DUK NISAN DARE

PAGE 5

by @1239900

A nutse Uwa ta danna horn a bakin gate ɗin gidan nasu tana jiran mai gadi ya buɗe mata. Buɗe gidan ke da wuya ta fahimci mahaifinta na gida bai fita ba kamar yanda ta yi zato. Sai da ta gaida mai gadin nasu kafin ta wuce ta adana motar ta a waje ajiye motoci, mayafinta ta sake ja ta lulluɓe duk inda ya dace a jikin ta kafin ta ɗauki jakar ta da wayoyin ta ta fita.

Tafe take tana sake gyara tsadaddiyar doguwar rigar ta gudun kar mahaifinta ya yi faɗan bata sanya hijabi ba. A babban parlourn gidan ta tarar da su suna karyawa cike da so da ƙaunar junan su,shigar ta ce ta katse musu hirar tasu suka zuba mata ido suna kallon ta. Cikin wata iriyar murya ta dattijai mahaifin Uwa ya ce.

"Ah ah Hafsat me kike yi a gida da sassafe haka? In ce dai lafiya ko?"

Sunkuyar da kai Uwa ta yi ƙasa tare da ƙarasawa cikin kyakkyawan wajen dining area ɗin gidan,sai da ta durƙusa har ƙasa ta gaishe da iyayen nata kafin ta samu waje saman kujera ta zauna,kanta a ƙasa ta sa hannu ta share hawayen dake zuba a idanun ta,ganin iyayen nata sun zuba mata idanu da wani irin yanayi a fuskokin su na tsoro sai ya sa zuciyar ta rauni k'warai da gaske ta hau zubar da hawaye,nan take hankalin su ya ƙara tashi mahaifiyar ta sai ta matso ta samu waje kusa da ita ta zauna ta kama hannayen ta dika biyun ta ce,

"Sanar dani damuwar ki Uwata, tashin hankalin ki tashin hankali na ne,ɓacin ranki ɓacin raina ne,wa ya taɓa ki yanzu garin Yola ya shaida na yi sabon maƙiyi?"

A sheƙe mahaifin Uwa ya kalli matar tashi da hankalin ta ya yi bala'in tashi,gyaran murya ya yi kafin ya ce,

"Ke muke sauraro ina sauri zan fita kar ki tsaida ni akan shirmen banza."

Nan take jikin Uwa ya fara rawa,dan kuwa ba ƙaramin tsoron mahaifin nata take ji ba,ɗan sakar mata fuskan da ya yi na ɗan lokaci ne ya sanya ta manta asalin shi waye,jiki na rawa ta furta.

"Abbah dama uhumm..dama Ruƙayya ce ke da ciki...shine... shine...."

Cike da ɓacin rai mahaifin ta ya kalle ta ya ce,

"Ruƙayya na da ciki ke kuma baki da shi shine kika zo nan gidan uban ki da ake rabawa a baki naki kason ko?"

Girgiza kai Uwa ta fara yi tana ja da baya daga saman kujerar da take kai,cike da masifa mahaifin ta ya fara magana,

"Uwa ki kiyaye ni akan wannan baƙin kishin naki,kin san Allah...duk sanda kika kaso auren ki a karo na biyu sai dai ki nemi gidan da zaki zauna,saboda ba zan ci gaba da ganin ki kina zawarci ba,ke bakya jin kunya ne ki yi ta abu kamar marar ilimin addini? Alhamdulillah ni na sani har a wajen Allah na fita haƙƙin ki Uwa,na baki ilimin addini har kin kai babban matakin da ko wa'azi zaki iya yiwa wasu,na baki ilimin zamani kin kai matakin Masters,sannan na baki na zaman duniya tinda ba a iya garin Yola kika yi karatu ba kin je gari-gari a faɗin ƙasar nan dan neman ilimi,amma duk da haka har yanzu baki ɗauki abinda nake faɗa maki ba balle abinda kika karanto a duniya,ke wace iriyar yarinya ce ne Uwa? Yaushe zaki yi hankali ki gane Allah ne mai yi a sanda ya so,kuma ya hana a sanda ya so? A kan ki aka fara rashin haihuwa?"

Ganin irin faɗan da mahaifinta ke yi mata ne ya sanya ta sanya kuka mai matuƙar ƙuna,dama ta riga ta sani in har ta same shi a gida to fa ba lallai burin ta ya cika ba,ita kuwa ko sama da ƙasa zasu game waje guda sai ta salwantar da yaran Ruƙayya har ma ta yi sanadiyyar raba su da duniyar kowa ya huta. Duk wani abu da Abbahn ta ke faɗa ba jin shi take yi ba a daidai wannan lokacin,zuciya da hankalin ta na can suna tunanin yanda zata aiwatar da mugun nufin dake cikin ranta,dukan table ɗin gaban ta da Abbah ya yi ne ya sanya ta zabura ta kwasa da gudu ta wuce sama tana gunjin kuka.

Cike da tsananin tausayi irin na ƴa da uwa Ummah ta kalli Abbah ta ce,

"Haba Abbahn Hafsat ! Me yasa zaka sake ƙunsa mata baƙin ciki akan wanda take ciki bayan baka bata dama ta sanar da mu damuwar ta ba dan...."

"Ke ji mana dakata min dan Allah ! Kina nufin tsayawa zan yi na ji shiriritar wannan yarinyar? Akan wanne dalili to? Kanta aka fara rashin haihuwa? Shin ta kai matan Annabi daraja ne tinda Allah bai basu haihuwa ba suma? Kar ki manta fa Nana Aisha har ta bar duniya bata taɓa haihuwa ba,to ita wacece dan Allah ya jarabce ta zata ɗaga hankalin ta muma ta ɗaga mana namu,na fa ga take-taken ta so take ta kashe auren ta dawo ta sake yin zaman zawarci a gidan nan,to ina mai tabbatar maku da ke da ita,duk sanda ta kaso auren ta zaku bar min gida na,ki kira ta tazo ta bar min gida ta koma gidan mijin ta,kar na dawo na tarar da ita a gidan nan,kin ji na faɗa maki."

A matuƙar hasale ya kwashi wayoyin shi guda uku masu tsananin tsada ya ɗauki makullin motar shi ya ja kujerar da yake kai baya ya fita ya bar parlour'n,yana fita drivern shi ya taso ya duƙa ya gaishe shi tare da karɓar makullin motar ya wuce gaba.

Sai da Ummah ta tabbatar da fitar shi sannan ta haura sama wajen Uwa dake ta risgar kuka kamar wata ƙaramar yarinya,Ummah na shiga Uwa ta tashi da gudu ta rungume ta tana ci gaba da kuka,cikin sigar rarrashi Ummah ta ce.

"Maza ki sanar dani abinda ke damun ki in magance maki shi,idan shi ba zai iya ba ni zan iya,haka kawai,so ake a kashe min ke da baƙin ciki? Shi yasan zafin rashin haihuwa ne yana namiji? To ba zai yu ba,babu wanda zai sanya min ke zubar hawaye haka ya kwana lafiya."

Cike da jin daɗi Uwa ta zauna ta sanar da Ummah duk abinda ke faruwa a gidan,har da ƙarin auren da Hajiya Dada ta ce Jubair ya ƙara matsawar ba a haifa masa magaji ba. Nan da nan kuwa ran Ummah ya ɓaci ta ce,

"Lallai ma Dada,ashe zata iya manta alaƙar zumuncin dake tsakanin mu ta bijiro da waɗannan halayen? Wa take da shi da ya wuce mu? Mu ne nata ko ta ƙi ko taso,kuma dukiyar Jubair da yardar Allah ke da ɗan da zaki haifa anan gaba zaku ci ta,tashi ki wanke fuskar ki ki shirya mu fita,ni za a kawowa lalata?"

Tsallen murna Uwa ta doka sannan ta ɗafe mahaifiyarta tana godiya da farin ciki,cikin tsananin murna ta ce,

"Dama na san ba zaki bar hawaye na ya zuba a banza ba,uwata mai share min hawaye na,uwata maganin kuka na,ki jima ki yi ƙarko Ummahna ina son ki."

Farin ciki ne ya mamaye zuciyar Ummah saboda ganin shalelen nata na murna,cikin ƙanƙanin lokaci suka shirya suka hau mota ɗaya suka bar gidan,tinda suka fita suka keta titin dake shinfiɗe a unguwar tasu ta Karewa,har suka shiga cikin gari basu daina gudu ba, nausawa suka yi cikin wata unguwa dake tsakiyar garin Yola,a ƙofar wani gida suka tsayar da motar su Ummah dake tuƙawa ta fito sanye da baƙin tabarau tana taunar chewing gum tana yatsina hanci tare da tsartar da yawu,a wulaƙance suke kallon unguwar da ta ke dauke da gidajen yaku bayi har suka tsaida kallon su akan gidan da ke gaban su,gida ne na ƙasa da aka yiwa flasta da siminti aka shafe shi da farar ƙasa tin daga waje har cikin gidan.

Bakunan su ɗauke da sallama suka shiga cikin gidan suna yatsina,wata mata suka gani da tsohon ciki tana zaune gaban ta wata yarinya ce duƙun-duƙun da ita tana kashi a poo,matar na riƙe da buta ta tsartar da yawu ta ce,

"Ah ah Hajiya yau kune ke tafe? Bismillah'n ku bari na ɗakko muku tabarma ku jira malam ɗin,dan kuwa ya zaga gona sai dai kuma idan zaki sa waya ki kira shi dan ya san da zuwan ku."

A yatsine Ummah ta tauna Chewing gum ɗin ta sannan ta buɗe jakar ta ta zaro waya ta kira malam,tana gama sanar da shi sun iso ta katse,cikin ƙanƙanin lokaci Malam ya iso yana washe baki,ɗakin da yake karɓar baƙi ya buɗe musu suka shiga ciki,waje ne mai kyau har da kujeru da carpet saboda tarbon baƙi irin su Ummah,duk da yanda wajen yake a share a tsaftace bai hana su Ummah yatsina ba kamar sun zauna a saman kashi,sai da Malam ya ajiye kaucin magungunan da ya samo a daji sannan ya zauna yana washe baki ya ce,

"Hajiya ku ne ke tafe da safen nan? Allah sarki, ai gona na je,ina hanyar dawowa kika kira ni."

"Uhumm Allah sarki, to sannu fa,damaaa.."

Murmushi ya yi sannan ya ce,

"Dakata Hajiya,ai wannan aikin da kuke tafe da shi na riga na san da shi,kun yi jinkiri k'warai baku zo da wuri ba,domin kuwa tin wata biyu da suka gabata nake saka ran zuwan ku amma shiru."

Cikin tsananin damuwa Uwa ta ce,

"Yanzu kana nufin Malam babu abinda zaka iya yi akan matsala ta?"

"Idan na ce maki ba zan iya komai ba ai ban amsa suna na shaƙundum ba ko? Maganar zubar da cikin ita abokiyar zaman ki nake magana akai yanzu,ina so ku sani shi wannan ciki sai an haifo shi duniya da ikon Allah,sannan cikin nan tin a daren da na yi mafarkin zuwan ki nake bincike dan in gano me za a haifa na kasa ganowa har yau,abu na gaba kuma shine zan baki maganin da zaki dinga sakawa yaran kishiyar ki a abinci sai dai sharaɗin maganin a hankali yake aiki,sai dai a wayi gari yaran sun bugawa Uban su muguwar sata ta ban mamaki sun gudu sun bar gidan,za su shiga duniya su yi karuwanci su lalace kamar yanda kike buri,sai dai kuma akwai wata babbar matsala..."

"Mu dai bamu ga matsala ba Malam,yanzu karb'i nan,duk wata matsala da ka gano ka kawar da ita,bana son jin komai bana son ganin komai,na yarda da kai, na amince da kai zaka share min kuka na da na ƴa ta, dan haka na bar maka wuƙa da nama a hannun ka,ka yanki inda ka so."

Gudun kar aikin shi ya lalace ya rasa inda yake samun cin abinci sai Malam ya tsuke baki bai sake magana ba,maƙudan kuɗin da za su kai kimanin dubu ɗari biyar ya amshe yana ta zuba godiya,nan da nan ya tashi ya hau haɗa magungunan da zai baiwa Uwa, yana kammalawa ya basu suka yi sallama suka wuce gida.

Koda suka je gida basu wani jima ba Ummah ta sallami Uwa ta ce ta koma gida kafin mahaifin ta ya dawo ya tarar da ita a gida,sai da ta sake jaddada mata yanda za ta yi amfani da magungunan sannan suka rabu kowa na farin cikin sun kamo bakin zaren matsalar su........... [07/04, 10:58 am] asiyahabibu93: DUK NISAN DARE...

RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨