PAGE 1
by @1239900
Tafe take tana bin kowanne lungu da saƙo na gidan da kallo kamar tsofaffin dubagarin da aka yi a zamanin baya. Tabaran idanunta ta cire ta kalli Kulu dake duƙe tana goge uniform ɗin Kubrah wadda ta baro kwance a saman kujera ta na yin assignment ɗin ta da bata samu damar yi ba a daren jiya,ƙwafa ta yi sannan ta ce,
"Ke Kulu ban hana ki yiwa sangartattun yaran nan guga ko wanki ba? Akan wanne dalili ɗana ya ɗauke ki aikin wanke-wanke da shara sai ki dinga tsallake hurumin ki kina shiga abinda babu ruwan ki?"
Nan take jikin Kulu ya ɗauki rawa kamar mai jin sanyi, kanta duƙe baki na makyarkyata ta ce,
"Hajiya Dada am dan Allah ki yi haƙuri,Kubrar ce babu lafiya jiya ta kwana da zazzaɓi shi yasa bata samu damar wanke tufafin nata ba balle ta goge,amma inshaa Allahu daga yau zan dinga tsayawa a matsayi na."
Cikin yatsina fuska Hajiya Dada ta ce,
"Da dai ya fiye maki,idan kuma ba haka ba zan sa kema a kore ki a samo wata,babu wanda ya isa ina koyawa jikokina tarbiyyar da aka gaza basu ya rusa min."
Kafin Hajiya Dada ta sake yin magana Kulu ta tattare kayan da take gogewa ta nufi ƙofar da zata sada ta da ɓangaren Ruƙayya,ta na shiga ta tarar da Kubrah zaune ta na shan tea da soyayyan ƙwai,da dukkan alamu ta yi wanka ta shirya kayan ta kawai take jira akai mata ta sanya,ganin Kulu riƙe da kayan makarantar ta rabi a goge rabi babu guga ne ya sanya ta miƙewa baki cike da ƙwai ta ce,
"Baaba Kulu ina gugar kuma?"
Juyawa Kulu ta yi tana kallon hanyar shiga parlourn ta kama leɓen ta na ƙasa ta haɗe da na sama ta riƙe da yatsun ta biyu,yin hakan da ta yi kaɗai ya gama isarwa da Kubrah saƙon ta,zumɓura baki Kubrah ta yi kafin ta karɓi kayan ta a zuciye ta wuce ɗakinta ta fara goge su da kanta. Zuciyar ta cike take da maganganu amma ta sani sarai yin maganarta ta daidai yake da ciwa mahaifiyarta mutunci da Hajiya Dada za ta yi,dan haka bakin ta ta tsuke ta kammala gugar ta sanya kayanta ta leƙa ɗakin ƙannen ta guda biyu Ihsan da Mubeenah,cikin ɗaga murya ta ce musu,
"Wato ba za ku yi sauri ku fito mu tafi ba har sai Hajiya Dada ta shigo ta tarar da ku ko?"
Cikin sauri ƴan matan da ba za su wuce shekaru sha uku da sha ɗaya ba suka fito suna rataya jakar su a kafaɗun su,a tare suka bar sashen nasu suka wuce sashen Hajiya Dada,zaune suka tarar da ita a saman tabarmar da ake ajiye mata kayan karin kumallon ta tana ta juya farfesun kayan cikin da ta zuba dan karyawa tana mitar an tsula masa ruwa. Gaishe ta su Kubrah suka yi kafin su yi mata sallama za su wuce makaranta,kamar ba ita ce ta gama masifa da muzurai ba haka ta sake musu fuska suka gaisa sannan ta yi musu addu'ar dawowa lafiya tare da samun ilimi mai albarka,sai da suka miƙe za su tafi Hajiya Dada ta kirawo Kubrah ta ce,
"Wato Kubrah jiya saboda ɗan aikin girkin da na saka ki da yamma,shine ya sa ki kwana da zazzaɓi har kika baiwa Kulu wanki da guga ko? Ki kiyaye ni fa Kubrah,kar na sake ganin haka ta faru daga yau,ni ba zan lamunci sakarci da sangarta ba,tinda iyayen ku sun kasa haifar min jika namiji ba zai yu ku kuma ku zama malalata ba,wuce ki bani waje kar ku makara."
Duƙar da kai Kubrah ta yi kafin ta sake yiwa Hajiya Dada sallama ta bar sashen nata rai a ɓace,a hankali ta furta,
"Wai girkin mutum goma sha takwas ne ɗan aiki a wajen ta,da alama tsohuwar nan so take ta nakasa wata gaɓar ta jiki na kafin rai ya yi halin shi a kan ta."
Sashen mahaifinsu ta bi ƙannen ta suka gaishe shi sannan suka yi masa sallama suka wuce wajen da motocin gidan ke ajiye. Drivern dake kai su makaranta ne ya taso da sauri yana washe baki,gaida shi suka yi kafin su rankaya gaba ɗaya su shiga haɗaɗɗiyar motar tasu su wuce makaranta.
**********************
Cikin shiga ta alfarma wadda ke nuni da irin dukiyar da ahalin Alhaji Jubair Ɗan Fullo ke da ita Ruƙayya ta fito dan zuwa gaishe da Hajiya Dada wadda take a matsayin surukar su. Tana shiga ta tarar da Uwa zaune a saman kujerar dake nesa da ta Hajiya Dada suna gaisawa,cike da murmushi ta ƙarasa shiga ta samu waje ta ɗan duƙa ta gaishe da Hajiya Dada,babu yabo babu fallasa Hajiya Dada ta amsa gaisuwar ta kafin ta ce,
"Maza samu waje ki zauna dama ina da magana daku dikan ku,ke Uwa ban san me kike nufi ba da har yau kin kasa maida hankali ki yi abinda ya sa na aurawa ɗana ke,shekaru fa tafiya suke yi,ku bar ganin Allah ya yi maku kyawun ƙira da wadata kuna nan kamar yara kuna lokacin ku,nan gaba kaɗan haihuwa zata tsaya maku,to idan baku kama jiki kun haifawa ɗana magaji ba sai yaushe za ku yi hakan?"
A yatsine Uwa ta kalli Hajiya Dada ta ce,
"Hajiya Dada ni dai dan Allah ki dena ci min mutunci a gaban kishiya,kullum kika tashi magana sai kin goranta min dalilin auro ni da kika sa Alhaji ya yi,haihuwa ai nufin Allah ne ba na mutum ba ballantana na baiwa kaina."
Baki Hajiya Dada ta saki tana kallon Uwa dake wani jujjuya idanu ta na murguɗa baki,maida kallon ta tayi ga Ruƙayya da ke zaune kanta duƙe ta na wasa da zoben zinaren dake yatsan ta,fuskar ta ɗauke da murmushi kamar koda taushe,cikin murmishi da son kawar da ɓacin ran da ta jiyo alamun Uwa ta dasawa Hajiya Dada ta ce,
"Inshaa Allahu Hajiya ba zaki bar duniya ba sai kin ga magajin Alhaji,ki yi haƙuri ki kwantar da hankalin ki,mu barwa Allah komai."
A hankali fushin da ke saman fuskar Hajiya Dada ya sauka,ta ce,
"Allah ya yarda Ruƙayya,Allah kuma ya sa wannan jika da nake ƙwalafucin samu ya fito daga wajen ki,dan ko babu komai ba ƙiyayya ce ta sa na ce Jubair ya ƙara aure ba,babban burin dake cikin zuciyata shine ya yi sanadiyyar da yasa na ce Jubair ya auro Uwani,duba da cewa a gidan da ta baro dika yara maza take haifa,sai gashi anan ta kasa koda ɓatan wata ne."
A zuciye Uwa ta buɗe baki da nufin gaggayawa Hajiya Dada baƙar magana,cikin sauri ta ja bakin ta ta kulle saboda shigar Jubair cikin parlourn sanye da wani yadi mai azabar laushi da kyau ruwan ƙasa,agogon shi na fata ruwan ƙasa da takalmin shi baƙi su suka ƙara yiwa shigar tashi kyau,karin hular shi Ruƙayya ta kalla ta saki murmushi ta sake duƙar da kanta ƙasa ta na wasa da zoben ta,murmushi shima ya sakar mata yana jin daɗin yanda take da tsananin kunya da kawaici.
Ƙamshin turaren shi ne ya sanya Uwa sake matsawa daf da shi ta narke jiki da murya ta ce,
"Har ka fito kenan gorko am."
"Eh alhamdulillah Allah ya nufa na fito,Hajiya Dada barka da safiya."
"Barka dai Boɗɗo manga,ka tashi lafiya?"
"Lafiya ƙalaou ya tashi Hajiya,ai cewa..."
Kallon da Jubair ya watsawa Uwa ne ya sanya ta tsuke bakin ta,nan take Ruƙayya da ta fahimci me yake nufi ta miƙe ta yiwa Dada Sallama ta bar sashen,sai da Uwani ta gama jan jiki tana zumɓura baki sannan ta miƙe ta bar sashen.
Tana fita Hajiya Dada ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce,
"Boɗɗo kana ji na ko? Yau idan ka dawo daga office ka zo zamu yi magana mai muhimmanci da kai."
Nan take gaban Jubair ya yanke ya faɗi,dan kuwa a duk sanda Dada ta ce masa tana da magana mai muhimmanci da shi abun baya ƙare musu ta daɗin rai........ [03/04, 2:29 pm] asiyahabibu93: DUK NISAN DARE......
RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH
*Ko labarin bai yi maki ba yanzu ki adana a wani wajen,saboda kada sai na yi gaba ki ce a tura maki daga farko.*