PAGE 3
by @1239900
"Ke zo nan!"
Jiki na rawa Fauziyyah ta miƙe za ta fita,ta na ayyanawa a ranta.
'Na shiga uku ni Fauziyyah me kuma na yi?'
Mamakin yanda har ta ji kiransa ta amsa ne ya kama Salman,cikin yin ƙasa da murya ya ce.
"Wai kana nufin wannan kiran da ka yi mata har ta ji ta amsa kuma ta na nan tafe? Gaskiya abokina kai bala'i ne."
Murmushin mugunta Abbas ya saki sannan ya ce.
"Kar ma ta amsa mana. Ai matsawar ina cikin gidan nan to fa kunnuwanta da zuciyarta a buɗe suke,ta yanda ko da motsi na yi ta san me nake buƙata kafin na furta,kuskure ɗaya za ta yi wajen ƙin fahimtar magana ko motsina jikin jakar ya faɗa mata."
Kalmar jaka da ya kira ta da shi a gaban abokansa ce ta daki zuciyarta,cikin ƙunar rai ta durƙusa a gabansa cike da ladabi ta ce.
"My king gani. Ku na buƙatar wani abun ne?"
Haɗe rai Abbas ya yi ya nuna Fauziyyah da yatsansa manuni, cike da wulaƙanci da izza da isa ya ce mata.
"Ke dan Uban ki wace iriyar shashasha ce? Yanzu ace na fita rana da zafi inuwa da damina na nemo abinda za a ci a gidan nan,amma na kawo baƙina ki haɗa mu da zallan dafaffen wake har da wani manja da yaji a ciki? To ina laifin ma ki dafa wake da shinkafa?"
Zuciyarta na tuƙuƙin baƙin cikin zagar mata mahaifi da ya yi a gaban abokansa,ta daure tare da jurewa kar ya gano halin da take ciki ta ja wa kanta mari ko jibgar wulaƙanci ta ce.
"My king ka yi haƙuri don Allah, nima shinkafa da waken na yi niyyar dafawa sai kuma na tarar da shinkafar ta ƙare shi yasa na yi amfani da iya abinda muke da shi kawai na dafa dan kar ka dawo babu abinci."
Cike da ɓacin ran tona masa asirin bashi da ƙwayar shinkafa a gidansa da ta yi gaban mutanen da yake nuna wa shi wani ne, ya daka mata tsawa tare da faɗin.
"Dalla malama tashi ki bani waje! Daƙiƙiya kawai. Kin duba buhun da na kawo ne jiya? Ki na nan kina jan jiki kamar akan ki aka fara ɗaukan ciki baki san ma akwai abinci a gidan ba. Bari mu gama zan shigo ne mu gauraya da ke. Ware ki bawa mutane waje."
Duk rugugin faɗan da yake yi bai dame ta ba da fari,saboda hankalinta ya yi nisa wajen tunanin yaushe ya shiga da buhu gidan? A ina kuma ya ajiye buhun? To ko dai a store ya ajiye bai sanar da ita ba? Ta na tafe tana tunani ta furta.
"Kai gaskiya ban ga wani buhu ba,saboda yana shigowa gidan na je na tarbe shi kamar yanda na saba yi kullum,da hannuna na karɓi jakarsa na ajiye a inda na saba rataye masa,to wanne buhu yake nufi?"
A bakin gado ta zauna tare da zabga tagumi. Ƙwaƙwalwarta ce ta tina mata kalamansa da ya ce.
'Bari mu gama zan shigo ne mu gauraya.'
Hankalinta ne ya yi mummunan tashi,dan kuwa ta san yau ɗin Allah ne kawai zai ƙwace ta a hannun Abbas. Wasu jijiyoyi ne raɗa-raɗa suka firfito a gaban goshinta,hancinta kuwa har wata zufa yake tsattsafarwa,idanuwanta sun kaɗa sun yi jawur saboda tashin hankali. Ta na nan zaune ta ji fitar su suna sake zuga shi akan ya ci gaba da riƙe wuta,domin kuwa kyawawan mata irin Fauziyyah idan suka samu waje juya miji suke yi,wataƙila ma albashinsa ita ce za ta dinga amshewa sai abinda ta bashi na kashewa a ciki. Idan kuwa ya kuskura ya bari hakan ta kasance,to fa babu shi babu ci gaba da more ƙuruciyarsa da ƴan shila,guzumayen ma ba kula shi za su yi ba. Wata iriyar dariya suka sanya suka tafa,shi kuwa gogan cikin haɗe girar sama da ta ƙasa ya ce.
"A da ne kafin mu yi aure take da wannan farin jinin. A yanzu kuwa ko me sharar kasuwa sai dai ya yi manage da ita,saboda ta zamo marar amfani."
Wasu irin zafafan hawaye ne suka fara gudun tsere a kuncin Fauziyyah da ke sauraron duk wata kalma dake fitowa daga bakin masoyinta,wanda ya kusa rasa ransa saboda tsoro da fargabar rasa ta da ya kusan yi a baya,namijin da ya sadaukar da jin daɗin sa saboda ya mallake ta,shin da gaske ne bata da wani amfani ko a wajen mai sharar kasuwa? Shin da gaske ne babu namijin da za ta burge ballantana har a so ta? Ashe shi yasa Abbas ɗinta abun ƙaunarta ya sauya daga masoyinta ya koma maƙiyinta? Lallai rashin gyara masifa ne,to amma ai laifinsa ne ta lalace har ta zamo marar amfanin da yake yawan kiranta. Tini ya dena sauke duk wani haƙƙinta da ya rataya a wuyansa. Turare wannan shi kaɗai yake siyawa kansa ya ɓoye,ko za ta yi warin bunsuru ne sai dai ta yi,amma bata isa taɓawa ba.Sutura kuwa kamar zata kashe Abbas masu kyau da tsada yake siya,takalman sa kaf babu ƙasa da na dubu goma,amma ita tin na lefe take ta murza ko na sallah baya yi mata ballantana idan ya ɗinka nasa ya tuna da ita. Sabulun wanka yake siyawa kansa mai kyau da tsada,ita kuma sai dai ta yi da na wanki,idan ya ƙare ta yi da omo,idan babu omo ta yi da zallan ruwa,shi yasa lokuta da dama ko ta yi wanka da ta yi aiki kaɗan sai ta fara warin hammata. Man shafawarsa na musamman ne,amma ita ko basilin be siya mata ba,tin mayukan lefenta da suka ƙare be sake sai mata mai ba balle hoda,shi yasa ko tsinke babu a saman mirror ɗinta da ya wuce kwalli da brush ɗin da take taje girar ta da shi. Idan tana son shafa mai sai dai idan ta faki ido ta tatse na leda da ta kan adana idan ta juye man. Lokuta ƙalilan ne take samu Barirah ta sammata mai a duk lokacin da ta sai me kyau na gyaran fata. Ranar da Mahaifiyar Abbas ta kawo mata basilin kuwa ririta shi ta dinga yi ta na adanawa,har sai da ya shekara be ƙare ba. Murmushi ta yi a lokacin da ta tina da mahaifiyarsa,mace ce itanmai mutunci da karamci,takaicin Abbas shi ne ya yi sanadiyyar da ta kamu da mummunan hawan jini. Yawan zuwa gidan ta tarar da Fauziyyah a cikin mawuyacin hali har itama nata ciwon ya tashi ne,ya sanya danginta suka bata shawarar ta rage zuwa gidan nasa,idan yaso duk sanda ta so ganin Fauziyyar ta dinga saka shi yana kai mata ita su gaisa,shi kuma ta dage da yi masa addu'a da fatan shiriya,watarana komai zai zamo labari. Wannan shawarar ce ta sa sai su shafe wata ɗaya zuwa biyu basu haɗu ba,wani sa'in ma har sukan kai wata uku Fauziyyah bata ga surukar tata ba. Sai dai shi yana zuwa kullum yana gaida ita,kasancewar wajen da yake koyarwa babu nisa sosai da gidan nasu.
Zumbur ta miƙe tsaye tare da binsa cikin ɗaki,saboda yanda ya fizgi hannunta na hagu ko tausayin tulelen cikin dake jikinta bai yi ba. Jikinta ne ya ɗauki rawa suna zuwa ƙofar bedroom ɗin su ta riƙe gini ta na yarfe hannunta na dama ta ce.
"My king don Allah ka tausaya min,ka ga halin da nake ciki. Ka yi haƙuri ka yafe min duk wani laifi da na yi maka,na yi alƙawari ba zan sake ba."
Mugun kallon da ya zuba mata da shanyayyun idanuwansa ne suka sanya ta haɗiye wani mugun yawu mai bala'in kauri,busassun laɓɓanta ta lashe ta ɗaga ƙafa da ƙyar ta bi bayansa zuciyarta na lugude kamar ana dakan sakwara.
A zafafe ya yarfe hannunta ya koma saman makeken gadon su mai tsananin kyau da tsada ya zauna. Huci yake yi kamar wani kumurcin maciji. Murya a shaƙe kamar ta ragon layyan da ya ci kuka ya gaji ya ce mata.
"Tuɓe."
Hawayen da suka maƙale suka ƙi fita ne saboda tashin hankali,suka samu damar fitowa daga idanuwanta suka hau kwaranya,cike da mutuwar jiki da saddaƙarwa Fauziyya ta hau warware ɗaurin ɗankwalinta. Ta riga ta sani tinda ya shiga wannan yanayin babu wanda ya isa ya ƙwace ta ko da kuwa mahaifiyarsa ce ta zo. Hannayenta na masifar rawa ta ɗaga rigarta tin daga ƙasa ta hau cirewa. Tsaye ta yi a gabansa kanta duƙe kamar wadda mijinta da surukanta suka kama a ɗakin kwarto. Kallon tsayayyu kuma cikakkun ƙirjinta ya yi ya haɗiyi wani mugun yawu,faffaɗan ƙugunta mai ɗauke da manyan cinyoyi ya koma bi da jajayen idanuwansa yana kallo. Muguntar da ya shirya mata ce ta sanya shi fashewa da dariya kamar wani zararre. Hannu ya sanya ya zaro wayarsa daga aljihunsa ya kunna ya koma ya jingina da allon gadon. Bai sake kallon inda take ba. Ita kuwa jikinta ne ya ɗauki rawa kamar mazari,ji take yi kamar ƙafafuwanta ba za su iya ci gaba da ɗaukar gangar jikinta ba. A gajiye ta hau motsa ƙafafunwanta tana ɗaga su daga wannan zuwa waccan. Sai da Abbas ya gama abinda ya mayar ibada sannan ya ɗaga idanuwansa da suka sake rinewa suka koma jajaye ya ce.
"Zo nan."
Da ƙyar Fauziyyah ta ɗaga ƙafafuwanta ta fara takawa zuwa gabansa,hannayenta sun yi sanyi ƙalau kamar wadda ta taɓa ƙanƙara,sai zufa suke tsiyayarwa,zama ta yi a wajen da ta riga ta saba da zarar ya yi mata irin wannan kiran,hannu na rawa ta hau zare masa safar ƙafarsa,tana gamawa ta cire masa dogon wandonsa da rigarsa ta ninke su ta mayar inda take ajiyewa kafin washegari kuma ta wankesu. Ta na kammalawa ta koma saman gadon ta zauna a gabansa tare da sadda kai ƙasa. A wulaƙance Abbas ke bin surar jikinta da wani malalacin kallo. Hannunsa ya sanya ya ɗaga haɓarta ya na kallo,cikin sauri ta buɗe nata idanuwan ta na bin cikin idanunsa da kallo gudun kar ta sake yin wani laifin. Cike da mugunta Abbas ya hau sarrafa gangar jikinta da ta ya ke kira da 'Marar amfani' a koda yaushe...... [12/9, 8:37 PM] HAERMEEBRAERH: MUGUN MIJI.
RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️ ✨