DUK NISAN DARE

PAGE 7

by @1239900

"Menene wannan Hafsat?"

A diririce Uwa ke kallon ƙullin magungunan da ta dawo dasu da rana daga wajen Malam. Duk maganganun da Jubair ke yi mata basa shiga kunnen ta,har sai da ya kula da hakan ya tab'o ta ya ce.

"Na ce wannan menene? Ko in ce na waye?"

Wani irin tsoro ne ya mamaye zuciyarta,amma sai ta sanya jarumta,cikin dakewa Uwa ta ce,

"Hammaah magani na ne da muka karɓo ɗazu a wajen mai bada maganin gargajiya,ban san ya akai suka zo nan ba,dama an gargaɗe ni kar na yi amfani da su ina zuwa."

Kafin Jubair ya yi wani yunƙuri har Uwa ta kwashe magungunan ta wuce toilet ɗin ɗaya daga cikin ɗakunan dake sashen ta zubar,flushing ɗin su ta yi tare da sauke ajiyar zuciya,hannun ta a saman ƙirjin ta ta baro band'akin tana waige tare da dudduba kowanne saƙo da lungu na sashen,a cikin zuciyar ta take ayyana,

'Anya wannan ba aikin Munkaila bane? Wato so yake ya tona min asiri shi yasa ya yi surkullen da magungunan suka kawo kansu da kansu nan ko? Babu komai mu zuba mu gani,duk nisan jifa ai ƙasa zai faɗo,haka zalika duk NISAN DARE GARI ZAI WAYE'

Firgita ta yi tare da ƙwalla ƙara ta ɗafe Jubair ta na kukan shagwab'ar da ta san yana rikita masa lissafi har ya manta kowa da komai face wannan shagwab'ar da ake zuba masa,cikin dasasshiyar murya Jubair ya ce,

"Hafsyna menene kuma? Kin ga baki yi min bayani akan wanda ya hana ki amfani da maganin da ke ce da kan ki kika...."

Kuka ta fashe da shi wanda ya sanya shi kasa ƙarasa maganar da ya yi niyyar yi,kafin ta ce,

"Hammaah ni fa ina ganin ba zan taɓa haihuwa da kai ba har abada,na fidda rai da maganar haihuwa musamman da yanzu shekaru na ke ƙara yawa."

Cike da tausayawa Jubair ya ɗauke ta a hannun shi kamar wata jinjira ya wuce da ita bedroom ya kwantar da ita a saman gado,a gefen ta ya kwanta ya fara lallashin ta da tausasan kalamai.

"Kar ki ce haka Hafsyna yara na ai naki ne,sannan yaran ki nawa ne,kar ki manta ke ɗin jinin jikina ce, ƴar'uwa ta ce ta jini,na sha faɗa maki mu ɗakko su Usman da Ali su dawo nan da zama idan hakan zai faranta maki,amma a duk sanda na yi maganar sai ki dinga fushi,na rasa me yasa baki ƙaunar zaman su a gidan nan,ko akwai wani dalilin da ya sa kike nesanta su da gidan nan ne wanda ban sani ba?"

Cike da kirsa da kisisina ta ce,

"Ba zaka gane ba Hammaah,zaman su Usman a gidan nan ba zai haifar da ɗa mai ido ba,saboda a shekarun baya hutu kawai suka zo aka fara nuna musu nan ɗin ba gidan uban su bane,to tinda uban su na da arziƙi daidai gwargwado ai kaga gwanda su yi zaman su a can,su kansu basu son zuwa tinda a ganin su na guje su na yi wani auren na manta da su."

Cike da ɗaure fuska Jubair ya tashi ya zauna yana fuskantar ta ya ce,

"A kaff gidan nan waye yake ƙyamatar yaran ki? Sanar dani yanzun nan na ɗauki mataki akan hakan,koda baki aure na Hafsat kina da ƴancin kawo ɗan ki gidan nan, ballantana kuma kina aure na."

"Haka dai kace Hammaah,amma matar ka ai bata san hakan ba,a ganin ta zaka fifita yarana saboda maza ne sama da nata,ni dai dan Allah a bar wannan maganar bana so ka sake tada ita,ana zaune lafiya a zo a dinga cewa nice dama fitinanniyar da ke tada rikici a gidan nan,kuma ka ga Hajiya Dada ba zata ji daɗi ba."

Shiru ya yi ranshi babu daɗi,saboda ba karamin tausayawa Uwa yake yi ba,duba da ya san yanda take masifar son ta haihu da shi,da wannan maganganun Uwa ta ɗauke hankalin shi da salon ta,wanda ya mantar da shi maganar ƙulle-ƙullen maganin da ya gani a saman dinning table.

Washegari da asubar fari Jubair ya tashi kamar koda yaushe,wanka ya yi tare da ɗaura alwala sannan ya fito ya sanya jallabiyar shi blue mai duhu tare da wandon ta,turaruka masu matukar tsada da ƙamshi ya fesa kafin ya tada sallah a saman abun sallah. Uwa kuwa a lokacin ta yi wani sabon juyi ta ci gaba da baccin ta cikin kwanciyar hankali da nishad'i. Jubair kuwa na idar da sallah ya miƙe ya fara haramar tafiya masallaci,dan kuwa duk rintsi duk wuya baya sallah a gida sai a masallaci,koda kuwa a wajen aiki yake ya ga lokacin sallah ya yi yakan wuce masallaci,wanda hakan da yake yi ba ƙaramin baiwa mutane mamaki yake ba,duba da cewa shi ɗin ɗan siyasa ne mai faɗa a ji,ba safai aka fiya ganin irin su a masallatai ba suna sallah kullum.

A hankali ya taka ya isa gaban Uwa da ke kwance lamɓas a cikin bargo,ɗan bubbuga pillown da take kai ya yi a hankali,ganin ko motsawa bata yi bane ya sanya shi tada ita da kyau,be ƙyale ta ba sai da ya ga ta zauna da kyau sannan ya ce,

"Ki tashi ki je kiyi wanka ki yi sallah,kar ki bari na dawo na tarar dake kina bacci zan saɓa maki,kin san bana son wasa da lokacin sallar nan da kike yi ko?"

Ɗaga kai ta yi tana miƙa kamar wata macijiya,da sauri Jubair ya wuce ya barta tana zaune tana nazarin shin ta tashi ta bi umarnin sa ne,ko kuma ta ɗan ƙara baccin kafin ya dawo? A hankali ta lallashi kanta ta miƙe ta faɗa bathroom ta yi wanka. Daure da towel ta fito tana waƙe-waƙe kamar ba lokacin sallar asuba bane. Kanta ta hau gogewa da ƙaramin towel tana tsane dogon gashin ta irin na fulanin asali mai yauƙi da santsi,tana ɗago kai ta kalli madubi sai ta ga wani abu ya gilma da gudu wanda bata gama tantance ko menene ba,ihu ta kurma ta haye gado tare da ƙanƙame bargo tana kuka,a haka Jubair ya dawo ya tarar da ita tana naɗe cikin bargo,tambayar duniya ya yi mata amma ta ƙi bashi amsa sam, ƙarshe ma kuka ta sanya masa tana faɗin ya lulluɓe ta ita tsoro take ji.

Da jin haka sai Jubair ya saki murmushi ya rungume ta a jikin shi yana tsokanar ta ya ce,

"Kin san Allah idan kina wani abun sai in rasa ke da Kubrah waye babba,kin yi sallah?"

Tsoron kar ya yi mata faɗa ne ya sanya ta cewa,

"Eh na yi sallah."

Maida musu bargon ya yi suka koma bacci.

Da safe bayan sun kammala duk wani abu da suka saba yi kafin Jubair ya fita aiki ne, Uwa ta koma sashenta ta sa Ubaida ta kira mata Munkaila,tana nan zaune ta harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya Munkaila ya shiga parlourn nata ya samu waje a ƙasa ya zauna,sai da ta gama ƙare masa kallo tin daga saman kan shi har ƙafafun shi sannan ta ce,

"Munkaila ko za ka iya sanar dani abinda ka ke so a gare ni da ya sa ka fara yi min kutse a cikin rayuwata? Idan dan ɗan abinda ya faru ne a tsakanin mu jiya ina so in sanar da kai na janye maganganu na,ni da kai na zan haɗa maka lefe na gani na faɗa na zame maka uwar ɗaki har ka mallaki Ubaida,sai dai ina da sharaɗi."

Cike da zumuɗi Munkaila ya ce,

"Hajiya na amince da kowanne sharaɗi zaki gindaya min,matsawar buri na zai cika."

Kallon shi ta yi tana nazarin sa da kyau,cikin murmushi ta furta,

"Kenan ka amince kai ne ka kai min magungunan da na dawo da su sashen Jubair,tinda babu wanda ya san da zaman su daga ni sai Ummahna sai malam da ya bani su."

Sosa ƙeya Munkaila ya yi kafin ya ce,

"Sai kuma Allah ba, Hajiya Allah ya taimake ki."

Murmushi ta sakar masa kafin ta ce,

"Malam Munkaila kenan,ashe dai kai ɗin ba na wasa bane."

Kallon ta kawai ya yi ya saki wani irin shu'umin murmushi,kafin ya ce,

"Ni dai Hajiya ki ƙoƙarta min ku aura min Ubaida,ita ce farin ciki na,na jima ina son na aureta amma tana ƙi saboda tana jin tsoron kar ki hana..."

Cikin ɗaga hannun ta na hagu Uwa ta ce,

"Magana ai ta ƙare,zan yi ƙoƙarin ganin ka auri Ubaida,ni kuma daga baya za ka tsaya tsayin daka ka cika min alƙawarin da ka ɗauka,idan ka amince shikenan."

"Na amince Hajiya,Allah ya saka da alkhairi ya ƙara girma."

"Amin,kana iya tafiya sai na sake neman ka."

Godiya Munkaila ya yi yana murna ya koma bakin aikin shi,itama Uwa murmushi take ta zabgawa tare da faɗin.

"Mu je zuwa,wai mahaukaci ya hau kura,yanzu za a fara wasan."

******************************

Babbar makaranta ce da ta ƙunshi ɗalibai masu matuƙar hazaƙa a garin Baltimore dake jihar Maryland a ƙasar US. Dare ne amma kai ka ce da tsakar rana matasan ke kai komo a cikin babban hall ɗin dake a tsakiyar makekiya kuma hamshaƙiyar makarantar,rana ce da kowanne ɗalibi ke cike da tsantsar farin ciki da annashuwa kasancewar rana ce ta prom,kowa ka gani tare yake da date ɗin shi.

Wasu matasa ne su uku a tsaye a waje suna kallon hanya tare da duba wayoyin su daga lokaci zuwa lokaci,suna kurɓar abun shan dake cikin kofunan hannayen su,cike da ƙaguwa Elsa ta kalli Mark cikin harshen turanci ta ce,

"Ni fa ina tunanin Queen ba zata samu damar zuwa ba,ina mamakin yanda iyayen ta ke juya rayuwarta,mun gode Allah ma mun kusan cika shekara 18,a lokacin da muka cika shekarun nan babu wanda ya isa ya nuna mana yatsa,barin gidan ma za mu yi."

Mark ne ya kalli Elsa ya mayar mata da martanin maganar ta cikin harshen turanci ya ce,

"Ba daga iyayen ta bane,daga wannan addinin nasu ne na musulunci,da an yi magana sai su ce haram kar mutum ya sha giya,haram kar mutum ya yi zina,haram kar mutum ya saka kaya bai rufe jikin shi ba, haram...."

Wani matashi ne fari tass dake tare da su ya katse Mark cikin sauri ya ce,

"Kar ku sake ku yi magana akan addinin mu haka,mu ci gaba da girmama junan mu kawai,mu jira zuwan Queen,idan kuma ba za ku jirata ba zaku iya tafiya,ni zan jira ta,kar ku manta mu abokai ne tin muna aji ɗaya,yau ranar farin ciki ce a wajen mu kar mu ɓata shi da surutun da bai dace ba."

Ganin yanda ran matashin da Elsa ta kira da Afdhal ya ɓaci ne ya sanya ta riƙe hannun shi ta na faɗin,

"Kwantar da hankalin ka,taron ya fara kawai ku zo mu shiga ciki."

Hannun shi ya zame ya ƙi bin su,yin hakan kuwa ya ɓata ran Mark dan haka sai ya fizgi hannun Elsa suka shige suka bar Afdhal tsaye yana ci gaba da jiran Queen ɗin tasu, ya jima a waje yana jiran ta bata zo ba dan haka sai kawai ya wuce wajen da suka aje motocin su ya ɗauki tashi ya wuce gidan su Queen dan ya ga abinda ya hana ta zuwa prom ɗin.

Isar shi gidan su Queen ke da wuya,sai ya tarar da gidan cikin hayaniya da ihun ta tana ta fashe-fashem abubuwa,duk yanda iyayen ta ke bata haƙuri akan ta nutsu ta ƙi natsuwa balle ta daina fasa musu kayayyakin gidan nasu.

Da sallama ya shiga gidan kamar koda yaushe ya gaishe da Ammar,Samhah mahaifiyar Queen na ta riƙe ta dan kar ta taka kwalabe amma haka ta ƙwace ta yi kan Afdhal da gudu ta rungume shi tana kuka,a daidai wannan lokacin ne ƙofar gidan ta sake buɗewa a karo na biyu Hajiya Dada,Jubair da Ruƙayya suka bayyana a gidan. Salatin da Hajiya Dada ta sanya ne ya dawo da dika mutanen gidan cikin hayyacin su suka zuba mata ido, cike da mamaki Hajiya Dada ta ce,

"Ammar me nake gani haka Malika kwance a ƙirjin wani ƙaton? Ko aure ka ɗaura mata da arne bamu da labari? Na shiga uku ni uwar Zubairu,ashe da bamu zo ba yau da mun ji mugun labari."

Ganin Hajiya Dada na kallon su Malika ta na maganganu tare da zubar da hawaye ne ya sanya Afdhal kwace jikin shi da ƙyar daga wajen Malika ya gudu,a gigice ta bi shi zata kamo shi ta yi tuntuɓe da kujerar da ta wurgar a hanya,kafin ta faɗi ƙasa cikin zafin nama Jubair ya miƙa hannu ya taro ta ta faɗa saman ƙirjin shi,wani irin bugawa zuciyar shi ta yi da karfi,idanu Malika ta zubawa kyakkyawar fuskar shi tana kallo ko ƙiftawa bata yi.........

*Shin me ya kawo Hajiya Dada da mai tsohon ciki ƙasar waje a daidai wannan lokacin?*

*Wace iriyar rayuwa Malika zata gudanar anan gaba a rayuwarta?*

*Uwa na samun nasarar cutar da Ruƙayya da yaranta kuwa? Ko dai reshe ne zai juye da mujiya?*

*KU BIYO NI DAN JIN YANDA ZATA KAYA,KAR KU ZAUNA DA DOGON NAZARIN DA BABU INDA ZAKU SAMU WARWAREWAR SHI FACE A WANNAN LITTAFI NA DUK NISAN DARE....* [09/04, 7:24 am] asiyahabibu93: DUK NISAN DARE....

RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨

*Wannan littafin na kuɗi ne,duk wanda yake group ɗin nan ya karanta bisa amana,dan Allah kar a yi sharing da friends a bari na kammala dika,sai a baiwa duk wanda za a baiwa,da ku yi sharing da ƙawayen ku gwanda ku taimaka ku tallata musu haja ta su saya ko da kuɗin cefanen su ne. Na gode.*