PAGE 4
by @1239900
Kwance ta yi kawai ta na jin duk wani bidiri da Abbas ke yi a kanta cike da mugunta da zalunci da rashin tausayi. Domin jin daɗin sa duk wani abu da zai faranta masa rai ya bashi nishaɗi shi ya dinga yi ko da kuwa ita zai zame mata azaba.Tsananin tausayin kanta ne ya sanya wasu zafafan hawaye gangarowa daga idanuwanta suka sauka a saman pillown da ta ɗora kanta. Kiran sallar magrib ne ya sanya Abbas haƙura ya ƙyale ta,domin kuwa ya tina da bai yi sallar la'asar ba. Kallonta ya yi ya ce mata.
"Ki shirya sauran na dare kuma."
Kuka ne ya kusan ƙwace mata,dan ta san babu abinda zai hana shi yin abinda ya furta sai ikon Allah. Dan haka dole ta yi haƙuri ta danne kukanta kafin ya fara yi mata masifa akan haƙƙinsa,se ka ce ita bata da wani haƙƙi nata da ya rataya a wuyansa.Cike da nishaɗi ya tashi ya zira gajeran wandonsa ya fito tsakar gida ya na miƙa. Barirah ce ta ɗaga labule za ta fita domin yin alwalar sallar magrib, ta na yin arba da Abbas sanye da gajeran wando ta yi saurin sakin labulen ta koma ɗakinta. Zama ta yi a kan kujera tare da zabga tagumi ta na jin tsana da takaicin Abbas na mamaye ranta. Tsaki ta zabga kafin ta ce.
"Jahilin banza da wofi kawai,da ma na sani da na gama girkina nayi wanka alwalar na yi gaba ɗaya,yanzu zai je ya ɓata lokaci nima ya ɓata min."
Ta na nan zaune ta ji ya ɗebi ruwa a bokiti ya shige banɗaki,cikin sauri ta miƙe ta fita da nufin ɗaukar buta ta yi alwalarta a gaggauce kafin ya fito. Fauziyyah ta gani a bakin ƙofar ɗakinta kwance kamar gawa. A guje ta isa wajenta ta na faɗin.
"Ke lafiya? Me ya same ki haka? Ko dai naƙuda kike yi?"
Girgiza kai Fauziyyah ta yi,a wahalce ta ce.
"Ruwa...ruwa zan...shaa Aunty."
Cikin sauri Barirah ta matsa kusa da randar da Fauziyyah ke zuba ruwa,ta ɗebo mata ta kafa mata kofin a bakinta,wani irin sha take yi wa ruwan kamar shi kaɗai ne abu mafi mahimmanci a rayuwarta. Ta na gama sha ta lumshe ido ta koma ƙasan ɗakin ta kwanta ta yi lamo. Tunda Abbas ya tashi daga jikinta take jin ƙishirwa,sai dai ta riga ta san ko mutuwa za ta yi ba zai bata ruwan nan ba,sai dai idan ta isa ƙiyama ta sha. Sanin hakan ne ya sa ta yi shiru har ya saka gajeran wandonsa ya bar ɗakin. Ya na fita ta ja doguwar rigarta ta mayar a jikinta. A hankali ta sauka daga gadon,da rarrafe da jan jiki ta iso bakin ƙofar ɗakin,sai ta fara jin jiri ya na neman ya sanya ta kwantawa a saman cikinta,cikin azama ta yi dabarar kwantawa a gefen ta na dama,ta na nan ta na ambaton sunan mai kowa mai komai ta ji motsin Barirah,farinciki ne ya mamaye zuciyarta,domin ta san ita ba za ta taɓa barinta a wulaƙance ta wuce ta ba.
Alwala Barirah ta yi idanuwanta na zubar da hawaye,ta na idarwa yana fitowa,ko ɗaga kai bata yi ta kalle shi ba ta bar wajen ta shige ɗakinta,sallah ta tada tana ci gaba da sharce hawaye. A sujjadarta ta ƙarshe sai da ta yi wa iyayenta da mijinta addu'a sannan ta yiwa Fauziyyah addu'a da fatan Allah ya kawo ƙarshen wannan zaman nasu ita da Abbas,domin a ganinta babu wani alkhairi da ke cikinsa,ba zai taɓa sauyawa ba.
A yanda ya ganta a sheme a tsakar parlour bai yi wani yunƙurin taimaka mata ba,sai ma ware ƙafafunsa da ya yi ya tsallake ta ya shige ɗaki,kaya ya sanya ya fesa turarukansa sannan ya tada sallah,caccaken kurciya ya yi ya sallame,cike da masifa ya koma parlour ya tsaya a saman kanta ya ce.
"Raguwar banza da wofi kawai. Ke wai yanzu sau biyun ne ya gajiyar dake tsabar rashin amfani? To ki buɗe kunnen ki da kyau ki ji ni,zamu haɗu dake zuwa anjima,dan haka gwanda ma ki miƙe ki ƙwarara jikin ki dan ba wai na samu abinda nake so bane,manage kawai na yi. Ni zan fita,ga wannan ki leƙa ki aiki yaro a siyo kalanzir ki saka a risho tinda dare ya yi kuma na ga itacen har yanzu da jiƙa ba lallai ki gama girkin da wuri ba,ni kuma yunwa nake ji sosai. Maza ki tashi ki dafa mana abinci,kar na dawo baki dafa komai ba."
A rikice ta tattaro ragowar ƙarfin da ya yi mata saura ta kalle shi ta ce.
"My king babu fa ƙwayar hatsi da ta rage a gidan nan,kuma na faɗa maka tin wancan satin abubuwa sun ƙare,ɗazu ma ban ci komai ba ku na juyewa duka."
Ji ya yi kamar ta watsa masa tafasasshen ruwa a fuska,a hasale ya daki ƙafarta tare da wara hannayensa ya yi mata daƙuwa sannan ya ce.
"Dan iyayen ki a gidan uban wa kika sanar dani abubuwa sun ƙare? Ko ni soko ne irin ki da zan manta abu mai mahimmanci irin wannan? Bari na mayar da ɗari biyu na za ta min amfani,kin san yanda zaki yi ki ciyar da kan ki. Ba kuma gwaninta kika yi ba da kika hana kan ki abinci kika bamu ni da abokaina,wannan neman suna da wajen zaman ba zai sauya kallon da nake yi maki ba."
Tsallake ta ya yi ya zari takalminsa ya bar gidan ya na ci gaba da masifa har ta dena jiyo shi. Kasa zubar da ko da hawaye ta yi domin ta ji daɗi a ranta. Wannan shi ne sakamakon soyayyar da ta samu a wajen mutumin da ta ɗauka ya fi kowa sonta da ƙaunarta a duniya. Murmushi ta yi ta yunƙura da ƙyar ta tashi. Ruwa ta ɗiba ta je ta dasa kujera a banɗaki ta yi wanka sannan ta fito. Sallar la'asar da be barsu sun yi ba ta gabatar sannan ta ɗora da magariba. Ta na nan zaune aka yi Isha'i,sai da ta yi Isha'i ta yi shafa'i da wutiri sannan ta kwanta a wajen ta na sauke ajiyar zuciya. Sallamar Barirah ce ta tashe ta zaune. Murmushi ta sakar mata sai ta ga idanuwan Barirah sun kumbura sun yi jawur,kwanon hannunta ta karɓa ta ajiye a gefe ta riƙe hannayenta ta ce.
"Don Allah Aunty ki dena damun kan ki saboda ni,ai bahaushe ya ce duk tsuntsun da ya jawo ruwa shi ruwa zai doka. Ni ce na jawa kaina duk abubuwan da Abbas yake yi min,ba dan komai ba sai dan soyayyar da na nuna masa,wadda har yanzu taƙi barin raina,ina jin son sa a cikin jini na wanda yake zaune a zuciya ta,ta yanda duk wani bugu da za ta yi sai ta harba min dafin soyayyarsa a sassan jikina. Kin ga kuwa dole na jure duk wani tukuici da yake bani."
"Ki gudu wajen ɗan'uwanki Fauziyyah,Abbas kashe ki yake so ya yi,ta ya zai bar mace da tsohon ciki da yunwa? Ga munanan kalamai babu lallashi ko tausayawa? Na gaji da ganin halin da kike ciki,idan har baki ɗauki mataki akan Abbas ba,mu zamu ɗauki matakin raba zuciyoyinmu da damuwa da tashin hankalin da kike ƙunsa a ƙarƙashinsa. Ki tashi ki ci abincin nan a gabana na wuce da kwanona,domin ni ba zan zauna zaman dafawa mara mutunci abinci ba kullum. Idan kika ga na bashi abincina to sai dai bashin zai kare ki daga zaluncinsa."
Murmushi kawai Fauziyyah ta yi,tabbas ta san kalaman Barirah akan gaskiya suke,amma yanayin yanda take aibata mata miji yana sukar ranta. Babu yanda ta iya kan dole ta ci abinci ta sha ruwa,Barirah ta wuce da kwanonta,cikin sauri Fauziyyah ta goge bakinta da brush sannan ta wanke hannunta da guntun sabulun wanki gudun kar ya gane. Zama ta yi ta na karanto ayoyin ƙur'ani da ka har Abbas ya dawo. Zaune ya tarar da ita ta sauya kaya daga wanda ta saka da rana,duk da cewa rigar ta koɗe sosai ta yi mata kyau,saboda ita ɗin kyakkyawa ce. Leda ya ajiye mata a gabanta sannan ya koma gefe ya ɗakko plate da cup ya zauna a kujera. Shayi haɗin kauri ya juye a cup sannan ya juye dankalin turawa da gasasshen kifi tare da soyayyan ƙwai a plate,sai ya kunce ledar bread ya fara aikawa cikinsa,ƙamshi da kyawun abincin da ya sa a gaba yana ci shi kaɗai ne ya sanya Fauziyyah saurin ɗaukan ledar gabanta ta sake furta masa kalmar godiya wadda ya ƙi amsa mata tin ta fari da ta yi masa. Ta na buɗewa ta ci karo da ruwan bunu da yankakken bread irin na wajen masu shayi da burodin nan. Ƙwalla ce ta taru a idanuwanta,sai kawai ta fasa ledar ruwan bunun ta dinga korawa a haka,domin ta riga ta san ko mutuwa za ta yi a gabansa ba zai lasa mata romon abinda yake ci ba,ballantana ya bata ta ci ɗin. Idan ta kurɓi ruwan bunun sai ya jima bai wuce a maƙoshinta ba saboda yanda yake ƙulle mata wuya da takaici. Tinda ta kalli Abbas sau ɗaya bata sake kallonsa ba har sai da ta ji ya yi gyatsa ya baje ƙafafuwansa har suna taɓo ta. Kallonsa ta yi ta ga ya rage kan kifin da guntun dankali da ƙwai,a ranta ta ji farinciki ya lulluɓe ta har sai da ta saki murmushi,da alama yau ƴan mutuncin na kusa kenan tinda ya rage mata,dan idan ya tashi irin wannan mugun halin nasa ko ya ƙoshi zai ce ta ajiye masa saura ta ɗumama masa gobe ya ci. Hannu ta kai za ta ɗauki plate ɗin ya buɗe idonsa guda ɗaya da ya lumshe,a hankali ya ware dika idanuwasa akan ta ya na binta da wani mugun kallo,cike da masifa da bala'i ya ce.
"To mayya baki na yi da za ki ɗaukar min?"
Kame-kame ta fara yi,cikin sanyin muryarta ta ce masa.
"Na ji ka taɓa ni ne da ƙafar ka,na zaci ka na nufin na ɗauka ne. To ka yi haƙuri don Allah."
"To ba nufi na kenan ba kwaɗayayyiya,tashi ki bar nan kafin na ɓalla ki. Marar godiyar Allah kawai,idan ba za ki ci abinda na baki ba ki zubar."
Da ƙyar Fauziyyah ta dafe ƙasa ta miƙe ta na jin yanda cikinta ya yi ƙasa sosai,ɗaki ta shiga ta adana bread ɗinta dan ta san zai yi mata amfani. Shi kuwa duk da ya ƙoshi sai ya sake baje ƙafa ya ci gaba da ɗurawa cikinsa. Ya na gamawa ya tashi ya wanke hannunsa,ko brush bai yi ba ya shiga bedroom ɗin,kwance ya ganta a yanda yake so,sai ya saki murmushi ya haye gadon.
Ita kuwa tana shiga ta hau yin duk abinda yake so,gudun kar ya tsamama mata jikinta fiye da yanda yake a wannan lokacin,ta samu waje ta kwanta ta na jiran shigar sa ɗakin.......... [12/9, 8:37 PM] HAERMEEBRAERH: MUGUN MIJI.
RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨