DUK NISAN DARE

PAGE 10

by @1239900

"Too ni wai yanzu da mai jego zan kira ki ko kuma UWAR MAGAJIN JUBAIR? Toh ! koma dai menene sunan ki ina yi maki barka da dawowa ƙasar ki ta gado lafiya,an tafi an barmu lafiya an same mu lafiya,abinda aka rasa kuma Allah ya jiƙan rai."

A rikice Kubrah,Ihsan da Mubeenah suka sauke idanun su akan mahaifiyarsu dake rizgar kukan da ta kasa riƙewa,cikin sauri ta bar parlourn ta shige ɗakinta,rai ɓace Kubrah ke bin Uwa da kallo tana hararar ta,dariya Uwa ta yi kafin ta ce,

"Allah sarki kar ki damu yarinya,ai tinda uwar ku ta iya haihuwar namiji shekarar nan,to ki bata shekara ɗaya zata sake haifo wani,kina son ganin hoton shi in nuna miki? Zo ki kalla Daddyn ku ya tura min,God the baby was so cuteee."

Hawaye Kubrah ta share ta wuce ɗakin da mahaifiyarta da kannen ta suka shige,ganin ɓacin rai a saman fuskokin Ruƙayya da yaranta ba ƙaramin faranta ran Uwa ya yi ba,cike da takun ƙasaita da yanga ta fita harabar gidan dan zuwa yiwa Hajiya Dada barka da dawowa,gayun da ta sha kaɗai ya isa ya nuna maka irin hutawar da Uwa ke yi a gidan. Ta na daf da shiga sashen Hajiya Dada Munkaila ya fito daga yi mata barka da dawowa,yanda yake sunkuyar da kai sai mutum ya rantse da Allah limamin wata unguwar ne,ido suka haɗa da Uwa ta zabga masa murmushin gamsuwa da aikin shi,shi ɗin ma murmishi ya yi mata tare da faɗin.

"Yanzu ma aka fara wasan Hajiya."

Ba tare da ta bashi amsar maganar shi ba, sai ta ce,

"Ka shigo sashena da safe ka karɓi tukuicin aikin ka."

Zubewa ya yi a wajen ya na zabga mata godiya,ba ta tsaya amsa godiyar shi ba ta wuce cikin sashen Hajiya Dada,ta na saka kanta cikin parlour'n ta ci wani wawan burki tare da ƙunduma wani irin ashar ɗin da babu wani mahaluƙi da ya taɓa yin irinsa a gidan. Cike da tsananin mamaki Hajiya Dada da Jubair suka ɗaga kai suna kallon ta,Malika kuwa da bata san ma'anar kalaman da ta furta ba tinda ta kalle ta sau ɗaya sai ta kauda kai ta sake gyara kwanciyar ta a jikin Jubair ta na latsa wayar ta. A harzuƙe Uwa ta karasa shiga parlourn ta janyo Malika ta wurgata gefe ta na sauke numfashi kamar mai ciwon hawan jini,cikin wata iriyar ƙwallar baƙin ciki Uwa ta ce,

"Wannan wacce ƴar iskar ce kuma ta zauna a jikin ka Jubair?"

A yatsine Malika ta kalli Uwa ta ce,

"Don't you ever call me that,suna na Queen, ohh sorry Malika,i am Ammar's daughter,idan baki sani ba ki sani,kar ki sake kirana da ƴar iska."

Cike da jin haushin abinda Uwa ta yi mata ta wuce ɗakin da aka shigar mata da kayan ta ta kulle ƙofar da ƙarfi har sai da su Jubair suka rintse idanun su,wata gwauruwar ajiyar zuciya Jubair ya sauke tare da faɗin.

"Hankalin ki ya kwanta kin ɓata mata rai daga zuwan ta,wai me yake damun ki ne Hafsat? Malikar ce baki sani ba ko kuma me?"

"Idan na san ta fa? Idan na san ta sai aka ce ta zo ta ruƙunƙume ka ta maƙale ka haka sai kace zata shige cikin ka?"

"She is just a child Hafsat,nawa Malikar take da zaki ɗaga hankali akan ta haka? Ke kin san a matsayin ƴa na ɗauke ta,haka zalika itama a matsayin uba ta ɗauke ni,a kaf duniyar nan bayan ke wa nake da shi a matsayin ɗan'uwa da ya wuce mahaifinta? Haba Hafsat ki dinga abu da hankali mana."

Cike da ɓacin rai Jubair ya miƙe ya bar sashem Hajiya Dada da ke bin su da kallo cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara,suna haɗa ido da Uwa sai ta sakar mata murmushi,Uwa kuwa zumɓura baki ta yi ta zauna a gefen Hajiya Dada ta ce.

"Yanzu dan Allah Hajiya menene laifi na dan na yi kishi akan Hammaah Jubair? Ina ce cikar soyayya kishi?"

"Ah ah cikar soyayya shine haƙuri,a koda yaushe idan kina so soyayyar ki ta yi nasara a zuciyar mijinki,ki sanya haƙuri,ki rage ƙorafi da bani-bani,zafin kishi da mahaukacin kishi na rusa soyayyar da aka gina ta cikin shekaru masu yawa,idan ba haka ba sai soyayyar da aka gina a ƙanƙanin lokaci ta yi mata zarra."

Hawaye ne suka fara zuba a kuncin Uwa kafin ta ce,

"Na riga da na san soyayyar Hammah Jubair ce ajali na watarana,ina son shi,ina kishin shi,ina tsananin ƙaunar shi,da so samu na ne kar wata ƴa mace ta kusance shi balle har aure ya haɗa su,da so samu na ne na kasance matar shi ni kaɗai har ƙarshen rayuwar mu."

Murmushi Hajiya Dada ta yi kafin ta ce.

"Wannan shine babban dalilin da ya sa kika ƙi zaman gidan mijin ki,kika baro ƴaƴan ki kika kaso auren ki dan kawai ki kasance da Jubair?"

"A yau ba zan ƙi amsa laifi na da kuka jima kuna tuhumata akai ba,na yarda na amince soyayyar Hammaah Jubair ce sanadiyyar rabuwata da gidan uban ƴaƴana,na baro yarana saboda na zama a ƙarƙashin kulawar mutumin da na fi so a duniya fiye da yanda nake son kai na,har yau idan na tuna kukan da Usman yake yi tare da yi min magiya akan kar na tafi na barsu abun na taɓa zuciyata,amma ya zan yi Hajiya? Zuciya ta da ruhina mallakin Jubair ne,idan ina so su ci gaba da rayuwa dole na sanya su cikin gangar jikin shi."

"Tirƙashi !"

Itace kalmar da Hajiya Dada ta furta tana kallon Uwa dake magana cikin wani irin yanayi na farin ciki da baƙin ciki,hawayen ta ta goge ta miƙe ta wuce sashen Jubair. Tana shiga ta tarar da shi yana waya da Ammar,bata ce masa komai ba ta wuce ɗakin shi ta haɗa masa ruwan wanka a kwamin wanka,tare da zuba duk wani kayan wanka da turarukan da Jubair ke amfani da su,maganin da Munkaila ya bata a ranar da ya sanar da ita rasuwar yaron Ruƙayya ta zaro ta zuba a cikin ruwan wankan ta juya da kyau sannan ta soke maganin ta fita,ko kallon inda take Jubair bai yi ba saboda har a wannan lokacin yana fushi da ita akan abinda ta aikata,cike da kirsa da kisisina Uwa ta isa gaban Jubair ta fara balle masa botiran rigar shi,idanunta ta zuba masa tana wani lumshe su tare da ware su a saman fuskar shi,cikin kashe murya da shagwaɓe ta Uwa ta ce,

"Haba Babyn Hafsy meye na ɓata rai haka? Kai ka san son da nake yi maka ne ya jawo nake tsananin kishin ka,sannan kar ka manta laifin ka ne fa har hakan ta faru,me yasa da muka yi waya da kai kafin ku dawo baka sanar dani zaku dawo tare da Malika ba? Sannan yarinyar nan na jima ban ganta ba,rabona da ita tin tana da shekara goma a duniya,yanzu na ganka da macen da ta fini tsawo da diri ka yi zaton zan kwantar da hankali na?"

Ajiyar zuciya mai ƙarfi Jubair ya sauke,dan kuwa ya gano inda ya yi ba daidai ba,tabbas bai kyauta ba da bai sanar da Uwa zuwan da zai yi da Malika ba,dan haka sai kawai ya lakace mata hanci ya yi gaba ya na faɗin,

"To a min afuwa ba zan sake ba shikenan? And please ki kama girman ki,kar ki bari raini ya shiga tsakanin ki da yarinyar nan,tarbiyyarta daban da wadda kika saba gani."

Kyaɓe baki Uwa ta yi ta isa gaban dinning table ta hau buɗe abincin da Ubaida ta jera tin kafin su dawo. Sai da ta tabbatar da Jubair ya shiga wanka sannan ta buɗe miyar ta barbaɗa maganin da ta saka a ruwan wankan Jubair ta jujjuya ta mayar ta rufe. Waje ta samu a saman kujera a parlour ta kwanta tana kallo hankalin ta kwance.

Koda Jubair ya fito daga wanka ɗaure da towel sai ya duba inda kayan shi suke ya zaɓo wasu ƙananan riga da wando masu laushi ya sanya,turarukan shi masu sanyin ƙamshi da tsada ya fesa kafin ya ɗan shafa lotion sama-sama ya fita,cikin ranshi yake yabon Ruƙayya,domin kuwa da girkin ta ne da ya ga tarairaya fiye da yanda ta saba yi masa,shi yasa a duk sanda ya yi tafiya yafi so ya dawo a ranar girkinta dan ya samu kulawa ta musamman.

A kwance ya ganta a kujera ta na bacci,murmushi ya yi sannan ya gyara mata kwanciyarta ya wuce saman dinning domin ya ci abinci,a hankali ya furta,

"Yanzu fa saboda girkin nan da ta yi shine take jin ta gaji har bacci ya ɗauke ta,Hafsyna raguwa kenan,shi yasa Ruƙy ke burge ni,sam bata da ƙiwa da lalaci."

Tana kwance tana jin kalaman shi da suka sanya ta murmusawa,fatan ta bai wuce ya zauna ya ci abincin nan ba,dan kuwa tana sane ta kwanta tai shiru dan kar ya ce su ci tare. Sai da ya kammala cin abincin shi ne ya wuce ya wanke bakin shi sannan ya duƙa ya ɗauke ta ya wuce bedroom da ita.

Malika kuwa tinda ta shiga ɗaki take fushi akan abinda Uwa ta yi mata,ba ƙaramar ƙiyayya take yiwa Uwa ba,gaba ɗaya sai ta ji bata son ta dama ba a gidan take ba,tsaki ta ja kafin ta shiga banɗaki ta yi wanka ta sauya kayan ta daga dogon wando da T-shirt zuwa wasu ƙananan kaya masu matuƙar bayyana surar jiki,tana kammalawa ta haye gado ta buɗe laptop ɗin ta ta yi connecting da WiFi ɗin gidan da Jubair ya sanar da ita password ɗin tun shigar su parlourn Hajiya Dada,sai da komai ya daidaita ne sannan ta kira iyayen ta video call,sun jima suna hira tana basu labarin tafiyarta da irin daɗin da ta ji na ganin su Kubrah,nan take ta sanar da mahaifiyarta tana son Kubrah,tana so su zama ƙawaye,murmushi Samhah ta yi ta ce,

'Sai ki dinga yi mata kirki idan kina son ta zama ƙawar ki,mu a Nigeria ba a bullying ƙawaye,ba kuma a nuna musu sarauta,wannan sunan naki na Queen ajiye shi za ki yi ki zama Malikar ki,ta haka ne za ta zama ƙawar ki.'

Buɗe baki Malika ta yi kafin ta ce,

"Dama yin abota da mutanen Nigeria wahala ne da shi haka?"

Dariya sosai Ammar da Samhah suka dinga yi,suna tsaka da hira ne Hajiya Dada ta buɗe ƙofa ta ce,

"Idan kin gama ki zo ki ci abinci kar ya yi sanyi."

Tura baki Malika ta yi sannan ta ce,

"In dai wannan mayyar na nan ba zan fito ba,bana so na ƙara ganin ta she is so mean."

"Bata nan,ta tafi tun d'azu,maza ki gama ki zo ki ci abinci kin ji jikallena?"

Cike da shagwab'a ta ɗaga kai tare da rufe laptop ɗin ta ko sallama bata yiwa iyayenta ba ta bi bayan Hajiya Dada,ta na zuwa ta buɗe abincin ta ga yawanci carbohydrates ya fi yawa,tsaki ta yi sannan ta miƙe ta ce.

"Ni bana son wannan,salad nake so na ci."

"To zauna na kirawo Kulu ta haɗa maki,bayan shi akwai wani abu da kike so kuma?"

"Eh sai smoothy ɗin abarba da kankana a ɗan saka ayaba guda ɗaya a ciki."

Waya Hajiya Dada ta zaro ta kirawo Kulu tare da bata umarnin abinda zata haɗawa Malika,tana ajiye wayar Malika ta ce,

"Grandma ina su Kubrah suke? Tinda muka zo ban sake ganin su ba."

"Suna ɓangaren su,ko zaki je ne? Sai ki ci abincin ki ma a can ku yi hira."

Cike da zumuɗi Malika ta tashi zata tafi,Hajiya Dada ce ta yi mata kwatancen ɓangaren Ruƙayya,har zata fita Hajiya ta kalli shigar dake jikin ta,sai ta kira ta ta ce,

"Malika kin san da cewa kin dawo Nigeria ko? Mu ta nan ba a saka kaya irin wannan sun yi ƙanana da yawa,a ɗaki ake saka su inda babu wanda zai gan ki,dan haka ki je ki duba a kayan ki idan akwai irin dogon wandon da kika saka da za mu zo gwanda ki saka irin shi,amma wannan ya yi guntu da yawa."

Baki Malika ta zumɓura ba dan ta so ba ta koma ɗakinta ta sauya kayan jikin ta,duk da cewa su ɗin ma babu abinda suka ɓoye na daga shape ɗin ta,sun dai fi wanda ta cire tsaho. Cikin fara'a ta fita dan zuwa sashen Ruƙayya,tana fita ta ci karo da Munkaila da Ubaida na tsaye a ƙofar da zata kai mutum sashen Uwa suna hira,suna ganin ta suka tsaya cak suna binta da kallo. Tana wucewa Munkaila ya kalli Ubaida ya yi ƙasa da murya ya ce...........[10/04, 6:15 pm] asiyahabibu93: DUK NISAN DARE...

RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨