreen ta siyar mana da gidanmu na gado kenan ko? Dama za ka iya cin amanar zumuncin dake a tsakaninmu Maheer?"

Cike da ƙunar rai Maheer ya ce.

'Excuse me? Me kake nufi da na zuga Mahreen ta siyar muku da gidanku na gado? Ohhh ! Ohhh ta nan kuma ka biyo Aabid? Duk ka manta rashin mutunci da wulaƙancin da ka aikata kenan? Aabid wai kana ma ina ne yanzu haka?'

"Ina ƙofar gidanmu a da;wanda ka shiga ka fita ka siyar da shi. Maheer ka sani ba zan taɓa barin wannan cin amanar ya tafi a banza ba."

Aabid na gama magana ya kashe wayarsa ya shige motarsa ransa a matuƙar ɓace ya nufi hanyar gidansa. A ɓangaren Maheer kuwa ya jima yana nazarin abinda ya faru a tsakaninsa da Aabid kafin ya sanya goshinsa a ƙasa ya yi wa Allah sujjada tare da miƙa godiyarsa a wajen Allah. Ba tare da tunanin duhun dare da ya fara shiga ba Maheer ya shirya yana cike da matsanancin farinciki ya bar gida........

MUGUWAR MACE.

NA: HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️