PAGE 9
by @1239900
Ganin yanda Mommy ta faɗi warwas a qasa ta suma ne ya sanya Hajiya 'Yar K'waisa data kama knob ɗin qofar ta zata shiga d'akin ta tsayawa ta yarfa hannu ɗaya tare da kama hab'a tace,
"Toooh ! Wata sabuwa kaza taji shiqar dare,me zan gani haka ni K'waisan alheri? Ke tada ta maza mu gani, Allah ya sa dai ba jinginanniyar gawa kuka kawo min muhallina ba,"
Da sauri Billy ta wuce dispenser dake a parlourn ta tsiyayo ruwa mai shegen sanyi ta sheqawa mommy, a gigice mommy ta farke facemask daga bakin ta bayan ta farka ta wage bakin tun qarfin ta ta kurma uban ihu,ganin bakin ta ne ya sanya Hajiya K'waisa buga nata ihun tare da faɗin,
"Na shiga uku ni K'waisa me nake gani haka a fuskar yarinyar nan bakin ta kamar an watsa qashi a bola? Ina zan kai wannan ragadadar leb'unan nata? Billy biyo ni, kai kuma kama gaban ka ka dawo watarana ba zan ɗauki iskancin nan naku ba da ranar Allah ba na cikin yanayi na kallon fitsara,"
Jiki ba k'wari Man ya yi wa Billy mata sallama tare da alqawarin zai dawo da dare, d'akin da Hajiyarta ta ta shige itama ta shiga,Mommy kuwa na nan ta na rarrafe ta bar gaban benen har wannan lokacin jiri take ji ga wani amai da yake taso mata, da ta tuna cewa yanzu fa a sama take ba a qasa ba sai ta ji hankalin ta ya sake tashi ta kurma ihu kamar me shigar iska.
A can cikin d'akin Hajiya K'waisa da ya gaji da haɗuwa kuwa Billy ce tsaye ta na tura baki Hajiya dake tsaye ta na sauya kaya a gaban Billy tace,
"Ke Billy wannan wace iriyar halitta ce haka? Ya zaki kawo min matsala a cikin gida haka muka yi dake?"
Murmushi Billy ta yi ta ce,
"Haba Hajiya ai wannan ba wata matsala bace,bakin ne fa kawai sannan tsorata ta yi fa da ta natsu zaki ga ba wani girma ne dashi ba na azo a gani, kuma ko ba komai ai tana da kyan ta da bata da kyan ma ai ba zaki nace a kawo maki ita ba,sannan baki ga yanda take sake da facemask bane koda yaushe? Bayan haka ma yanzu fa irin su ake so ko kin manta ne? Ai wannan babbar kadara ce ki yi tunani da kyau ki gani"
Shiru Hajiya K'waisa ta yi kafin daga baya ta saki wani shu'umin murmushi ta ce,
"Kuma fa haka ne Billy ni nakan manta da cewa wata arhar ma tsada ce,ba komai na san yanda zan gyara baqar tukunyata ta fidda min farin tuwo,kama ta dan Allah kar ta mace min saboda tsoro ku garin ku ba ko dan irin benen nan ne na gidan me gari ko me unguwa ake cewa whatever? Allah dai ya wadaran naka ya lalace Jakin dawa ya ga na gida,wannan idan zuwa taro Abuja ya tashi sai dai a tura ta ta mota dan ba zan jera da ita ba ta kore min customers, maza maza jeki ni,"
Hajiya K'waisa ta qarasa maganar ta tana yarfa hannu tare da nuna wa Billy hanyar waje,cikin dariya Billy ta kama hanyar fita daga baya ta hau mita ta na faɗin,
"Yanzu da ki ka kore min Man d'ina ya kike so na yi fisabillahi"
"Ki kunna live a gidan ki na TikTok da ranar nan ba zaki rasa 'yan balaja'u ba irin ki sai ku yi wa juna abinda kuka saba har ku gamsu, ni jeki ina da appointment ne da likita."
"Ok to sai kin dawo,Allah yasa dai wannan karon a dace,"
"Ameeen kedai"
Billy na fita direct wajen Mommy ta nufa ta kama ta ta yi wani d'aki da ita wanda ya ke ɗauke da makeken gado, d'aki ne mai kyau sosai sai dai be kai na Hajiya K'waisa kyau da tsaruwa ba, a hankali wannan kyan d'akin ya fara ɗauke hankalin Mommy daga tunanin inda take, bayan wasu mintunan sai ga Mommy ta ware ana ta ganin d'aki da ita, babban abinda ya fi burge ta bai wuce band'aki da ta gani a cikin d'aki ba irin wanda take gani a waya,ga bathtub mai shegen kyau ga kayan wanka kala-kala, murna ce ta kama ta ta shiga bayin Billy na nuna mata komai na ciki da yanda ake amfani da shi, wajen heather ta kaita, ta dage sosai tana nuna mata yanda ake amfani da ita saboda kar ta je ta babbake kan ta da ruwan zafi, Mommy kuwa ta natsu sosai dan jin yanda ake amfani da komai cikin sauqi ta haddace komai saboda dama tana gani a waya, ko benen ma tana ganin shi a waya kalar wannan murd'ad'd'en ne bata taɓa gani ba, sannan kuma bata taɓa hawa ba shi yasa da ta ji ta a saman ta hango qasa da nisa ta fara jin jiri har hakan ta kai ta ga suma,a haka suka gama ganin d'akin ta kuma tabbatar wa da Billy ta gane komai da yanda ake amfani da komai sannan ta wuce ta bar Mommy na zuba qauyanci.
Billy d'akin ta ta shige ta yi wanka ta fito daga band'akin haihuwar uwar ta ta ɗauki laptop ɗinta ta kunna sannan ta shiga social Media, har na zauna na d'akko maku rahoton dalilin da yasa ta zauna babu kaya na ga abinda take aikatawa ya yi munin da hannu na ba zai iya rubutawa ba, saboda ban taɓa tsammani ko tunanin akwai 'ya'yan musulmin da ke aikata irin wannan lalatar ba, da sauri na ja mata qofar na koma d'akin mommy.
Kwance na ganta a gado tana mulmula daga wannan wajen ta koma wancan, can sai ta miqe da gudu ta d'akko jakar ta ta zaro wayar ta da ta sha faci da salatef ta kunna, No Sule ta lalubo ta kira, ta jima tana ringing kafin daga baya ya ɗauka, yanayin yanda yake magana kaɗai ya isa ya sanar da ita a halin da yake ciki dan kuwa ita ba baquwar shiga irin wannan yanayin bace, kuma ta san me yayan nata yake aikatawa a duk sanda ya rufe qofar d'akin sa da ranar Allah yace zai yi barci kar a dame shi.
Cikin jin wani irin shauqi da kewar shamsu tace,
"Sule dan Allah idan ka gama abinda ka ke yi ka kai wa su Innoh waya mu gaisa na faɗa masu na iso lafiya, Sule ka ga gidan da aka kawo ni kuwa? Innalillahi sule wannan shi ake kira da aljannar duniya, wayyoo Allah ka ji laushin gadon da nake kwance akai kuwa? Ka ga kyan makewayin su kuwa? Makewayin mugun zabgege sukutum da guda aka ce nawa ne ni kaɗai,sannan d'akin ma duk girman shi da tsaruwar shi wai nawa ne ni kaɗai"
Tun Sule na jin ya matsu ta kashe waya ya ci gaba da abinda yake yi sai ya ji kwad'ayin son ganin wajen dan ya kwad'aitu da son zuwa kanon nan shima dai, dan kuwa duk 'Yammatan da yake faman biya wa buqatar sha'awar su ta waya suna ce masa a kano suke wasu a wasu sassan jahohin arewa suke kaɗan ne a kudu,Sule ya yi qaurin sunanda da ace mutanen da yake mu'amala da shi za su san asalin ko shi wanene tabbas da babu mai sake kula shi a cikin su,da muryar shi mai shegen daɗi yake yaudarar matan da suka kwashe kayan su daga gaban ma'aikin Allah suka kai gaban shaid'an suke kwasar ilimin yanda za a saɓa wa Allah.
Sunan da Sule ke amfani da shi a social media ma kan shi abun kyama ne ga dikkan mutum mai hankali, dan kuwa baya ma b'oye abinda yake aikatawa a social media. Da damar matan da ke tura masa kuɗi da data ta waya da account ɗin shi sun matsu su yi tozali da gwarzon kyakkyawan namijin da muryar shi ke ɗebe masu kewa amma sule ya yi fafur ya ki yarda kowa ya gan shi. Hasali ma hoton wani matashin buzu ya sanya a profile picture ɗin shi na kowanne kafa ta sada zumunta da yake amfani da shi, dan haka da damar matan nan sun amince wa kan su sule fa kyakkyawan saurayi ne mai kuma murya mai daɗi.Duk wadda Sule ya yarda ya nunawa kanshi to fa shaƙuwar su ta kai shaƙuwa ne ya sanya shi bayyana mata asalin fuskar shi.
Sun jima sosai Mommy ta na bashi labarin yanayin gidan da aka sauke ta kafin daga baya su yi sallama ya kuma yi mata alqawarin idan Baban su ya dawo zai haɗa ta da shi da mutanen gidan ta waya su gaisa,kafin nan zai sanar da Innoh sun isa lafiya, godiya ta yi masa suka yi sallama ta kashe wayar.
Band'aki ta shiga ta tara ruwa a kwamin wanka ta zuba kayan wanka kamar yanda Billy ta sanar da ita ta shiga ta kwanta yanda taga turawa na yi a cikin ruwa idan sun shiga haka itama ta yi.
Ta jima zaune ciki tana dirzar jikin ta kafin daga baya ta fita saboda k'wank'wasawa qofar da ta ji ana yi,towel ta d'aura a jikin ta sannan ta fita kan nan ya sha wanki sai d'igar ruwa yake yi ya cunkushe waje ɗaya,fatar ta sai ta qara wani sheqi da kyau da santsi tare da ɗaukan idanu.
Tana fita taga wata matashiya ɗauke da babban faranti abinci da fruits da ruwa sai lemon kwali da sauri ta nufe ta zata Karb'a matashiyar ta haɗe fuska tace,
"Umarnin inda za a ajiye kawai zaki bani"
Jikin Mommy ne ya yi sanyi ganin irin kallon da matashiyar ke yi mata, kallo ne irin na kyankyami da raini ɗin nan, shanye wa ta yi ta nuna mata gefen gado inda wani ɗan qaramin table yake tace,
"Ajiye min a can"
"Ok"
Shine kawai abinda matashiyar ta ce ta wuce ta ajiye sannan ta fita tare da banko qofar d'akin saida Mommy ta kulle idanun ta.
Yarinyar na komawa kitchen ta jingina da jikin locker ɗin kitchen carbinet,abokan aikin ta dake cikin kitchen ɗin kuwa mace ɗaya namiji ɗaya suna nan tsaye suna ci gaba da aikace-aikacen su, tsayuwar ta ke da wuya gaba ɗayan su sai suka yo kan ta suna tambayarta,
"Ke bamu mu sha,ita kuma wannan wacece?"
"Hummm ni fa ina mamakin irin waɗannan mutanen, wai ace ko kunya basu ji suke baro gaban iyayen su su zo su dinga yin abin duk da wannan...."
"Keee Zubaida kama bakin ki,kar ki je ki yi shuka a idon makwarwa,mu dai ba dai ana biyan mu kud'in dake kashe mana buqatun mu ba? To mu kama kammu Allah ya shirye su, mu kuma ya kare mana imanin mu"
"Humm Ameen Sallau kai ma dai ka faɗa, Allah ya kyauta"
"Amma ai ba dai-dai bane mu dinga aiki a qarqashin waɗanda mun san daga inda kud'in su ke fitowa ko?"
"Ruby? Tsaya sauraren wa'azin muzuru ni dai kin ga na yi nan,ke in banda abinki ina ruwan ki da hanyar samun su? Ke dai ba hanyar taki samun bace damuwar ki? Kin tabbata ba wani mugun abun kike aikata wa ba ki ke samun kud'in ki to ke ina ruwan ki da inda suke samun nasu? Kin ga karb'i nan wanke min wannan na fara ɗora na dare,"
Aikace-aikacen su suka ci gaba da yi suna 'yan hirarrakin su sama-sama.
A can d'aki kuwa Zubaida na fita Mommy ta dira a saman abincin nan ta hau saɓa masa kamanni,ganin nama kaca-kaca a saman abinci ga kuma farfesun kayan ciki da juice kalar wanda bata taɓa gani ba ya gigita tunanin ta,ko ta kan shinkafar bata bi ba dan kuwa naman kaɗai ya wadatar da ita, sai da ta ci ta qoshi sannan ta kora da ruwan roba ta miqe tana sakin wata muguwar gyasa.
Billy ce ta shiga d'akin cikin wata iriyar shigar da sai a irin Nigerian films din nan na 'yan iska Mommy ke ganin mata sun yi ta, ga wani uban gashin doki da ta saka a kan ta sai mutum ya rantse da Allah a kanta ya tsiro dan ba ta inda ya nuna sanya shi aka yi.
Zara zaran faratan hannun ta irin na hannun Hajiya K'waisa ne suka fi bawa Mommy sha'awa dan kuwa an yi masu fenti me kyau an saka masu stones masu kyalli a jiki, tafe take ta na cin chewing gum ta na yatsina ta shiga d'akin riqe da wata jaka a hannun ta ta miqa wa Mommy ta ce,
"Sanya wannan mu je saloon ki na buqatar gyara kafin muzo dinner da Hajiya anjima, dan ganin kan ki kaɗai zai iya haifar mata da tashin zuciya ta qi cin abincin"
Washe baki Mommy ta yi tace,
"Laaa ai na ma wanke kan, na shiga kwamin wankan nan na haɗa ruwa kamar yanda ki ka faɗa min na yi,"
"Uhumm na gani amma ai baki fita ba dan ko brush baki yi ba, yanzu dai jeki ki saka wannan mu tafi lokaci na qure wa"
A gaban Billy Mommy ta cire towel ɗin ta ta hau sanya kayan da aka bata, hakan da ta yi kuwa ba qaramar fitina ya kunna wa Billy ba da ta jima ta na fakon ta tinda ba tun yau ba suka saba cire kaya a gaban junan su, a cewar su ai duk mata ne meye a ciki? Abinda Billy ke da shi Mommy na da shi dan haka ba wani abu bane dan sun ga junan su tsirara,danne abinda take ji game da mommyn ta yi ta ayyana a ranta,
'Idan kere na yawo zabo na yawo watarana za su haɗu ne, Allah dai ya kai damo ga harawa...'
"Ina ta magana baki jini ba, nace na gama mayafi zan saka ko hijabi?"
"Mommy wai me yasa ki ke abu ne kamar wata ba wayayyiya ba? Ke nan fa ko yawo kika so yi tsirara ba me hana ki,taho mu wuce ko baki ga meye a jiki na ba?"
(Hummm yarinya ta gwada yawo a kano tsirara ta ga ikon Allah...ba sai na yi dogon sharhi ba)
Da waɗannan kayan Billy da Mommy suka shirya suka ja qofar d'akin za su fita, takalmin da mommy ta saka mai tsini ne,saboda rashin sabo sai ya dinga gurd'e mata qafa, suna fita daga d'akin kuwa hankalin ta ya yi bala'in tashi saboda tunawa da ta yi dole ta benen nan za su sake bi su sauka qasa............
*A zo a kama mommyn gaye a saukar ta qarrr* [09/08, 10:37 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI