PAGE :6
by @1239900
D'akin Innoh Mommy ta nufa cike da k'warin guiwa, ta na shiga ta gan ta jingine da allon gado gefen fuska ya kumbura sai hawaye ke tarara daga idanun ta, cike da qunshe dariya Mommy ta ƙarasa gabanta ta zauna ta ce,
"Sannu Innohta Allah ya baki lafiya,a gaskiya ban ji daɗin abinda Baaba ta yi miki ba, wannan da da tsautsayi haqorin ta ya huda fatar ki ai da yanzu wani labarin ake yi kuma ba wannan ba"
Cikin jimanta lamarin Innoh ta ce,
"Duba min hanya 'Yannan wai makaho ya so gulma"
Mommy kasa riqe dariyarta ta yi ta d'aga haqoran ta sama dasashi a waje ta dinga keta dariya, cikin dariya ta ce,
"Innoh baki daddara ba ko? Garin yawan karin maganarki ki ke jawa kan ki bala'i wajen aljanun Baaba, kin san dai su ba qabilar Hausa bane ki kiyayi yin karin magana a gaban Baaba"
Karkata kai Innoh ta yi sannan ta ce,
"Koh? Habaa mana,ko da na ji ashe ba Hausawa bane ,haka kawai daga ka yi yaren ka sai abu ya zama masifa ita ta yi nata yaren mana wani ya hana ta? "
"Ba wannan ba ma Innoh,kin san duk fa dan ta ga ɗan ta yana da azziqi ne shi yasa take abinda take so a gidan nan Baba na bin bayan ta,da ace Zaki lallab'a Baba ya bar ni na bi Billy birni da ba k'aramin kuɗi zan samu ba kin ga yanda take wadaqa da nera kuwa? Ni yanzu ma ga wannan dubu biyar ɗin ki qara da naki dan kuwa nima daga yanzu na yi alqawarin duk abinda na samu naku ne ke da Baba da 'yan uwa na"
Cikin washe baki Innoh ta ce,
"Alhamdulillahi haihuwa mai rana,Allah ya yi miki albarka Momiyataaa zuwa aikatau birni kamar an yi an gama ne bari Baban naku ya dawo"
"To ! Toh !! In dawo a yi uwar me kuma? Uwar sababi da baki gajiya? Ina can na tafi nema maki maganin da zai saukar da haushin da muqamuqin ki ya yi ki na nan ki na a bari na dawo,to gani kwad'o na za a yi a ci ko me?"
"Kai dai ba ka cin ribar zance Malam,abun arziki na Kiran ka sai ka dinga ja wa kan ka tsiya,duba nan"
Kud'in hannun ta zata bashi Mommy ta yi saurin katse ta ta hanyar miqa masa sauran dubu biyar ɗin hannun ta ta ce,
"Ah ah ba sai kin bashi naki ba, ga nashi yo ni me zan yi da kuɗi iyayena na da buqatar su? Ai ba abinda zan yi da su ni,yanzu ni a rayuwata bani da burin da ya wuce na samo kuɗi na kashe maku su"
"To ka ji da kunnen ka ko? Yarinya mai tausayi irin wannan ka ke hana wa zuwa aikatau birni,tun daga qofar gidan su Balki za ka san yarinyar nan ta dangwalo arziki,ka wa Allah malam ka bar yarinyar nan ta tafi Itama ko mun samu a dena wulaqanta mu dan za a bamu zakka,ka duba ka ga muqamuqi na yanda ya kumbura saboda kawai na yi hausar da ba a gane me na ce ba"
"Ga aboniki na siyo maki an ce ya na ɗauke zafin ciwon da ya danganci qashi da tsoka, ke Mommy karb'i murza mata wajen ya sauka,dangane da zuwan ki birni aikatau kuma zan sake duba lamarin,dan kuwa yau da na ga suturar da ke jikin ja'irar yarinyar nan sai na ji dama ace Mommy ce ta saka,se wani walwali take ta na sheqi kamar 'yar wani hamshaqin,nan kuwa daga Saida dusa uban ta bai wuce kowa ba,ke ki ma fara haɗa kayan ki zuwa birni ya kama ki, yarinya mai tausayi irin haka za mu tauye a gida?"
Cike da murna Mommy ta ɗauki aboniki ta hau lafta wa Innoh ta na yi ta na qara lasa masu duk wani labarin jin daɗi da za su samu a gaba idan suka barta ta tafi birni,wani uban ihu Innoh ta kurma ta miqe tsaye zumbur kamar wadda cinnaka ko kunama ta ciza,waje ta fita da gudu ta yi hanyar randunan su,ta na zuwa ta buɗe ta yi rashin sa'a babu ruwa har wani bushewa suka yi saboda rashin ruwan da ba a zuba ba taqamar suna da rijiya.
Rijiya ta nufa a guje ta zura guga ta na ihu hawaye na bin kumatun ta,jin fuskar ta take yi kamar ba a jikin ta ba, jiki na rawa ta janyo ruwan ta kwara a fuskar ta sai ta ji wani sanyi mai daɗi na ratsa ta,a hankali zafin ya sake dawo mata sabo dal, Yadiko da su Saddiqa da Ameerah duk sun fito sun yi cirko-cirko saboda rashin sanin abinda ya gigita Innoh,Sule ne ya fito daga d'akin shi ya na hamma ya ce,
"Baba mun shiga uku kar dai Aljana 'yar shanono da ke kan Baaba ce ta sake dawo wa Innoh,"
Baaba wadda zuwan ta kenan ta d'aga siraran hannun ta ta ce,
"Haram, kar ka yi wa bakanuwa Jinin Fulanin kanawa sharri, ita dai ta san Allah ya isan waye ya ciyo ta ta haukace"
Cikin tsananin masifar zafin da Innoh ke ji ta kalli Baaba ta ce,
"Ban ga hauka ba, sai dai ki gan shi a kan ki,wayyooo Allah aboniki zai qona ni"
Ruwa Ameerah ta sake janyowa Innoh Sule kuwa ya zaro tabarya ya ce,
"Ina abonikin yake na sheme ɗan wahala?"
Cike da dariya Mommy ta ce,
"Ba fa mutum bane Yah Sule, man zafi aboniki na murza mata a muqamuqin ta da ya kumbura ka san shi akwai zafi,in banda abun Baba ma ai Robb kaɗai ya isa amma ya kwaso aboniki"
Ɗan liti dai sai zare ido yake yi bai ce komai ba, dan kuwa maganar Mommy gaskiya ce da ya sani da Robb ya shigo mata da shi, yanzu dai aikin gama ya gama sai dai ta yi hakuri Allah ya kiyaye na gaba. Zamewa ya yi ya bar gidan dan kar ma ta yi masa tijarar ta da ta saba.
Yadiko ce ta d'akko wani kyallen yadi mai laushi ta bawa Innoh ta ce ta goge wajen zai rage zafin, ta na sakawa zafin ya haɗe mata ya mata yawa, ga zafin kumburin da kuncin ta ya yi,ga na aboniki,ga kuma na goga tsumma da take yi a wajen, wani nishin wahala ta sauke ta ce,
"Kwad'ayi mabud'in wahala,ina zaman zamana a d'aki daga jin za a bada zakka na tashi na hau rawar jiki,gashi nan na ci kud'in zakka da azaba"
"Innoh magana ki ke yi ne?"
"In ce uwar me to ni ina a wannan halin na tsakanin rayuwa da mutuwa?"
Baya Ameerah ta ja ta bar ta a wajen ta na ci gaba da goge muqamuqin ta tare da zuba ruwa mai sanyi a wajen,a haka Yadiko ta wuce madafin su ta hau sharewa dan kuwa ita ce za ta karb'i girki a ranar, duk halin da Innoh ke ciki bai hana ta zabga tsaki ba tare da hararar Yadiko da bata san ma ta na yi ba.
Bayan wasu awanni fuskar Innoh ta saɓe daga kumburin da ta yi, shatin kaqoran Baaba ma ya baje, sai zazzaɓi da ciwon kai mai zafi ya rufe ta sakamakon kuka da shiga tashin hankali da damuwa da ta yi,ta na nan kwance ta hau tunanin ya zama dole su bar Mommy tafiya birni aikatau ko babu komai duk wata za ta dinga samun 'yan kud'ad'e irin yanda Mahaifiyar Billy da Baaba ke samu, nan take ta ga wautar ta da ta biye wa Ɗan liti suka hana Mommy tafiya birni, a cewar shi ita mace sai ana saka mata ido, an saka mata ido ma ya ta qare ballantana ba a saka mata ba?
A can d'akin Mommy kuwa ta riga da ta gama sanar da Billy amincewar iyayen ta game da tafiyar su tare,nan take suka dinga murna,wani videon da suka yi a gidan mai gari Billy ta yi posting a status d'in ta a qasa ta rubuta (Gidan grandma akwai daɗi amma hutu ya qare, guys ina nan dawowa Abuja nan da wasu kwanaki, na yi missing ɗin ku qawaye na).
Mutanen ta da ta ke zabga wa qaryar ita 'yar sanata ce tuni suka hau yi mata comment, ana yaba wa kyawun da ta yi, wasu har tambayar ta suke yi a wanne gari grandma ɗin ta take ita kuwa ta karkace ta ce a cikin garin Kano take da zama.
Albishir ta yi wa Hajiyan ta da zuwan Mommy, nan take ta tura mata dubu hamsin ta account ɗin ta sannan ta ce ta tabbata ta kawo mata Mommy kar a samu wata matsalar da za a ce an fasa zuwa, nan take ta yi mata alqawarin zata kawo mata Mommy har gida.
Kayan ta ta gama haɗawa a akwati sannan ta wuce tasha ta ciro kud'in da aka tura mata ta yi gida, mahaifan ta ta baiwa dubu biyar biyar sannan ta ware wasu dubu biyar ɗin da niyyar ta baiwa Mommy ta qara wa iyayen ta dan su yarda ana samun kuɗi ta hanyar aikatau.
Da yamma liss ana daf da Kiran magariba ta isa gidan su Billy,a tsakar gida ta tadda Yadiko da ta fito daga wanka Saddiq ya na mata shagwab'ar yunwa yake ji ta yi ta gama girki ta zuba masa miyar da ke ta dahuwa a Saman garwashi a hankali,in dai girki ne Yadiko ta ciri tuta ta wannan fannin fiye da Innoh, dan kuwa in ba alale da dambu ba Innoh bata k'ware a girki ba,hasali ma ita sam bata qaunar yin girki musamman tuwo idan ta tuqa kafin safiya a yi d'umame ya sake, shi yasa lokuta da dama sai dai kowa ya ji da kan shi da safe ranar girkin ta. Billy durqusawa ta yi ta gaishe da Yadiko kamar wata ta Allah, sannan ta ce,
"Ina mutuniya ta kuwa ko ana ciki ana sallah?"
"Ko ana ciki ana latsa waya ba? Ke yanzu da magaribar nan ana ta Kiran sallah aljanu na ta gilmawa shine ki ka fito a haka ki ka zo gidan su ƙawa? Dibi kayan jikin ki fa ki na d'aga hijabin ki na ga babu wata suturar arziki a haka ki ka banka uban hijabi,yanzu ba kya jin tsoron iska ta d'aga ko wani tsautsayi ya faru a ga jikin ki?"
Cikin kosawa da maganganun Yadiko Billy ta ce,
"Wanda ya gani shi ya jiyo, ni ba wa'azi na zo ki yi min ba,ki je can ki yi ta zuba wa 'yar ki wa'azin naki wataqila ya yi mata amfani, gata nan kullum cikin hijabi bamu san me take b'oyewa ba, wa ya sani ma ko ta d'akko na shege a waje?"
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una, Balkisu daga yi maki nasiha Zaki jefi 'ya ta da wannan mugun alkaba'in? To ba ita ba ma ke kan ki da dikkan musulmi ina nema maku tsari da wannan mummunar jarabawa Allah ya baki hakuri qawar ki na d'aki,"
"Tun farko da haka ki ka ce min da baki b'ata mana rai ba da ni da ke"
"Humm duniya ce ta fi bagaruwa iya jima, Allah ya kyauta"
D'akin ta ta shige ta bar Saddiq na kallon Billy kamar ya je ya make ta, ita kuwa d'akin su Mommy ta afka ta na shiga ta gan ta kwance a rufe da zani ta na ta latsar waya,zube wa ta yi a jikin ta ta na d'aka mata duka ta ce,
" 'Yar duniya ana can ana sallah ki na nan ki na kallon harkar duniya,mu ga me ki ke kallo,yanzu na haɗu da wannan kishiyar uwar taku mai shegen kinibibi kamar ta fi kowa tsoron Allah a duniya"
"Hummmm Yadiko ko? Haka take ai duk ta bi ta ishe ni ko ganin ta bana qaunar yi a gidan nan ita da waɗannan shegun yaran nata"
"Humm ai kin kusa tafiya ki basu waje qawata, kin ga ga wannan ki sake qara wa su Innoh gobe da sassafe zamu bar garin nan, ina so mu isa da wuri ido na ganin ido saboda lalacewar hanya"
"Tom Allah ya kaimu, na gode sosai qawata akan irin wannan qoqarin da ki ke yi min a gaskiya banda masoyiya kaff garin nan sama da ke"
Murmushin gefen baki Billy ta yi sannan ta ce,
"Babu komai ai yi wa kai ne"
A haka suka kwanta tare babu sallah babu salati suka ci gaba da kallon fina-finan da aka tura masu na turanci wanda anan ne suke qara gogewa da yaren turanci,sai dai kashh kusan rabin film ɗin bashi da kyan gani,amma su ko a jikin su, suna gani suna qarin bayani akan abinda suke kallo. Billy bata bar gidan ba sai bayan isha'i,ta bar gidan ɗauke da kayan Mommy da ba su fi kala bakwai ba wanda a ciki biyu ne kawai na sallahn ta sauran dika Billyn ce ta bata. Billy kuwa ta tafi da su ne a cewar ta ba za a ɗaukar mata jakar buhu a bi ta Kano da shi ba, za ta je ta yi wa kayan waje a akwatin ta tun da ta rage kaya ta babbayar,godiya sosai Mommy ta yi mata sannan ta koma d'aki ta kwanta.
Da dare Ɗan liti ya siyo wa kowa tsiren ɗari uku-uku har Baaba,hakan da ya yi ya hasala Innoh ta dinga masifa ta na fad'in ai kowa na da kud'in shi me zai sa shi kashe kuɗi a banza? Bai kula ta ba ya ɗauki nasu shi da Yadiko da yaran ta zai tafi wanda kafin hakan sai da Innoh ta qirga shi tsaff tsoka bayan tsoka dan kuwa a cewar ta kar a yi rashin adalci.
D'akin Yadiko ba shi da wadatar kayan d'aki daga gadon ta da sif sai ɗan qaramin madubi shikenan ledar tsakar d'akin ma ta yi yagewar da ta fi rabi amma a haka ta gyare d'akin ta tasss,Saddiqa ce zaune a gaban Mahaifiyar ta ta na jin haddar ta Ɗan liti ya shiga bakin sa ɗauke da sallama, murmushi ya sakarwa Yadiko gaba ɗaya dasorin shi suka bayyana itan ma sai ta sakar masa murmushi sannan ya qarasa shiga ya ajiye leda ɗaya a gaban ta, ya miqa wa Saddiqa nata ya ba wa Saddiq nashi sannan ya ce,
"To maza a tashi a je makwanci a kwanta ko? Sai da safe,"
"To Baba Allah ya tashe mu lafiya"
"Amin"
Yaran na fita Yadiko ta fita Itama ta je rijiya ta kindimi ruwa ta kai wa Ɗan liti na wanka, sabulun ta irin koren nan na wanki ta sa a kwandon wanka duk ta kai masa ta cika buta da ruwa ta ajiye ta koma d'aki.
"Mata ta 'yar aljannah,shi yasa fa idan mutum ya tashi aure malamai suka ce Annabin rahama ya bada shawara da maza su auri mai addini,yau kwana na biyu rabo na da wanka tun wancan zuwan da na yi na tafi da wanka na sai yau zan sake wani, yo ita kan ta uwar garken wato uwar awaki wajen rashin son wanka ba ta yi ba balle mijin ta ya yi,"
"Hummmm malam kenan"
Shine kawai abinda Yadiko ta ce, dan bata son halin shi na son a d'akko zancen Innoh a yi ta zagin ta, dan kuwa yin hakan ba dai-dai bane,Hakan kuma na tabbatar mata da cewa Shima idan ya koma wajen Innoh suna yi da ita. Jin ba za ta ce masa komai bane ya sanya shi tashi ya na fad'in,
"Bari na je na dawo akwai labari, da kuma neman shawara da za ki bani"
"To malam Allah ya sa na baka mai amfani da albarka"
"Ameen"
A haka Ɗan liti ya tafi wanka ya gama ya yi alwala dan kuwa bai yi isha'i ba ya na can wajen me nama aka shiga masallaci ya qi barin abinda yake yi ya tafi sai da aka gama yanka masa sannan ya yi gida.
Bayan ya gama shiri har sun ci abinci ya kishingid'a a gefen gado ya ce,
"Dama shawara nake nema game da yarinyar nan Mommy, kamar yanda ki ka sani ta jima ta na so ta tafi birni na ke hanawa,to shine d'azu ta zo min da jawabai na gansuwa kuma na gamsu na amince ta tafi, uwar ta ma ta amince amma har yanzu na rasa me ya sa na kasa haƙuri na kwantar da hankali na,ke wace shawara ki ke ganin ya dace a bi?"
Gyara zama Yadiko ta yi sosai ta buɗe baki ta ce........... [09/08, 10:37 pm] Aunty Hameeda: *GIDAN ƊAN LITI*
RUBUTAWA: HAMIDA SANUSI AHMAD (HAERMEEBRAEH)