PAGE 9
by @1239900
Banda addu'a babu abinda Hajiya Dada ke yi ita da Jubair,ƙarshe waje ya samu ya zauna a gefen Hajiya Dada ya jingina kanshi a kafaɗarta tare da lumshe idanun shi,sun jima sosai a haka suna jira kafin nurses su buɗe ƙofa a gangaro da Ruƙayya a saman gado kamar matacciya,cikin azama Hajiya Dada da Jubair suka miƙe suka nufi inda Ruƙayya ke kwance kamar gawa, a rikice Jubair ke tambayar su dalilin da yasa ya ga matar shi a haka,kwantar masa da hankali suka yi kafin likita ya hau yi masa bayani cikin harshen turanci.
"Mr Jubair ka yi haƙuri da abinda zan sanar da kai yanzu,abu na farko shine duba da yanayin wahalar da matar ka ta sha kafin ta haihu,tana buƙatar hutu sosai kafin ta sake ɗaukan wani cikin,yana da kyau ku bi duk wata hanya da zata fiye maku sauƙi ku yi tsarin iyali na kimanin shekaru biyu zuwa uku, abu....."
"Dr. Dan Allah ka sanar dani me ya same ta naga bata motsi? Sannan ina abinda aka haifa yake? Na ji kuka sau ɗaya daga nan ban sake jin komai ba wai me yake faruwa ne?"
Hajiya Dada dake zaune a saman kujera a gefen Ruƙayya da ke sanye da bututun dake bata oxygen ce ta kalli Jubair ta share hawayen ta sannan ta ce,
"Dan Allah ka tambaye su me ya sami ƴar mutane ta ke a sanƙame kamar gawa? Sannan ina jika na dan kuwa na jiyo kukan shi."
Ɗaga kan da Hajiya Dada zata yi sai ta ga an shigo da jariri cikin wani irin yanayin da ya sanya ta dafe sandar ta zata tashi, da sauri Jubair ya kama ta ya taimaka mata yana rarraba idanu tsakanin likita da jinjirin dake naɗe kamar gawa. Banda kiran sunan Allah babu abinda Hajiya Dada da Jubair ke yi.
Lokacin da likita ya sanar da shi mutuwar kyakkyawan jaririn nasu ƙarfin imani da Allah ne ya sanya su kamewa ba tare da sun yi hargowa ko nuna karaya ba,hawaye wani na dukan wani haka suke zuba a kuncin Hajiya Dada.
Jubair ne ya karb'i kyakkyawan jaririn nasu fari tasss mai kama da iyayen shi yana kallo,ƙwallar idanun shi ya share ya sumbace shi kafin ya zaro wayar shi ya ɗauke shi hotuna da videos,yana gamawa sai ya miƙawa Hajiya Dada ta karɓe shi tare da fashewa da kuka mai tsananin cin rai,cikin kuka da sarƙewar kalamai Hajiya Dada ta ce,
"Allah..Allah..mun gode maka...Allah ka sa mai ceto ne,Ruƙayya Allah ya baki lafiya,shikenan mun rasa magaji Jubair, innalillahi wa inna'ilaihirraji'un."
Haƙuri Jubair ya dinga baiwa Hajiya Dada kafin ya samu ya kira Ammar ya sanar da shi abinda ke faruwa. Suna nan ana ci gaba da kula da Ruƙayya Ammar ya iso shi da Malika da Samhah da ke ta kuka mai tsanani na tausayawa,ganin irin halin da Jubair ke ciki ne ya sanya Malika rungume shi ta fashe da kuka,cike da shagwab'a ta ce,
"Papa please don't cry, don't be sad ba gamu ba,har yanzu kana da ni da su Kubrah, ka dena damuwa please."
Murmushin karfin hali Jubair ya yi mata ya shafi kuncin ta kafin ya miƙe ya isa gaban gadon Ruƙayya dake ta sharar bacci,kallon ta yake yi cike da tausayawa,ta ci burin samarwa Hajiya Dada farin ciki ta hanyar haifar ɗa namiji,ta yi yawon asibitoci dan ta san gender ɗin abinda zata haifa sai dai Allah ya lulluɓe mata duk binciken da akai ba a gane gender ba,ashe Allah hakeem ya yi musu kyautar ɗa namiji ne,hamdala ya samu kanshi da yi a ƙalla yana saka rai watarana za a haifa masa ɗa namiji a gidan shi.
Sun jima zaune kafin daga baya duk su tafi gida a bar Jubair a wajenta koda zata tashi cikin dare ta yi tozali da shi,cemetery ɗin da ake binne musulmai Ammar ya nufa da jinjirin bayan an yi masa wanka an sallace shi aka binne shi.
Bayan kwana biyar da haihuwar Rukayya,Hajiya Dada ta ce su fara shirin komawa gida,washegari Jubair ya ɗauki Malika suka fita zaga gari dan yin bankwana da juna kamar yanda ya saba yi duk zuwan da yake yi,tinda suka fita tun safe basu dawo ba sai da dare,sun ci su sha a waje sun yi siyayya niƙi-niƙi kamar wanda za a buɗe ƙaramin shago,Ruƙayya ce ta ga yanda Malika ke ta ɓata rai kai da ka gani zaka san kaɗan take jira ta saka kukan rikici,murmushi ta yi kafin ta ce,
"Yanzu duk yawon nan da kuka sha bai ishe ki ba Queen? Lallai akwai aiki kenan ranar rabuwa."
Kamar an watsawa Malika kashin akwaki a kayan sallah haka ta buɗe baki da murya ta dinga rusa kuka,cikin tsananin takaicin halayyar ta Samhah ta hau yi mata faɗa,Ammar ne ya sakko daga bene yana bin Hajiya Dada da kallo,da ido ta yi masa alama kafin ya ƙarasa sakkowa ya zauna kusa da Malika,kama hannun ta ya yi ya zaunar da ita a gefen shi cikin sigar lallashi ya ce,
"Queen meye haka kike yi ne uhum? Nan da wasu watanni fa za ki cika 18 years,ke ba karamar yarinya bace kuma,yanzu ki yi shiru ki faɗa min me kike so ayi."
A hankali ta fara rage kukan ta ta koma gefen Jubair ta zauna,cike da shagwab'a ta ce,
"Ni ina son Papa ya zauna anan,bana son ya barni in jima ban gan shi ba."
Dariya Ruƙayya ta fashe da ita kafin ta yi saurin rufe baki tana ƙunshe dariyar,Jubair ne ya yi mata harar wasa kafin ya kalli Malika ya ce,
"Baby i can't stay here kin sani,ko kin manta da sauran ƴan'uwan ki dake gida Nigeria? Kin manta da muƙami na a garin mu? Ba zai yu na zauna anan ba."
Ammar ne ya miƙe ya zaro visa ya damƙa a hannun Malika sannan ya ce,
"To me zai hana ke tinda kin gama High School ɗinki ki bisu? Dama ba abinda kika jima ki na so bane wato zuwa Nigeria wajen Papa?"
Kallon Ammar ta yi cike da maɗaukakin farin ciki,sai ta maida kallon ta ga Jubair da ke cike da mamaki shima,Hajiya Dada kuwa kafe Malika ta yi da ido ta na jiran ta ji amsar botsararriyar jikar ta ta,babu zato ko tsammani suka ga Malika ta kurma uban ihu ta ɗale mahaifinta tana murna tare da sumbatar shi. A guje ta haye sama ta shige ɗakin ta ta kulle ƙofa,Jubair ne ya kalli Ammar ya ce,
"Yanzu ka tabbata ba zata yi rigima ba idan ta bi mu?"
Kafin Ammar ya amsa shi Hajiya Dada ta cafe maganar ta hanyar cewa,
"Ai kar ka wani damu da rikicin da za ta yi,dama na jima ina fatan yarinyar nan ta koma gida duba da yanayin tarbiyyar ƙasar nan ya sha banban da al'adu da ɗabi'unmu tare da addinin mu,dole ne idan muna son kare iyalan mu daga wuta kamar yanda Alkur'ani ya ce to fa sai mun tsaya tsayin daka mun haɗa ƙarfi da ƙarfe mun basu tarbiyya ta gari,Allah ya sani na yi iya bakin ƙoƙari na dan ganin tarbiyyar ku ta inganta,to fa ba zan tsaya na zuba ido da raina da lafiyata ita kaɗai ta taso a sangarce a lalace ba,a gaban idanun mu yarinyar nan ke rungume a ƙirjin wani namijin da ba muharramin ta ba,kuma bata ji cewar ta aikata ba daidai ba balle ta gyara,zaman ta a wajen mu zai sa a hankali,yau da gobe ta gane abinda take yi ba daidai bane."
Ammar ne ya amshe maganar da faɗin,
"Shi yasa muka haɗa baki da Hajiya Dada akan ta bi ku kawai,shaƙuwar dake tsakanin ku zata sauyata watarana."
Duk da cewa cikin zuciyar Samhah bata son yin nesa da ƴar ta amma kuma ta san cewa hakan shine mafita akan gurɓacewar da tarbiyyar Malika ta samu. Haka suka ci gaba da tattaunawa ba tare da Jubair ya ji menene ra'ayin Ruƙayya akan tafiya da Malika ba,ita kuwa Ruƙayya hirar ta take yi da Samhah,inda Samhah ke yi mata ƙarin bayani akan halayya da ɗabi'un Malika da ba kowa ne ya san tana da su ba.
Malika kuwa na ɗaki tana sanar da ƙawaye da abokan ta maganar tafiyar ta,tare da gayyatar su party kafin su tafi,Afdhal ba karamin shiga tashin hankali ya yi ba har sai da ya fara zuba mata larabci ba tare da ta san me yake faɗa ba. Farin cikin da Malika ke ciki ne ya mantar da ita kewar abokan nata da iyayenta,Nigeria da mutanen cikinta kawai take hangowa a idanun ta,daren ranar da ƙyar ta yi bacci saboda murna da haɗa kayan ta da za ta yi tafiya da su.
Washegari da yamma su Afdhal suka zo a mota suka ɗauki Malika dake sanye da wata siririya kuma yaloluwar rigar da za a kira da rigar shan iska,Hajiya Dada na kallon su bata tanka musu ba dan kuwa ta ƙudurta a ranta wannan ne na ƙarshe,idan ta je Yola ta ga a gidan uban da zata dinga yin wannan shigar. Tinda suka tafi kuwa basu dawo da Malika ba sai ƙarfe huɗu na asuba,lokacin da ta dawo Jubair ya zaci zai ganta a buge kamar yanda yake ganin yaran turawa na yin party a shawu a bugu,sai ya ganta ragas cike da farin ciki da kyaututtukan da ƙawayen ta suka bata. Ammar ne ya dafa kafaɗar Jubair ya ce,
"Broth yana daga cikin godiyar da a kullum nake yiwa Allah da ya sa Malika bata shaye-shaye,ba kuma ta biyewa samari suna aikata zina da sunan soyayya,ita tana da ra'ayin sex after marriage ne,ka bar Malika da kafiya akan abinda take so,saka matsattsu da ƙananan kaya,yawan shiga cikin maza tare da taɓa jikin namiji kamar wani ƙawarta,sai ɗan banzan son yin party da jin kiɗa da rawa,shi yasa a kullum idan ina yi mata faɗa ranta ke ɓaci saboda a ganin ta ita bata aikata komai mara kyau."
Tinda Jubair ya ji babu wanda ya taɓa kusantar Malika kuma bata shan giya,sai ya ji wata iriyar natsuwa da kwanciyar hankali sun ziyarce shi,nan take ya maida hankali yana sauraron duk wani abu da take so da wanda bata so dan su kiyaye wajen kula da ita.
Washegari da misalin uku na rana jirgin su Jubair ya tashi daga Baltimore Washington international airport(BWI),Malika ko ƙwalla bata yi ba wai dan zata rabu da iyayen nata,sune ma suka rungume ta suna jin kamar idan ta tafi ba zasu sake ganinta ba.
Tafiyar awanni sha ɗaya da minti ashirin da biyar ce ta sauke su a filin jirgin garin Yolan Adamawa ta fulanin asali,banda baza idanu da firfita da hannu babu abinda Malika take yi,domin kuwa sun dawo ana tsananin zafi.
Ruƙayya ce ta juyar da fuskarta tare da share ƙwallar dake gangaro mata saboda tunawa da rasa ɗanta ƙwalli ɗaya namijin da suka ƙwallafawa rai daga ita har surukarta,tsakanin Jubair da Hajiya Dada babu wanda ya kula da halin da take ciki saboda suna can suna lallaɓa Queen Malika dake shagwab'ar zafi take ji.
A haka suka ja akwatinansu suka nufi inda motar su ke tsaye tana jiran su, suna isa driver ya fito ya durƙusa cike da murna yana gaishe da iyayen gidan nashi,jibgegiyar motar da aka zo ɗaukan su Malika ta kalla ta ce,
"Wooww what a nice ride Papa."
Murmushi Jubair ya yi kafin ya ce,
"Sai ma mun je gida zaki ga wasu,ina fatan su burge ki."
"Da gaske Papa?"
Ɗaga mata kai kawai ya yi yana murmushi,nan take Malika ta ja hannun shi suka wuce cikin mota suka zauna,Ruƙayya kuwa sai ja ƙafafun ta tana yaƙe ta bi bayan su ta yiwa kanta mazauni a gefen Hajiya Dada,duk inda suka wuce sai Jubair ya yiwa Malika bayani har suka isa gida.
Bayan mai gadi ya buɗe ƙofa sun shiga cikin gidan ne Malika ta buɗe baki tana jinjina kyawu da tsaruwar gidan,su Kubrah ne suka fito a guje suna ihun murna suka nufo Ruƙayya tare da tambayar ta ina ƙanwar su ko ƙanin su.
Munkailah ne ya biyo bayan Ubaida dake washe baki tana son ta ɗauki rahoton abinda aka haifa ta kai wa uwar ɗakin ta batare da ta san ta riga ta sanin me ya sami jariri ba,Kulu kuwa kaya ta fara shigarwa ta na faɗin,
"Bari na je na juye ruwan wankan jego Hajiya,sannun ku da dawowa lafiya."
Jiki babu ƙwari Ruƙayya ta wuce sashenta tare da yaran ta da ke ta tambayar ta abinda aka haifa,tana shiga parlourn sashenta ta durƙushe a tsakiyar wajen ta rushe da wani irin kuka mai tsananin ban tausayi,kuka ne da ta riƙe shi tun a lokacin da ta farka daga gadon asibiti aka bata tabbacin yaron ta ya koma har an binne shi,kwanan ta biyu bata san inda kanta yake ba balle ta rungume shi,banda hotuna da videos da Jubair ya yi da bata san ya kalar abinda ta haifa yake ba.
Tana tsaka da kuka ta ji ƙamshin turaren Uwa na dukan hancin ta,cikin sauri ta miƙe da niyyar ta shige bedroom ɗinta, dan kuwa bata son Uwa ta ganta a wannan yanayin,sai dai ta riga da ta makaro,domin kuwa tana miƙewa ta juya idanun ta suka sauka akan fuskar Uwa da ke bayyanar da wani irin shu'umin murmushi mai cike da ma'anoni masu yawa........ [09/04, 9:41 am] asiyahabibu93: DUK NISAN DARE...
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨