PAGE 6
by @1239900
Lokacin da ta isa gida ta tarar da gidan shiru kamar babu kowa,kasancewar yara suna makaranta kowa kuma na sashen shi,Jubair ko ya tafi office sai dare zai dawo. Tana fitowa daga mota sashenta ta wuce,a bakin ƙofa ta tarar da Ubaida da Munkaila mai share-sharen harabar gidan da kula da shuke-shuke suna hira kamar wasu tsofaffin masoya,a wulaƙance take bin su da kallo kafin ta dakawa Ubaida tsawa ta ce.
"Inyeee lallai ne Ubaida,meye haka nake gani da rana tsaka a sashena? Wuce ciki mu je shashasha kawai wadda bata nemawa kanta nasara a rayuwa,ke yanzu fisabillahi ki zo aiki gidan nan sannan ki ɓige da soyayya da ɗan aiki?"
Cike da ɓacin rai Munkaila ya kalle ta ya ƙure ta da idanu,kallon shi Uwa ta yi taga irin kallon da yake yi mata,nan take ranta ya ɓaci,cikin fushi ta hau masifa ta na faɗin.
"Maza ka zo ka tattara naka ya naka ka bar gidan nan mara mutunci kawai,ni ka ke yiwa mugun kallo kamar wata sa'ar ka?"
Karkace kai Munkaila ya yi sannan ya ce,
"Hajiya ita soyayya babu ruwanta da talaka balle mai kuɗi,babu ruwanta da babba ko yaro,Ubaida na so na nima kuma ina son ta,rayuwar nan fa ƙwarya ta bi ƙwarya ake yi,ni ne daidai ita,itama kuma ita ce daidai ni,maganar barin aiki Hajiya ai ba ke ce kika ɗauke ni aiki ba,Hajiya Dada ce ta ɗauke ni aiki,dan haka ita kaɗai ce zata kore ni na koru a gidan nan."
Baki sake Ubaida da Uwa ke kallon Munkaila,cike da tsananin fushi Uwa ta tunkare shi zata mare shi,babu ɓata lokaci Munkaila ya sanya hannu ya tare marin sannan ya yarfe hannun ta gefe yana binta da wani mugun kallo,a hasale Uwa ta nufi sashen Hajiya Dada ta na masifa,ko da ta shiga sai ta same ta kashingiɗe ta na karanta ƙur'ani idanun ta sanye da farin gilashi,suna haɗa ido da Hajiya Dada ta ji wani irin kwarjinin Hajiyar ya dirar mata,cikin sassauta murya ta ce.
"Hajiya kina da labarin cewa gab kike da jin mugun labari a gidan nan?"
A kaikaice Hajiya Dada ta kalle ta ta ce,
"Sallamar kenan Uwa? Sannan wanne irin mugun labari kike magana akai?"
"Munkaila Hajiya zai jawowa gidan nan mugun tabo,yanzu na dawo na ganshi a sashena yana zubawa Ubaida soyayyar zamani wadda za ta iya kai su ga dana sani,da na yi masa magana sai ya nemi ya gaggaya min baƙar magana,har yana ikirarin babu wanda ya isa ya kore shi a gidan nan ko wanene tinda ya riga ya shigo ya shigo kenan."
Kallon ta Hajiya Dada ta yi na wasu ƴan sakwanni kafin ta ce,
"Miƙo min wayata."
Kamar Uwa zata kifa dan sauri haka ta ƙarasa kujera ta ɗauki wayar Hajiya ta miƙa mata,babu ɓata lokaci Hajiya ta kira Munkaila ta ce su je shi da Ubaida sashen ta tana son ganin su,nan take Uwa ta samu waje a gefen Hajiya ta zauna ta na ci gaba da yi mata pampo,Hajiya kuwa na ci gaba da sauraron ta tana nazarin maganganun ta,basu wani jima suna zaune ba Ubaida da ke sanye da wani uban mayafi ta fara shigowa,Munkaila na biye da ita a bayan ta,waje suka samu suka fara gaishe da Hajiya Dada kafin daga baya su ce
"Hajiya gamu."
Ajiye waya Hajiya Dada ta yi a gefen ta kafin ta ce,
"Munkaila menene tsakanin ka da Ubaida?"
A kunyace Munkaila ya ce
"Hajiya soyayya ce ta tsakani da Allah a tsakani na da ita wadda nake fatan ta kaimu ga aure."
"Ubaidah abinda Munkaila ya faɗa gaskiya ne?"
A kunyace Ubaida ta gyaɗa kai ta ce,
"Eh Hajiya abinda ya faɗa gaskiya ne."
Murmushi Hajiya tayi kafin ta ce,
"To Alhamdulillahi,ai babu wani aibu a tarayyar su,sai dai idan ba auren ta za ka yi ba Munkaila kar ka kuskura ka yaudare ta,zan ci mutuncin ka sannan zan maida kai inda ka fito,darajar zaman tare da muka yi da iyayen ka a can baya shi yasa na ɗakko ka na kawo ka nan dan ka yi aiki ka dinga kyautata musu,ka riƙe aikin ka da kyau bana son shiririta,na baku nan da wata ɗaya ku daidaita kan ku, da yardar Allah manya za su shiga maganar ku a ɗaura maku aure."
Cike da murna da farin ciki Munkaila da Ubaida suka bar parlour'n bayan Hajiya ta sallame su,Uwa kuwa ji ta yi kamar an watsa mata ruwan zafi,nan take wata iriyar tsanar Munkaila ta mamaye zuciyarta har tana jin zata iya rabuwa da Ubaida a matsayin mai aiki ta samu wata,babu ko sallama kamar yanda ta shigo ta mike zata bar sashen Hajiya Dada,cike da murmushi ta ce
"Uwa kenan,ki dinga sanyawa zuciyar ki salama,na rasa me yasa zuciyar ki ke cike da ƙiyayya mai tsanani,to ba wannan ba ma,in ce dai kin samo abinda ya fitar dake daga gidan?"
Wani irin shu'umin murmushi ne ya ƙwacewa Uwa saboda tina inda suka je da Ummahn ta da ta yi,cike da jin daɗi mara misaltuwa ta ce,
"K'warai na samo maganin matsala ta,wanda nake fatan ya baiwa kowa mamaki a duk sanda buri na ya cika."
"To Allah ya cika miki burin ki na alkhairi Uwata,ina fatan kin baro Batula lafiya da Baban naki ko? Ya labarin su Usumanu mai duniya?"
Murmushi Uwa ta yi kafin ta ce,
"Kowa yana nan lafiya,su Usman kuwa ni banda wani labari akan su Hajiya,tinda uban su ya nuna min fin ƙarfi akan su,ni kuwa na tattara su na watsar su je can su karata tinda ba nema na suke yi ba suma."
Girgiza kai Hajiya ta yi,dan kuwa bata son hirar ta tsawaita Uwa ta zuba mata shirmen ta wanda a kullum bata gajiya da shi,a shekarun ta talatin da bakwai a duniya bata san ciwon kanta ba to yaushe zata sani?
Sashenta ta wuce hannun ta riƙe da jakar ta da wayoyin ta,tana daf zata sanya ƙafa cikin sashenta ne Munkaila ya fito daga inda yake a laɓe,a matuƙar tsorace Uwa ta juya suka haɗa idanu da Munkaila,nan take ta ji wani irin yarrr tin daga kanta har zuwa kafafun ta,murmushi ya sakar mata wanda ya sanya jikin Uwa ɗaukar wata iriyar rawa,cike da tsoro ta ja baya baki na rawa ta ce,
"Munkaila menene haka? Kar ka matso nan zan yi maka ihun kwarto."
Wata iriyar dariya mai sauti Munkaila ya saki kafin ya nuna ta ya ce,
"Ke a zaton ki ɗan asirin da kika je kika karɓo zai yi tasiri a wajen yaran da kakar su ke nema musu maganin tsari kullum? Lallai Uwa ban taɓa sanin ke sokuwa bace sai yau,an faɗa maki Hajiya Dada a zaune take? Bari na sanar dake wani abu da baki sani ba,Hajiya Dada macece mai tsananin ibada,ta na son jikokin ta matuƙa gaya kamar yanda take son ɗanta,kwalafucin ɗa namiji da take yi ba shi ne yake nufin su matan bata son su ba,duk wani tsari da ake baiwa yara saboda mugun baki da maitar ido babu wanda bata baiwa jikokin ta ba,kuma ni ɗinnan da kike gani nine ke samo mata,dan haka wannan ɗan abun da kika karɓo babu abinda zai yi musu,idan kuma kika dage sai kin yi amfani da shi to tabbas ƙaiƙayi ne zai koma kan masheƙiya,shawarar da zan baki shine ki nemi magani a inda aka san magani,ba wai inda ake koyon sanin magani ba."
Munkaila na gama faɗa mata kalaman da suka sanya zufa tsattsafo mata ta kowacce kafa ta jikin ta ya bar wajen ya koma bakin aikin shi,hankalin Uwa a tashe ta shige ɗaki ta kulle ƙofa ta zauna a ƙasan carpet ta zabga tagumi,cikin zuciyarta take faɗin,
'Ya akai ya san na dawo da magani? Anya Munkaila ba aljani bane? To ko dai maye ne? Na shiga uku ni Uwa ya zan yi da wannan sabon al'amarin da ya tinkaro ni? Hakan na nufin mun yi asarar kuɗin mu kenan a banza?'
Wayarta da ta yi ringing ce ta firgita ta ta miƙe tsaye a tsorace,a hankali ta dawo cikin natsuwar ta sannan ta ɗauki wayar,hannun ta na rawa ta bi kiran Ummahn ta da ya katse,tana jin muryar Ummahn ta sai ta fashe da kuka,cike da damuwa Ummahn ta ce,
'Ke Uwata lafiya? Me ya faru kike kuka haka?'
"Ummah na shiga uku,yau na takalo faɗa da aljani."
A tsorace Ummah ta ce,
'Kin shiga uku ko mun shiga uku Uwa? A ina ki kai gamo da aljanin? Ko dai malam Shaƙundum ne ya yi mana turen aljanun?'
Cikin kuka Uwa ta labartawa Ummahnta duk abinda ya faru,a rikice Ummahnta ta ce,
'Ya akai ya san inda muka je da abinda muka karɓo? Duk yanda akai wannan hatsabibi ne Uwa,kar ki sake ki yi wasa da shi,ki jawo shi a jiki,yanda ya san sirrin Hajiya da ɗan ta har da jikokin ta,to ba ƙaramin amfani zai yi mana ba a wannan tafiyar,sannan kamar yanda ya ce ki dakata kar ki yi amfani da maganin nan mu jira mu ga nan da lokacin da zaki gama yaudaro mana shi,mu yi amfani da shi dan cimma burin mu.'
Kalaman Ummah ba ƙaramin kwanciyar hankali suka dasawa Uwa ba a ran ta,a hankali ta samu bakin gadonta ta zauna suka ci gaba da ƙulla yanda za su samu nasarar mallake dukiya da gidan Jubair baki ɗaya.
Uwa ce zata karɓi girki a wannan ranae, dan haka sai ta maida hankali wajen girka abinci mai daɗin gaske da taimakon Ubaida wadda ta ƙware a girke-girken zamani da na gargajiya, sai da Uwa ta gama jera komai a sashen Jubair kamar yanda suka saba sannan ta dawo sashen ta ta faɗa wanka,ta jima tana dirzar jikin ta da kayan wanka masu gyara fata sannan ta yi alwala ta fito zuwa ɗakin ta,kwalliya ta tsara mai kyau kafin ta gama dare ya yi har ma Jubair ya dawo,shiryawa ta yi cikin wani leshi mai laushi da tsada,an yi masa wani irin matsattsen ɗinki sai ta feshe jikin ta da turaruka ta yafa wani yalolon mayafi ta ɗauki wayar ta ta kulle ɗakunan ta,sallama ta yiwa Ubaida sannan ta wuce sashen Jubair.
Ƙamshin jikin ta ne ya daki hancin shi dan haka cikin wani irin yanayi ya ɗaga kai ya kalli kyakkyawar bafulatanar dake gaban shi tana taku kamar wata hawainiya,murmushi suka sakarwa junan su,hannu Jubair ya buɗewa Uwa ta taka a yangance ta je gare shi ta zauna a saman ƙafafun shi,a shagwab'e ta ce,
"Gaskiya ni dai Hammaah ka tashi mu je mu ci abinci idan yaso sai mu zo mu yi kalar hirar da ka ke so,yau baka ji irin gajiyar da na yi ba."
Murmushi ya yi sannan ya ce,
"To ke dama yaushe ne baki gajiya fisabillahi Hafsy?"
"Au haka ma zaka ce? Kar fa ka manta ni ban saba aikin wahala ba ko a gidan mu,amma saboda matar ka ta saba da wahala tana maka girki ka tursasa ni nima nake yi maka girki da kaina,ka ga kuwa dole na gaji."
Nan take Jubair ya haɗe fuska kamar bai taɓa dariya ba,dan kuwa ya tsani duk abinda zai taɓa darajar Ruƙayyan shi,tashi ya yi a ɗan hasale ya wuce wajen cin abincin,turus ya tsaya ya yi yana kallon saman dinning table ɗin,ganin ya tsaya yana kallon saman dinning ne ya sanya Uwa ƙarasawa,tana isa ta ƙame cike da matsanancin tsoro da fargaba tare da tashin hankali,menene wannan take gani?
'Munkaila.'
Shine sunan da ya ɗarsu a zuciyar ta............ [07/04, 6:46 pm] asiyahabibu93: DUK NISAN DARE...
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH
LAST FREE PAGE.
*Idan kina son ci gaban labarin DUK NISAN DARE garzaya ki sheƙa ɗarin ki biyat #500 a wannan account ɗin 0006366584 Ja'iz bank Hamida sanusi Ahmad,sai ki tura shaidar biya ta wannan lambar ***. Da zarar kin yi haka zaki ji ki a paid group. Na gode. Saboda yanayin yau da gobe ban yi alƙawarin yin posting kullum ba,amma zan yi iyakar iyawata na dinga yin posting akai-akai inshaa Allahu.*