PAGE 2
by @1239900
Kasa furta komai ta yi a cikin sujjadarta saboda bata da sauran kalaman da suka rage wanda bata roƙi Allah da su ba. A cikin zuciyarta ma bata iya ayyana komai ba,domin gani take yi idan ta roƙi Allah akan zamantakewarta da Abbas za ta yi saɓo. Ta jima ta na kuka kafin ta ɗaga ta ci gaba da yin sallar,ta na idarwa ta fara yin azkar,bacci ne mai daɗi ya ɗauketa a wajen. Ta na nan kwance ta na bacci Barirah ta fita tsakar gidan ta hau sharewa har cikin kitchen ɗin Fauziyyah. Kasancewar gidan na Abbas ne haya suke yi a ciki sai ya zamana kitchen ɗin Fauziyyah shine asalin ginin bulo da siminti,na Barirah kuwa Shehu ne ya nemi izinin Abbas ɗin ya yi mata shi da katako da langalanga,aka buga masa kanta tare da saka tayal a ƙasa sai ya dawo sak irin na Fauziyya. Kashe kuɗin da Abbas ya yi wajen ginin gidan shi ne dalilin da ya sa yake sanya mata ido sosai dan ganin ta tsaftace gidan a koda yaushe gudun kar ta lalata masa wahalarsa. Barirah na kammala shara ta haɗe kwanukansu ta wanke musu tas,sannan ta leƙa ta samo mai ruwa ya cika ko ina ta biya sa kuɗinsa ya tafi. Ganin ta rage wa Fauziyyah ayyukanta ne ya sanya ta shiga ɗaki ta duba wayarta,gani ta yi sha ɗaya na rana ta yi,gashi ranar Juma'a ce Abbas da wuri yake dawowa,cikin sauri ta isa ɗakin Fauziyya da niyyar tashinta dan ta ɗora abincin rana. Ta na shiga ta ganta kwance ta na ta sharar bacci har da munsharinta,da dikkan alamu baccin ya yi mata daɗi. Cike da tausayawa ta duƙa ta hau taɓa ƙafafun Fauziyyar a hankali ta na kiran sunan ta. Sannu a hankali take buɗe idanuwanta har ta sauke su a saman fuskar Barirah,bakinta ta share wanda yawun bacci ya ke kwaranya tsabar daɗin da baccin ya yi mata ta na lumshe ido,fuskarta ɗauke da murmushi ta ce.
"Na dame ki da munshari ko Aunty? Kwana biyu My king na faɗa sosai akan hakan,wai idan ina bacci komawa nake yi kamar rago."
Wani baƙin ciki ne ya tokare wa Barirah wuya,dan ganin yanda take bayyana mijinta na aure yana danganta ta da rago kuma tana bada labari har tana dariya,cikin haɗe fuska Barirah ta ce.
"To ni ba wannan ne ya kawo ni ba,ki tashi ki samarwa ɗan jarabar naki abinci,idan kuma babu ne tin wuri ki sanar dani."
Murmushi Fauziyyah ta sake yi,domin tinda ta ci kukanta a sallah ta yi bacci,sai ta tashi zuciyarta wasai babu wani sauran ƙunci. Cikin muryarta mai sanyi da daɗin sauraro ta ce.
"Akwai abinda zan dafa mana Aunty,na gode Allah Ya bar zumunci."
Miƙewa Barirah ta yi ta na amsa addu'ar da Fauziyyah ta yi mata ta wuce nata ɗakin,domin ita nata mijin sai yamma yake dawowa,ɗan kasuwa ne a kwari ya na siyar da kayan shafe-shafe na mata,har haɗa na sakawa lefe yake yi.
Fitar Barirah ke da wuya Fauziyyah ta dafa ƙasa ta tashi da ƙyar ta hau gyaran ɗakin,duk da cewa ba wani datti ya yi ba,amma idanuwan Abbas kamar na mayen dake gani har hanji suke,duk inda datti yake ko da ƙura ce idan ya gani sai ya yi faɗa,haka zalika idan abu aka ajiye a inda bai dace ba komai ƙanƙantar abun nan ya gani sai ya yi masifa,wani lokacin ma har hannu yake kai mata. Ta na kammala gyara ɗakinta da parlour sai ta fito hannunta riƙe da ɗankwalinta ta wuce kitchen ta na ɗaurawa a saman kanta. Waken da ya rage musu ta ɗakko,wanda ko kofi biyu be kai ba,tsincewa ta yi ta wanke ta shiga kitchen ɗin Barirah kamar yanda ta yi mata izinin duk sanda za ta yi girki Abbas baya nan ta dinga amfani da gas ɗinta,cikin sauri ta zuba waken a tukunya ta zuba ruwa ta saka gishiri kaɗan ta jefa kanwa ta rufe. Waje ta koma ta shiga kitchen ɗinta ta ɗakko wani ragowar barkonon da take da shi da maggi biyu da ya rage sai uban gishiri da ya siyo leda baƙa guda dan ganin arharsa. Ɗiba ta yi ta hau dakawa,sai da ya daku ya yi luƙui sannan ta kwashe. Ci gaba da aikace-aikace ta yi har waken ya dahu ya yi laushi tuɓus ya farfashe. Manja ta soya da albasar Barirah sannan ta samu mazubi mai kyau da take zuba masa abinci a ciki ta kai kitchen ɗinta ta rufe. Godiya ta leƙa ta yi wa Barirah wadda idan da sabo ta saba,shi yasa kawai bata amsa ta ba sai ta tambaye ta ko akwai wani abu da take so? Girgiza kai Fauziyyah ta yi tare da cewa.
"Bana buƙatar komai Aunty na gode Allah Ya jiƙan magabata."
"Amin Fauziyyah."
Cikin gaggawa Fauziyya ta shiga ɗakinta ta cire kayanta ta fito da wanda Abbas ya cire kafin ya fita,wanki ta tsugunna ta yi ta ɗauraye su ta shanya,ta na gamawa ta ɗebi ruwa ba tare da ta koma ta sanya hijabin da zai rufe mata jiki ba ta faɗa wanka. Ta jima tana dirzar fatarta kafin ta fito. Ruwan dake jikinta ne ya bawa zanin jikinta damar mannewa a manyan mazaunanta da ke ɗauke da cinyoyi manya,gashin kanta mai yalwar tsawo da cika ta ɗaure shi a bayanta har ruwa ya taɓa shi yana ɗiga,wasu daga cikin gashin nata ne suka manne a dokin wuyanta da gefen fuskarta,farar fatarta mai ɗaukan hankali sai sheƙi take yi,gashin fuskarta duk ya kwanta gwanin burge mai kallo. A haka ta duƙa ta yi alwala sannan ta miƙe dan komawa ɗaki. Kamar daga sama aka wurgo su babu sallama sai hayaniya da darerekunsu. Wata iriyar faɗuwa gaban Fauziyyah ya yi,nan take ta gane wautar da ta tafka na rashin sanya hijabi dan suturce jikinta. Nasihar da Barirah ke yawan yi mata ce ta faɗo mata a rai.
'Fauziyyah ina mamakin yanda kike zama ki saki jikin ki a waje,bayan kin san kina da sura mai ɗaukan hankalin mace ƴar'uwa ki ma ballantana namiji wanda dama mace ce abokiyar jin daɗin rayuwarsa. Ko baki san cewa duk shaƙuwa da zaman da mukai dake ba be kamata ace Shehu na ganin jikin ki ba? Kar ki ɗauka wai kishi nake yi da ke,ah ah gaskiya nake faɗa miki. Matsalar mu hausawa muna ɗaukan zama babu hijabi har wani wanda ba muharramin mu ba ya ga surar jikin mu ba a bakin komai ba,musamman yaran maƙota da mijin maƙota,sai mu dinga ganin ai an saba,ko kuma haya muke yi to ya zamu yi ai dole a gauraye.'
A nutse Fauziyyah ta ce.
'Aunty shi ne ke hana ni saka hijabi ko mayafi,wai a cewarsa yana alfahari da kyauna,yana so duniya ta san wace iriyar mace ya aura.'
'Lallai kuwa zai kai ki wuta idan baki gyara ba,domin za a wayi gari tin kina son suturce jikin ki da kan ki,kema zaki saba da zama babu suturar arziƙi.'
Lallai wannan lokacin Barirah ke jiyewa Fauziyyah zuwansa,gashi har ta saba da rashin rufe jikinta. Sauri ta sanya za ta gudu ɗaki don ta rufe jikinta. Abbas ya dubi abokansa ya ga yanda suke bin mazaunan Fauziyyah da kallo cike da kwaɗayi da burgewa. Murmushin jin daɗi ya yi sannan ya haɗe fuska ya kalle ta,cike da isa da taƙama ya ce.
"Ki na saka ɗaya ƙafar a ɗaki zaki gamu da ni. Oya maza wuce ki ɗakko waccan tabarmar ki shimfiɗa mana sannan ki kawo wa mutane abinci."
Babu yanda ta iya haka ta juya kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki gudun kar ta yi dogon motsi jikinta ya juya. Sai dai duk da yanda take taka tsantsan hakan bai hana jikin nata juyawa ba,ganin yanda take tafiya bata kaɗa jikinta yanda ta saba ne ya sanya Abbas sake daka mata tsawa ya na faɗin.
"Dalla Malama ki kama jiki ki ɗakkowa mutane wajen zama,shashasha kawai wadda bata san yanda za ta tarbi miji ba idan ya dawo daga wahalar nema mata abinda za ta ci."
Cikin hanzari ta wuce ta ɗakko tabarmar da ta ji jiki,sai dai a wanke take tsaf babu datti,ta shimfiɗa musu. Juyawar nan da za ta yi ta shiga ɗaki zaninta ya kusan kuncewa,da sauri ta kama zanin ta faɗa ɗaki,ta na jin Abbas na masifa ya na faɗin.
"To yanzu Fauziyyah abincin ma sai na roƙa ki kawo mana? Kin san Allah ki dena saka ni yawan magana bana so,idan kuma kika bari na sake yi miki magana na lahira sai ya fiki jin daɗi."
Wani irin dogon tsaki Barirah ta ja a daidai lokacin da take fitowa daga ɗakinta za ta yi alwala,ido suka haɗa da Abbas da abokansa ta kuwa daka musu harara tare da faɗin.
"Me na ci ban bawa mutum ba ake ƙure ni da mugun kallo? Allah dai ya kai mutum lahirar nan ya banbance mana jin daɗin duniyar da na ƙiyama,aikin banza kawai,namiji har namiji amma basirarsa ta kare wajen musgunawa mace mai rauni."
Kallon Abbas abokansa suka yi,wani da ake kira da Salman ne ya ce.
"Tab ! Lallai matar nan ta ci ta ƙoshi,haya fa take a gidanka amma take iya faɗa maka maganganu yanda ranta ke so baka yanka musu tikitin barin gidanka ba."
Abbas bai ce komai ba har sai da Barirah ta shige banɗaki sannan ya yi ƙasa da murya ya ce.
"Idan na kore su ai kaina na cuta,ni kaɗai na san irin amfanin da zaman su yake yi min a cikin gidan nan. Sannan kuma wannan matar da kake gani ta riga ta shanye mijin,kana taɓa ta ko ka faɗa mata baƙar magana ubanka zai ci,ka dai ganta daf da ƙasa ba ta da wani kyan arziƙi,to a wajensa Fauziyyahta mummuna ce."
Nan da nan suka hau musanta kalamansa akan Fauziyyah suka ɗora da yabon shape ɗinta da surar ta tare da muryarta,Fauziyya na ɗaki ta na saka wata jemammiyar doguwar rigarta da ta ji jiki tin ta lefen ta,gashi yanzu auren su ya doshi shekara uku da rabi, ɗankwalin rigar ta ɗaura tare da rufe gashin kanta ta can ƙarshe,hakan sai ya bawa gaban kan nata bayyana kamar tana sane ta yi hakan. Takaicin hirar ta da Abbas yake yi wa abokansa ce ta sanya ta zama a bakin gado ta zabga tagumi,me yasa Abbas yake yi mata haka? Me yasa ba ya iya riƙe sirrin auratayyar su har sai ya sanar da abokansa hankalinsa ke kwanciya? Me yasa kuma baya tashi yabon ta sai abokan sun zo gidan? Meye amfanin yabon da yake yi mata a wajen mutane amma ita ko sau ɗaya bai taɓa yaba ƙoƙarinta ko bajintar da ta yi masa ba? Kiran sunanta da ta jiyo Abbas ya yi a ƙufule ne ya dawo da ita hayyacinta ta miƙe da sauri ta nufi kitchen. A jikinta take jin yanda idanuwansu ke kallon saƙo da lungu na jikinta. Ƙwalla ce ta taru a idanunta,a haka ta duƙa ta ɗakko abincin ta ɗora a babban faranti ta zuba ruwan randa a jug dan tini ya siyar mata da fridge da deep freezer ɗinta manya,wai babu wajen ajiye su,duk lokacin da suka yi gidan da ya fi wannan girma zai siya mata.
Cikin takunta mai cike da natsuwa ta ƙarasa gaban su ta durƙusa ta ajiye abincin,gaishe su ta yi kanta a ƙasa suka amsa sannan ta dafa gini ta miƙe ta koma ɗaki. Ta na shiga Rabi'u ya ce.
"A gaskiya Abbas duk cikin mu kai kaɗai ne ka yi dacen macen nuna wa duniya ba ma sa'a ba kaɗai,ka ga mace kamar ka sace ta ka gudu?."
Dariya suka saka Abbas kuwa ya na jin kansa kamar ya fashe dan girma,Salman ne ya ce.
"Allah sarki Babangida,yanzu da yana nan fa da ya ce,wannan abun da kuke yi haramun ne,Allah ya haramta,kai kuma ka zauna kamar mara kishin iyalinsa wasu na yabon matarka,ni duk wanda ya yaba surar mata ta ba sai na zare takobi na fille wa jahili kai ba."
Dariya suka bushe da ita suka tafa,cikin shaƙiyanci Abbas ya ce.
"Ahhh shikenan Babangida ya tafi,ta wanke ta bashi ya kurɓe."
Salman yana dariya ya hau daidaita fuskarsa ya na kwaikwayar Babangida da baya wajen ya ce.
"Ah ka manta ni na sha abuna a haka? Ai bata wanke ba ta sirka da wani abu, concentrate na sha. Ku fa gani kuke yi yiwa matayen ku mugun hali da musgunawa shi ne yake riƙe muku su ko? Ku sani soyayya ce ke riƙe da su kawai da biyayyar aure,ina jiye muku lokacin da zaku kai su bango su juyo kan ku da tasu kalar azabar ba za ku ji daɗi ba."
Dariya suka sake bushewa da ita,cikin isa da izza Abbas ya ce.
"Ni mace ta isa ta juya ni? Kuna gani fa ana zaune wannan ƙwailar tasa za ta kira shi a waya,jiki na rawa yake tafiya,ni yanzu da nake da mace kamar Fauziyya ta isa ma ta min haka? Kun dai ganta kun shaida yanda take da kyau da duk wani abu da namiji zai nema a wajen mace,amma bata isa ina faɗa tana faɗa ba,ballantana mu yi sa'insa ko ta saɓa umarnina."
Dariya suka kece da ita Rabi'u ya daki kafaɗarsa ya ce.
"Shegen sama,ai nake faɗa maka abokina kai kam ka gama dacewa a duniya,saura ƙiyamar ka kawai. Ka samu mai siffofin hurul'ini tin a duniya."
Buɗe kwanon abincin Abbas ya yi da niyyar su ci idanuwansa suka sauka akan dafaffen waken da ya ji manja da yaji,nan take yawun bakin su ya tsinke,kasancewar abincin manja ya gaji haka. Sai dai girman kai da mugunta irin ta Abbas ta sanya shi rufe kwanon ya na muzurai,sai da ya haɗiye yawun da ya cika masa baki ya daidaita natsuwarsa sannan ya ce........ [12/9, 8:37 PM] HAERMEEBRAERH: MUGUN MIJI.
RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨