PAGE 8
by @1239900
Tinda saurayin Billy da ta yi ƙarya tace driver ne ya sauya hanya Mommy ke sake ware idanu ta na kallon yanda cikin garin kano yake, ji take yi kan ta kamar yana juya mata saboda ganin cikowar mutane kala-kala,ta ga farare ta ga baqaqe sannan ta ga dogayen mutane da gajeru har da wadanni,wasu ma in ta kalle su sai ta ga kamar ba mutane ba tsabar yanayin halittar su ko dan tsakanin kyawun su ko kuma munin su,ga masu kuɗi nan kaca-kaca a cikin luntsuma-luntsuman motoci, sannan ga talakawa nan suna yawo da qafafun su, sai kuma jama'ar da suke a tsaka tsakiya wasu a adaidaita sahu wasu a motocin su masu sauqin kuɗi, sannan wasu kuma a babura, ta na kallon wani bawan Allah fari tass a babur ɗin shi sai mahaifin ta Ɗan liti ya faɗo mata a rai,tsaki ta ɗan ja dan tunawa da tayi bashi da waya da ta yi,yanzu da yana da waya balle ta kira ta sanar da shi ta iso lafiya, masu tura abubuwan sana'o'in su ta gani suna ta turawa hankali kwance basu ko tsoron motocin dake sharara gudu,ga almajirai nan a saman tituna suna bara jinsin maza da mata yara da manya wasu ma kamar matan aure dan kuwa ga goyon su nan a bayan su,can kuma idon ta ya hango mata masu saida pure water da chocolates da fruits sai ratsa tsakanin motoci suke yi suna talla ko a jikin su.
Ta na nan tana tunani ta ga sojoji a bakin wani gate, cikin ta ne ya bada wata iriyar qara nan take zufa ta karyo mata duk kuwa da sanyin ACn motar da ke bugawa,turanci taji saurayin Billy na yi a cikin abinda ta tsinta ta ji yana fad'in zai d'akko wani ɗan uwan sa ne a ciki,nan dai ya kammala abinda zai yi suka shige ciki, cikin rawar murya ta ce musu,
"Balki ina ne nan kuka kawo ni na ga sojoji da bindiga ni Hadiza kuma wa za ku d'akko?"
Gimtse dariyar ta Billy ta yi ta ce,
"Idan mun shiga zaki gani, ba dai ke kin ce kin ji kin gani ba sai kin zo kano aikatau? To idanun ki zasu sha kallo yau Mommy, and kar ki sake kira na da Balki ki kira ni da Billy idan baza ki iya ba ki ce Billisious"
Nan da nan Mommy ta kwaye facemask ta fara zubo da ruwan hawaye ta ce,
"Billy ki wa Allah ki faɗa min me muka zo yi anan kada wasan da ki ke yi min ya kashe ni dan kuwa ji na nake yi kamar na haɗiyi zuciya na mutu"
"Kin ga shikenan kin hutar da sojoji nuna maki kuskuren biyo ni da ki ka yi"
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una na hyiga uku ni mommy na kawo kaina gidan halaka gidan bala'i da masifa,sai da Yadiko tace kar a barni na zo amma muka dage sai na zo gashi nan yanzu zan mutu a banza ban yi aure ba balle na ga k'wai na"
Saurayin Billy ne cikin dariya ya kalli Mommy ba facemask ya ce,
"Waiii gayauna sunan wani ai dole a dinga saya baki, Baby dan Allah ki bar yi mata irin wannan wasan ki duba ki ga yanda 'yar mutane ta yi jawur kamar an kara ta a rana ko an mulke ta da barkono?"
Dariya sosai Billy ta dinga yi ta juya ta daki Mommy a cinya sannan ta ce,
"Shege na qauye sai tsoron ɗan sanda,duk ina iskancin naki yake Mommy? Dalla share hawayen ki, karb'i nan ki gyara ki shafa powder wajen wata harkar arziqi na kawo mu, kuma nan ba wajen sojoji bane, tun bayan da muka wuce wadancan na gate ɗin kin sake ganin wasu ne? Nan wajen saukar jirgi da tashin shi ne wato airport ,wata yawa nake so na kare a TikTok da IG account ɗina, na ce na je kano wajen grandma d'ina ina so su ganni zan koma Abuja ne ta jirgi kin gane?"
Wata wawuyar ajiyar zuciya Mommy ta sauke sannan ta maida facemask ɗin ta ta goge hancin ta da shi ta yar ta window sannan ta d'akko sabo ta mayar fuskar ta,a hankali jiki ba k'wari ta gyara fuskarta su Billy na ta yi mata tsiya.
Ta na gama gyarawa suka fita Billy ta riqe akwatin ta a hannu,mommy riƙe da ƙaramar jakar sallahn ta,tafe suke suna yanga kamar waɗanda za su yi tafiya da gaske,shi kuma saurayin Billy na biye da su ya na yi masu video, Billy dake ta saba a waye take da irin waɗannan abubuwan sai ta gyara wayar ta ta na yi masu video itama ta yanda mutane za su zaci tabbas da gaske wajen shiga jirgi za su domin komawa Abuja,Billy ce ta karkace baki ta na ta iyayi ta na video a cikin videon nata take cewa,
"Hello guys ya kuke? Ya kewa ta? To alhamdulillahi gani dai da sister na zamu koma gida mun gama shan hutu a kanon dabo, kanawa ina gaishe ku ina godiya da kulawar ku a gare ni sai na sake dawowa,ku dakace ni idan na isa gida lafiya na huta zan buɗe live a TikTok zamu gwangwaje yau yehhhh can't wait to see you my guys...muahhh love you byeee"
Ta na gamawa ta yi editing ta yi duk abinda ya kamata ta yi posting a social network accounts ɗin ta gaba ɗaya sannan suka yi wasu hotunan suka juya zuwa mota.
Billy ba k'aramin tashin kan Mommy ta yi ba da abinda ta aikata ko banza itama ta samu wani sabon ilimin kuma itama zata yaqi nata mutanen da wannan video da hotuna, a haka suka maida akwatinan su suka kama hanya suka tafi, ko da suka koma gate ba wanda ya tambaye su ina wanda suka d'akko ɗin haka suka wuce zuwa gida.
Tafiyar da suka yi bata da nisa sosai suka isa wata unguwa mai bala'in kyau kamar ba a garin kano ba, dan kuwa a ganin Mommy daga wannan unguwar babu wata unguwa da zata fita kyau a garin kanon,gidaje ne tsiraru kamar sababbi tafka-tafka, basu tsaya a ko ina ba sai a ɗaya daga cikin gidajen,a bakin gate motar ta tsaya mai gadi ya leqo ya duba su da kyau sannan ya yi musu sannu da zuwa suka shige cikin gidan da ya gigita tunanin Mommy, idanun ta har wani kwalla suke kawowa saboda farin ciki, bata taɓa tunanin zata shiga irin wannan gidan ba a rayuwar ta.
A wajen ajiye motoci taga sun tsaya saurayin Billy ya ajiye motar a cikin jerin manyan motocin da ta gani a gidan wajen guda uku.
Wani matashi ne sanye da uniform kalar ruwan ƙasa ya zo ya fitar da akwatinan su Mommy ya wuce da su cikin gidan, sannan su Billy suka riqe hannun juna da saurayin ta suka yi wa Mommy alamar ta bisu ciki, mommy kuwa ta saki baki tana kallon gidan da ya tafi da imanin ta,ginin bene ne mai bala'in girma da kyau, tin daga waje ta ke tunanin shin ya cikin zai kasance ne? A matse kuma a qage take cilla qafa ta na sauri dan tsabar matsuwa ta ga cikin gidan.
Babbar qofa mai jan katako da golden ado a jikin ta aka buɗe suka shiga, tsayawa Mommy ta yi cak saboda ganin kyawun wajen, duk yanda za a kwatanta wa mutum ba zai gane ba matsawar ba ciki ya shiga ya gane wa idanun sa ba,mommy ta shagala da kallon qafar benen da zai sada ka da koma wanne irin dukiya da kayan alatu ne a saman gidan ta ji Billy na wani irin nishi,juyawa ta yi ta ganta manne a jikin saurayin nan kamar za su cinye junan su saboda yanda suke sumbatar juna,bata gama dawowa cikin hayyacin ta ba ta ji takun takalmi masu tsini suna sakkowa daga saman benen nan da yake a laulaye kamar zubin maganin sauro, ta na d'aga kai sama idanun ta suka sauka akan wata baiwar Allah mai bala'in kyau da ado ta na sakkowa cikin yanga da natsuwa,qirjin ta Mommy ta kalla sai ta ji ta raina kan ta,duk da yanda mutane ke yaba kyawun halittarta jikin ta sai ta ga matar nan ta doke ta ta shanye dan kuwa jikin ta kamar na turawa ko kuma larabawa haka yake,kai koma wacce qabila ce wannan ba ta qasar mu Nigeria bace sam.
Qamshin jikin matar kaɗai ya isa ya jefa mai shaqa cikin yanayi na natsuwa da samun kwanciyar hankali,wasu riga da wando ne a jikin ta baqaqe rigar daga sama ba abinda ba a gani har bra ɗin da ta sanya ana gani, sai mazaunan ta da suka cika wandon ya yi fam da shi gwanin sha'awa,gashin ta kuwa har gadon baya yake ya na reto, nan take Mommy ta ayyana a ranta,
'Lallai dole a ga dukiya mai tarin yawa da kuma kayan more rayuwa irin haka,ashe gidan mutanen qasar waje ne, Allah ya sa abarni na yi aiki anan gidan ni ko me wanke-wanke aka ɗauke ni an gama min komai ba....'
Wata iriyar muryar da ta kasa tantancewa ce ta yi magana cikin yaren hausa ta yi nasarar katsewa Mommy tunanin da take yi,cikin sauri ta juya tare da zubewa a gaban baiwar Allah'n nan da ta qarasa sakkowa ta zauna a ɗaya daga cikin manyan fararen kujerun nan masu ratsin golden color a jikin su ta ɗora qafa ɗaya kan ɗaya ta kalli su Billy da ganin fitowar ta bai sa sun rabu da juna ba sai ma faɗa wa saman kujera da suka yi su na ci gaba da aikawa junan su saqonni masu sanya mommy jin kunya, dan kuwa duk iskancin ta bata taɓa bari wani ya gan ta a halin biya wa kan ta buqata ba ko kuma a kama su ita da shamsu suna romancing juna,ko mutum ya gan su to fa ba da sanin su bane amma ba wai su da kan su su yi diplaying abinda suke aikatawa ba a bainar nasi kamar na su Billy.
"Wai ku dan uwar ku ba magana nake yi muku ba tun ɗazu? Zan ci mutuncin ku fa dan iskanci mun yi bak'uwa ba za ku tsaya ku yi introducing ɗin ta ba a waje na sai ku kama juna kamar waɗanda suka shekara basu ga juna ba?"
Da kyar su Billy suka rabu da jikin junan su suna maida numfarfashi, cikin sarqewar murya Billy tace,
"Afwan uwar d'aki na,kin san lamarin ne in ka rabu da rijalu na kwana ɗaya sai ka dinga jin ka kamar ka fi shekara baku tare,to yanzu dai na cika alqawari na da na ɗaukar miki gaki ga Mommy mai suna Hadiza a qauyen Ba Mugu, ko dake ko a can qauyen namu ma da Mommy ake kiran ta,Mommy gaki ga uwar d'aki na Hajiya K'waisa danake baki labarin kirki da arziqin ta, wasu mutane kuma suna kiran ta da Hajiya 'Yar k'waisa,amma ni ina kiran ta da Hajiyata dan kuwa da ita nake taqama na ke tink'aho na ke jin nima wata ce a duniyar nan tamu da irin mu ne kawai ke shanawa"
Hannu Hajiya ta d'aga sannan ta ce,
"Ya isa haka Billy introduction ɗin ya yi yawa, ki bari a hankali zata gane komai, kuma za ta san komai, sannan za ta so komai da zata gane wa idanun ta,ai shi gani da ido ya kori ji ko? Ki barta kawai duk wanda ya yi hakuri da kunun maraice zai kai ga tuwon dare ai,yanzu ki kai ta d'akin da ke kusa da naki daga yau nan ne d'akin ta,kar ku manta ku shirya qarfe bakwai ku sakko yin dinner da ni,ni yanzu zan shirya ne na fita zan je wani waje mai mahimmanci ba zan samu yin lunch da ku ba,"
Ba tare da sun baiwa mommy amsar tarin tambayoyin dake cikin kai da zuciyar ba,ko su bata damar cewa alif, Billy da saurayin ta suka kama hannun juna suka fara tafiya zuwa sama, har sun fara taka matakalar benen inda Hajiyar da aka kira da Hajiya K'waisa ta haye sai saurayin Billy ya ce,
"Ke ! ki yi sauri ki zo dalla kar ki b'ata min lokaci ina da wajen zuwa"
Da sauri Mommy ta sa qafa ta bi bayan su zuciyar ta cike da tarin tambayoyi bakin ta kuma ta na jin shi kamar an d'aure mata shi saboda rashin damar magana da ta kasa samun yi.
Da kyar ta iya dafe qarfen jikin matakalar benen ta dinga bin bayan su har suka isa saman da aka lailaye shi da wani abu da mommy ta kira da katako mai k'yalli a ran ta, kamar dai yanda can ƙasan yake haka saman yake, jin kanta ta yi ya na wani irin juya mata kamar za ta yi amai ko kuma ta faɗi, da sauri ta riqe qarfen da ya raba mutum da hantsilowa ƙasa, ta na hango qasa kuwa sai kanta ya fara juyawa fiye da da,nan take ta zube a wajen a sume.................... [09/08, 10:37 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI