PAGE 3
by @1239900
Sai da Jubair ya kira wayar sama da sau biyu kafin a amsa,a can ɗaya ɓangaren ya jiyo ana ta yin faɗa da harshen turanci,murmushi Jubair ya yi kafin ya ce,
"Bro ka kwantar da hankalin ka ka dena tada jijiyar wuyan ka akan ƙanƙanin abu,ji yanda ka ke faɗa da tsakar daren nan dan na san ku yanzu dare ne a wajen ku."
'Exactly my point bro,ita to bata san dare ba sam,can you believe this girl wai fita zata yi da friends ɗin ta?'
"Please ka dena matsa mata,she is just a kid,ka dinga yawaita yi mata addu'a tinda kai da kanka ka san irin wajen da kuke,dole ne irin haka ta faru dama."
'No ba dole bane ta zama kamar su,mutane nawa ka sani a nan ƙasar da ke riƙo da addininsu da al'adarsu? Amma ita a kullum abinda take so shi zata aikata ko muna so ko bama so,kana ganin hakan ya dace?'
Jinjina kai Jubair ya yi kamar Ammar na ganin shi kafin ya ce,
"Bai dace ba gaskiya,yanzu yanda za ai bani ita na mata magana."
Cikin abinda bai fi mintuna biyu ba Jubair ya ji muryar matashiyar budurwar ta na gaida shi a shagwab'e,da jin muryar ta zaka gane kuka take yi,da wata iriyar murya Jubair ya kira sunan ta,sai da ta gaji da yanga da shagwab'a kafin ta amsa da,
'Yes Papa.'
Da harshen hausa Jubair ya furta,
"Babyn Papa me yasa kike rashin jin magana? Yanzu dare ya yi ki koma ki kwanta kar na sake jin kin fita da dare."
'Me yasa Papa?'
"Saboda ke musulma ce babu kyau mace ta fita da dare da friends maza,haramun ne Allah ya hana."
'Ok idan da mata ne fa?'
"Wai ina za ku je ma tukunna?"
'Club'
"Subhanallahi ! Ku yi me da ƙananan shekarun ku?"
'Today is Elsa's birthday Papa,we just want to have some fun, please Papa ka barni in tafi suna ta jira na.'
Yarinyar ta ƙarasa maganar ta cike da matsananciyar shagwab'a,nan take Ammar ya lumshe idanun shi cike da takaici dan ya san ta taɓo daidai inda yake gudu a wajen ɗan'uwan nashi,Jubair kuwa sake narkewa ya yi a kujera ya na jin yanda Babyn tashi ke zuba shagwab'a kamar ta na ganin shi,cikin sanyin murya ya ce,
"My beautiful Queen ki yi haƙuri ki je ki kwanta ki yi bacci,na yi maki alƙawari zan aiko maki da kuɗi mai yawa da zaki sai mata wani abu mai kyau ki bata, bana so ki dinga fita da dare,duk abinda iyayen ki basu so ki dena yin shi kin ji? Haramun ne Allah na ƙona masu tsallake maganar iyayen su a wuta,ko ki na so ki shiga wutar Allah?"
A shagwab'e ta girgiza kai,cike da murmushin samun nasara Ammar ya karɓi wayar ya ce,
'Bro na gode,ka ganta can ta fita waje,na tabbata sallamar su zata yi,ina mamakin yanda yarinyar nan ke tsananin jin maganar ka,ko da yake bari na dena mamaki,abun na tsakanin ƴa da uba ne,babu mai shiga gudun jin kunya.'
Murmushi Jubair ya yi mai sauti kafin ya ce,
"Lallai kam,gwanda da ka gano hakan da kan ka."
'Ka yi haƙuri mun ɓata maka lokaci,me ya sa ka kira ni a wannan lokacin? Na san in dai ba wata matsalar ce ta taso ba baka kira na da dare.'
Ajiyar zuciya Jubair ya sauke mai nauyi kafin ya ce,
"Humm same matsalar da na saba fuskanta ce wannan karon ma ta tunkaro ni,Hajiya ta kafe sai na ƙara aure saboda samun magaji,na rasa ta yanda zan ɓullo mata,fata na Allah yasa wannan cikin da Ruƙy ke ɗauke da shi mu samu namiji,ka ga hankalin kowa sai ya kwanta."
'Allah sarki Hajiya,ta kasa manta baya ne shi yasa,ka san bayan Allah da manzon sa Uwa tafi kowa so da tausayin ɗan ta,dan haka ni duk abinda take yi baya damu na,hasali ma daɗi nake ji a ƙalla muna da ita,ka sani bani da kowa yanzu a duniya da ya wuce Hajiya Dada, dan haka dole ne mu haɗa kai mu faranta mata matsawar abinda ta nema a wajen mu bai kaucewa hanyar addini ba,wanda na sani, ka sani ba zata taɓa umartar mu da mu yi abinda yake haramun ba.'
"Haka ne Bro,yanzu to menene mafita?"
'Mafita ɗaya ce ka lallashe ta for now,ka nuna mata ta yi haƙuri a jira a ga me Ruƙy zata haifa,idan aka samu abinda ake nema shikenan,maganar aure babu ita,idan kuma ba a samu ba sai ka nemo matar aure kamar yanda take so ka aura,kaga kafin nan sai mu dage da addu'ar Allah yasa a dace da rabon alkhairi.'
"Alhamdulillah, na gode ɗan'uwana,ban taɓa neman shawara a wajen kaba ba tare da ka kawo min mafita ba,wannan shawarar ita zan bi...ƙarar me nake ji haka kamar kiɗa?"
Dariya Ammar ya yi kafin ya ce,
'A gida ake Birthday party ɗin,kai wannan ƴar taka duniya ce,mugun tsoron ta ƙawayen suke ji har mazan,na tabbata zuwa ta yi ta ce musu a yi party'n anan,ni kuma ba zan hana su ba,i have my CCTV camera everywhere,a yi party lafiya.'
Dariya suka yi,kafin su ci gaba da hirar su akan business ɗin da Ammar ke yi da kuma ɓangaren aikin gwamnatin da Jubair ke yi.
******************************
Tinda Hajiya Dada ta tabbatar da cikin dake jikin Ruƙayya take bata wata iriyar kulawar da bata taɓa bata ba a lokutan baya da take haihuwa,domin kuwa tana ji a jikin ta lokacin samun Magajin Jubair ne ya zo. Ita kuwa Ruƙayya a kullum cikin zullumi da tunani take,shin ya Hajiya Dada za ta yi idan ta sake haifar mace? Wannan tunanin na gigita ta har ya sanya ta fara ramewa. Hajiya Dada kuwa ta yi zaton ko rashin cin abinci ne yake sanya ta rama,dan haka da kanta watarana take shiga kitchen da su Kubrah tai ta nuna musu yanda ake wasu girke-girken na gargajiya,musamman wanda masu ciki suka fi kwaɗayi,dangin su; alalen gwangwani da manja da yaji,dambun masara da manja da yaji,dambun shinkafa da zogale da gyad'a da yaji,ɗanwakeda mai da yaji,ƙosan rogo da masar gero wanda take sanya Kulu ta daka ƙuli-ƙuli mai daɗi.
Duk abinda suke yi Uwa na samun labari a wajen mai aikin ta Ubaida,dan haka baƙin ciki da damuwa sun taru sun mamaye zuciyarta ta rasa ta inda zata ɓullo wa lamarin,takaicin duniya ya haɗe mata waje ɗaya musamman idan ta tina maganar ƙarin auren da Hajiya Dada ta sanya Jubair yi,gaba ɗaya sai hankalin ta ya kasu kashi biyu.
Yau ma kamar kullum kwance take ta gaza rintsawa sai juyi take yi a gado,kewar mijinta da a kullum take jin da ita ya fara aura ko bata haihuwa babu wanda ya isa ya sanya shi ƙara aure ballantana su raba wajen kwana. Ƙwafa ta yi ta ja dogon tsaki kafin ta tashi zaune ta ja rigar baccin ta ta rufe jikin ta da kyau,sauka ta yi daga gadon ta faɗa banɗaki ta yi fitsari ta fito,hamma ta yi kafin ta kalli kanta a madubi tin daga sama har zuwa faffaɗan ƙugun ta,a hankali ta furta,
"Me na nema na rasa a jiki na da Jubair ya fi son Ruƙayya akai na? Ko da na san ba zan nuna mata komai ba a fagen kyau amma na fita wayewa da sanin duniya,duk yanda nake sake masa jiki na na gatanta shi bai sa hankalin shi ya karkato waje na ba,ga uwa uba ɗokin haihuwar nan da suke yi kamar ba a taɓa haihuwa ba a gidan nan,meye laifi na dan ban haihu ba ake fifita wata akai na? Ba zai yuwu na zauna ina ji ina gani wata banza ƴar fulanin rugga ta fini daraja a idon miji ba,ko banza ni jinin shi ce dole ya so ni fiye da yanda zai so ta,Allah ya kaimu safiya komai zai zo ƙarshe a gidan nan."
Uwa na gama cin alwashi da surutan ta ta bi lafiyar makeken gadon ta ta kwanta,sai da ta daidaita sanyin AC'n ɗakin sannan ta lulluɓe jikin ta babu addu'ar bacci ta ajiye remote ɗin AC a gefen gadon ta rintse ido.
Washegari da sassafe ta tashi ta sheƙa wanka ta kira Ubaida ta ce ta gyara mata ɗakin ta da wuri dan zata fita,a ƙa'idar ta idan zata fita ko zata bar sashen ta a bude sai ta kulle ɗakunan ta guda ukun.
Cikin sauri kuwa Ubaida ta hau gyaran gidan da ba wani datti ya yi ba ta haɗa musu abin karyawa,sai da suka ci suka ƙoshi sannan Uwa ta fita sashen Hajiya Dada cikin kwalliya ta alfarma sai baza ƙamshi take yi,ko da ta isa ta tarar da sashen Hajiyan shiru,hakan ya nuna har a wannan lokacin Hajiya Dada bata fito parlour ba. Bakin ta ɗauke da sallama ta tsaya a ƙofar ɗakin Hajiya Dada,sai da ta sanya fuskar tausayi sannan ta murɗa hannun ƙofar ta shiga ɗakin, a zaune ta tarar da Hajiya Dada riƙe da littafin addu'o'in ta tana karantawa,sai da ta kammala abinda take yi ta kalli Uwa dake ta sharar hawaye ta na goge majinar da babu ita a hancin ta,murmushi Hajiya Dada ta yi dan kuwa ta riga da ta san halin ƴar ta ta, ta san watarana haka zata faru,dan haka sai ta yi mata nuni da kusa da ita,cike da shagwab'a Uwa ta isa gaban Hajiya Dada ta tanƙwashe ƙafa ta sake fashewa da kuka,a hankali Hajiya Dada ta ce,
"Ki sanar dani abinda ya kawo ki wajena Uwata, ko kuma ki koma sashen ki,idan kin gama kukan sai ki dawo."
Hawaye Uwa ta share sannan ta gyara zamanta ta ce..................... [03/04, 2:29 pm] asiyahabibu93: DUK NISAN DARE...
RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH