MUGUN MIJI

PAGE 5

by @1239900

Tsananin azaba da gajiyar da Abbas ya tarawa Fauziyyah ne suka yi sanadiyyar sanya ta nannauyan bacci. Shi kuwa gogan bai kwanta ba har sai da ya lalubo brodin da ta adana saboda amfanin kanta,ya koma ya haɗa shayi da kayan tea ɗin da ya ɓoye a aljihun rigarsa. Zaune yake a gefen gado ya na kurɓar shayi ya na latsa waya,fuskarsa ɗauke da murmushi ya jiyo muryar Fauziyyah a cikin bacci ta na faɗin.

"Don Allah ku tafi dani zai kashe ni,Ummah na yi kewar ki da yawa,zan bi ku.......Allah ka shiga lamurana,Allah ka kuɓutar da ni daga zaluncin Abbas...Allah na tuba ba zan sake....."

Wani irin mahaukacin duka Abbas ya buga wa cinyarta da ke buɗe,a gigice ta farka daga nannauyan baccinta ta na sosa wajen tare da kwaɓe baki za ta yi kuka,sai da ya ajiye cup ɗin da yake shan shayi a ciki,ya ƙarasa tauna burodin da ke bakinsa sannan ya sa yatsansa a saman laɓɓansa yana zare mata idanuwansa ya ce.

"Yi min shiru munafuka,wato ƙara ta kike kai wa Allah kina bacci dan tsabar mugunta da munafurci ko? Fauziyyah wai me na tsare miki a duniya ne kike son ganin baya na?"

Hawaye ke zuba daga idanun Fauziyyah kamar ruwan korama mai gudana. Ita bata san lokacin da ta kai shi ƙara wajen Allah ba da yake faɗa akai,ta san dai tana bacci mai daɗi cike da mafarkin iyayenta ya ɗasa mata mugun duka a cinya. Tsawar da ya daka mata ne ta sanya ta girgiza kai ta na bashi haƙuri,cikin kuka ta ce.

"My king akan me zan kai ƙarar ka wajen Allah bayan auren soyayya muka yi ba na ƙiyayya ba? Don Allah ka yi haƙuri ba zan sake ba to."

"Ohh ba za ki sake ba to,watom ma ƙarya na yi miki ko? Fauziyyah ki fita daga idona na rufe,kar ki bari kaina ya juye na yi maki shegen duka a zo ana cewa kuma bani da mutunci,tom."

Ya yi ƙwafa ya haye gado ya kwanta ya na kaɗa ƙafafu tsabar masifa na cin zuciyarsa. Fauziyyah kuwa tin da ta farka sai ta kasa komawa bacci. Da misalin biyu na dare yunwa ta addabe ta sai ta hau duba bread ɗinta,babu inda bata duba ba amma bata gansa ba,sai guntun da Abbas ya rage da shayi kaɗan a saman ƙaramin table. Kallonsa ta yi ta ga ya yi bacci, ga uban munshari da yake ta ja,a hankali ta ja jikinta ta ɗauki cup ɗin ta hau shan shayin da guntun burodin,ta sani da safe ko da ta bari ma lalacewa zai yi,ba kuma sha ze yi ba,iyaka ya yi mata masifarsa da baya gajiya. Ta na gamawa ta yi niyyar tashi dan ta tsarkake jikinta,sai dai taku ɗaya zuwa biyu da za ta yi ta ji ruwa na bin ƙafarta,tare da ciwon mara mai tsanani. Cike da tashin hankali ta kalli Abbas da ke sharar bacci,cikin matsananciyar damuwa ta ce.

"Ya zan yi ni Fauziyya? Idan na tada shi yanzu na shiga uku,musamman idan ba haihuwar bace ba. Allah ka kawo min agaji."

Jiki babu ƙwari ta dafa gini ta shiga banɗaki,wanka ta yi sannan ta dawo ɗakin ta hau safa da marwa. Leɓenta ta dinga cizawa tare da jan gashin kanta,idan azaba ta yi azaba sai ta duƙa ta zuba salati ta hau nishi,da ta lafa mata sai ta miƙe ta ci gaba da sintiri. Ganin abun ba zai lafa mata ba ne ya sanya ta shiga ɗakin gabanta na masifar faɗuwa ta daki ƙafar Abbas a hankali,juyi ya yi ya koma baccinsa ba tare da ya buɗe ido ba. Sake tashin sa ta yi a karo na biyu,a hasale ya farka ya wurga mata mugun kallon da ya sanya ta duƙewa a wajen ta na nishi da ƙyar,cikin jin azabar naƙuda ta ce.

"Don Allah My king ka taimaka min zan mutu."

Hawaye ne suka fara zuba a idanuwanta,cike da hargowa Abbas ya ce.

"Yanzu Fauziyyah saboda tsabar iskanci ina bacci za ki tada ni ki sanar dani zaki mutu? To wahayi aka yi miki ko me? Ina ce ƙarata kika gama kaiwa wajen Allah ɗazu? To ki tabbata yanzu ma kin nemi taimako daga wajen Allah,dan ni bacci nake ji,gobe akwai inda zamu je da abokaina."

Daskarewa Fauziyyah ta yi a wajen da take a duƙe tsabar mamakin furucinsa. Ƙafarta ce fa ɗaya a duniya ɗaya a lahira ita da irin da ya dasa mata a mahaifa har ya isa girbewa,amma shi bashi da sauran imani da tausayin da zai kalle su da idanun rahama ballantana har ya taimaka musu. Da jan jiki ta fita daga ɗakin ta na gunjin kuka kamar ranta zai fita ta zauna a tsakar gida,jin kukanta ne ya sanya Barirah da Shehu fitowa tsakar gidan. Ganin halin da take ciki ne ya sanya Barirah rikicewa ta isa gabanta a guje ta tallabo ta ta na faɗin.

"Me yake damun ki Fauziyyah? Wannan dai kamar naƙuda kika fara ko?"

Kai kawai Fauziyyah ta iya ɗaga wa Barirah,wani irin zafi zuciyarta ke yi mata,ga azabar zafin naƙuda na ratsa ta. Da gudu Barirah ta shiga ɗakinta ta ɗakko wata ƙatuwar leda mai kyau,hijabinta ta ƙarasa sakawa sannan ta kalli Shehu ta ce masa.

"Hubby ina ga fa dole ka je gidan Malam Idris ya taimaka mana da mota,tinda ka ga mu machine gare mu."

"To ina shi ɗan rainin wayon yake?"

Shehu ya faɗa ya na kallon Fauziyyah da hanyar ɗakin nata,murmushin takaici kawai ta yi ba tare da ta iya furta masa komai ba. Barirah ce ta ja tsaki sannan ta harari ƙofar ɗakin nasu ta ce.

"Don Allah Hubby ka je ka taso Malam Idris ni ba zan iya karɓar haihuwa a gida ba,saboda ban iya ba ban san ya ake yi ba."

Cikin sauri Shehu ya fita waje ya sa makulli ya buɗe gidan ya nufi hanyar gidan maƙocinsu dake da mota. Barirah kuwa igiya ta kalla ta ga zannuwa guda biyu da Fauziyyah ta ke wanka da su a wanke da hijabinta,sai kawai ta ɗauke su ta ninke ta saka a cikin ledar da ta fito da ita ta miƙawa Fauziyyah hijabin dan ta saka. Ta na nan tsaye ta na jiran Shehu,hankalinta a tashe ta ji motsin Abbas,shigowar Shehu ke da wuya Abbas ya fito hannunsa riƙe da rigarsa ya na ƙoƙarin sakawa ya ce.

"Gidan uban wa za ku kai min matata da tsohon daren nan?"

Shehu ji ya yi kamar ya ɗura masa ashar,sai ya danne ya bashi matsayinsa na mijin Fauziyyah ya ce.

"Baka ga naƙuda take yi ba? Asibiti za mu kai ta mana."

"Da yawun wa za ku kai ta asibitin to?"

"Da yawun..."

Hannu Shehu ya ɗaga wa Barirah ya ce.

"Za mu kai ta asibiti yanzu ko da matsiyacin yawunka ko babu,idan ya so ka biyo ta da takardar saki a can ka ga idan ta gama iddah ba za ta samu mijin da ya fi ka ba? Shashasha kawai. Ke barira kamo ta mu wuce kin ji."

Cikin sauri ta taimakawa Fauziyyah ta miƙe ta na bin kyakkyawar fuskar Abbas da kallo, wataƙila wannan kallon shine kallo na ƙarshe da za ta yi masa,murmushi ta sakar masa ta gyara zaman hijabinta da Barirah ta bata dan ta saka suka fara takawa zuwa waje. A hasale Abbas ya ɗaga murya ya na faɗin.

"Ai na faɗa mata tin cikin nan yana ƙarami ni ba zan je asibiti ba,a nemo ungozoma ta zo har gida ta karɓi haihuwarta,dan haka idan kuka kuskura kuka kai ta asibiti sai dai ku yi hidimar asibitin kuwa,sisi na ba zai yi ciwo ba."

Ya na magana ya na ɗaga hannaye kamar me shirin kai musu duka,babu wanda ya kula yinsa suka wuce suka barshi ya na banbamin faɗa. Ganin fa da gaske asibitin za su kai ta ne ya sanya shi saurin kulle ɗakin su,ya tada nashi machine ɗin ya bi su,ya na fita ya tarar da har sun shige mota Malam Idris ya tada za su tafi,cikin gaggawa ya kulle gidan ya bi bayan su,a hanya ya zaro wayarsa ya kalli lokaci,ƙarfe uku da kwata na dare. Gudu kawai suke zubawa saboda titin babu kowa. Kai tsaye asibitin Aminu Kano suka wuce saboda a can Barirah ke ganin likita. Suna zuwa suka yi duk abinda ya dace,kafin su kammala naƙudar ta taso gadan-gadan,ɗakin haihuwa aka kai Fauziyyah cikin gaggawa. Abbas na ƙarasa shigowa Fauziyyah ta silluɓo jaririyarta kyakkyawa mai kama da iyayenta. Nurse ce ta leƙo ta ce.

"Ina ƴan'uwan Fauziyyah Aliyu? Ku kawo kayan jariri. Ga kuma wannan za ku siyo abubuwan da aka rubuta a jiki ku kawo yanzu."

Wata takarda ta miƙa wa shehu, ya karɓa ko ta kan Abbas bai bi ba ya wuce ya na hamdala ta sauka lafiya. Barirah ce ta miƙa ƙatuwar ledar nan ta koma gefe ta na wasar baki,suna haɗa ido da Abbas ta zabga masa harara tare da sakin wani mugun tsaki,shi ɗin ma hararar ta ya yi tare da rama tsakin da ta yi masa sannan ya ce.

"Duk tsiyar ki dai ba za a taɓa sauya wa tuwo suna ba,ni ɗin dai da ba kya so ni ne uban yarinyar,to don haka ki dena wani zaƙewa da yi min shisshigi a lamura na,idan haihuwar kike so kema ki dage ki haifi naki."

Kallon Abbas Barirah ta yi ranta a matuƙar ɓace,cikin tsananin ɓacin rai ta ce masa.

"Inda za ka tabbatar da cewa ita haihuwa ta Allah ce ba ta mutum ba kenan tinda ka haihu ni ban haihu ba. Allah ya na bawa wanda ya so ya hana wanda ya so,kuma shi ɗin ne dai ya baka mu kuma da muke so bai bamu ba,ba dan komai ba sai dan hakan ya zame mana aya a rayuwarmu."

"Oho dai,duk wannan rawar kan da kike yi nine dai uban ƴar,kuma sisina ba zai yi ciwo ba,tinda ba a nemi shawarata ba balle izinina aka kawo min mata nan wajen."

Barirah bata sake kula Abbas ba saboda ɓacin ran da ya dasa mata,wanda ya fi na da. Shehu da Malam Idris na dawowa Abbas ya buga tsaki ya ci gaba da habaici da surutai na kore kunya da hauka. Cikin ɓacin rai Malam Idris ya kalle shi ya ce.

"Kai dai Abashe an yi mugun miji kuma azzalumi,yanzu ace matar ka za ta haihu ko tsinke ba ka siya mata ka ajiye ba,sannan ka tasa masu taimaka maka a gaba da rashin arziƙi? Da ace yarinyar nan za ta bani dama alƙur'an ba za ta koma gidan ka ba,daga asibiti sai gidan iyayenta,dan ko ka ƙi sakin ta sai na maka ka a kotu ka sake ta dan dole."

Dariya Abbas ya fashe da ita sannan ya ce.

"Ai dama na san sai kun yi gulmata tinda kuka fita tare,wato har ya baka labarin ban siyi ko tsinke ba ko? To ban siya ba ɗin sai me? Ko ni na saka shi kashe kuɗin sa? Dama ai ba domin Allah suke taimakon ba tinda har suke iya yayata abinda suka yi mana."

Ganin haukan na Abbas azimun ne sai kowa ya bawa banza a jiyarsa,shi kuwa tunda ya ga ta haihu lafiya,an fito da jaririya ya ganta ya yi mata addu'a,sai kawai ya bawa nurse ita ya wuce gida. Ya na isa gida ana kiran assalatu. Bai wani damu ba ya shige ɗakinsa ya kwanta,cike da tinani da soyayyar jaririyarsa bacci mai mugun nauyi ya ɗauke shi.......... [12/9, 8:37 PM] HAERMEEBRAERH: MUGUN MIJI.

RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨