MUGUN MIJI

PAGE 8

by @1239900

Kafaɗa Barirah ta ɗaga tare da kyaɓe baki sannan ta ce.

"Bari na kama bakina na tsuke,dan kuwa na san yarinyar nan tsaf za ta ƙaryata ni a gaban uwar mijinta dan kawai ta kare shegen mijin nan nata. Amma ai rana dubu ta ɓarawo ce,rana ɗaya tak kuma ta mai kaya,a juri zuwa rafi da tulu,dan watarana zai fashe."

Ɗakinta ta shige ta hau gyarawa,kafin daga baya ta koma kitchen ɗinta ta duba ruwan wankan da ta saka wa Fauziyyah. Ganin ya tafasa ne ya sanya ta zuwa ta ɗakko babban bokiti ta kwashe ruwan,sai ta tsaya ta na jiran Abbas ya fito ta saka roba a banɗakin ta juye sai ta ƙaro sauran. Ta jima sosai ta na jiransa a bakin ƙofar kitchen ɗinta kafin ya fito ya na goge kansa da ƙaramin towel,ko kallon inda yake Barirah bata yi ba,shi kuwa tsayawa ya yi ya na kallon yanda ruwan zafin gabanta ke turiri. Ji ya yi kamar ya je ya ɗauka ta ya tsoma a ciki tsabar yanda yake jin tsanarta a ransa.

Harara ya banka mata kafin ya ajiye bokitinsa da ƙarfi,ya shige ɗaki. Hira ya tarar da Fauziyyah na yi ita da Hajiyansa,hannunta riƙe da jaririyarsa da ke bacci,murmushi ya yi ya wuce ɗaki ya na faɗin.

"Gaskiya Hajiya yarinyar nan da ni take kama sosai."

Cikin ɗaga murya yanda Abbas ɗin zai iya jiyo ta ta ce.

"Eh to ba zan yi maka musu ba,dan kuwa ta ɗakko kamannin ku kai da Fauziyyah dika. Amma fa ku sani shi jariri ba a shaidar kamanninsa,yanzu zai yi kama da iyayensa da ya girma ya koma kama da kakanninsa ko da maƙotansu."

Dariya sosai Fauziyyah ta yi,jin sautin dariyarta a cikin kunnuwanta ne ya sanya ta tsagaitawa,a hankali take ƙoƙarin tina lokaci na ƙarshe a rayuwarta da ta yi dariyar farinciki ba yaƙe ba ko murmushin takaicin halin ƙuncin da take fuskanta a hannun Abbas. Ƙwalla ce ta taru a idanuwanta,cikin sauri ta hau ƙoƙarin mayar da su,sai dai kalaman Abbas ne suka dawo da ita daga duniyar da ta lula,cikin wani irin amon sautin da ya sanya Hajiya yin shiru ta na nazarin kalaman sa ya ce.

"Lallai kuwa idan yarinya ta yi kama da maƙota sai a tuntuɓi uwarta a ji garin yaya ƴarta ta je kalan dangi har ta yi kama da maƙota?"

Suna nan zaune kowa da abinda yake saƙawa a cikin ransa Abbas ya fito cikin shiri,cike da munafurci ya kalli Fauziyyah ya ce.

"My Queen na gode sosai da ɗawainiyar da kike yi dani,duk da cewa kin haihu kina cikin jego baki manta ba sai da kika fitar min da kayan da zan saka,sannan kika goge min takalmi na,Allah Ya yi miki albarka."

Fauziyyah ji ta yi kamar ya kwaɗa mata guduma a kanta,a razane ta ɗaga kai ta na kallon fuskarsa,tsoro ne ya kamata domin tinawa da rayuwarsu ta baya da ta yi,fatan ta Allah kar ya jarabce ta da maimaita rayuwarta ta baya a gidan Abbas,wannan ma da take ciki neman mafita da salama take yi,me zai kai shi dawo da hannun agogo baya yanzu? Abbas kuwa jakarsa ya rataya ya na kallon fuskar Hajiyansa da ke zabga murmushi,cikin farinciki Hajiya ta ce.

"Ai kana shiga bayi ta tashi ta shige ciki,ashe kayan ka ta ɗakko maka baiwar Allah. Da kuwa na ga tana goge maka takalmi sai da na hana ta,amma sai ta ce wai ladan take kwaɗayi,tinda ta haihu lafiya me zai hana ta goge takalmin ka? Allah dai ya dawwamar da ku cikin zaman lafiya,ina alfahari da sauyawar da ka yi Abbas. Allah Ya yi muku albarka ya sa haihuwar nan da kika yi ta zame muku sanadin samun dawwamammen zaman lafiya a tsakanin ku."

"Amin Ya Allah Hajiyata. To ni na wuce. My Queen ki kula da kan ki da baby,sai na dawo. Ga wannan ko za a siyi wani abun."

Nera dubu ya ajiye mata a gabanta, sannan ya bawa Hajiyansa dubu biyu ya bar gidan ransa ƙwal kamar an yafe masa zunubansa. Fauziyyah kuwa murmushi kawai ta yi,dan kuwa banda Allah babu wanda ya kaita sanin halayyen Abbas gaba ɗayansu. Kuɗin ta ɗauke daga ƙasa ta adana masa abunsa a parlourn. Sallama Barirah ta yi ta ce ta taso su je su yi wanka. Babu musu ta miƙe ta shiga ɗaki ta ɗauki abubuwan da take da buƙata ta wuce banɗaki.

Suna kammala wankan Barirah ta ce.

"To bari na ɗan kwanta na huta tinda ga Hajiya nan,idan anjima sai na tashi na ɗora abincin rana,idan kin ji yunwa kafin na farka ki shiga kitchen ɗina ki haɗa shayi mai kyau ba tsalala ba.kayan tea ɗin suna cikin loka,sai ki buɗe ƙaramin fridge akwai bread ki ci ki ƙoshi. Idan na tashi da wuri zan yi miki tuwo,mai jego sai da abinci mai gina jiki. Ko akwai abinda kike buƙata na yi miki yanzu?"

Kallon Barirah kawai Fauziyyah take yi,ji take yi kamar ta ɗauketa ta buɗe zuciyarta ta sanya ta a ciki tsabar son da take yi mata. Babu zato ko tsammani Barirah ta ji Fauziyyah a jikinta ta saki wani marayan kuka,nan da nan idanuwanta suka ciko da ƙwalla itama. Tsananin tausayin Fauziyyah da take dannewa ya taso ya mamaye zuciyarta. Da ƙyar Fauziyyah ta ɗaga ta ta durƙusa ta hau godiya,cikin sauri Barirah ta ɗaga ta ta na sassauta murya ta ce.

"Kar ki manta kayan shayin nan fa an saye su ne da kuɗin da yayan ki ya aiko a saya maki abun duk da kike buƙata ba da kuɗin mu ba,dan haka babu wata godiya da za ki yi min,sai dai ki godewa Allah,ki kuma godewa Yayan ki."

"Kuma ai dole ne na gode muku da ke da Yayah Shehu,Allah Ya saka muku da alkhairi ya baku abinda kuke nema duniya da lahira."

"To Amin,bari na wuce ɗaki sai anjima ɗin."

Ɗaki Barirah ta wuce ta bar Fauziyyah na wanke idanuwanta dan kar Hajiya ta gane ta yi kuka. Ta na gamawa ta shiga ɗaki ta shirya cikin wata tsohuwar atampar ta. Ta na fitowa Hajiya ta haɗe fuska ta ce.

"Me zan gani haka wai ɗuwaiwai ya mutu ya bar zani? Wannan atampar baki rabu da ita ba dama Fauziyyah? Don Allah wuce ki je ki sauya wasu kayan tin ƴan barka basu fara zuwa ba."

Murmushin yaƙe Fauziyyah ta yi kafin ta ce.

"Ai Hajiya tinda cikin nan ya tsufa My king yake kwashe wanki na kaf ya kai wajen wankau,sai dai kawai na zo na ga an dawo da su a wanke,to yanzu ma tinda na ga babu kaya na na ce duk yanda akai ya kai su wajen wanki ne da muna asibiti."

"Au dama ba shine ya kai ki asibitin ba?"

Kame-kame Fauziyyah ta fara yi,cikin sauri ta ce.

"Eh ba shi ya kaini ba,sai daga baya ya je,da yake na fara naƙuda baya nan sai Aunty da mijinta suka kai ni a motar Malam Idris."

Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke mai ƙarfi,cikin sanyin murya ta kalli Fauziyyah ta ce.

"Ai da har hankalina ya tashi,na zaci har yanzu Abbas na yi miki halayensa na baya,na ji daɗi matuƙa da ya sauya."

Jinjina kai kawai Fauziyyah ta yi ba tare da ta ce komai ba. Gyangyaɗin da Fauziyyah ke yi ne a zaune ya sanya Hajiya bata umarnin ta je ɗaki ta kwanta. Ta na shiga ɗakin babu jimawa ƴan barka suka dinga shiga gidan. Hajiya ce ta yi ta tarbon su ta na sanar da su Fauziyyah ta samu bacci.

Da misalin ƙarfe biyu na rana Barirah ta farka daga baccin gajiya. A gaggauce ta yi alwala ta yi sallah,ganin babu wadataccen lokaci sai ta ɗora taliyar da ta ji naman rago da kayan lambu,ta na gamawa ta zuba wa kowa ta fara kaiwa Hajiya da ke zaune a saman abun sallah ta na jan carbi. Na Fauziyyah kuma a wani sabon babban food flask ɗinta ta zuba,sai ta kai mata ɗaki da plate da duk abinda zata buƙata. Ko ta kan Abbas bata bi ba dan ta san a cikin na Fauziyyah zai ci tinda da yawa.

Babu jimawa kuwa Abbas ya yi sallama shi da abokansa,jaririyar ya shiga ya ɗauka ya na wasar baki tare da sanar da Hajiya tare yake da abokansa. Ko da ya koma sai ya ga har sun shimfiɗa tabarma sun zauna,miƙa musu yarinyar ya yi yana faɗin.

"Kun gani ko? Dama na faɗa muku da ni take kama ai."

Fatan alkhairi suka yi musu da taya shi murnar zamowa uba da yayi. Daga nan sai ya karɓe ta ya mayar da ita wajen Hajiya. Ɗaki ya shiga ya tarar da Fauziyyah zaune a bakin gado za ta zuba abinci ta ci,haɗe fuska ya yi ya ce mata.

"Dan iskanci kina jin na dawo shine kika yi zaman ki? Ko ki ma ɗan leƙo ki yi min sannu da zuwa ko? Da kyau,ba laifin ki bane. Ina abincina ba ni kaɗai bane ina da baƙi."

Kallon abincin ya yi a wulaƙance ya ce.

"Ɗan wannan abincin kawai aka dafa?"

Kasa cewa komai Fauziyyah ta yi,saboda rasa ta inda za ta fara yi masa bayani take yi idan yana faɗan rashin dalili. Kafin ta yi wani yunƙuri ya rufe flask ɗin ya ɗauka ya fita musu da shi waje shi da abokansa,ba tare da ya damu da tambayarta taci ko bata ci ba.

Tagumi Fauziyyah ta buga tana jin yanda cikinta ke kukan yunwa. Barirah na ɗaki ta ga gilmawar sabon food flask ɗinta a hannun Abbas,sai ta fito a fusace ta nufi ɗakin Fauziyyah. Ta na zuwa ta tarar da ita a bakin gado ta zabga tagumi,cike da masifa ta buɗe baki za ta yi magana,amma Fauziyyah ta yi saurin tashi tsaye ta kama hannunta ta jimƙe sosai,ganin yanda idanuwanta suka ciko da ƙwalla ne ya sanya Barirah sassauta muryarta ta ce.

"Wai kina nufin baki ci abincin ba wannan ɗan rainin wayon ya fitarwa garada wahalata waje?"

Cikin rawar murya Fauziyyah ta ce.

"Don Allah Aunty idan har kina son farincikina ki yi haƙuri ki barsu su ci su tafi. Kin ga Hajiya na nan bana so ta san me yake faruwa."

"Idan kuma bana son farincikin naki fa? Dalla ni sakar min hannu."

A hasale Barirah ta ƙwace hannunta ta fita daga ɗakin.......... [12/9, 8:37 PM] HAERMEEBRAERH: MUGUN MIJI.

RIBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✍️✨