PAGE 4
by @1239900
Idanu Hajiya Dada ta zubawa Uwa da ke sharɓar kuka ta na bayani,ganin yanda kalaman ta ke dukan zuciyar Hajiya Dada ne ya sanya Uwa sake rushewa da kuka ta ce,
"Na gaji Hajiya, na gaji, shekara ɗai-ɗai har shekara goma ace har yanzu ko ɓatan wata ban taɓa yi ba? Gashi yanzu Yah Jubair ba ta ni yake yi ba,dama haka yake yi min a duk sanda Ruƙayya ta samu juna biyu,ballantana yanzu da ya ƙwallafa ran zai samu magaji daga wajen ta,dan Allah ki yi mini izini na je gida in nemi maganin haihuwa ko Allah zai sa na dace nima."
Kukan da take rizga ne ya sake karyar da zuciyar Hajiya Dada, nan take ta ɗauki duka laifin abubuwan dake faruwa ta ɗorawa kanta,domin kuwa da bata fifita haihuwar ɗa namiji akan mace ba da ƴar ƴar'uwar ta bata riski kanta a cikin wannan hali na tsangwamar kai da damuwa ba,uwa uba ƙiri-ƙiri take nuna banbanci tsakanin surukan nata biyu,lallai son samun magajin Jubair na neman ya jefa ta ga halaka ta hanyar raba kawunan matan ɗan ta,cikin murya mai taushi Dada ta ce,
"Uwata ki yi haƙuri akan duk wani abu da kika ga yana faruwa a gidan nan,ke yarinya ce baki san irin wahalar rayuwar da muka fuskanta bane a lokacin da na rasa mahaifin Jubair,na yi zaton rayuwata zata ƙare nima saboda tsananin shiga ƙunci,damuwa ɗimuwa da tashin hankali,na fuskanci tsangwamar dangin miji da tsananin ƙiyayyar su bayan rasuwar mijina,wanda a lokacin ne ya kamata su lallashe ni,su tallafe mu kasancewar mun rasa wani babban jigo a rayuwar mu,amma inaa su ba ta rasuwar jinin su suke yi ba,babban abinda ke gaban su shine na yi na gama takaba a raba dukiya su karɓi ɗan su,sai su barni na sha wahalar rayuwa,sun manta cewa bani da kowa sai miji na da ɗana,sun manta cewa miji na shine ya zame min uwa,ya kuma zame min uba,ƙanwata mace ce ba namiji ba itama a ƙarƙashin wani take,to da wa zan jingina na ji sanyi? Zuciya ta ta yi sanyi ta samu natsuwa a wancan lokacin saboda na san koda sun karɓi ɗan su zan samu muhallin da zan zauna ba zan wulaƙanta ba duba da cewa Abbahn Jubair na da dukiya mai tarin yawa,sai dai kashh ! Abinda nake fata bai samu gare ni ba,domin kuwa ina gama takaba,ƴan'uwan miji na suka kore ni a gidan da muke da zama suka bani dubu uku wai iya wannan na samu a matsayin gado na,ina gidajen Alhaji? Ina makarantu da ya gina ake karɓar kuɗaɗe masu yawa? Ina asibitin da ya gina? Ina motocin da ake masa fatauci da su? Dubu uku su ne kawai gadon da na samu ko sune kawai abinda suka ga damar bani? Me dubu uku zata yi min? Shin wulaƙanci ne ya sanya suka bani dubu uku a matsayin gado na ko tozarci da cin amana?"
Numfasawa Hajiya Dada tayi idanun ta sun kaɗa sun yi jawur,tsananin ɓacin rai da damuwar dake cikin ranta ne suka bayyana a fuskar ta har suka yi sanadiyyar dasawa Uwa nadamar tunkarar ta da zancen haihuwa,a hankali Uwa ta ji muryar Hajiya Dada na ci gaba da magana.
"Da na zauna na yi nazari sai na ga to me zai dame ni dan sun tattare dukiya sun cinye? Na rasa mai dukiyar ma na haƙura nake ci gaba da numfashi sai dan an karɓe dukiyar da ya tafi ya bari,inda ya je fa suma za su je,lokaci kawai suke jira,abu ɗaya na sani kawai shine babu wanda ya isa ya raba ni da ɗana,ko shi wanene,domin kuwa na san tinda basu ƙaunaci mahaifin shi domin Allah ba,shima ba son shi suke yi domin Allah ba,dan haka ba zan bar musu yarona ba ko mai rintsi komai wahala. Wannan shine dalilin da ya sa na ɗauke Jubair yana da ƙananan shekaru a duniya muka bar gidan mahaifin shi,gidan da na yi rayuwar jin daɗi da mulki da sarautar da mijina ya bani,gidan da na haifi gwarzon namiji kamar Jubair. A lokacin da na bar gidan ne muna tafe cikin tsananin yunwa da ƙishirwa motar mahaifin Ammar ta buge ni,kusan shine dalilin da ya sa nake da wannan ciwon guiwar da ya ƙi ci yaƙi cinyewa.
Mahaifin Ammar ya kula da mu,ya wadata mu da duk wani abun more rayuwa da muka buƙata a wancan lokacin,bai taɓa banbanta tsakanin Ammar da Jubair ba wajen kulawa,tufatarwa,shayarwa tare da makarantar da suka je. Kasancewar mahaifiyar Ammar ta rasu sai mahaifin shi yaso ya maye gurbinta da ni,sai dai kafin hakan ta kasance ya kamu da mummunan ciwon ciki,cikin dare ya rasu ya barni da Ammar da Jubair cikin maraici da kaɗaici,kasancewar bashi da kowa ne ya bani damar ci gaba da kula da Ammar da Jubair har suka girma na aurar da su,dake Allah shine mai yanda yaso sai ya ƙaddara Ammar ba zai zauna ya yi rayuwa damu anan ba,yana can turai a Baltimore yana zaune da matar shi da yarinyarsu. Ina fatan a cikin wannan ɗan taƙaitaccen tarihin da na baki zaki gane dalili na na son samun yaro namiji da nake fatan ya zamewa Jubair da dikkan musulmi sanyin idaniya tinda har yanzu iyayen Jubair na bibiyar shi,duk dukiyar da suka danne ta ƙare babu ita saboda ba mallakin su bane,yanzu sun dawo suna manne masa suna son su samu wata damar da zasu cutar min da yaro,shi yasa duk satin duniya sai sun zo wai sun kawo masa ziyara ne,ni ba zan raba shi da dangin mahaifin shi ba,tinda ko banza siyasa yake yi,bana son saboda abinda ke tsakanin mu a samu wanda za su yi masa yarfe ko ƙage irin na ƴan siyasa ace bashi da uba ko wani abu makamancin haka."
Ƙwallar da Uwa ta gani a idanun Hajiya Dada ne suka sake sanyaya mata jiki, tabbas ta fahimci dalilin Hajiya Dada na son haihuwar ɗa namiji a gidan Jubair,amma me yasa ita har yanzu ko ɓari bata taɓa yi ba balle ta saka ran zata iya zama uwar magajin gidan Jubair? Cikin sanyin murya ta ce.
"Na fahimce ki Hajiya Dada,inshaa Allahu ba zaki mutu ba sai kin ga jika namiji daga Yah Jubair,ina fata Allah yasa nice zan kasance mai sa'ar da zata faranta ran ki anan gaba,ki taya ni da addu'a ni kaina ina son na haihu,na rasa dalilin da yasa shekara goma da aure ban taɓa ɓatan wata ba."
"Inshaa Allahu zan ci gaba da taya ki da addu'a fiye da yanda nake yi a baya,ni kaina zan fi son na samu jika namiji daga wajen ki,domin kuwa bahaushe yace so sone amma son kai ya fi."
Ruƙayya dake tsaye a ƙofar ɗakin Hajiya Dada ce ta shafa cikin ta cikin wani irin yanayi ta juya zata bar sashen gaba ɗaya,zuciyarta banda bugawa da tashin hankali babu abinda take ci gaba da yi,idan bata samu ɗa namiji ba a yanda Hajiya Dada ta ƙwallafa rai tabbas akwai matsala,dole ne ta je asibiti a duba mata abinda za ta haifa ko dan kwanciyar hankalin kowa.
Karo ta yi da Jubair da ya shiga sashen dan gaishe da mahaifiyar shi,cike da jin nauyin shi ta raɓe gefe ta bashi waje dan ya shiga, kallon ta ya yi ya ga sauyin yanayi a tattare da ita,nan take ya jata jikin shi yana tambayar ta dalilin sauyawar yanayin ta,cikin sanyin muryar da take da shi ta ce.
"Babu komai, na dai kula kamar Hajiya na tattaunawa da Uwa ne,shi yasa na dawo gudun kar na katse musu hira."
Murmushi Jubair ya yi mai sauti kafin ya shafi kuncin Ruƙayya ya ce,
"Ruƙyna sarkin hankali,a kullum natsuwar ki da kamun kan ki tare da sanin yakamatan ki ke ƙara dasa min zazzafan son ki a raina,har abada ba za ayi macen da zata samu irin son da nake maki ba a zuciyata,taho mu je mu ma a yi hirar da mu."
Kalaman shi ba ƙaramin daɗi suka yiwa zuciyar ta ba,har sai da suka yi sanadiyyar sauyawar kalar fuskar ta ta yi ja saboda kunya,kanta a ƙasa ta ke bin shi har suka isa parlourn Hajiya Dada,sallama Jubair ya kwaɗa kafin su yiwa kansu mazauni a kujerun dake jere a parlourn. Babu jimawa Hajiya Dada da Uwa suka fito a tare,sai da Uwa ta yi matsanancin ƙoƙari kafin ta iya danne kishin dake barazanar sanya ta hauka ta iya gaishe da Jubair,sanin cewa ba zata kula Ruƙayya bane ya sanya Ruƙayya gaishe ta tare da tambayar yanda ta kwana,a yatsine Uwa ta ce,
"Ƙalau na kwana ya son ran ki?"
Murmushi kawai Ruƙayya ta yi ta miƙe dan haɗawa Hajiya Dada shayi,Uwa na ganin haka sai ta sha gaban Ruƙayya tana faɗin,
"Ni fa bana son baƙin iyayi da son a sani,sai wani tafiya kike ki na turo ciki gaba ke ga mai ciki ko? Mtsssww ! matsa ni dan Allah ki bani waje."
Ba tare da Ruƙayya ta yi jayayya da Uwa ba ta yiwa Hajiya Dada sallama ta bar sashen ranta na mata suya akan abinda Uwa ke yi mata. Jubair kuwa kafe Uwa ya yi da ido,dan kuwa bai isa yi mata faɗa a gaban Hajiya ba ya riga da ya san da wannan,a tsarin tarbiyyar gidan ma gaba ɗaya idan Hajiya na waje babu mai yanke hukunci. Uwa kuwa duk kallon da Jubair ke wurga mata tana sane da shi,hakan kuwa ya ƙara zama sanadiyyar ƙarin tsanar Ruƙayya a ran ta,sai da Hajiya ta bari Uwa ta ɗauki mug zata haɗa shayi ta ce.
"Kema ajiye ki bar nan,da alama duk maganganun da muka yi dake basu zauna a zuciyar ki ba,kunnuwan ki suka shiga suka fita."
Cike da zumɓura baki ta baro wajen ta tsaya a tsakiyar parlourn ta ce,
"Hajiya to kin amince na je gida yau?"
Kallon Jubair Hajiya ta yi sannan ta ce,
"To kai ka ji,matar ka na son taje gida neman maganin haihuwa,ka amince ta tafi?"
A ladabce Jubair ya ce,
"Hajiya ai duk abinda kuka ce shi za a yi."
Sai da Hajiya ta nisa sannan ta ce,
"Ki gaishe min da Batula,kar kuma ki sake ki kwana dan na san halin ki sarai."
Cike da farin ciki Uwa ta bar sashen Hajiya Dada,sai da ta gama shiryawa tsaf cikin tsadaddun tufafin ta sannan ta ɗauki makullin motar ta ta sallami Ubaida ta nufi harabar gidan. Su Kubrah ta gani sun shiga mota za a kai su makaranta,ɗauke kai ta yi ta kunna ta ta motar ta shige tana ƙwafa,cike da ƙunar zuciya ta ce,
"Matan ma ba barin su zan yi ki mora ba balle har ki haifi magajin mai gidan,matsiyaciya dangin babu"
A hasale ta dinga dannawa mai gadi horn duk da cewa gate ɗin gidan a buɗe yake,bata dena horn ba har sai da ta bar gidan,girgiza kai mai gadi ya yi yana jinjina masifa da gadara irin ta Uwa.
A bangaren Ruƙayya kuwa tana komawa sashen ta sai ta samu waje ta zauna tare da lumshe idanun ta,rayuwar gwagwarmaya da hannu baka hannu ƙwaryar da ta yi a baya ita da iyayenta da ƙannen ta mata biyu ta tinano,sannan ta koma kan irin daular da take ciki a yanzu,shin haihuwar namiji wata ɗaukaka gare shi ta musamman har da ake ta nanata zance daya akai? Menene makomar ta idan har bata samu haihuwar namiji ba kenan?........ [05/04, 2:20 pm] asiyahabibu93: DUK NISAN DARE....
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨