DUK NISAN DARE

PAGE 8

by @1239900

A hankali Ruƙayyah ta zagaye su ta wuce ciki ta samu waje ta zauna saboda ta yi matuƙar gajiya kamar wanda suka tako da ƙafa haka take jin ta,gilmawar ta ne ya sanya Jubair saurin dawowa hayyacin shi,riƙe da hannun Malika ya nufi tsakiyar parlourn da duk ta wargaza komai kamar wata yarinyar goye,cike da dakiya ya kalle ta ya ce,

"Yanzu baby duk ke ce kika yi wannan ɓarnar?"

Sunne kai ta yi tana wasa da hannayen ta,cike da shagwab'a ta ce,

"Papa ban san zaka zo ba,da na san zaka zo da na haƙura da zuwa prom ɗin,da ni zan je ɗakko ku a airport."

Hajiya Dada ce ta karɓe zancen da cewa,

"Ina fa za ki so uban naki ya ga wannan ta'asar da kika yi? Shi wanda kika raina a gidan shi ya ƙyale ki,ai dagewa zai yi ya baki jikin ki ya kammale miki shi waje ɗaya,wataƙila kin samu natsuwa,yarinya sai kace rainon gwauro?....ah ah Samhah me nake gani haka? Kema ciki ne da ke? Kun gama turancin kenan?"

Cike da jin kunya Samhah ta wuce ɗakin da suke ajiye kayan share-sharen su da goge-goge,murmushi Ammar ya yi kafin ya kama hannun Hajiya Dada ya samar mata da wajen zama,itan ma murmushin ta saki ta ce,

"Alhamdulillah mun godewa Allah,ya Allah ba dan hali na ba Allah ka azurta yaran nan da ƴaƴa maza,wanda za su tausaya musu a lokacin da tsufa ya riske su,Allah ka basu masu albarka,Allah yasa kar na mutu sai naga magadan ku."

Jubair ne ya buɗe baki zai yi magana,Ammar ya riga shi ta hanyar faɗin,

"Ameeen Hajjajunmu Allah ya ƙara maki imani da lafiya,ku yi haƙuri ban samu na zo na ɗakko ku ba,na so na yi surprising mutanen gidan ne sai dai kawai su ga na ɗakko ku,amma hakan bai samu ba wannan rigimammiyar ƴar taka duk ta rusa komai."

Ammar ne ya kalli Malika da ta maƙale shi ta zauna daf da shi kamar zata zauna a cinyar shi ya ce,

"Kar ka ɗorawa babyna laifi,da ace ka sanar da ita zuwa na da duk haka bata faru ba,gashi nan garin bata surprise ita ta baka,ka duba ka ga yanda ta farfashe abubuwa masu tsada?"

"Humm Allah dai ya shirya mana zuri'a,mu ta can wa ya isa ya mana wannan iya shegen bamu duba masa fatar sa ba?"

Zumɓura baki Malika ta yi a lokacin da Hajiya Dada ta gama maganarta tana kallon ta,cike da jin haushin an sata gaba ta miƙe cikin wasu irin kaya matsattsu kuma yagaggu,dan kuwa ta gaban rigar gaba ɗaya a fafake yake,iya saman cikakkun ƙirjinta ne kawai a rufe,sai gefen cinyar ta da yake a tsage har ƙasa,ba kaɗan ba jar rigar ta karɓi jikin ta,tsukakken ƙugun ta ɗaure yake da wani siririn golden belt ɗin da ya sha stones masu kyau sai walƙiya yake,gashin ta irin na fulanin asali ta karkaɗa kafin ta sa hannu ta cire dogayen takalman dake ƙafar ta ta riƙe su a hannu ta haye sama. Duk abinda Malika ke aikatawa idanun Jubair na kai,a haka Samhah ta kammala kwashe kwalaben da suka fashe ta goge wajen ta mayar da kayan aikin ma'ajiyar su. Ƙararrawar dake sanar da zuwan ɓaki aka kaɗa,cikin azama Ammar da ya san wanda ke danna ƙararrawar ya miƙe yana murmushi, restaurant ɗin da ya yi order abinci da abun sha ne suka kawo abinci dan tarbon baƙi,sai da ya karɓa ya sallame su ne ya koma da abinci niƙi-niƙi. Ya riga da ya san idan Samhah ta san da zuwan su za ta ce za ta yi girki,kuma ba zata iya ba duba da cewa ba wani aikin wahala take yi ba da cikin.

Sai da suka shiga ɗakunan da aka sauke su suka yi wanka suka shirya sannan suka fito cin abinci,Ammar ne ya kalli Ruƙayya da ke sunkuyar da kai ya yi murmushi sannan ya ce,

"Ni fa Ruƙy kina bani mamaki,har yanzu da muka yi shekaru kusan goma sha takwas baki iya sakin jikin ki da mu? Gaskiya ke a fulanin ma ta daban ce."

Murmushi ta yi kawai ta samu waje a inda Jubair ya fitar mata da kujera ta zauna riƙe da cikin ta da ya yi tsini sosai,suna zama Malika ta sakko cikin gajeran wando iya cinyoyin ta da wata rigar sanyi ƙatuwa mai dogayen hannuwa,gashin kanta a baje a saman kafaɗun ta tana waya tare da bada tabbacin gata nan fitowa.

Ko ta kan mutanen gidan bata bi ba ta tunkari kofar fita daga gidan,sai da ta tsaya ta sanya takalminta ta ɗaure igiyar shi sannan ta ce,

"Pops na fita wajen Afdhal yana waje yana jira na yanzu zan dawo."

Hajiya Dada ce ta kalli Ammar sannan ta kalli Jubair,kafin ta maida dubanta kan Malika da ta buɗe ƙofar ta yi waje abunta hankali kwance,cike da ɓacin rai Hajiya Dada ta ce,

"Ba zai yu ba ! Inaaa ba zan lamunci iya shege ba,jikar tawa ce ke yawo tsirara cinyoyi waje? A gabana... a gaban idanun ku ta fita ta tafi wajen wani ƙato duk baku hana ba? To kai Ammar meye amfanin ka kenan? Ai dole yarinya ta raina ku a yi mata magana ta hau zuba shegen turanci kamar ƴar joji bush."

Shiru wajen ya ɗauka,domin kuwa gaba ɗayan su suna jin hucin ɓacin ran Hajiya Dada na sauka a jikin su,wajen cin abincin ta bari ta wuce ɗakin da aka sauke su ita da Ruƙayya,ganin haka ne ya sanya Ruƙayya miƙewa da ƙyar ta ɗebi abincin daidai yanda ta san Hajiya Dada zata iya ci ta bi bayan ta da shi.

Iska Ammar ya furzar ya na dafe kan shi,a hankali ya furta,

"Irin wannan ɓacin ran nake jiye mana shi yasa nake hana ta wasu abubuwan,ke kuma sai ki ce wai ai haka ake yi ba matsala bane,da ace kin taimaka min wajen baiwa yarinyar nan tarbiyya irin ta addinin mu da al'adar mu da haka bata faru ba."

Jubair ne ya yi saurin cewa,

"Kar ka ɗora mata laifi ɗan'uwana,yarinyar nan tana zuwa makaranta,makaranta babba wadda ta haɗa da INTERNATIONAL students,mutane ne ta kowanne fanni na duniya take tare da su shi yasa ta koyo wasu halayen da babu su a al'ada da addinin mu,da ace a Nigeria take ai wani abun ba zata yi shi ba,kai dai kawai mu yi ta taya ta da addu'a shine mafita."

Ruƙayya ce ta dawo ɗauke da abincin da ta kai wa Hajiya Dada ta kalli Jubair da Ammar ta ce,

"Taƙi ci,dan Allah ku je ku lallashe ta,dan ko a jirgi ma banga ta ci wani abun kirki ba."

Ammar ne ya karb'i abincin ya tafi ɗakin Hajiya Dada,ya jima sosai suna tattaunawa kafin ya dawo ya na hamdala,zaune ya tarar da su Jubair a parlour suna hira,a hankali ya isa bakin window ya na leƙen su Malika dake hira ita da Afdhal riƙe da hannun junan su,girgiza kai ya yi cike da takaici ya bar wajen,duk hirar da ake yi hankalin shi na kan Malika. Sai da suka kusan barin parlour'n sannan ta shigo gidan cike da maɗaukakin farin ciki,kusa da Jubair ta zauna ta na washe baki ta ce,

"Papa gobe friends d'ina za su haɗa min party saboda rashin samun damar halartar prom da ban yi ba,abokai na su na so na da yawa."

Ta ƙarasa maganar ta cikin wani ƙayataccen murmushi ta ɗauki Apple ɗin dake saman table ɗin gabanta ta gatsa, Samhah ce ta ce.

"Su na dai tsoron ki,tinda idan basu yi maki abinda kike so ba zaki hau fushi da su ki na yi musu masifa."

A shagwab'e Malika ta kalli Ammar ta ce,

"Daaaddd."

Murmushi kawai ya yi ya shafi kanta ya tattara mugs ɗin da suka sha shayi ya wuce kitchen da su,zuciyar shi fal tunani kala-kala.

Washegari da safe su Jubair asibitin da Ruƙayya ta saba haihuwa a duk sanda ta samu ciki suka tafi,duk wani abu da ya kamata su yi sun yi sun kammala lafiya,daga nan sai suka wuce siyayya wani babban mall,zuwan su ke da wuya Ruƙayya ta ga wasu masoya na sumbatar junan su a tsakiyar mutane ko kunya basu ji, a matuƙar kunyace ta laɓe a bayan Jubair tana tafiya kanta a ƙasa,banda dariya babu abinda Jubair ke yi mata,cike da tsokana ya ce,

"Madam ko muma za mu nuna musu tamu kalar soyayyar irin ta ƴan Nigeria ne?"

Cikin sauri ta girgiza kanta ta yi gaba ta bar shi a baya yana yi mata dariya. Haka rayuwar su Jubair ta ci gaba da gudana a kasar turai suna jiran ranar haihuwa ta zo,dan kuwa daf take da haihuwar,Samhah kuwa watan cikin ta takwas ta na da sauran wata ɗaya kafin ta haihu.

Duk wani rashin ji da zuwa party,da yawo babu sururar arziƙi da Malika ke yi akan idanun Hajiya Dada,sai dai Jubair kanshi ya yi mamakin yanda ta dena damuwa da hakan balle ta yi faɗa akai. Malika kuwa ta ji daɗin yanda Grandma ɗin nata bata saka mata ido ba wannan zuwan balle ta hana ta rawar gaban hantsi.

****************************

A can Nigeria kuwa hankalin Uwa ya kasa kwanciya tin bayan da su Jubair suka wuce ƙasar waje,duk wani duba da tsubbace-tsubbace ta yi akan sanin abinda Ruƙayya zata haifa amma abun ya ci tura, ƙarshe ma Munkaila ne ya zaunar da ita ya yi mata bayani dalla-dalla wanda ya sake sanya ta ciki damuwa,cike da tashin hankali ta kalli Munkaila wanda shigar shi sashe nata kenan babu jimawa ta ce.

"Yanzu ka na nufin haka zan zauna ba tare da sanin me Ruƙayya zata haifa ba? Ai a zato na ƙarfin tsafin naka ya kai inda ya kai,ashe kai ma kamar sauran ne duk ha'inci kuka saka a gaba,aikin banza ma malam tashi ka bani waje."

Rai a matuƙar ɓace Munkaila ya kalli Uwa ya ce,

"Duk ƙarfin tsafi na bai kai ya hukuncin Allah da kike son ja da shi ba,baki da labarin akwai abinda idan Allah ya shiga lamarin babu bokan duniyan da ya isa ya kutsa ta cikin shi? Raina ƙarfin baiwar da Allah ya min ta sanin ilimin bokanci da kike yi watarana zai hana ki samun nasara akan maƙiyan ki,da ace kin tsaya mun yi magana a natse da wataƙila na baki shawarar yanda zaki kawar da ko me aka haifa namiji ko mace,ni Munkaila aiki nake da baƙaƙen rauhanai babu inda ba zan aike su ba a faɗin duniyar nan."

Kalaman Munkaila sun shiga jikin Uwa har sun sanya mata wata iriyar yarda da shi tare da imani mai ƙarfi akan karfin tsafinsa. Cikin washe baki Uwa ta ce,

"Ka yi hanƙuri Munkailan Ubaidaa,ɓacin rai ne ya sa na faɗi abinda na faɗa,na baka wuƙa da nama akan lamarin nan,idan har ka yi sanadiyyar hallakar da abinda Ruƙayya ta haifa a can turan zan yi maka kyauta mai tsoka ta ban mamaki."

Ba tare da Munkaila ya ce mata komai ba ya miƙe ya bar parlour'n ya wuce ɗakin shi dake ɓangaren ma'aikatan gidan,wata jakar shi tsohuwa tukuf da ta gaji da shan iskar duniya ya zaro a ghana most go ɗin shi. Wani buzun fatar damisa ya zaro daga jakar ya shimfiɗa ya kalli yamma,nan take ya sa hannu ya dinga zaro sauran kayayyakin da yake da buƙata. Ya jima ya na wasu irin surkulle kafin ya tashi ya tattare kayan shi ya mayar dasu maɓoyar su.

Wani irin shu'umin murmushi ya saki kafin ya hau yiwa kan shi kirari.

***************************

Tun da safe da su Ruƙayya suka tashi take jin jikinta na yi mata wani irin ciwo musamman marar ta da bayanta,Hajiya Dada kuwa na kula da yanayin ta,dan haka suna kammala cin abincin safe ta sa Jubair ya ɗauki akwatin da suka haɗa kayan haihuwar su tin a Nigeria suka wuce asibiti. Lokacin da suka tafi Ammar ya na office,Samhah kuwa dake aikinta daga gida tana can tana meeting,Queen Malika kuwa ta na ɗakinta tana bacci saboda kwana da suka yi party ita da ƙawayenta.

Kamar jira ake su isa asibitin naƙuda ta tasowa Ruƙayya gadan-gadan,cikin sauri aka shirya ta cikin rigar da masu ciki ke sanyawa aka shiga da ita ɗakin haihuwa.

A can Nigeria kuwa Munkaila na tsaye ya na aske shuka ya yi murmushi ya ce,

"Lokacin aikin ka ya yi ƙaramin su babban su"........... [09/04, 7:24 am] asiyahabibu93: DUK NISAN DARE...

RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨