PAGE 2
by @1239900
Sai da Hajiya Dada ta gyara zama ta karɓi mug ɗin da Jubair ya gama haɗa mata tea ta kurɓa sau uku kafin ta ajiye a gabanta ta kalle shi,tanƙwashe ƙafafunta ta yi ta sake kallon shi da kulawa ta ce,
"Boɗɗo am kar ka ga na dame ka akan maganar samun magajin nan da nake yawaita yi maka,ina so ka sani tin a shekarun baya rayuwa ta sauya balle kuma a yanzu da zamani ya kara tafiya,ba wai ina kushe yara matan da Allah ya baka bane,kai ka san ina son su sosai a zuciyata,kawai ina jin tsoron duk sanda aka ce yau babu kai bamu san ya rayuwar su zata kasance ba,ina jin tsoron kada ƴan'uwan mahaifinka su maimaita musu abinda suka yi maka a lokacin da mahaifin ka ya rasu ya barmu daga ni sai kai tare da tarin dukiya,kar ka manta sai da muka rasa muhallin zama duk yawan gidajen mahaifin ka,sannan sai da ƙwayar hatsi ta gagari bakin da ke ciyar da mutane sama da goma a rana,Jubair ka dage ka nemi wani auren ko Allah zai sa a dace ka haifi ɗa namiji wanda zai taso ya tallafi zuri'ar ka bayan babu kai."
Cikin zuciyar Jubair cike take da maganganu masu tarin yawa,sai dai ba zai iya furta mata su ba,tinda ba yau ne suka fara irin waɗannan maganganun ba,fatan shi bai wuce Allah ya cika mata burin ta ba ya bashi ɗa namiji mai albarka. Cikin sanyin murya Jubair ya ce,
"Inshaa Allahu Hajiya burin ki zai cika,zaki ga ɗa namiji a gidan nan watarana,abinda nake so ni dake mu yi shine,mu ci gaba da tsananta addu'a,sannan mu zuba idanu har Allah ya amsa mana ya cika mana burin mu."
Sosa ƙeyar shi ya fara yi yana sunkuyar da kai tare da murmushi,kallon shi Hajiya Dada ta yi itama fuskar ta ɗauke da murmushi ta ce,
"Sanar dani daddaɗan labarin dake cikin zuciyar ka Babana."
Miƙewa ya yi tsaye ya ɗebi wayoyin shi ya kama hanyar fita,sai da ya kusan zuwa bakin ƙofa sannan ya ce,
"Da alama wannan karon baki gano cewa Ruƙayya na ɗauke da juna biyu ba,wataƙila addu'ar mu Allah zai amsa shi yasa baki gane ba har ya kai watanni huɗu a duniya."
Yana kaiwa nan a maganar shi ya buɗe ƙofa ya fita yana dariya mai cike da jin nauyin mahaifiyar tashi,Dada kuwa kasa motsawa tayi saboda wani irin farin ciki da ya lulluɓe ta,murmushi take ta zabgawa tare da godewa Allah a fili. Kasa ci gaba da karyawar ta yi ta miƙe ta ja sandar ƙarfenta da take amfani da ita saboda ciwon guiwa ta nufi sashen Ruƙayya.
Ko da ta shiga ta tarar da Kulu na goge parlour tana ƴan waƙe-waƙenta irin na dattijan da suka taso a ƙauye,cikin fara'ar da Hajiya Dada ta kasa ɓoyewa ta ce,
"Kulu aiki ake yi ne?"
Sai da Kulu ta durƙusa ta kwashi gaisuwa sannan ta washe baki ta ce,
"Eh Hajiya Dada aiki nake ɗan ragewa kafin na je na ɗora girkin rana."
"Allah ya taimaka, ina ita uwar ɗakin naki take?"
"Ta na ciki Hajiya, ko a kira ta ne duk da dai na ga bata jima da kwantawa ba,da alama bacci zata maida."
"Allah sarki,barta ta rintsa anjima zan sake dawowa."
Kakarin aman da Hajiya Dada ta jiyo daga ɗakin Ruƙayya ne ya sanya ta takawa ta nufi ɗakin cikin sauri,tana shiga ta tarar da Ruƙayya zaune a ƙasan makeken banɗakin nata da ya gaji da haɗuwa ta na ta kelaya amai wanda banda ruwa da majina babu komai a cikin shi. Cike da tausayawa Hajiya Dada ta kamata ta zaunar da ita a saman toilet wanda marfin shi ke sanye da carpet,a galabaice Ruƙayya ta buɗe idanun ta da suke lumshewa saboda azaba ta kalli Dada, cike da jin kunya ta hau kame-kame tana son ta ja towel ta rufe jikin ta dake sanye da wata doguwar riga mara nauyi.
"Ke samawa kan ki lafiya ki wanke fuskar ki kin ji,wataƙila aman ma ya ragu,yo Allah na tuba wace kunya ce kuma kike ji Ruƙayya aure shekara da shekaru ana tare? Maza yunƙura ki kwarawa fuskar ki ruwa ko kin ji salama,anya ma kin karya kuwa? Dan na ga alamar babu komai a cikin ki da ya wuce ruwa, Kulu !"
Hajiya Dada ta ware murya ta ƙwalawa kulu kira,kamar wadda ke tsaye a bakin ƙofa haka Kulu ta shiga banɗakin ta duƙa a gaban Hajiya Dada cike da girmamawa,idanun ta ne suka sauka akan aman da Ruƙayya ta yi sai ta hau yi mata sannu tare da fatan Allah ya bata lafiya ya rabata da abinda take ɗauke da shi a cikin ta lafiya.
Shiru Ruƙayya ta yi ba tare da ta amsa ba saboda tsananin jin kunyar Hajiya Dada,murmushi Hajiya Dada ta yi sannan ta ce,
"Kulu kama ta ki taimaka mata,da ta kimtsa a dafa mata wani abun ta ci ta sha shayi,idan kuma kunu take so a dama mata,kar a bari ta dinga zama da yunwa,Allah ya baki lafiya ya sa wannan karon ki haifa min magajin Boɗɗo."
Kulu ce ta amsa addu'ar Hajiya Dada kafin ta tashi daga durƙuson da tai ta fara taimakawa Ruƙayya kamar yanda Hajiya ta yi mata umarni. Ita kuwa Dada sashen Uwa ta nufa ta same ta zaune a parlour ta na waya da ƙawarta, jin shigar Hajiya Dada parlourn ta ne ya sanya ta yin saurin kashe wayar ta miƙe tsaye tana zare ido tare da fatan Allah yasa Hajiya Dada bata ji maganganun da take yi a waya ba.
Ko zama Hajiya bata yi ba ta kalli Uwa ta ce,
"Uwa ina so ki sani wannan rashin kunya da firiritar da kike yi a gidan nan babu inda za su kai ki,ki bar ganin alaƙar zumuncin dake a tsakani na da mahaifiyar ki har ya yi sanadiyyar da na roƙi alfarma aka aura wa Boɗɗo ke,kamar yanda na roƙi ƴar'uwata aka bani auren ki,ina iya sanya ɗana ya sake ki ya kawo wata,domin ba kan ki farau ba,kar ki manta mata ɗai-ɗai sama da uku Jubair ya aura kafin ke,dan haka a kullum ki dinga sanyawa ran ki zaki iya komawa rayuwar zawarcin da kika bari in har baki dena sa'insa da ni ba,ni ba sa'ar ki bace,ba zan lamunci rashin tarbiyya ba,kin ji na faɗa miko? Ga mata can sun dage suna ɗaukar ciki ke kina nan kina kishin banza."
A gigice Uwa ta kalli Hajiya Dada,domin kuwa duk a cikin maganganun ta babu wanda ya daki fatar jikin ta balle ya huda tsokar jiki da ƙashin ta har ya yi nasarar shiga zuciyarta,cikin tashin hankali ta buɗe baki zata yi magana sai ta ga Hajiya Dada na rufe mata ƙofar parlourn ta.
Hankali a tashe ta ɗauki wayar ta ta wuce sashen Rukayya,ta na shiga ta ganta zaune Kulu ta kara mata pillow ta kwanta,cike da kasala ta ce,
"Kulu kin dai san warin farfesun nan ne ya tada min da zuciya har nake aman nan ko? Ni dai a barni da ruwan sanyi idan na sha ina jin daɗi a rai na,lafiya kalau na tashi gashi nan yanzu kin sa na rabke."
Cikin murmushi Kulu ta ce,
"Daurewa zaki yi ki ci koda kaɗan ne Hajiyata,ko ba dan ke ba ki ci dan abinda ke cikin ki,zaki samu kuzari."
Shagwab'e fuska Ruƙayya ta yi kafin ta ce,
"Wancan ma fa ban ci ba,na ajiye na koma ɗaki na kwanta,shine fa ina kwanciyar na ji amai na damuna,dan Allah kar ki sake kawo min shi ki dai bani ragowar kunun gyad'ar Alhaji na sha."
A gigice Uwa ta kalli Kulu da Ruƙayya ta ce,
"Wacece ke da cikin? Kar dai ki sanar dani Ruƙayya ciki kika sake yi ni ina zaune ko ɓatan wata ban taɓa yi ba?"
Wani irin kallon mamaki suka bi Uwa da shi,nan take idanun Uwa suka fara zubar da hawaye ta bar sashen Ruƙayya a guje ta na kuka kamar wata ƙaramar yarinya,kallon juna su Ruƙayya suka yi suna tambayar junan su da ido me hakan ke nufi? Kasa baiwa junan su amsa suka yi sai kawai Kulu ta ci gaba da zubawa Ruƙayya ragowar kunun gyad'ar da ta damawa Jubair.
A bangaren Jubair kuwa tinda driver ya ajiye shi a office ya shiga ya samu waje ya zauna yana nazarin maganganun Hajiya Dada,shin ya zai yi ne ya samar mata da farin cikin da take nema shekara da shekaru? Ganin kan shi ya kulle ne ya sanya shi ɗaukan wayar shi ya lalubo lambar da yake ganin zata bashi mafita akan matsalar da ke damun zuciyar shi.............. [03/04, 2:29 pm] asiyahabibu93: DUK NISAN DARE...
RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH