A GARIN MU

PAGE 1

by @1239900

Jihar Zamfara, jiha ce mai tarin albarka, jiha ce mai cike da arziƙi noma, ma'adanai, da kiwo, Allah ya azurta Zamfara da mutanen kirki tun kafuwar ta, ya sanya ta zama ƙasa mai tarin albarka, da ruƙo da addinin musulunci, jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin Nigeria da suka yi tashe a tsaida shari'ar Musulunci shekaru masu yawa da suka gabata.

An san mutanen jihar Zamfara da son zaman lafiya, gaskiya, amana, juriya, jarumta,ilimi, kasuwanci, sana'o'i, sarauta, da dik wani abu na jin dadin rayuwa.

Zamfara gari ne na zaman lafiya a baya, gari ne da aka yanke shi daga jihar Sokoto,a zamanin General Sani Abacha, a 1st October 1996, shine shugaban qasar da ya ba ta 'yancinta, ta zama jaha kamar sauran jahohi a qasar nan ta Nigeria.

Jihar Zamfara ta tara sarakuna, da shuwagabannin gwamnati masu adalci a baya, ta yanda qasar ta zamanto a koda yaushe cikin aminci take, kowanne dan jahar kuma kowanne yare, da addini ya ke zaune cikin kwanciyar hankali, ba fargaba, ba tashin hankali ballantana tsoro. Wannan ita ce jihar Zamfara a shekarun da suka gabata.

Garin Gusau shi ne babban birnin jihar zamfara, gari ne da ya qunshi al'umma kala-kala, mabanbanta, yaruka daban-daban, da addinai mabambanta.

Gwamna Halliru Murtala Gusau shi ne Gwamna mai ci na yanzu a jihar Zamfara,ya na zaune da iyalan shi a unguwar GRA, lokaci zuwa lokaci kuma sukan yi wa gidan gwamnati tsinke su yi wasu ƴan kwanaki ko kuma su je Abuja domin su huta. Gwamna Halliru ba shi da abin so a duniya sama da iyalin shi, dan haka komai ya ke yi a duniyar siyasa domin su ne, Hajiya Ikilima wadda aka fi kira da Hajiya Ikee, ita ce matar shi tilo, sai yaran su biyu Sultan me shakara Ashirin da tara, da Sultana Mai shekara Ashirin da biyar,dikkan su sun yi karatu ne a University of Westminster London, in da Sultan na da BSc a Architectural Technology, Sultana Kuma na da BA a Arabic and linguistics.

Dikkanin su sun samu gata kalar wanda in da za a hada su da sauran yaran gwamnonin Nigeria, zai yi wahala a samu ya su, kama daga dukiya,da tsaro, saboda tsaron da suke samu in Sun samu amincewar iyayen su har su ka fita, to sai mutum ya rantse Gwamna ne da kan shi ke yawo, motocin sojoji da 'yan sanda ne kawai mutum zai hango su na biye da su dik inda suka dosa.

Yau kusan sati biyu kenan, Sultana na roqar mahaifiyar ta da su bata dama ta fara aiki itama, dan kasar ta ta mori ilimin da Allah ya hore mata sai dai kamar kullum roƙonta ya tafi a iska kamar an sheƙe hatsi. Kamar koda yaushe yau ma Hajiya Ikee shiru ta yi wa Sultana dake ta magiya ta ci gaba da ɗaukan inibinta ta na jefawa a baki, hankali kwance, qafar ta kuwa mai aikin su ce Me Buruji ke matsa mata, kan ta a qasa, saboda tsoron had'a ido da uwar gidan nata.

Cikin tausaya wa Sultana ta ce,

"Baaba je ki kitchen za mu yi magana da Hajiya"

"To ran ki shi daɗe"

Mai Buruji ta faɗa tare da miƙewa tsaye a duƙe kamar wadda take a fadar matar sarki. Da sauri Hajiya Ikee ta kalli Sultana ta ce,

"Na hwa san mi kike yi Sultana ,wato Ina Sanya Me Buruji wahala ko? Shi na kin ka kore ta, tau ki kiyaye ni, kar ki koma yi min haka nan ban so, and da ki ke damu na akan ki hwara aiki,Ni misshamin kai da aikin ki? Daddyn ku ya ce ba za ku yi aiki ba, kuma na goyi da bayan shi, % saboda ku ba diyan talaka kuke ba, albashin ga dai in shi kika so ana baki duk wata, dangi ma aka basu albashi ba tare da sun tai aikin komi ba balle ke? Dan haka daga yau kada ke ko ɗan'uwanki ku sake tunkara ta da wanga batu, kin ishen da d'umin banza, haba! "

Cikin fushi Hajiya Ikee ta tashi za ta bar tafkeke kuma ƙayataccen parlourn na su, wanda tsayawa ma fadin had'uwar shi, bata lokacin mai karatu ne.

Da sauri Sultana ta rungume Mahaifiyarta ta baya, tare da dora kan ta a saman bayanta, cikin kalamai masu taushi Sultana ta ce.

"Mum Dan Allah ki yi hakuri indai ni ta ba zan koma yin magana akan aikin gwamnati ba a gidan nan, zan yi hakurai, don Allah ki dena hushi da ni."

Juyawa Hajiya Ikee ta yi ta na dan Murmushi, sannan ta koma ta zauna a kujerar da ta tashi ta ce,

"Ni fa mamaki kuke ban diyan ga, ku na abu saikace ba kuyi karatu a qasar waje ba, kamar wadan da sun ka yi cudanya da talakawa, Allah ya daukaka ku, amma kullum burin ku bai wuce ku ga kun wulaqanta kanku ba,"

Murmushin takaici Sultana ta yi, dan ta san in tai magana, yanzu ran mahaifiyar ta zai qara ɓaci,sai kawai ta ja bakinta ta yi shiru tana ci gaba da bawa mahaifiyarta haƙuri. Halayyar su Sultana da iyayensu akwai banbanci mai tarin yawa, shi yasa ko a dangi ake mamakin yanayin tarbiyyar da suke da ita wadda ta sha bamban da ta iyayen su. Su kuwa su Sultana da Sultan ba su ga abun mamaki ba, domin su kaɗai suka san yanda aka yi suka samu tarbiyyar mai kyau. Bayan haka duk wani musulmi ya kwana ya kuma tashi da sanin Ubangiji Allah ya na yin yadda ya so, a sanda ya so ba tare da neman izinin kowa ba, sun sani da izinin shi, da ikon shi ne suka zamo yara na gari,har tarbiyyar da suke da ita ta sha banban da halayyar iyayen su.

A lokacin da aka kai su Sultana makaranta a qasar waje bayan sun kammala primary a nan Nigeria a garin Abuja,wadda makaranta ce mai haɗe da islamiyya. Yara na samun ilimi na mai tarin yawa,kama daga kan duk abinda ya shafi boko da islamiyyar, shi yasa su Sultana suka samu nasarar haddace qur'ani tun su na Nigeria, wanda iyayen nasu basu wani damu da hakan ba sannan basu ɗauke shi a wata nasarar da za su tallata ko su kambama ba, fatansu a kullum bai wuce na yaran nasu su samu kyakkyawan result da zai kai su babbar makarantar gaba da primary dake a qasar turai. Da taimakon malamansu da jajircewar su su Sultana suka samu kyakkyawan sakamakon tafiya karatu ƙasar waje. Babu ɓata lokaci Gwamna ya kai su makarantar gaba da Sakandire a London, wannan shine dalilin da ya sa ba su samu damar ci gaba da karatun Islama ba, sai bayan da suka shiga jami'a lokacin hankali ya shige su, Sultan ya ga haddar su na zubewa, shi ne ya sama masu wani malami Bature Musulmi masanin addini sosai, ya ke koyar da su addinin su, ba tare da mahaifansu sun suni ba, a lokacin da suka kai musu ziyara suka ga abinda yaran ke yi,basu wani damu ba sai ma tambayar su karatun su na boko da ya kai su ƙasar da suka hau yi, domin yana daga cikin babban burin iyayen nasu su ga yaransu sun zamo masu ilimin boko ta yanda daraja da qima tare da ajin su zai ɗagu a cikin takwarorin siyasarsu.

Akan dole Sultana ta ci gaba da hira da Hajiya Ikee ba dan ta so ba. Sai ta danne burin ta na koyarwa a makarantar jami'a ta ci gaba da amsa Hajiyan sama-sama kamar bata so.

**********************

A ɓangaren Me Buruji kuwa,tana komawa bangaren masu aiki sai ta ja hannun kishiyar ta me suna Lamishi, suka koma gefe,nan ta labarta mata me ya faru a ciki tsakanin Sultana da Hajiya,da kuma yanda Sultana ta kuɓutar da ita daga bautawa Hajiyan ta hanyar yi mata tausa. kama baki Lamishi ta yi tana jinjina kai kafin ta ce,

"Ohhh ni Lamishi ina tausayawa yaran nan,domin ba su samu iyayen ƙwarai ba wallah,abun na bani mamaki kamar ba su ne suka haife su ba, Allah ya kyauta, mu je ki ƙarasa aikin ki, da ki ka tafi ki ka bari, walle ban qarasa maki,nima nawa ya isan"

"Lamishi hoo, yanzu dan goge kici (kitchen) ɗin ne ba za ki iya ƙarasa min ba?"

"Ke walle ban iyawa, tafi kawai ki ƙarasa ki na gamawa mu tafi gida,kin fi kowa sanin wancan dan mutuwar zuciyan da yaran shi na can na jiran mu samo mu kai musu su lasa, bada aniya ki yi ki gama."

Babu bata lokaci kuwa Me Buruji ta kammala aikin ta, suka yi wa sauran ma'aikatan sallama, dauke da ledojin da suka cika da abincin da aka ci aka rage,masu aiki kuma sai su tattara su raba a tsakaninsu. Sai da suka tsaya a gate aka duba kayan su sannan suka fita. Dan sahu suka tsayar suka dauki hanyar unguwar su da ke a TUDUN FAILA.

A qofar gida suka tadda mijin nasu zaune da abokan shi suna manne da jikin gini, sanye yake da wasu jemammun tufafi,yana hango su ya washe baki,tare da ɗagowa daga jikin katangar ya na lashe busassun labban shi. Lamishi ce ta saki guntun tsaki ta ce,

"Kalli mijinki mai matacciyar zuciya sai wani lashe baki yake yi kamar wani baƙin maye, ga shegun abokansa sun bi sun wani maƙale a jikin gini kamar dangin ƙadangaru...kaiii Allah ya wadaran wannan mutuwar zuciya irin ta su Ɗantalo"

"Ameen ke dai"

Mai Buruji ta amsa tana harar mazan dake zaune a ƙofar gidansu. Ko gaishe da abokan mijin nasu ba su yi ba suka fada gidan, su na jin su na gaishe su, tare da yi masu sanu da dawowa amma ko kallo ba su ishe su ba, ɓata rai DanTalo ya yi, ya tattare qasan rigarsa ya afka cikin gidan nasu ya na fadin.

"Ina zuwa na samu wadan can lalatatun, ba dan na amince musu zuwa aikin ba ai ko titin gidan Gwauna ba su isa wucewa ta wajen ba, shine dan tsabar raini abokaina na gaishe ku zaku yi kunnen uwar shegu ku shige gida ko? To ba wata sheeee....."

Maganar shi ce ta maqale a maƙoshinsa sakamakon yin arba da ya yi da wata sharbebiyar kaza tana maiqo Lamishi ta raba ta biyu ta ajiye a farantin silver. Kallon shi suka yi a tare cikin daure fuska, Lamishi ta ce,

"Ba wata sheee me?"

Cikin inda inda Dan Talo ya ce,

"Ba wata 'yar shimi na sauya? Zahi ni ka ji yau"

"Ahayyyeeeeee, ayyuuuriiiriiiii, Dan Talo amanar Lamishi da Me Buruji "

Tafawa suka yi, shi kuma ya hau yaƙe, dan ya san sun fahimci kwana ya sha.......

Ku dakace Ni a shafi na gaba, dan jin yanda zata kaya...

Comment Vote Share. [26/03, 9:12 pm] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: A GARINMU

WRITTEN BY HAERMEEBRAEH